Showing 3001 words to 6000 words out of 18680 words

Chapter 2 - UWAR GAFALALLU book 1 By Oum Yasmeen .txt

07 Jan 2025

2094

tayi ta fito tana cewa wallahi momcy idan har ba zaki gyara halinki ba mu tare da dana sani


kai ka kai turƙashi mufeeda ashe bayan tafiya ta niger rashin kunyar ki ta kara gaba to yanzu ni ko mahaifiyar ki , kike faɗawa haka...,


baba lami ta faɗa tana kama haɓa


baba gaskiya ce dole a faɗa wallahi bana jin dadin rayuwar nan da muke Please mu canza mu koma irin ko wanne gida mana jin sallamar mahaifinta ta ɗago amsawa tayi ai kafin kace me kowa ya tashi ya fita ƙarasa shigowa yayi cikin sanyin murya kamar ko da yaushe tace baba sannu da dawowa


yauwa yar kirki Allah yayi miki albarka


sauran kuma Allah ya kwashe musu wallahi idirisa ka dena raba kan ya'yan ka


girgiza kai yayi a ko wacce rana yakan yi dana sani mara adadi na zaɓowa ya'yansa uwa bata gari ba shima rashin dacen uwa bata gari ba shi ya jefa shi halin da ya shiga a baya kallon mahaifiyar sa yayi yace


''baba kin dawo lafiya..,
kallon ledar hannunsa take yi tana sakace hakoranta tace


''lafiya qalou me ka shigo da shi ne...,


tabbas hausawa sunce me hali baya fasa halinsa ƙasa yayi da kansa yace


'' taliya ce na samo dakyar bayan nayi faskare a gonar Alhaji mansur gwarzo shi ya saka kuka ga ban dawo da wuri ba ga manja nan ku dafa kowa yaci...,


baba wazai ci wannan abar saidai ban ƙi ba kai da mufeeda kwaci


jalila ta faɗa tana gyara zaman riga a jikinta duk tabi ta dameta...


banza yayi mata yana yi mata fatan shiriya ko sau daya be Allah wadai da halin ya'yansa ba ko yayi mu su baki addu'a ce yana tafi ko yana zaune yi musu yake ungo lami baya yaran nan su dafa mana


Wani kallon hadarin kaji tayi masa sannan ta ɗauke kanta mikawa mufeeda yayi ta amsa tana godiya ƙara cewa yayi Allah yayi miki albarka ya kai ki inda zaki huta


a zuciya ya amsa da amin murhunsu ta nufa tana kokarin saka icce da sauri asabe ta kwace tace


''wallahi baku isa ba tab ni zaku dura da ka...,


Momcy girki zanyi fa


dawanau zaki dafa


dan ubanki shi da ya baki ai sai ya kawo miki iccen da zaki kona


mufeeda ajiye jike ki waje akwai ledoji ki zo ki dafa mana wallahi bani da kuɗin icce


kai ta gyaɗa mai ta fita ta jima kafin ta dawo ajiye wa tayi ta soma haɗa huta kuttumar uba nan kusa da kajina kike wannan aiki salon ki babbaka min su




shiru tayi jikinta duk yayi sanyi bayadda ta iya da mahaifiyar ta amma sam halinta ba me kyau bane matsa gefe tayi da kyar taliyar ta dawo saboda rashin makamashi


Bayan ta gama ta soya manja tace




'' momcy a zobo muku...,


girgiza kai tayi tana cewa Allah ya sawwaƙe ni dacin fara damai ko magi babu yawa a gidan jero (prison)


Baba lami na zobo miki
aa barshi kina jin abin da asabe ta faɗa ita da take da sauran kwarinta balle ni a'a kuci kayar ku


daga haka ba wanda ta ƙara yiwa tayi zobo musu tayi wadali ishi suka ci har da ragowa tashi sumy tayi tana zuba wata uwar miƙa da hamma zuwa yanzu ta dawo dai-dai amma ba sosai ba tashi tayi ta shiga toilet wanka tayi a lokacin ana kiraye kirayen la'asar aunty sumy baki ji ana kiran salla ba zaki koma


makka naji ana kira ta faɗa tana zabga mata uwar harara shiga daki tayi


ci gaba da alwalarta tayi bayan ta idar ta tashi ta shiga daki shinfiɗa daduma tayi ta ɗauki hijabin da ya rage musu ta saka ta tada sallah




TUDUN YOLA


cikin sauri yake toki babban burinsa ya isa gida so yake ya ga gaskiya saboda gudun da yake zabgawa ai kuwa ya isa a yan mintoci ƙalilan tun daga nan babbar ma'aikatar wutar lantarki horn yayi me gadi ya buɗe mai parking yayi ya fito cikin sauri stairs case bibbiyu yake haɗawa na barandar inda zata sada shi da main parlour


Cikin sauri yake komai Hajiya ya tarar tana zagaye yawa me ɗawafi tana ganinsa tace


'' doctor ya zo yanzu haka yana ciki asharaf anya kuwa ba ƙasar waje zamu ƙara fita ba ko zasu gano abin da ke damun inteesar...,


ƙasa yayi da idanuwansa duk irin dauriya tasa nema yake ya zubar da kwalla a hankali ya buɗa baƙin sa yace


'' Hajiya kawai mu haƙura mu barwa Allah sau biyar ana fita da ita ba canji kullum abin kara gaba yake wancan satin likita ce min yayi a ƙara taka tsantsan da ita saboda lakarta tana gab da ƙarasa zubewa...,


yanzun nan nake ce mata na fito da ita ta sha iska kai ta gyaɗa min shine na dorata a kan wheelchair na fito da ita wallahi bansan yadda akai ta zabe ba wai photo ka zata gani


runtsai idanuwansa yayi yana roƙon Allah ya bashi ikon cinye jarabawar nan yana cikin mahuyacin hali ya rasa matar sa sakamakon haɗari
inteesar ce ka dai ta rage masa sai yayyunsa biyun da kanin sa junaid


duk wanda ya kalli haɗarin sai ya shiga roɗani motar lotsaiwa tayi jini sai mulala yake ba wanda yayi zaton za a samu mutum ɗaya ya tsira a cikin motar sai gashi inteesar ta tsira lokacin da motar take murginowa nusaiba ta cillota banda kujewa da tayi ba abin da ya sameta sai daga baya an kaita asibiti aka ga lakarta ta sami matsala haɗa gawar ta aka kai ta gidan gaskiya ba irin kuɗin da inteesar bata lashe ba amma ji kake shiru ba wani ci gaba maganar ta ma ba fita take sosai ba...


Fitowar likita ita ta katsai mai tunanin sa da sauri ya karasa gurin doctor Imam yace


'' doctor me yake damunta..?,


calm down ansh komai ya zo da sauki yanzu haka ma tana bacci nayi mata allura kamar yadda na faɗa maka zan kara maimaita maka inteesar tana buƙatar me kulawa da ita har tayi bacci Ummina take faɗi dole idan muna so tunaninta ya dawo normal irin nada




UWAR GAFALALLU


OUMYASMEEN




3-5




sai an nemo wacce zata zame mata copy din mahaifiyar ta cemin tayi zan nemo mata umminta nace mata eh yarinyar abar tausayi ce kamar ta ta haɗu da wannan lalurar


gumine ya wanke mai fuska handkerchief ya zaro a aljihunsa ya goge zufar dake tsassafomasa yace


'' insha Allahu zan yi maganin matsalar...,


wani kallo Hajiya tayi mai ta maida hankalin ta gun doctor tace


'' dr na gode sosai...,


bakomai Hajiya ki huta lafiya sai anjima


to mu jima da yawa


fita yayi shiga dakin sukai tana kwance kalbar da Hajiya tayi mata ta kara yi mata kyau an mata ado da beat pink da blue colour adon rigar ta zama yayi a bakin dan gadon ta yana shafa fuskarta


Allah ya baki lafiya takwarata


a hankali ya motsa lalɓansa yace


'' amin...,
wacce shawara ka yanke akan batun doctor


ba ƙaramin saka shi rudani maganar Hajiya tayi ba sarai yasan halinta kamar yunwar cikin sa gashi doctor ya ƙara saka ta a hanya daman kullum maganar ta nusaiba ta tafi baza ta dawo ba kayi kokarin fitar da ita a ranka tsakanin ka da ita addu'a


ganin kamar baya sauraronta tace ...kai da kai fa nake


Hajiya wallahi ban san abin yi ba


ban gane ba lafiyar ka ƙalau kuwa asharaf


ta gumi yayi yana fargabar a bin da Hajiya zata ce ba zai iya zama da ko wacce mace ba tun da nusaiba ta tafi ta barmai duniyar zai ci gaba da zama har shima randa kwanansa zai ƙare yana fatan Allah ya haɗa su a aljanna


wallahi asharaf buɗe kunnen ka da kyau ka jini idan har baka nemi mafita ba to wallahi ni da kaina zan ne mi wacce naga ta dace na aura baka shima mahaifinka ya zuba maka ido yanzu Junaid yau sauran wata biyar a yi bikinsa amma kai ko a jikin ka rayuwar ka kake ba abin da ya dame ka


ina ji ina gani ba zan rasa inteesar ba bayan kana da maganin matsalar ta na rasa yar uwata na zo na ƙara rasa nusaiba ita nake gani nake jin sanyi a raina ita kaɗai ce ajiyar da nake gani kamar yar uwata hamdiya to itama Ubangiji ya dauke ta


shiru yayi ya kasa kwakkwaran motsi har ta gama ya tashi yace


'' zan shiga daga ciki bazan koma gun aiki ba .....,


okay haka kurum tace masa ganin kamar ranta a ɓace yake ya ɗurƙusa yace


'' Hajiya kiyi hakuri insha Allahu komai zai zo ƙarshe..,


murmushi tayi ta dafa kansa tace


'' da yardar Allah , Allah zai zaɓa a maka matar da zaka ji daɗin zama da ita zata kula da maraicin inteesar nasan abin da kake hange kenan shi ya saka ka kasa aure insha Allahu zaka sami farin ciki Allah ba zai taɓar da kai ba...,


tasho yayi yana murmushi fakar idonsa tayi ta goge kwalla hakika suna cikin jarabawa Sai dai Allah ya basu ikon cinye ta


fita yayi kai tsaye shashinsa ya shiga ciro wayar sa yayi ya ajie sannan ya kwanta a kan kujera yana kallon P.O.P ya lura duniyar tunani




UNGUWAR YAN BITA,KOFAR NASARA


tun daga nesa kake hango yan ca'ca damƙam sai bugata suke asabe ce ta fito tana gyara daurin zanin ta da taba a faranti irin na silver din nan da goro har da letar ta ajiye wa tayi tana cewa


yauwa jagwa gashi nan ta dubu biyar ce cib wallahi naga ba haka ba billahillazi sai ka biyani ficikata ba za tayi ciwo ba


asabe idan zaki dinga zargina to wallahi zan dena amsar kayan ki ke kenan kullum zuciyar ki da tsatsa


kut langa langa ce ba tsatsa ba sau nawa kake min runto


shafa gemunsa yayi yace sau uban talle


ehyi mee kace


yar dariyar shaƙiyanci yayi yana cewa a'a ba magana kika ji nayi


sarai ta gane sunan babanta ya kirawo ya ce sau uban talle tashi tayi tace


'' na tafi police station..belin sunusi...,


to sai kin dawo


gyautai ne ya ɗago da sauro yace '' Asabe ina zuwa haka da yammacin nan..kike sauri kamar zaki tashi sama ko wani abin ne ya faru ki dan tsakura min...,


wani kallon banza tayi mai tace '' Gyautai inda ka aike ni...,


to abin kuma har da faɗar magana cewar gyautai yana har haɗa katin karta


gyara matafinta tayi tace


'' ajiye ni kayi da zakai min wannan maganar wallahi gyautai ka kiyayeni ke kenan jiya a yau ko ca'car nan ba wani min sa'a kake ba...,


girgiza kai yayi yace ''Allah ya baki hakuri amma wallahi zaki zo ki same ni saina karta miki rashin mutunci.., yana gama faɗar haka ya juya ya ci gaba da ca'car sa.,


wata dariya ta sheƙe da ita tace


'' mudai kartawa juna har ni zaka faɗawa tashanci ka manta wacece ni..,


ina fa namanta wane besan halin uwantale ba kudai ga kunan duk ba na Allah gwara mu gidan mu gidan malamai ne


wata uwar dariya tayi tana buga cinya tare da rausaya irin na tsofaffin yan bariki sannan ta juyawa tayi ta fara tafiya wayar ta ce ta fara ringing a ciki ta soke ta da sauri ta fito da ita ganin sunan D.P.O wata uwar dariya tayi tana cewa shegen kaya yaga har yanzu be ji wani motsina ba shine yanzu ya biyo sawu na to gari yaci wuta aljihu ba ko sisi


ɗagawa tayi ta kara a kunne tace '' to uban son kuɗi daman tun da naga ka kama yarona kuɗi kake nema..,


D.P.O yace '' ki zo da wuri wallahi dan gobe zan tattara su na kai kotu babban laifi ya aikata kuma har ke ta shafa domin cewa yayi ke ce dilar sai da kayan maye duk wani kayan maye kina siyar wa har hodar ibilis dan haka idan baki zo ba har ke ta shafa ato...,


a fusace tace '' kai anya kuwa kanka ɗaya na zama dilar kayan maye na zauna a haka kai kasan wallahi nafi karfin gidan da nake zaune sai dai zama a j.r.a kuma wallahi karya kake kace ya faɗa maka haka , haka kurum sai ka bushi iska ka dinga kama mini yara to wallahi hawainiyar ka ta kiyaye ramata gani nan zuwa dubi biyar zan baka daga ita ko kobo bayan ƙara ba domin wallahi a haka ma da nawa na ƙara kasan an kama ANAI to na batar da kuɗi wallahi kafi a sako shi hukuncin shekara biyar fa aka yanka mai to ko wata bakwai beba suka sako shi yanzu a kudin da suke tarawa sauran dubu uku yar satar nan ba samu suke sunayi ba yanzu kowa taka tsantsan yake da abin sa rayuwa tayi tsada.. yanzu so nake na tafi nijar na nema musu sa'ar rufe ido damfara za su fara wallahi ina dalili bani da komai ya ƙare...,


cikin ɗaga murya D.P.O yace


'' to wallahi kar ma ki sake ki zo, me kika mai dani ban san me nake ba kome belin kwatan dan ta'adda shi ne za kiyi a 5k yawa belin ƙaramin ɓarawo tab gyara kalaman baƙin ki kema kinsan bazai saɓo ba bindiga a ruwa...,


da sauri ta tari numfashin sa tace '' to ka ci gaba da riƙe shi......yawa da chainanci nake maka bayani ka kasa fahimta kana ga jibi ajon dan bashir ya kake so nayi da raina sarai kasan yadda ajo yake ba sai na tsaya ina yi maka dogon bayani ba dole rance zanci nima na fito na watsa yan dubu dubu...,


ke wai da ruwa muke magana...kin tsaya kina yi min sokiburutsu kema baki wuce na jefa ki a cell ba


hhhhhhh anayi muna jin dadi ni asabe reza zaka jefa a cell tab to wallahi ka iya baƙin ka ni abin kunya baya na bashi sai na tona asirinko ko banza zan samu sassauci a gurin hukuma amma kai fa ba hukuncin da baka sani ba ka take kana karbar haram


ta faɗa tana girgiza yawa a gabasa take jin wayar ta tace kitt da sauri ta duba dariya tayi ta soke ta a inda ta fito da ita


kamar saukar a rado taji durowar mutum yace '' ke kawo wayar hannun ki..,


da sauri ta ɗago tana hura hanci tace


'' ban gane ba...,


zaki fito da ita ko sai nayi gunduwa gunduwa da naman ki


Cikin sauri asabe tace '' a'a sala sala za kai da nama na dan kuka ashe haka ka zama.,


da sauri wanda yake laɓe ya fito shine wanda idan ya kwata zai cilla mai ya gudu yana shan sholisho yace


'' baba ankar mana uwar gafalallu ce..da hallacan zo mu ware..,


a'a hafizu da ka barsa na ci kuttumar ubansa wallahi har yanzu nima ina ji da dabanci banda haihuwa da ta gama buɗa kashina ai wallahi da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba


cewar asabe tana kulle mayafinta a ƙugu


wucewa sukai ba tare da sunce mata komai ba kunce mayafinta tayi ta daura a kafaɗa ta ci gaba da tafiya tana yar waƙa bakin titi ta fita batare da ta tsayar da me napep ba ta fara tafiya har ta isa police station


tana shaga tace '' dan bala ina DPO yake..,


banza yayi mata ya ci gaba da rubutun sa doka kantar da yake rubutu tayi tace


'' kai dan bala ba da kai nake ba amma ka ci gaba da rubutun ka bawa banza ajiyata to wallahi zanyi maganin ka har ni zaka kalla ka watsar yawa sa'ar wasan ka...?,


daga littafin sa yayi yana dubawa tamkar da dutsai take magana a fusace ta warce littafin tace


'' tambayar ka nake ina DPO yake...?,


ya tafi koyo sallama ya bata amsa kamar ba shi yayi magana ba


kama kugu tayi ta ajiye littafin tace


'' to yanzu na fahimci inda ka dosa kuma zanyi maganin ka ...,


kofur inusa ne ya shigo yana cewa tab yau manyan ƙasa ne a gidan namu


gyatsuna fuska tayi tace


'' kai ni ajie wannan wasan a gefe tawa ce ta kawo ni shi wannan cutar kurumta ce ta kama shi na tambaye shi yayi shiru yana yi min kallon hadarin kaji..,


kofur inusa yace


'' hajjaju me ya faru duk wata hanya ta kurɗa kurɗa kinsan na kware a gurin nan ba inda bana shiga na fito indai da hatumin na sara kina mannamin zaki ji information..,


zama tayi a kan benchi tace


''hmmm kufa tsiyata da ku kenan komai kuɗi wallahi ku guje ranar da Ubangiji zai damƙe ku ina ji ye muku wannan rana amma ku bakwaji haram kuka saka a gaba duk inda cin hanci yake kuna nan ku dashi kamar dan jumane da dan jummai..,


kinga faɗamin me ya kawo ki na lura yau ba arziki kika zo gurin nan cewar kofur inusa


kamar kuwa ka sani dan wallahi kalma kaɗan za ayi min na zubar da haƙoran mutum wallahi har ni za a nunawa rashin mutunci


cikin daga murya kofur yace


'' asabe reza tamayar ki nayi me ya kawo ki...?, amma kin tsaya kina tayi min wasu zantuttuka ga abin da na tambaye ki amsar da kike bani dabam to bani da lokacin fast fast maza ki faɗamin ina da abin yi...,


to sai ka nuna wanda bashi da abin yi ta faɗa tana harararsa


ke ki fita idan sa'insa kika zo yi gurin nan dan bala ya faɗa yana haɗe rai domin sam ba shiri suke da ita ba


tofa yau nake ganin kudirar Allah yanzu fa tsab zai iya dagani ya fitar dani to wallahi ba ka san wace mace ba za ka haɗu da dana sani mara a dad'i ta faɗa tana wura hanci




a'a abin duk be kai haka ba mu nan gurin wajen sasanci ne ba gurin tada tarzoma ba ke asabe me ya kawo ki gwara kiyi kiyi ki bar gurin nan domin na lura yau transformer kika haɗiyo Alkur'an baza ki amayar mana da ita a nan ba yanzu jikin ki sai yayi tsami hukuma gaba take da kowa cewar kofur inusa


tamkar me shirin dauko duniya haka ta zura hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login