Showing 9001 words to 12000 words out of 18680 words

Chapter 4 - UWAR GAFALALLU book 1 By Oum Yasmeen .txt

07 Jan 2025

2098

ya Allah tana fara tafiya sai da yaga tayi nisa sannan ya juya ya tafi part dinsa yana shiga junaid ya shigo da yake dakin su yana kallon na juna kallon a gogon parlour ASHRAF yayi yace


''9:30 kai kuwa ina kaje haka kasan fa Alhaji baya son yawa Junaid a dinga kiyaye wa kar kuma ya saka maka dokar fita..,


kallon a gogon dake manne a bango Junaid yayi yace


'' wallahi naje gidan su Abubakar ban san lokaci ya ja haka ba amma insha Allahu zan dinga kiyaye wa hakan ba zata sake faruwa ba ...,


Kai ASHRAF ya jinjina yace


'' Allah ya saka yana shiga dakinsa shirin bacci yayi sannan ya kwanta..,


Washegari


cikin sauri take haɗa musu breakfast Hajiya ce ta fito tace


'' a'a nusaiba har kin tashi kin fara aiki...?,


Eh wallahi Hajiya bana so na ɓatawa yaya lokaci ransa ya ɓaci yayta jira shi ya saka na ɗora da wuri cewar nusaiba kanta tsaye domin ta manta da halin hajiya na zolaya yanzu zata tusata a gaba


dafa table din kitchen Hajiya tayi tace


'' kaga me miji wato kar ki ɓara mai rai daman haka ake so matar kware ta dinga yi..,


murmushi tayi batar da tace komai ba


fita Hajiya tayi bayan ta gama ta kwashi komai ta kai dining jin sallamar su ta ɗago amsa wa tayi tana gaishe da Alhaji har ƙasa


Cikin kulawa ya amsa jawa kowa kujera tayi sannan ta zauna zuwa kowa tayi junaid na tsokanarta Alhaji na tare mata shi kuwa ASHRAF kamar baya gurin cin abincin sa yake cikin kwanciyar hankali bayan ya gama ya saka tissue ya goge bakinsa ta tashi zai bar gurin yana cewa


Zan tafi gun aiki


kallon sa alhaji yayi yana cewa gaskiya bana son zuwan ka wajen wutar nan ga kasuwanci nan idan ma baka san zama a ƙasar nan ga shaguna na Dubai kaje kayi kasuwancin sai da gold ana samu sosai


ƙasa yayi da kansa baya so ya tashi a jingina da ƙarfin mahaifin sa yafi so ya nemi nasa yasan zafin nema dariya Hajiya tayi tana cewa ASH ba magana naga kayi shiru


sosa ƙeyarsa yayi yana cewa sai na dawo na tafi


Alhaji ne yace


'' Allah ya kiyaye hanya ya bada nasara da sa'a tun da kafi son nan sai mu bika da addu'a...,


wallahi kuwa Hajiya ta faɗa tana kallon nusaiba ta ci gaba da cewa nucy ba rakiya...?,


kai ta gyaɗa mata a hankali tace


'' Hajiya ba sai na raka shi ba..,


kwaji da shi zama ku dawo dai-dai ne ta faɗa tana tashi daga gurin shiga bedroom dinta tayi bayan kowa ya gama ta kwashe kayan ta kai su kitchen


akwana a tashi ba wuya yau ta kama juma'a za ayi daurin aure sosai manyan ƙasar nan suka halarci daurin auren NUSAIBA ABDUL HADE da ASHRAF MANSUR GWARZO amma ban da dangin mahaifin nusaiba kalilan ne suka zo domin ba son auren suke ba akan wani ban zan dalilinsu mara makama da abin yi gani suke Hajiya ta nuna musu kuɗi taya yaya yarinya ta taso a gunta kumu ta aurer da ita ba tare da ta Da musu da ita ba dan tana taƙama da kuɗi...


bayan an gama daurin aure da yamma akai lecture daga nan a ka wuce da ita dakin ta ba abin da Hajiya da Alhaji suka rage ta dashi komai sun mata haka kowa ya watsai ya bar ta ita kaɗai bata da tarin ƙawaye bayan isha na shigo gidan....


nima da yake bani da abokanai abokina ɗaya salim shima a waje muka rabu shiga nayi tare da addu'ar Allah ya kade mana fita Allah ya bamu zaman lafiya tura kofar nayi abin da na zata shi ya faru a buɗe take na shiga bakina dauke da sallama bakowa a parlour direct bedroom na nufa nayi sallama


ɗagowa tayi ta amsa min sallama ta tsayawa nayi ina kallon ko ina tare da da yiwa Allah godiya da ta cika mana burin mu mun mallaki juna


tun da mukai aure ba mu da taɓa samu. Saɓani ba nusaiba tana da haƙuri za kai mata ta dauke kai ni ko da tasan Kai mata din har Allah ya azurta mu da yarinya,


ranar da zata tafi ganin dangin ta lokacin inteesar tana da two year hatsari ya faru me kama da almara ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya gama tunaninsa tafiya ya fara har ya shiga palour sa zama yayi akan two seater ya zuba ta gumi kallon agogo yayi karfe 12:00 gaskiya ya dade a zaune a gurin nan haka ya kwashi lokaci..




Wannan kenan


baccin tane yayi nisa ta tamkar daga sama taji ana bugu tashi tayi tana kunna yar ƙaramar fitila tana jan tsaki ashe naja bata dawo ba tun daga zuwa ciro kudi tashi tayi jin zata karya musu kofar da suke ƙarawa da ita ta fita tayi ta isa soro ta buɗe kofa ta tsaya a baya tana liƙe bak'ar motar da aka kawo naja a cikin ta har da tinted to munafuka uban me kika tsaya yi sauran kuma kice mata na dawo


dan ubanki bani kuɗin da kika ciro da wanda kika samo ni wallahi bansan ke yar marasa bace sai yau


wallahi momcy be bani wani kuɗi ba yau muka haɗu dashi ta faɗa tana turɓune fuska


uban be baki wani kuɗi ba bani ko ya zu wallahi na caje ki asabe ta faɗa tana zaro ido




ba yadda ta iya haka ta miƙa mata kudin murmushi tayi tana kirga su dubu arba'in cis tace


'' ina dubu biyar din ta kwalas...?wallahi naja ki kiyaye ni kuɗin nan zu zasu wanke ki daga laifin da ki kaimin,


zun buro baki tayi ta miƙa mata amsa tayi tana washe baki Allah ya tsare ya kuma buɗa kofofin hanyar samu...


saboda takaici kasa barin gurin nayi ƙafafuwana sun kasa ɗauka ta yan zu rufa'i ko kirana ba yayi saboda taje har gidan su taja mai kunne tashi nayi na bar gurin ganin sun tafi sun barni kulle kofar nayi na koma ciki shiga daki nayi runtsai ido nayi ganin tashin hankalin da na gani jalila sumy suna ta aikata masha'a kamar ba yan uwa ba kamar addinin mu be yi hani da wannan dabi'ar ba kasa shiga nayi na dauro alwala na daman da hijabi a jikina shiga dakin baba lami nayi sai sharar bacci take har da mun shari shim fida daduma nayi na fara nafila


bayan na idar bacci ya ɗauke ni can kuwa ɗaki ai ko a jikin su ganin mufeeda ta gansu breast din sumy da shi jalila tayi bacci basa tunanin Ubangiji zai iya ɗaukan ransu a haka a kuma tashe su a haka me za su ce mai jin kiran sallar asuba suka tashi ko wacce taje tayi wanka ta dauro alwala kallon su mufeeda tayi tana cewa


kuji tsoron Allah abin da kuke aikatawa ba me kyau bane abu mafi muni


tun kafin ta ƙarasa sumy tace


'' kiyi mana shiru wallahi kema baki wuce na kwantar da ke ba na kwakuleki tas...,


kai ta girgiza ta bar gurin ƙasa sheƙewa sukai da dariya suka tafa


har sun tada kabbarar salla suka ji muryar takwalas da sauri suka sallame sallar suka fito yana sanye da jallabiya yaci dauri ture kaga tsiya wata uwar buɗa ya saki yace


'' kut gaskiya mutane na kun yi kyau kunyi acan acan dan tafiya lagos da nayi shine kuka tara wannan kayan aiki haka to gaskiya nima ba za a barni a baya ba ina momcy take ...?,


dariya sumy tayi tace


'' tana bacci kai ma wallahi Lagos ta amshe ka..,


kan bura ubancan kayyasa ai anan kano ba komai ake ba sai da naje Lagos sanna na ƙara fahimtar rayuwa wallahi idan har zata bar ku hmmm kudi ta riga da ta zama attajira sufa ba irin biyan nan suke ba musanman ma ki haɗu da direba ko yare ba abin da basa kashewa mace


ya faɗa yana buga cinya hadi da fari


naja ce tace '' dan Allah ta kwalas ...?,


murguɗa baki yayi yana fari da idanuwansa yace '' zauna wasa har lokacin ki yayi ya ƙare ba abin da kika tara can fa ba me damuwa da wani kowa harkar gaban sa yake...,




Ikon Allah yanzu kowa sai yayi sabgar gaban sa ba me damuwa da kowa anya kuwa jalila ba nan za mu tafi ba cewar naja


gyara daurin kirjin ta tayi tana cewa nima fa abin da nake tunani kenan wallahi gwara mu shiga sahun manyan mata


wata uwar shewa suka saki tare da cewa a hayye ras wannan shewa ita ta tasar da momcy ta fito dai-dai shigowar baba cikin daure fuska yace


'' kai bana ce maka kar ka ƙara shigo min gida ba ..?,


gaskiya ba ruwan ka malam ya kake yawa ne nan ina gidan yake kwango dai amma wannan ba gida bane ka bari sai arziki ya zo ya same ka kana kwanciyar asarar nan da kake kayi gida wallahi ba ruwan ka da kawayena da suke zuwa guna da kuma na ya'yana naga ma gado aka ci aka bar maka shine kake tun ƙawo da shi


Asabe ta faɗa tana yatsuna fuska da tabe baki


kasa magana yayi sai ma kasa da yayi da kansa ya wuce be ƙara ce mai komai ba bayan kaddarar da Allah ya yi mai to Ubangiji sai ya ƙara jarabar sa da asabe bayan ya shiryu shiga daki yayi yana jan carbi ko zai samu saukin zuciyar sa


kunga zo mu shiga daki takwalas sai ka sako da ga farko asabe ta faɗa tana nuna musu dakin ta shiga sukai ya dinga basu labari momcy tace




'' bara mu gama bakin ajo ko bayan ka tafi ne sa tawo har waccen yarinyar sai an tafi da ita naji dakai na wallahi...,


sai ma karshen watan nan zan tafi sai mu tafi tare


hakan ma yafi yi min gwara su sauka a hannun ki


ai momcy ina faɗa miki gida na gina kowa ya zo ya shiga ya bani yan kudina a agege


kai ka akai kace litkafa taci uwar ta da


Kware da gaske ai ina tare da addu'ar iyaye


ai kuwa Ubangiji bazai taɓar da ke fa ji sukai an ɗaga labulan dakin zaro ido sukai gaban su ya yanke ya waɗi ɓare baki takwalas yayi yana cewa


Kai lafiya ka zo ka tsaya mana a ka da zabgegiyar huƙa


yimin shiru ko yanzu naci kuttumar..ubanka ba wajen ka na zo ba ya faɗa yana kallon asabe


tashi yar kwalas yayi yana girgiza kugu yace


'' ke idan kana ta ƙama da kai dan dabane ni naje inda baka je ba naje inda aka fika dabanci da iskanci Dan haka maza wuce ka bani guri dan iskan ƙarya


ai be ƙarasa ba yaji saukar duba a bakin sa ihu ya saka yana cewa na shiga uku momcy ku duba min ya cire min hanci ko


momcy da cikin ta ya ɗuri uwa bama tasan me yake cewa ba kai a sabe da sauri ta ɗago jikin ta yana rawa yaci gaba da cewa


daman na faɗa miki inhar kere na yawo zabo ma yana yawo rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya kin saka an kai ni gidan yari to yau zan aika ki lahira dan uwar....ki ke shegiyar ƙarya ce kuma wallahi sai nayi maganin wa'yannan ya'yan naki ba sune yan zuga ki ba to duk yanzu zan yanke musu hukunci kai kuma dan daud ko to yau zan dawo da kai kalar ka ta ainiyi a zaton ki zan dawwama a gidan yari ko


to yau zan ci ubanki ala'ada waje zan nuna miki jiya ba yau bace......






UWAR GAFALALLU




EPISODE 10-11


UWAR GAFALALLU




EPISODE 10-11




Gumi ne ya shiga wanke momcy tasan bata kyauta ba takurewa guri ɗaya su sumy sukai jikin su har rawa yake takwalas kuwa sai zare ido yake be taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba wannan wacce irin rana ce


Wannan shi ake kira da ya taka sahun ɓarawo yace '' talge dan girman Allah kai min rai wallahi Allah ban shirya mutuwa ba...,


wata dariya ya saki irin ta arnan nan kamar anyi ruwa an ɗauke sai kuma ya murtuƙe fuska yace '' wallahi sai na ci uban ku..,
jin hayaniya baba lami da baba suka fito turus sukai baba lami ta dafe kirjinta tace '' innalillahi wa'inna'laihir raji'un idirisa kaga a kwashe kwashen asabe abin da ta kwaso mana insha Allahu sai dai abin ki ya ƙare miki a kai...,


kai lafiya ka shigo mana gida


wani kallo talge yayi mai sannan yace '' ba gurin ka nazo ba dan hakai ba idan kai wasa wallahi kai ma yanzu nan zan sala sala da naman ka..,


kama haɓa baba lami yar gumama tayi tace '' idirisa yi baya ita da tajawa kanta ya yanka ta ya soya ka na ganin huƙar nan sai kyalli take to wallahi maza zo mu bar gurin nan...,


Mufeeda ce taji abin yayi yawa ta fito tace '' baba me ke faruwa...,


zaro ido tayi ganin talge yana juya huƙarsa ja da baya tayi baba lami tace '' mufeeda kinga abin da uwar ki asabe reza ta jawo mana ko ai gata nan cikin ta ya ɗuri ruwa duk wannan masifar nan tata da daga murya kinji ta tayi muƙus a daki yawa anyi ruwa an ɗauke ko su futsararrun ya'yan nata kin ji su shiru...,


ke rufe min baki ko yanzu nayi miki ba dad'i wallahi


rufe bakin ta tayi tana zare ido ta ƙara ja baya a hankali har ta rufo kofar ta jikake garam ganin baba lami ta gudu mufeeda ma ta shige daki sai baba da yake kallon kudirar Allah yace '' bawan Allah zo ka faɗa min me tayi maka..,




cake huƙa yayi ya bushi sigari ya fesar yace '' wannan shegiyar matar nan da kake gani annamimiya ce ni ta saka a ka kai gidan dan kande dan tana da daurin gindi ta saka a ka daure ni wiwi na ta sara ta hanani kudi na shi ne nazo ta bani ta hanani tare da fadamin mugayen kalamai yau sai naci uwar ta wallahi..,


ƙasa yayi da kansa zuciyar sa ba dadi be san yaushe a sabe za tayi hankali ba yace '' kai hakuri yanzu ta dauki kuɗin ka ta baka shikkenan magana ta ƙare..,


kai saita baƙin ka ni kake faɗawa haka aini ban san hakuri ba ko baki ji sunan nawa ba talge sai da wuta


ya faɗa yana cije baki


bawan Allah ina haɗa ka da girman Allah da manzon sa kai hakuri ta fito maka da kuɗin ka


jikinsa ne yayi sanyi yace '' billahilla'zi da ace ba ka hadani da Allah ba bazan bar gurin nan ba sai na aikata abin da nayi niya yasin in badan rashin mutunci ya za ayi ta dauki kayana nayi magana ta saka a kulle ni..,


kai hakuri bata kyauta ba Allah ya wuci zuciyar ka


cikin sauri take fito da kuɗi bama ta san nawa ta miƙo mai ba amsa yayi yana zurawa a aljihu dubu goma yake bin ta da alama ma wannan kuɗin ya fi ƙarfin dubu goma ɗaukan huƙar yayi ya fita


da sauri ta fito tana zabga gumi yawa an tsumata a cikin ruwa gyara daurin daukwalinta tayi tana haɗe rai kar ma ya ga fuskar yi mata magana girgiza kai yayi yana mata addu'ar shiriya ya koma daki baba lami yar gumama tana jin alamun kurar ta lafa Cikin sauri ta fito tana cewa amma bansan iskancin ki a sabe ya kai haka ba sai yau wallahi


kiri kiri ina so na tafi kasuwa da wuri amma halin ki be bari na tafi ba wallahi tur da wannan dabi'ar take fyece majina tayi ta ci gaba da cewa


kwata kwata ke ba san wacce irin mace bace gaki nan ba ƙirar fasali yawa bukka


takwalas ne ya fito yace


'' yau dai momcy kin birkita yar tsohowa..,


Uwar ka ce tsohuwa bani ba billahilla'zi ku kiyayeni kar nayi muku ba dad'i in banda raini har ni zaka kalla kacewa tsohuwa shege da fuskarka yawa anyi daura yar zunubi


sai a lokacin ma asabe ta ƙarewa baba kallo har jagira tayi bakin nan sai maiƙo yake idon ta yawa wata aljana dariyace ta kubbuce mata ai kuwa ta dinga yi


tab ku na cikin daki ku fito yan iskan karya asabe dai ta kamu da cutar mental sai dai hakuri...


da daddai da daddai suka fito ganin mahaifiyar su na dariya tuƙuru sai suka ɗauka ko duk a cikin rudewa ce ɗagowa tayi ta ƙara kallon baba kamu ashe har bra ta saka tayi sama maman nata yayi ƙasa ya zube yawa slipper yauwa idirisa fito


fitowa yayi yace '' baba gani...,


kaga daman wata Magana ce me mahimmanci zanyi dan ma dai daya dan uwan naka ba ya nan


to baba muna jin ki


wata uwar harara ta zabgawa asabe tace '' wallahi ki fita a idona na rufe asabe yan zun nan sai nayi miki ba dadi kin gama haukan kin tashi kome kuma kuma har yanzu da sauran ki..,


shiru tayi ta nemi guri ta zauna baba ta ci gaba da cewa to bayan mutuwar uban ku ban ƙara tunanin aure ba sai yanzu cikin yardar Allah zan yi aure mijin nawa a gidan nan zai tare


da sauri ya ɗago ji maganar shazali sai saɓa babbar riga yake wane a gurin idirisa kyalli kai kuma awa


haba baba me isaka duk harkar da zaku zubar mana da mutunci ita kuke yin ta to yasin ba za ayi auren nan ba ya faɗa yana gyaɗa bulala tashi sumy tayi saboda kan nasa ba dadi tsab zai iya dukan su shi daman haka a ka haife shi yana da cutar taɓin ƙwaƙwalwa naja ma.ganin kamar yau abin ya tashi sai ta matsa daga kusa da shi


Baba lami tace


'' idirisa yau babu wani labari ne naga gidan kamas...,


yan zunnan zan fita na nemo insha Allahu komai ya tsaya wallahi


taɓe baki tayi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login