Showing 3001 words to 6000 words out of 36805 words

Chapter 2 - Rainon Soja Book 3 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt

13 Jan 2025

3802

regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*








35~36
_________________________


Ɗan Gimtse fuska Jidder tayi tana caɓe baki tare da ƙoƙarin magana dai dai Mami na saukowa cikin shigar ta na kamala complete house wife. Yanzu fa Mami abu yayi sauƙi wannan shigar turawan an daina shi ba kullum ba . Sai dai har yanzu yanda take takonta kasan macece mai kamar maza Wato police ”. Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki tana ɗan karkacewa tare da kallon Hoton da suke kallo har da jidder wacce tayi tamkar yau ta fara ganin Ma'eesha a Duniya . That's my baby girl da nake baki labari Ma'eesha ta kenan! Mami ta furta tana faɗaɗa fara'ar ta . Caɓe baki Hajiya Hajara tayi tana kallon gyefen ta da shirin zama , don taji labarin Ma'eeshan tun kamin zuwan ta a bakin mutane da Dama . Sai dai kurum taji bata ra'ayin ta duba ga maganganun da jidder da faɗa mata akan yanda suke nuna soyayyar su ga yarinyar da basu san Asalin ta ba . Ganin tana shirin zama ne yasa Mami saurin dakatar da ita da cewa “ A'a Hajara anan kuma ? Mu shiga daga ciki ” . Hummmm ta numfasa tana kallon Bushira kana tace “ Ki jira mu ”. Tom Ranki ya daɗe ....Bushira ta furta tana yin ƙasss da kanta . Bin bayan Mami su duka suka yi Hajiya Hajara da jidder dake ta jin dadin Yanda Mom Hajara ta nuna akan Ma'eesha a Zuciyar ta tana cewa “ Ai ma Wani Abu sai Ya Haidar ya dawo dake zaki ci ubanki ne”.


Falon Mami na sama suka shiga inda suka yi ma kan su masauki , Gaba Ɗaya Hajiya Hajara ta sauya fuskar ta babu Annuri don da magana fal a Zuciyar ta gami da Wannan baƙuwar fuskar da ta gani a cikin a halin General Saleh Yelwa . Tum-tum mat ta zauna inda Itama mami ta zauna gaban su shaƙe da kayan motsa baki . Ita kam jidder Resting chair ɗin dake daga gyefe kaɗan ta nema ta zauna , tana zaman jiran mene zai fito daga bakin Hajiya Hajara. Don kaf dangi anyi ittifaƙi da Rashin kirkinta musamman idan Abu bai mata ba .


Dan Tsawa Mami tayi tana Binta da kallo , don ganin yanda ta lula Duniyar tunani yasa ta tuno da maganan likita don ba'a daɗe da dawo da ita daga India ba akan lafiyar ƙwaƙwalwarta , don a shekarun baya Ta samu matsala na mantuwa, inda a yanzu ma Wasu Kaɗan ne daga cikin rayuwarta na baya ta iya tunawa dashi , shine Rayuwar ahalinta. Ta ɗebi shekaru a wani ƙauyen Fulani tana rayuwa da mutane masu amana , sai kuma rana ƙwatsaaam ta tuna da Ɓangare na Rayuwar ta da Iyalanta wannan ne sanadiyyar dawowan ta har aka yi nasaran ganin ta. Fatan su a yanzu shine kar ta tuna da Abubuwa da yawa da suka faru , wanda ya haddasa masu baƙin ciki a rayuwar ta mara iyaka . Har kuma iya yanzu suka tuno da Wannan mutumi babu Abin da suke bin sa dashi sai ALLAH ya isa!


Hummmm Jan numfashi Mami tayi kana tace “ Hajara tunanin me kike yi haka ? , Da Wani Abu ne ?” . Sauke lemun hannun ta tayi tana mai dashi saman plate ɗin dake gaban ta . Kana ta kalli Mami fuska babu walwala tace “ Ina Boy? Ya girma sosai ko? ”.




Yana tare da Ma'eesha ina zai tuna da ke Mom? Ai idan suna tare bai ganin kowa , har gwara shi da Khalil ma , don ko me zata yi ba'a mata faɗa ”. Muryar jidder ya katse su wacce take latsa wayar ta tana kwararo zance . Ya ishe Ni haka! Kuji mun mara kunya dake ake yi ne? . Mami ta katse Ta cike da Tsawa , Wannan yasa Jidder kallon ta tare da kama bakin ta .


Haba Mamin Haidar Meye na wannan faɗan haka ? Jidder ce kike ma wannan tsawan nawa duka take ? Ai wannan zaki firgita mata tunani ne , Aƙwai shekarun da idan yara basu kai ba wani Hayaniya duka bai kamata da ayi masu shi ba. Tsayawa Mami tayi tana kallon Mom Hajara don bata yi wani mamaki ba ,don tasan halin Hajara da son nata. Cike da San yi ta furta “ Ta dame Ni da Ma'eesha tun da nake ban taɓa ganin masifaffiya irin jidder ba. Wai ita wannan Ma'eesha wacece? Kai Anya??? .


Mom Hajara ta furta tana bin mami da Wani irin kallo . Yarinya ce mai kyau hankali da tarbiyya momy ga haƙuri ba irin Wancen mummunan mai ƙaton Goshi ba .


Saurin juyawa Duka suka yi suna kallon hanyar shigowa inda Khalil ke takowa cike da takon sa . Fuskar sa Sake yana kallon ɓangaren da Jidder take ya watsa mata Wani irin harara da sai da ta shiga taitayin ta. Kallon su duka tayi kawai sai ta miƙe tana saka kukan sarganci da Gata tare da cewa “ Mami nafi shekara goma a cikin wannan halin hantarar da suke yi mun , tun da Ma'eesha ta shigo Rayuwar mu nake fuskantar tsana.....Kawai sai ta rushe da kuka da gudu tana juyawa tare da barin falon . Kyaji dashi halin ki zaki gyara. Mami ta furta tana jan ɗan tsaki tare da tsuwa tana gyara zama .


Zama Khalil yayi a kujeran da jidder ta miƙe kana muryar Hajiya Hajara ya katse su tana cewa “ Gaskiya Nima naji na tsani wannan Yarinyar haba..........!




Don Allah kar ki karanta mun idan baki biyani ba . Ga masu buƙatar payment regular payment ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 tare da shaidar biya evidence of payment .idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 .#Antymmnteddy.
[1/21, 8:10 PM] Real~Mamanteddy: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*








_________________________


*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*






*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*








37~38
_________________________




Gaba ɗaya kun fifita yarinya yar tsuntuwa ce fa? Meye kuke yi ne haka ? Gaskiya raina ya fara ɓaci yanzu zan tashi na bar cikin gidan nan , kuma dana san Wannan Zan taho na tadda da banzo ba . Hajiya Hajara ta furta tana miƙewa tare da Ɗaukar fankacecen Gilashin idon ta wanda ta Ajiye a gyefe . Sanin hali yafi sanin kama ,wannan yasa Mami saurin riƙo hannun ta , don ta san ta da zuciya irin na Haidar a yanda mami ke cewa ita ya ɗebo a saurin ƙufula da fushi . Habawa Hajara me yayi Zafi? Don Allah ki zauna . Yanzu ya gida ya kuma Hajiyar ta mu ?. Mami ta furta zancen cike da Sanyi da kuma rarrashi .


Ɗan jimmmm Hajiya Hajara tayi kana tace “ Kowa lafiya amma ba fa zaki gane kan gadona ba sai naji kin rarraso mun Jidder ta dawo mun cigaba da Hira ”.


Murmushi Mami tayi kana ta gyaɗa mata kai tana furta “ Shikenn Bara naje da kaina ma na rarraso Miki ita . Amma....Aaaaaammmm Khalil taho ka kira mun Boy yanzu tun da shi bai neme Ni ba . Hmmm. Wani guntun Numfashi Ya sauke , a hankali ya fara tuno da sihirtaccen ƙyawunta da Wannan murmushin nata . Gani suka yi ya saki Murmushi yana furta “ I miss You so much ”. 🤔To! Kai kuma da Wane? Matar da zaka Aura Maryam ko kuwa wacce kake magana? Mom Hajara ta katse shi tana bin sa da kallon rashin fahimta .


No mom , Ma'eesha nake nufi nayi kyawarta da Wannan murmushin nata.....mtswwwww! Mom Hajara ta ja dogon tsaki kana tace “ Anya Wannan yarinyar ba maƙiya ne ba suka jefo ta cikin gidan nan don wani mugun Abun?. Subhanallah! Mami ta furta tana ɓata rai ƙwarai wanda hakan yasa Hajiya Hajara miƙa masa waya tana cewa “ Kira mun shi yanzu ”.


Amsar Wayar yayi bai ce mata komai ba, don ransa sa ya fara sosuwa da maganan Mom Hajara ɗin . Gani tayi ya fara kiran Wayar Haidar ta Wayar sa , duk da yasan ba wani jituwa ke tsakanin su ba . Wata ƙil ya ɗaga ko kuma akasin haka ”.


**
Ɓangaren Aliyu kuwa yana Tsaye yana kange da Waya a kunnen sa suna Magana da Aminin nasa Areef wanda yake ta cewa “ Ina jinka, tun tuni kana ta Wani kame kame da fa magana a bakin ka amma kana mun shiru ya dai? . Ƙwanciya Areef yayi yana ɗan sosa ƙyayarsa don bai san ta ina zai fara masa bayanin lamarin ba . Mtswwwww! Dogon tsaki Ali yaja cike da fushi don bai san shiru Gashi dai ɓakin Miskili amma shi sam bai san ayi masa shiru wannan yasa shi cewa “ Zan kashe waya na fa”. I'm sorry Ali kana jina? . A'a ban jinka ”. Ya basa amsa dai dai yana kallon shigowar kiran Khalil amma ya watsar bai bi takai ba. Hummm Babban yayan mu kenan! Areeef ya furta yana wata yar dariya wanda Aliyu kai tsaye yace “ Kaje maganan ka Yallaɓai ”.


Hummmm Aliyu Ni kuwa nace kunyi ma Ma'eesha miji ne?🤔🤣ƙitttttt! Yaji Aliyu ya katse kiran , wanda shi kan sa bai san dalilin da yasa shi yin hakan ba . Bai tsaya kuma jin ƙarikon mai zaice ba ,don tuni ya fahimci inda ya dosa a kalmar sa guda ”. Tsayawa yayi yana cizan laɓɓansa na ƙasa tare da dunkule hannun sa Zuciyar sa na masa zafi da Huci. Me yasa sai Ma'eesha? Ya furta cikin Tsawa yana saurin juyawa tare da nufar Bedroom ɗin sa inda ya barta tana shan Cofee don shi titir a shan Cofee yake . Hummmmm! Da ƙarfi taji saukar Ajiyar zuciyar sa kana cikin sauri ta juyo tana kallon sa .




Mamaki ne ya kamata ganin yanda gumi ke karyo masa Wannan yasa ta miƙewa daga tsaye , amma sai da hannu cike da Wannan isan nasa ya dakatar da ita yana mata Alama da ta zauna . Babu musu ta ja ta zauna , Amma Bata daina kallon sa ba , haka bakinta ya kasa shiru wurin furta “ Uncle motsa jini kayi naga Gumi ne a fuskar ka da jikin ka?”. Girgiza mata kai yayi kamin a ɗan daƙile yace “ No”. To wannan gumin fa? . Cike da Arrogant voice ɗin shi ya furta “ I hate Norse ”. Gummmm tayi da bakin ta tana komawa tare da shan Cofee ɗin tana kallon sa a sace a sace . Keeeee!!! Kin ma iya Cofee? . Ya furta cike da neman ta da laifi don ya fanshe Haushin shi ya bata Wahalar don yau ji yake tamkar ya bugi banza! A ganin sa itace take sakar masu fuska har su samu damar tunanin son ta .




Kin iya Cofee?? Ya kara Tambayar ta fuska Gimtse babu fara'a . Dan kallon sa tayi tana lumshe lumsassun idanun ta kamin ta girgiza masa kai tana cewa “ Aa ban iya ba , Mami ke yi sai kuma yanzu kai da kayi mun . You Are very stupid , kina nufin Common thing Cofee baki iya ba???..........Good night lavs🫶🏻🤣🤣😻 yau dai Ma'eesha taga banu a hannun Aliyu , Allah ya ƙwaceta don yau da wuya bata daku ba . Mu tara a next page 39~40 .


*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biyani ba . Ga Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 Vtu transfer Kuma ta wannan number 09061466409*
[1/22, 1:35 PM] Real~Mamanteddy: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*








_________________________


*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*






*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*






39~40
_________________________


Yayi zancen yana wani irin haɗe giran sama da ƙasa . Kallon ta ya kuma yi a karo na biyu ganin yanda jikin ta ke tsuma da kyarma yasa shi cike da Miskilalliyar Murya wanda ba don tana gab dashi ba sam ba zata ji mene yake furtawa ba. “Cofeee??? Ya nanata cike da Muryar damuwa, kana yace “ Maza zauna ki haɗa mun Wani yanzu ”. A hankali ta zauna tana fara jan flask ɗin ruwan zafi kamin ta fara ɗaukar Cofee cup tana kallon sa a ido ido . Gimtse fuska yayi yana hura hanci tare da tattare gida . Wayyo Mami Daddy Uncle yau duka ne yake son yi . Ta furta a Zuciyar ta dai dai tana ɗagowa zata zuba sugar kenan taji tsawar sa yana furta “ Meye kuma na Damuwa a dai dai Wannan lokacin? ”.


Mtsww! Yar ƙaramar tsaki yayi yana kallon ta ganin yanda tayi masa ƙurrr da ido . Kin gama ne? Ya furta yana kallon cup din hannun ta. Sam ta manta da sugar a tunanin ta ta zuba ashe babu sai one tea spoon da ta sanya . Cikin Sauri ta miƙa masa tana ja baya , amsa yayi yana motsi da ƙafarsa kana yace “ zo ki mun massage! Ko shima baki iya ba?”. No! Na iya ,Ai ina yi ma Mami idan ta dawo Aiki ta gaji kuma tana cewa na fa iya sosai . Kauda kan sa yayi yana miƙar da ƙafansa tare da cewa “ Oya zo ki fara ”. Matsawa tayi da wannan lukutar jikin nata tana zama daga ƙasan carpet tare da Kama Ƙafarsa tana matsa masa a hankali. Laushin hannun ta ne yasa shi fara mancewa da damuwar sa . A hankali yake sauke Ajiyar zuciya, Wanda ita kan ta tunani ta fara yi kodai Allurar sojan ce zata motsa masa ? , Amma a haka cike da Ɗari ɗari ta furta “ Uncle baka sha Cofee ɗin ba?”.




A hankali ya ware Lulun idanun sa yana kallon fuskar ta dake fidda masa da Annuri , hummm jan numfashi yayi yana kauda idanun sa daga gareta tare da kai Cup din Cofee ɗin zuwa bakin sa . Ɗan kurɓa yayi ƙafan yayi saurin kallon ta yana Aje cup ɗin tare da furta “ Oh my God! Ma'eesha meye wannan kika yi? Wai da gaske Cofee baki iya ba? . Ya furta a matuƙar zafafe , kina mace ko Cofee baki iya ba bare kuma akai ma tea da Kayan karin kumallo . Yau zan shiga jikin ki da ƙyau zan yi maganin rawar kan ki . Ai kin iya soyayya!🤔. Cikin Muryar kuka tana shirin ƙwarma masa ihu ta furta “ Innalillahi wa.....yi mun shiru daga nan ko yanzu bakin ki yayi jini, ai baki da macece sai ALLAH daga Ni yau sai ke a cikin gidan nan .


Cikin dakakkiyar Muryar sa ya furta “ Oya! your knee should be Down ”.


Tuni kukan ta ya ƙaru tsoron sa ya ƙara kamata , zubewa tayi a ƙasa tana Ɗaura Gwiwowin ta bisa tiles ɗin falon tare da haɗe hannayen ta tana furta “ Don Allah Uncle ɗina kayi haƙuri pls uncle Aliyu Wallahi zan haɗa maka Wani me Daɗi kaji Uncle Haidar?”. Kamin ya bata Amsa ne kiran Khalil ya kuma shigo masa a karo na uku wannan yasa shi Ɗagawa a ƙufule yana furta “ What?”.


Yanda Khalil yaji Muryar sa yasa jikin sa ɗan yin sanyi , don yasan halin Ali kar yazo yana jin masifa ne ya sauke akan ma'eesha don wannan sababben sa ne , idan yana fushi to akan kowa sauke Haushin sa yake yi . Please Ali ka rage Faɗa , Ka tambayi ya nake? Ammmm.....Sorry ya akayi ? Muryar Haidar ya katse shi , wanda jin hakan yasa Khalil furta “ Ya kake? Ina amanar mu? . Ɗammm jim Haidar yayi kana ya kalli inda Ma'eesha ke matsar ƙwallah, cije labɓan sa yayi na ƙasa kana yace “ Khalil Amanar mu ko Amanata? Meye haɗin ka da ita? .


Saurin kallon sa Ma'eesha tayi tana furta “ Ya Khalil ne ?. Wani irin mugun kallo Aliyou ya watsa mata wanda ya sata ja baya tana cigaba da Abin da ya sata amma idanun ta basu sauka akan daina kallon sa ba .


Kai kana da matsala wallahi Aliyu , dama Mom ce tazo tana son magana da kai , sai ka bata Ma'eesha su gaisa kamin ku dawo ta ganta”. Ɗannnnnnnn ...................🫶🏻🙌🏻✍🏻.
[1/22, 6:36 PM] Real~Mamanteddy: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*






_________________________


*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*




*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*






41~42
_________________________


Ɗannnn jim yayi kana yace “ Mom Hajara ce? Bara na kira”. Kai da'alla malam dakata mana , gafa ta kuyi magana kana ƙoƙarin ɓata mun lokaci? kana Wani mun magana kaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login