Showing 6001 words to 9000 words out of 18680 words

Chapter 3 - UWAR GAFALALLU book 1 By Oum Yasmeen .txt

07 Jan 2025

2095

a zaninta tana lalube tsayawa sukai suna kallon kudirar Allah sai can ta fito da kudi washe baki tayi tace


'' kofur ina DPO..?,


kauda fuska yayi yana gyara zaman hularsa kallon sajan dan bala yake domin shine gaba dashi yanzu yana ba dai-dai ba DPO zai ta magana yawa yayi me wanna hali nasa shi yake gudu




UWAR GAFALALLU




Episode 6-7




tofa kai ma nayi maka magana kayi shiru me hakan ke nufi wallahi ni karamin aikina ne na shiga har office dinsa to wajen nan baƙona ne bani da wani lokaci wani satin nijar zani naje na nemo sa'ar da yaran nan zasu dinga samin dan na ɓatarwa komai ya tsaya chak dan kuɗin da suke tarawa shima yanzu ba wani bane da yake yanzu ba lokacin siyasa bane, ba dan siyasan da nake gani dan haka raina duk a bace yake kuyiwa kanku kiyamal laili ku fadamin inda yake,
bayan kuma shi ya ce na zo ya kama sunusi


kallon kallo suka shiga tsakanin su ba me magana sajan dan bala ne yace


'' yana ganawa da baki ne ...,


ai be rufi bakin saba sai gashi ya fito yana washe baki yawa gonar audiga shi da wata yar duniya sai gyara mayafinta take yana ganin ta yace


'' sweet sai mun ƙara haduwa nagode da kawo miin ziyara da kikai...,


wani far tayi da idonta tace


'' sweet kar ka damu insha'Allah zaka dinga ganina akai akai..,


wata dariya DPO yayi yana shafa ƙaton cikin sa yace


'' aikuwa sweet nagode sosai...,


hannu ya daga mata har ta kulewa ganinsa sannan ya juyi kan asabe yace


'' asabe yar tasha ke da nace miki karki zo shi ne kika zo me zan miki belin katotan dan ta'adda zan bayar a dubu biyar yawa belin ƙaramin ɓarawo me satar kaji to ko masu satar waya idan sun kawo min ziyara haka kurum batare da wani abu ba dubu hamsin suke bani shi yasa ka zaki ga bana kama su na barsu suna yadda suka ga dama a garin nan balle belin dan daba makashi mutum nawa ya naƙasta a ƙa'ida ma wallahi gidan gyaran hali za a kai shi ai mai daurin rai da rai amma saboda kin daure mai ai gashi nan yana yawo a gari...,




kwantar da murya tayi tace


'' DPO ka temaka wallahi dubu biyar ɗin nan ce dani kuma kaga ...,


kinga bana son dogon bayani shigo daga ciki tashi tayi ta bi bayan sa zama tayi a kan kujera shima ya zauna a tasa yace


'' ci gaba ina jin ki...,


yauwa temakawa za kai ka sakar min shi a haka yanzu harkar damfara nake so su fara wallahi gari fa yaci wuta ji kake ɗib ba wani bayani yan siyasa ma yanzu ba lokacin zaɓe bane kasan ita wannan gwamnatin bawan Allah nan baya yawo da yan daba sai ma ya nema musu abin yi


dan shiru yayi sannan yace


'' to bani amma wallahi dan kece da ace wata ce wallahi bazan karɓa haka ba ko kuɗin da na kashe mai ban mayar ba ga zagina da yadin Ka yi kullum sai ya saka na a siyo mai tabar wiwi da maganin sauro saboda tsabar samun waje har da a siyo mai turaren wuta nace wallahi baka isaba nan dakin uwar'ka bane ko gidan uwar gafalallu ne...,


rausayar da kai tayi tana cewa nagode DPO Allah ya barmu tare Allah ya saka wata ran a baka IG


wai za aga iya shege ai harka zan fara da yan fashi kinsab fa sun fi kawo kudi me tsoka wallahi wata miliyan ashirin a sati sai na jita a account dina wallahi


Kai DPO wai ina zaka kai kuɗi haka


hmm nima bani kaɗai nake cinyewa ba ni da abokanan hurɗata muke cinyewa sun fini ma ci wallahi sai da kuɗi suke zama idan ba kuɗi wallahi kashi ya fika mutunci a idon su shi yasa ka nake neman kuɗi hurjajhan domin a samu a faranta musu rai


cewar DPO yana amsar kuɗin da ta bashi


tashi tayi tana cewa to zo muje ka sako shi mu tafi tare domin wallahi bazan yadda ba na tafi na barsa ka sake saben lale


tashi yayi yana cewa ke ko irin kewarnan tawa baki ba


haɗe rai tayi tace '' wallahi tun da nayi aure na bar wannan sabgar ko sha'awa bata bani wallahi daidai har a kwanar dan gora na zauna zaman kaina kai duniya haka ma fa tayi mana da kyau wasu su nan sun haukace...,


amma kika saka ya'yan ki a wannan hanya kinsan da haka ya faɗa yana kafeta da ido domin har yanzu da kyen jikinta komai yana nan kamar ba ita ta haifi zaratan yan matan nan ba har guda hudu rigis lashe baki yayi ya ci gaba da cewa


Please ko sau ɗaya a bani na taɓa


sai kuma fa kayi wallahi haka kurum da aurena


to biyo ni ki amshe shi wallahi ya bari muka ƙara kama shi hmmm sai ya gammace kiɗa da karatu dan wallahi sai na goge mai duk wata hadda dake kansa ban da rashin mutunci ace duk wani fadan daba kai ne a sauhun gaba kwanaki fa gwamna ya kirawo shi akai sulhu amma shine ya ƙara jan wata tawagar


kaga bana son dogon jawabi muje ta faɗa tana gyara zaman mayafin ta a jikinta domin idan ba wuta wuta tayi mai ba sai dare yayi mata anan kuma kyalli baya son ta kai dare duk inda taje magariba tayi mata a gida dan ma dai ba wai tsoransa take ji ba be isa ya saka mata doka tabi ba ....




batare da yace mata komai ba ya fita binsa tayi har baƙin cell ya bude sunusi fitowa yayi daman yana baƙin kofa wata uwar miƙa yayi yace


'' hajiya asabe reza...sai yan zu kika ga damar zuwa..,
kaga nususi idan baka godemin ba ai baka tsinemin ba dududu kuɗin da kuke tarawa nawa yake ....?


yanzu ma sai da na saka jagwa ya ɗan har hadomin sannan na samu damar tawowa wallahi rashin hakurinka yayi yawa yasin


to ai shikkenan hakan ma na gode a gidan mu wane yazo sai ke da bakya gajiya damu


au ashe ka gane gaskiya wuce mu tafi


cewar asabe tana dafa kafaɗar sa


kai kuma zamu haɗu a way ne wallahi sunusi ya faɗa yana mai da idanuwansa ciki


dariya DPO yayi yace '' wa kake faɗawa haka lallai yaron nan wallahi idan bakai wasa ba sai na mayar da kai inda ka fito wallahi..,


wani kallo sunusi yayi mai yana nuna mai ya tsunsa biyu tankaɗa ƙeyar'sa tayi tana cewa maza maza mu tafi shige mu tafi shigewa yayi yana faɗi yaci uban malin malin da takalmi combos da hula
irin ta kaurayen nan kai bani wayata tunda bata tsoho bace


kofur inusa ya miƙo mai warta yayi yana cewa wallahi da kudina a ciki naga babu sai na dawo anyi ta wallahi domin bazan yadda ba haka kurum ku cinye min kudina


da sauri asabe tace '' kai wanne kuɗi kake magana...?,


to uwar son kuɗi katina ne na saka na dari biyu sunusi ya faɗa yana bincika wayar sa


to bana son neman magana shige mu tafi bana son bar baɗa haka kurum ka ƙara ballo min ruwa har nawa kuka tara da zan ƙara zuwa belin ka wallahi sai dai akai ka gidan yari idan na samu na fito daga kai


cewar asabe tana tankaɗa keyar sa sukai waje ci gaba tayi da magana tana cewa yauwa nifa a kafa na tawo dan haka idan zaka iya to sai ka tawo mu daɓa dan wallahi bani da kuɗin mota


ƙaramar wayarsa ya fito da ita yana lallatsawa dakyar take dannuwa sunƙuyawa yayi yana neman tsinke yace


'' Bara na kirawo honourable ya turo min da kuɗi domin wallahi ba zan iya tafiya a ƙafa ba yawa wani doki ai sai maƙiya ma su yi dariya ana nunani da baki ana cewa ga sunusi ta ƙare mai idan ke zaki iya tafiya to ga hanya nan mu haɗu a gida kawai...idan ma ban same shi ba zan kirawo bazzawara ta turomin kuɗi...,


asabe dundu tayi mai tace


'' a'a kirawo shi idan naji zai bayar sai ka bani kudina ni zan tafi a ƙafa..tafiyar nawa take..,


kai ka kai ni kika daka me nayi miki wannan wanne irin cin zaline sunusi ya faɗa yana ɗagowa ganin bata kula shi ba ya ci gaba da kiran amma ba a ɗauka ba duk wanda ya kira ba a picking kamar haɗin baki suka juyo a tare suka kalli juna wata dariya asabe tayi har da buga cinya tace


'' me kake jira naga jikin ka yayi la'asar kaga tun kafin dare yayi mana a nan gurin kazo mu tafi..,


Ba tare da yace mata komai ba ya fara tafiya binsa tayi har suka isa gida ba me ce wa dan uwansa kala al'adar gidan ce bayan sallar magariba wa'yannan masu ca'car zasu kasa gurmi ai ta kiɗa mahauta nata sudda baru dan haka kafin isha tayi har sun hallara,


wani maroƙine ya taso yana cewa cau cau cau sarkin daba ko wa yaƙi bin umarninka yanzu lahira za tayi baƙo huƙa ya ƙarba a hannun wani yana wulwulawa


sosai maroƙin nan ke wasa shi kuɗi yan gurin suka fara zuba mai ana liƙi shiga gida tayi ta bar su da sauri tace


'' innalillahi me zan gani jalila daman ban gama kashe wutar nan ba shi ne kuka ƙara wurata har ta kai ku da gwada yar ƙashi ..,




Cikin haƙi jalila tace '' wallahi momcy idan ban karya yarinyar nan ba wallahi Allah ba zata fahimci ni da ita da babbanci takwalas ne ya turo da kuɗi yace gashi nan mayi kunshin bikin ajo shine wai dubu daya zata bamu ta riƙe dubu shidda..,


taɓarya ta dauko a kusa da bayi tace


'' ku cika juna ki na sauke muku allon kafaɗa wannan wanne irin iskanci ne ku bani kuɗin kowa ya rasa da man ke jalila baki kawo min balance ba maza maza ke sumy zo ki ciro min kuɗin nan wallahi kun rasa saboda da tsabar mammaƙo wanda kika je gurin sa ko kobo bani da tabbacin ya baki...,


rabuwa sukai har rigar naja ta yage bako kunya ta bata rufe jikin ta ba duk kirjinta a buɗe


maza ku miƙo min tun kafin na ci mutuncin ku asabe ta faɗa tana kafe su da idanuwanta


miko ATM din tayi amsa tayi tana cewa mene pin din


Kau da kai naja tayi ita bawai faɗar ne ba za tayi ba yanzu momcy zata samu damar ɗaukar mata kuɗi tana yi mata bincike tace


'' kawo naje na curo har yanzu sumy bata cikin hayyacinta...,


miƙa mata tayi ta amsa shiga daki tayi ta canza kaya ta fita neman guri jalila tayi ta zauna akan tabarmar da mufeeda ta shinfiɗa


Lami yar gumama tace


'' sai yanzu kika dawo..,


wallahi baba sai yanzu dakyar ya bani shi kinsan fa yanzu komai ya tsaya asabe ta faɗa tana zama ɗaukan kayan da ke gaban baba tayi tana cewa kai wannan riga tayi kyau




Ajiye ninƙin da take tayi tace


'' nima wallahi naga kyawunta yan zun nan challi ta kawo min su gobe insha Allahu yarinyar nan zata dauka mi tafi kasuwa..,


ni wallahi Allah bana son zuwa gurin yan gumamar nan yan iska ne wallahi mufeeda ta faɗa tana turo baki


wani kallo baba lami tayi mata sannan tace


'' dan kan uwar ki sai kin je su wa'yannan manyan mata ne ke ce ƙarama duk da dai kina nema ki kere'su ga kirga dangi nan duk ya cika miki kirji yawa za su faso kirjin ki su fito amma ba fuss tsuliyar me duki...,


turo baki tayi tana kunƙini ta tashi jin an kira sallar magariba tashi tayi ta dauro alwala bayan ta idar ta kalle su tace


'' baba an kira sallar magariba fa..,


ba wanda ya tanka ta balle baba da ta cika tayi fam ninke kayanta ta ci gaba dayi tana rera wakarta da tashi tayi ta shiga daki ta tada salla


zama tayi har aka kira sallar isha'i lokacin kuma har gidan su ya fara dinkewa da jama'a na kallon gurmi bata fita ba ta kwanta a ɗaya tana jan carbi domin hana zuciyar ta tunanin komai


ke miko min mayafina kinga naja shiru yawa an aiki bawa garin su kar dai yau ba a nan zata kwana ba


tashi nayi zuciyata na ƙuna na miko mata mayafin ta sannan na koma na zauna fita tayi tana sababi




TUDUN YOLA


ƘARFE 8:45


baka jin karar komai sai ta chokali da AC kowa ya mai da hankali kan abincin da suke ci ido Hajiya ta karawa Ashraf tace


'' Ash kamar akwai abin da ke damunka tun dazu sai juya chocali kake ka kasa ci idan har ba zaka hana kanka tunani ba wallahi zakai mutuwar tsaye ka takurawa zuciyar ka sai tunani kake mara makama da abin yi to wallahi ka rufawa kanka asiri ni wallahi abin ka har tsoro yake bani ai wannan rashin tawakkali ne yanzu ina iyayena ba hakura nayi ba na ci gaba da rayuwa bawai tana yi min dadi ba a'a kawai dai na ɗauki hakuri amma kai ke nan ai ta abu ɗaya..,




ƙasa yayi da kansa kallon sa mahaifinsa yayi yana cewa haba Ashraf yan zu kai takure kanka da kayi shine jin dadin ka kome Ubangiji yana jaraba mune yaga iya kacin imanin mu mutane nawa suke naman damar da Allah ya baka mutane nawa suke cikin wani mawuyacin hali amma sun saka hakuri da dangana Ubangiji fa yana jarabtar bayin sa na kware ne


Ashraf sunkuyar da kai yayi yace


'' insha Allah zan ɗauki nasihar ku bawai na kasa cire nusaiba a raina bane yanzu wannan lalurar da inteesar take ciki ita take ƙara jefa ni cikin rudani...,


damuwar ka ba zata saka ta samu lafiya ba sai ma ayi biyu da kwance uwa kwance kaga ba amfani ke na ko Hajiya ta fada tana goge bakinta da tissue


Kai ya jinjina sannan ya ci gaba da cin abincin sa dan ƙadan ya ci daman shi dabi'arsa ce baya cin abinci da yawa tashi yayi yana cewa Hajiya Alhaji sai da safe insha Allahu nan da wani satin zan kaiwa junaid ziyara Cyprus daga nan zan biya nayi umara


to masha Allah Allah Ya kai mu lokacin


Alhaji ya faɗa cikin kulawa


Hajiya tace


'' insha Allahu lokacin da matar ka zaka tafi..,


ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya fara tafiya hajiya ta kasa fahimtar sa shi ba wai zama da macen ne bazai iya ba a'a gani yake ba matar da zata iya kula da inteesar gwara su zauna su biyu har ta girma yayi mata aure ba zai juri ganin ana wulakanta mai yarinya ba


musamman ma , matan yanzu da kansu kaɗai suka sani babban burin su idan sun shigo ba wanda zai raɓi mijin su sai su kaɗai da yan uwansu wata ma kuwa duk wani naka saita rabaka dashi sun matana da ita rayuwa shiga da fice ce wanda beba ma akai mai balle kinyi wata da addabawa uwar miji ta manta da wannan karatun cewa


itama uwar miji ce wata rana yana wannan tunani har ya kasara shashinsa chak ya tsaya ganin kamar tana yi mai murmushi ta wara hannu wanta biyu da sauri zai kamota sai ta ɓace runtsai ido yayi jijiyoyin kansa sun fito rada rada tabbas shi da kansa yasan ba lafiya yake ba anya kuwa be zama dis order ba ta ko ina ya kasa haɗa son da yake wa nusaiba ta ko ina tayiwa mata fintinkau adai zamanin nan ba lallai a samu kamar ta ba
🤔
dakyar ya ja ƙafafuwansa ya dauko mukulli ya buɗe shiga yayi tsayawa yayi yana kallon ko ina na gurin kamar yau fa aka kawo masa ita a matsayin mata duniyar tunani ya lula


wai waye adon tafiya


wallahi nusaiba ji nake kamar na janyo ranar nan ta dawo yau


Ashraf ya faɗa yana kafeta da idanuwansa


kau da kai nusaiba tayi tana wasa da hijabinta tace


'' da yau da ranar juma'a duk ɗaya ce a gurin Allah, Allah dai ya kai mu da rai da lafiya...,




Anya kuwa ban fiki son mu kasance tare ba


rufe fuskarta tayi da tafukan hannayen ta tace


'' bansan da wanne baki zan kwatanta maka irin adadin son da nake maka ba..,


ni wallahi sweet anya kuwa wannan kunyar take zata bari ki nunamin son da kike min


jin gina tayi a jikin kujera tace


'' kaidai Allah ya nuna mana lokacin lafiya..,


sarkin wayo maganar ce bakya so ko


har abada bazan gaji da sauraron daddaɗar muryar ka ba ina rokar Ubangiji idan zaka mutu mu mutu tare bazan iya rayuwa idan bakai son ka shine jini na jikina kaga kuwa mutum zai iya rayuwa ba idan babu jini


lumshe idanuwa yayi sai kuma ya buɗe su yawa me jin bacci yace


'' nima bazan iya rayuwa babu ke ba Allah ya raya mu tare ya kashe mu tare..,


amin ya Allah


tashi yayi yace


'' zan shiga daga ciki lokacin da Hajiya ta diba mana ya cika tsoro take kar nayi aika aika..,


murmushi tayi batare da tace mai komai ba wallahi maganganun sa kunya suke bata ashe shima ba kanwar lasa bane a satin nan fa lamarinsa har mamaki yake bata kamar ba yayan da tasani bane me muzurai da tsare gida amma a yanzu kam ita sheda ce ko kallon da yake mata na zallar so ne magana fanake miki kinyi shiru ko na zo na raka ki dakin ki
Ashraf ya faɗa yana ƙara kafeta da idanuwansa


rufe baki tayi tana zaro Ido


UWAR GAFALALLU


EPISODE 8-9


PERFECTLY PEN'S


rufe bakin ta tayi tana zaro Ido tace
Please yaya ka rufan asiri ka tafi kar Hajiya ta biyo sahun mu wallahi Allah jiya faɗa tayo min sosai tace sai ta hana ni fita idan an kai ni gidan mayi kome za mu yi


dariya yayi ya nuna mata hanya yace


'' Hajiya kenan ta gama isarta ƙarshe dai dole ta kawo miki bissalam Allah ya tashe mu lafiya..,


nusaiba tace '' amin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login