Showing 24001 words to 27000 words out of 36805 words
Chapter 9 - Rainon Soja Book 3 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
ya furta yana ƙoƙarin miƙewa daga ƙayataccen kujeran da yake zaune . A'a Alhaji ka zauna ,kai da kake fama da jiki ,Bara Ni na leƙa na gani . Barau ya katse shi yana miƙewa. Girgiza kai Alhaji Adamu yayi yana cewa “ A'a ko ɗaya mu tafi dai tare zai fi ” .
A farfajiyar gidan Alhaji Adamu kuwa yan aikin gidan ne cike da su Hajiya Falmata da Turai matar Alhaji Adamu ta uku . Kowa na sallami tare da faɗin Albarkacin bakin sa bisa ga Ganin Basiru da suka yi ya zauna a ƙasa yana zunduma ihu tare da tsine ma Rabi , yana tona ashirin duk abun da suke yi , Tare da fashewa da kuka yana cewa “ Ashe tana da cutar karya garkuwar jiki HIV . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un......Kalmar da kake ji mata nayi kenan suna tafe hannu . Ihu yake yana karawa yana me yasa Rabi zaki mun haka ? Rabi kin cuce Ni.
Ran Malam barau ne ya ɓaci da tun da suka iso wurin basu yi magana ba suna sauraren duk abun da ke faruwa. Muryar Hajiya Falmata ce ya katse su tana cewa “ To ai sai a kira Uwar ɗakin ta Atika , tazo taji Ashe Ƴar ɗakin nata Cutar ƙanjamau take dashi. Tafe hannu Bibbiyu Turai tayi tana cewa “ To ko dai itama ƙanjamau ɗin ne da ita , Wannan jinya ta fara yawa......Ahirr! Ya ishe Ni haka!! Muryar Alhaji Adamu ya katse su cikin fushi da tsaye . Wannan wani irin shashanci ne kuke yi haka . Kowa ta wuce ta bani wuri. Nan take kowa ta juya , da makarƙabanta . Shi kam Barau cike da fushi ya faɗa Basiru da faɗa da zagin ƙwal kana yace “ Idan ba kai cikakken Mara kunya ba , ku gama lalata kazo kana faɗa mana anan uban me zamuyi maka. Wallahi duk ranan da ka sake dawowa cikin gidan nan sai na Saka An yi maka raga raga dukan da tun da uwarka ta kawo duniya babu wani mahaluƙi da ya taɓa yi maka tashi ka fice mawa mutane tantirin banza.
**
11:am (Lagos)
Jirgin su ya sauka .
Don dama da Wuri yake son su isa. Bin airport ɗin take da kallo . Kana ta kalli Aliyu dake sauka stairs ɗin idanun sa cikin baƙar gilashin nan nasa na Rashin kirki . Murmushi yayi mata yana kai hannun sa tare da riƙo nata, a hankali ya ɗan rage Tsawon sa zuwa saitin kunnen ta yana furta “ Ina sonki Ma'eesha....Allah ya taimaka mami ta Bani ke da ƙyaaar...” Huwwwmmm Numfashi ta sauke ba tare da tace masa komai ba , don a yanzu duk wannan surutun nata ta ne meshi ta rasa. Ko me yasa?🤔 .
Wani irin kallo tayi masa cikin sauri tana bin Motocin da ta gani na sojoji da kallo , kaman Wani Shugaban ƙasa. Motoci ne kusan 12 , guda 7 duka sojoji ne a ciki ....Wayyo Uncle mu gudu sojojin nan fa basu da imani baka fuskokin su ba? . Ta furta maganan ita sam ta manta Uncle ɗin nata fa Soja ne babba. Don a gida take ganin sa bata san shi ba a waje. Hannu tasa tana shigewa jikin sa tare da ƙanƙane shi tana furta “ Uncle tsoro nake ji bindigogi ne fa a hannun su”. Murmushi yayi yana yin ƙasa da Muryar sa kana yace “ Babu abun da zasu yi Miki kin manta Uncle Aliyu shima soja ne ? Mu tafi kinji ki saki jiki. Cike da Yarinta ta sakin masa murmushi don ita sam ta manta ta burkice gaba ɗaya . Oho yanzu na tuna, to mu tafi. Ta furta tana kokarin sauya hanya ba inda Sojojin suke jiran su ba .....Hannun sa yasa yana riƙota tare da nufar motocin nasu, Ma'eesha kuwa duk...............!
[1/28, 5:24 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
70-71
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Duk ta rikice sosai ta manne da jikin sa , gani tayi sojojin na ƙame masa wasu na buɗe masu moton , ita ta fara shiga , kana ya shima ya shigo daga baya yana zama tayi saurin ƙwantar da kan ta bisa ƙirjinsa. Murmushi yayi yana kai hannun sa tare da Shafa bayan ta a hankali ya furta “ Ashe dama kina da Tsoro, ai na ɗauka masu surutu irin naki basa da Tsoro haka”. shiru tayi tana ƙara maƙale masa kana tace “ Uncle ba dai Laifi mukayi ba ko?”. Duk da shi ba mutum bane ma'abocin dariya amma a wannan karon sai da ya dara . Kawai sai ya girgiza kai yana ɗaura laɓɓansa a saman Goshin ta yana sumbatar ta . Abun da Ma'eesha ba ta sani ba shine , wannan tafiyar da sukayo na masa ƙarin matsayi ne zuwa Major a soja. Mami da Daddy sun san da hakan , amma ita Bata sani ba sam , kuma ganin yana da mata yasa Mami a wannan karon cewa su taho taren da Ma'eesha zai fi . To pah yanzu Ma'eesha ta ga rundunar sojoji to ya zata yi kuma kenan? Gashi a Bisa abin da bata sani ba ma sam.
A wani irin babban wuri taga motocin sun tsaya. Inda Aliyu ya ɗago yana kallon ta tare da shafa fuskar ta yana ɗan sakar mata murmushi. Ki dakata anan yanzu zan je na dawo ”. Ya furta yana miƙa ƙafarsa tare da ficewa daga cikin moton yana barin Ma'eesha da take ta bin wurin da kallo .....Mutane ne sun fi yawan da ba zasu ƙirgu ba . Duk da sojoji sun fi yawa kowa da kakin sa . Wannan ya tabbatar mata da taron sojoji ake yi. Dan komawa tayi ta ƙwantar da kan ta jikin seat ɗin tana furta “ ai Uncle ka zaɓa ma makanka zaman lafiya , ina zan fito a wannan rundunar jibi yanda kowa ya riƙe bindiga yazo a harboni a kashe banxa, ko a rashin sani ne ko da gangar Soja ya kashe ka fa an ce ya kashe banxa a wofi , ai gwara na zauna anan Allah ya taimaka kaima ALLAH dai ya dawo da kai.........tunanin ta ne ya katse sakamakon ganin Aliyu Haidar da tayi ya buɗe moton yana cikin kakin sa na soja ,bayan sa sojoji ne ke bin sa. Taho muje daga can mu zauna😲”. Taso ta ce a'a ,amma ganin sojojin dake bayan sa yasa ta saukowa a hankali tana gyara mayafin kannta da tayi rolling don dama ita Tafiye saka Abaya for all the time kayan sun fi burgeta ko a yanzu wani Black abaya ne jikin ta Wanda akayi masa Adon flower da red. Zama tayi a tare dashi a wani side da ban da aka ware masu , inda take bin komai na Wurin da kallon tsanaki. Zaman su kenan taji an fara kiran sunan Uncle ɗin nata kamar haka “ MAJOR ALIYU SALEH YELWA...” kallon sa tayi a maimakon taji an yi tafi sai gani tayi Sojojin suna masa fareti na girma tare da Sarawa suna ƙamewa . A hankali yayi mata magana a kunne yana mikewa cikin zumma irin nashi tare da nufar can high table. Ita dai har yanzu ta kasa fahimtar inda wannan al'amuran suka dosa. Major naji fa yace ? Ba Canonel bane ? Yaushe ne Uncle ya koma Major kuma? .hummm Numfasawa tayi tana kallon direction ɗin can da yake . Kana ta kalli inda ya miƙe yanzu. Saurin kai hannun ta tayi tana Ɗaukar littafin da ta gani da alama ya manta dashi ne . Diary book.! Ta furta a sarari kana ta riƙe tana cigaba da jin jawabinsa da Manyan General a sojojin ke yi tana saurara . Kusan mintuna sha biyar kana ta buɗe Lemu tana fara sha don ta fara gajiya da zama .
“.....Humwwwmm Sauke numfashi tayi tana kai hannun ta haka kawai tare da buɗe diary ɗin a cewan ta zama ya isheta sai tana ganin sa tamkar story book ne. A lokaci daya fuskar ta ya sauya idanun ta da take lumshe su tana ƙara ware su. Farko kuma mafari~ ta ga ya rubuta da shekara ta 2008 . Wannan shine fara rubutun diary book Dina na farko a duniya a wannan shekara . A ranar wata Talata na........Labarin Ta ne ciki tun daga Farkon yanda ya tsinceta da yanda yayi Rainon ta . Kai har murmushi idan tayi ko taci Abu sai ya rubuta yau Ma'eesha na taci Abu kaza kuma taji dadi ,nan gaba Irin shi za'a rinƙa yi mata . Yau Ma'eesha ta fara zuwa skull da dabara na irin na kaza da kaza. Kar ka takaf labarin duk abun da ya faru take karantawa , Wanda kamin tayi Rabi tuni ta jiƙe da hawaye har da su sharɓan majinu tana sharewa da Hanckie . Wani irin kuka ta fashe dashi tana furta “ Why dad! Me yasa zaka nemi kashe shi , Ni baku kashe Ni ba? Kuka dinga azabtar dashi ....Wayyo Ni Ma'eesha ta furta tana sakin kuka a hankali mai taɓa zuciya da karya ta. Saurin juyawa tayi tana juya baya yanda Ali ba zai iya hangota ba tana cigaba da karanta diary ɗin .....”
**
Bin Nasreen da kallo Mami ke yi inda take karkaɗa a tsakiyar falon ta . Mamaki ne ya kama Hajiya Hajara wacce bata daɗe da isowa gidan ba . Keeee wacece ke? Kalmar da Jidder tayi kenan cike da Tsiwa da masifa irin nata . Wani irin kallo Nasreen ta watsa mata , kana ta saki Murmushi na yan bariki tana cewa “ Ayyya ƙanwata Yayan naki Haidar bai taɓa baki labarina ba , ikon Allah! To sunana Nasreen , kuma nice matar da zai Aura nan kusa!
Topa! Jidder ta furta a wulaƙance tana bin Nasreen da wani matsiyacin kallo . Kana tace “ ammm To munji zaki iya tafiya ko sai na saka an fitar dake babu mutunci ?” . Jidder! Mami ta furta tana ƙoƙarin magana Hajiya Hajara ta katse ta da cewa “ A'a ai barta tun da itama tazo mana da rashin kunya ai sai ayi maganin ta . To ko Ali ya rasa mata ba zai Aure ki ba , ai gwara mara Asalin da ya Aura akan ki , don ko ba komai mun san halinta mai kyau da ko mara kyau . Amma ke ji bita da Allah , Mom Hajara ta furta tana bin Attachment ɗin kan Nasreen da kallo .
Ke dattijiwa shiga taitayin ki , idan ba haka ba zan nuna Miki ƙarshen rashin kunya ta! Kamin ta rufe baki ne jidder ta ɗaga hannu tana tsinke fuskar Nasreen da mari ji kake tassssss dai dai Khalil wanda ke shigowa yana furta “ Da ƙyau.....! masifa!
Ni kika mara ? Kin san Wacce Ni Nasreen? Ko ke Wacce an mare ki , aka ce miki ina ɗaukar wargi ne ke Wacce da zaki shigo har cikin gida ki nemi cin ma iyaye na mutumcu and kina expecting ki fita kisha lafiya . To ko iyayen ki ne basu isa ba bare ke!
Jidder ta furta cike da Masifar ta .
Murmushi Mom Hajara tayi tana cewa “ Khalil ku fice mun da Wannan mara kunyar yarinyar , Sannan Ni da iyayen ta xanyi , a cikin a wa biyu nake so ku bin ciko mun komai nata , Dama ance ɗan kuka mai ja ma uwa da uba . Zaki san wacece Hajiya Hajara , zaki ga yanda iyayenki zasu taho su dafa ƙafana su na bada haƙuri fice mun da gani tabbatacciya”. Mom Hajara ta furta cikin Tsawa , inda Nasreen dake dafe da kunci ta furta “ Zan fita , amma wallahi rayuwar ku sai na jefa ta cikin masifa, sannan kuma ba zaku taɓa gane kan gadon ɗan ku ba har abada , sai dai idan ya Aure Ni zaku ma ku gani”.
[1/28, 8:12 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
72-73
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Tana furta hakan da sauri ta juya cike da ƙafa tana ficewa daga falon . Bin ta da kallo mami tayi kamin ta furta “ Ikon ALLAH! Wannan yarinyar daga ina take haka? Kar ki damu Mami kiyi Haƙuri, zan sa a binciko mun naga yar gidan uban waye? . Khalil ya furta yana janye idanun sa daga hanyar da Nasreen ta wuce . Mom Hajara ce ta furta “ a yau nake so ba sai gobe ba! Murmushi Khalil yayi yana furta “ Kiyi Haƙuri Momy yau inshallah ”. Juyawa yayi yana bin bayan Nasreen don shima ran sa sosai ya ɓaci da ita .....Bin bayan sa Suka yi da kallo Mami na sauke wani irin gwauron Numfashi kana tace “ Ya tabbata Ali yana kula watsatstsun mata irin wannan yarinyar kenan? . Ta furta zancen tana kallon su tare da faɗawa cikin wani irin yanayi na daban.
Kallon ta jidder tayi tana kallon mom Hajara wacce itama har a lokacin take cika kana tace “ Ƙwarai mami to kina tsammanin Ya Khalil ba gaskiya zai faɗa ba kenan ?”. A'a ba haka nake nufi ba , Kar ki manta Khalil na son ma'eesha a jikina ina jin Haidar na yin wani abun amma ban taɓa kawo masa wannan cikin rashin jin sa ba .
Gimtse fuska Mom Hajara tayi tana gyara Zaman mayafin ta kana tace “ Ohhhh wai ke Mamin Haidar bakya taɓa magana ne ba tare da kin saka sunan ma'eesha ba? Komai Ma'eesha Ma'eesha haba don Allah....! Ita yarinya wata can ƙasa gajera ga ƙiba mara sha'awa mtswww.....” ta ja dogon tsaki tana komawa tare da zama bisa kujeran dake kusa da ita .
Uhm”. Jidder ta furta tana ɗaga ƙafarta tare da cewa “ Mom sai kinyi haƙuri , Ai wannan ma kaɗan ne tun da bata gurin , suyi ta mata ɓarin jiki kamar wacce aka ce Aljannar su na ƙarƙashin ƙafafunta . Ni yanzu zan tafi 1:30pm muke da shiga exam .
Ɗagowa Mom Hajara tayi tana kallon ta kamin ta kalli ƙaton agogon falon , ba distance learning kike yi ba ? . Yessss Mom shi nake yi , Amma exam kin san aƙwai wasu da dole sai Mutum yaje hall ya rubuta . Ok Allah ya bada Sa'a . Amin Jidder ta furta tana gyara mayafin ta . Kana ta kalli mami tare da hugging ɗin ta “ Bye bye mom sai na dawo ”. Ta furta tana ficewa daga Falon .
Murmushi Mom Hajara tayi cike da son nata ta furta “ Yarinya mai hankali kenan! . Kallon ta Mami tayi tana caɓe baki kamin ta zauna , Muryar Mom Hajara na cigaba da cewa “ Kin ga har Khalil yasa an binciken yarinyar , Ga taxt din shi ya shigo . Ohk duba ɗiyar Wacece? Mami ta furta tana kallon Mom Hajara wacce take scrolling chart ɗin. Ɗan gyara zaman medical Glass din ta tayi kana tace “ Waye Alhaji Adamu Billionier ? Wai inkiya ɗin sa kenan .
Kallon ta mami tayi tana furta kai anya Alhaji Adamu Billionier ina dai jin sunan sa kamar ɗan kasuwa ne babba , amma ban tabbatar ba gaskiya . Ƴar sa ce kenan? . Girgiza kai Mom Hajara tayi kana tace “ eh a abin cikar da aka yi ba. Amma yanzu zamu sani ai ...daga gobe zasu bata wadataccen tarbiyyar da idan taga mutane zata san yanda ake masu magana da dadin lafazi ”.
**
Gaba ɗaya Ma'eesha ta gama birkicewa kuka take yi kamar ran ta zai fita . Ƙoƙarin controlling kan ta take yi amma ta gagara , Wayyo Uncle ban ƙyauta ba , na zalunce ka , ban maka halarci ba ban kuma maka Adalci ba . Ka yafe mun Uncle.............🥹 Tana maganan tana jin yanda yake jawabi ta Mick cikin Arrogant voice ɗin nan nashi na jarumta . Muryar sa ta ji yana kiran sunan ta wanda gaban ta sai da ya faɗi....cikin sauri ta fara dai daita natsuwar ta tana rufe diary ɗin kana ta goge hawayen fuskar ta wanda bata tsammanin zasu iya daina zuba har ta isa gare sa ”. Ƴammata da manyan mata kowa a wurin crushing ɗin Wannan soja ake yi , wanda in his young age ya zama major . Da dama na tambayar baya da mata ko? Suna jin an ce eh sai ko wacce ta kara gyara zama tana jiran a gama taro ta amshi card numbern sa .
Cike da Wannan takon nata with confidence na RAINON SOJA take takawa ixuwa inda Yake . Gaba ɗaya hankulan mutanen ya dawo akan Wannan kyaƙyƙyawar yarinya wacce ta shige zuƙatan mutane da dama . Sunan murmushi take yi amma wasu irin hawaye ne ke bin kuncinta wanda ta rasa fahimtar na menene ita kan ta . Nishaɗi take ji ko akasin haka , ga narkakkiyar tausayin sa dake tsuma ta . Ƙanwar sa ce hala? Kaji wurin an fara maganganu ƙasa ƙasa . Wow she's beautiful.....Muryar Aliyu ne ya kuma katse su inda suka ji ya yi magana ta Mick da cewa “ That's my wife ❤️ uuuwhmmmmw💋 ya hura mata Wani irin sumbata a Mick ....ihu aka