Showing 48001 words to 51000 words out of 105124 words

Chapter 17 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

18956

yayi zan fita"
Mufeeda a ranta tace


"Yaya Ammar manya maganin ƙanana, na gane Lagon ka sarai, Jambakin nan da gashin nan ba ƙaramin tafiya suke da kai ba"


Ta kamo hannun sa tace
"Yau Friday ya kamata a yanke maka farce" bece komai ba ita kuma ta ci gaba da wasa da yatsun hannun sa, can ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa takai hannun ta fuskar sa tace
"in taɓa?"
"in kika taɓa sekin biya"
"dan Allah sau ɗaya fa"
"kika isheni sena aske gemun nan"
"aikuwa idan ka aske na dena kulaka, dan ina son gemun nan sosai"
Ammar yace
"tashi ki kawomin Abinci"
Ta tashi ta kawo masa Abinci, ta haɗa musu Tea, zata sa masa Madara yace "bar madarar nan ki shanye abarki, naga ta kusa ƙarewa"
"Se insha tea da Madara kai kuma ka sha ba Madara?"
"Eh kece 'yar gayu ai, ni ban damu da shan me Madara ba, kiyi Addu'a Allah ya hore kafin ta ƙare in siyo wata"


Shiru tayi tana kallon sa, duk faɗan Ammar yana da sauƙin kai Sosai, kuma yana matukar ƙoƙarin ganin ya wadata da Abinci, baya bata Abinci mara daɗi, ko alawar da tayi jiya da madarar be mata faɗa ba.


"Allah ya ƙara maka Arziki na halal My love"
"Ameen" ya amsa mata.


Suka kammala karyawa, ta ɗakko nail cuter ta yanke masa farce tsaf.


Ammar yace "in Allah ya kaimu ranar Saturday zamu ɗan fita, Umma nata mita har yanzu ban kaiki ba"


"Wayyo Allah daɗi, Allah ya kaimu lafiya nima na ƙagu ka kaini in gansu"


Wasa2 Ammar seda ya kusa makara zuwa masallaci saboda yadda Mufeeda ta narke masa a jiki take ta zuba taɓarar ta iri2.


Se azahar sannan yai wankan juma'a ya fita salla.




******************


Fa'iza taga abubuwa sunƙi tafiya yadda take so, ta kuma wanke ƙafa ta tafi gidan Yaya Jidda, suna ta hira Fa'iza fa sako maganar gidan Ammar
"Nikam Yaya Jidda kinje gidan Yaya Ammar kuwa?"


"hmm ina fa naje, idan naje gurin wa zani gurin wannan ƙwailar Yarinyar kokuwa? Bani da lokacin su daga shi har ita"


"Amma ai gidan ɗan uwan ki ne Yaya Jidda ya kamata ku dinga zuwa kiga a wani hali hake ciki? Idan kuma ya tattara ya koma gurin ta gaba ɗaya fa, ku kuma ko oho kenan?"


"Aini bana son zuwa inga abunda ze ɓata min rai, ranar da nayi masa magana akan wulaƙancin da tayi muku, seda mukayi faɗa dashi ya kare ta"


Fa'iza tace "kinji abunda nake gaya miki ko Yaya Jidda wallahi ki dinga zuwa, idan ba haka ba ana ganin ƙanƙantar ta da haka zata raba shi da kowa, tunda tun yanzu ya fara goyon bayan ta"
Jidda tace "kuma fa hakane, zanyi ƙoƙari inje gidan nasa, zan kuma yiwa umma maganar ta ja masa kunne, akan ya kula da 'yan uwan sa, dan nasan ita zata gaya masa yaji ko kuma Maryam, in be ga dama ba idan Maryam ta faɗi magana ze rusa maganar uban kowa ya ɗau tata, duk wannan masifar tasa ita baya yi mata"


Fa' iza tace "haba dai Yaya Maryam ɗin?"
"ita fa, ai baya shiri da kowa a cikin mu kamar ita, indai Maryam na san abu ze hana kansa ya hana uban kowa ya bata"
Jinjina kai Fa'iza tayi, a ranta tace "dole inje in ziga Yaya Maryam itama, zata taimaka min"
Suka ci gaba da hirar su daga nan suka yi sallama.




A hanya Fa'iza tana tafe tana zancen zuci akan ya zata ɓullowa lamarin Ammar, taji ana mata horn tsayawa tayi ta juya, me motar yazo dai2 inda take sannan ya sauke baƙin gashin motar yace
"Manya maganin ƙanana, ke kuwa talaka na ganin ki"
Murmushi tayi tace "Ba gashi ka ganni ba, yaushe rabon da in ganka?"


"Shigo motar se muyi magana" ba musu ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shige.
Ya kalleta yace "Ni ko a bikin Ammar ban ganki ba ina kika shiga haka?"
Tsaki ta ɗanyi tace


"me zanje inyi masa a gurin bikin, dan abun kunya kuna gani kuka barshi ya auri wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar, bayan a duniya ya tsani Auren ƙaramar Yarinya"


"kinfi kowa sanin Halin sa ɗan uwan ku ne, ke zaki gayawa wani halinsa, shekaranjiya na haɗu da shi da matar tasa ya kaita Asibiti se zuba shagwaba take yi, Wallahi Yarinyar nan za tayi saurin tafiya da Imani namiji, duk jin kan Ammar lallaɓa ta yake ranar, ina ga ko ciki ne da ita "


Wani dogon tsaki ta ja tace
"dan Allah ka dena ɓata min rai, dan abun kunya 'yar wannan Yarinyar Ammar zewa ciki, mtseww"


Dariya sosai Faruk yayi yace "Kai
Fa' iza, to shi kna ruwan sa, Wallahi tun ranar ɗaurin Aure da naga yarinyar nan na kasa samun nutsuwa, wallahi dana ga Yarinyar nan kafin bikin su da bazan taɓa bari Ammar ya aure ta ba, Idan naga Yadda take wa Ammar shagwaba wani irin kishi ne yake kamani, Wallahi ina jin ƙaunar yarinyar nan har a cikin zuciya ta"


Wani irin Murmushi Fa'iza tayi tace "dagaske kana son ta"
"Wallahi Fa'iza ina mata so bana wasa ba, ni ko ban Aure ta ba kawai dai in same ta, kin gane ai balle ma ina son in Aure ta, wallahi tunda naganta mata ta dena birgeni"


Jinjina kai tayi tace
"Me ze hana mu haɗa kai mu taimaki juna?"


Ya gyara zama yace "kamar Yaya kenan?"
Murmushi tayi tace "zamuyi waya"




********************


Kasa nutsuwa Yaya Jidda tayi, dan haka ta tambayi mijin ta zata fita unguwa, shiryawa tayi ta tafi gidan su Ammar.


Koda Mufeeda ta buɗewa Jidda ƙofa taga kammanin ta da Ammar, sannu da zuwa tayi mata tai mata iso ciki, wani irin kallon banza take bin Mufeeda dashi.


Tun kafin Jidda ta shiga falon idon ta ya sauka akan jibgin kayan Abincin dake ɗakin tsakar gida, tayi ƙwafa suka shiga falon.


Ta kalli Mufeeda tace
"Ina Ammar ɗin?"
"be daɗe da fita ba kuma, yana gida tun ɗazu, amma se in kira shi a waya"


"Ammar ɗin da yake fita tun farar Safiya shine yake zaune a gida har bayan azahar sannan ya fita"


Shiru Mufeeda tayi tace "bari in kawo miki ruwa"


"Ke dawo bana son gulma, ni bazan sha ruwan ki ba, sannan ki buɗe kunne da kyau ki jini, Wallahi daga yau idan wani daga dangin mu yazo kika kuma masa wulaƙanci sekin bar gidan nan dan baze yuwu ba, 'yar mitsitsiya dake kin san wulaƙanci, su Fa' iza sa'anin kine da zasu zo ki musu rashin mutunci, ko gidan uban kine? "


Mufeeda ta girgiza mata kai alamar A'a, Mufeeda a ranta tace" wannan ce Jidda kenan? "


" to ko yanzu yai niyya ze iya sakinki ya auri wata, 'yan uwa kuwa ba' a canza su, ance miyar ki hadda kaji alhalin be kaiwa namu iyayen ba, shafaffiya da mai, ni ina tunanin kin haɗawa Ammar da ƙulumboto dan Ammar ba sakaran namijj bane, daga zuwan ki ki kainainaye shi, kalli uban kayan Abincin daya tile miki a ɗaki, Amma iyayen mu ko oho, se anyi magana yace bashi da kuɗi ina ya samu kuɗin daya siya miki wannan kayan haka? Algunguma baki isa ki rabamu dashi ba"


Jidda taiwa Mufeeda cin mutunci tsaf, Sam Mufeeda bata tanka mata ba, se dai zuciyar Mufeeda kaman ta fashe, ga Jidda ta girme ta sosai balle tace zata rama.


Seda ta gama sannan ta tashi ta tafi, bayan tafiyar ta se da Mufeeda tayi kuka dan ba ƙaramin jin zafin abunda Jidda tayi mata tai ba.




Ammar ne ya dawo ya tarar da ita a falo, ba haka ya saba ganin ta haka ba in ya dawo, amma ya basar ya miƙo mata leda yace


"gwada wannan takalmin in gani ɗazu na ganshi yayi kyau na siyo miki"


Ƙoƙarin maida hawayen idon ta take, Ammar ya ga idon ta da ƙwalla, ya ɗan haɗe rai yace
"kukan me kike yi?"


"bakomai bafa kuka nake ba"


"bana son ƙarya, meke damunki?"


"bana jin daɗi ne"


A fusace yace "ƙarya kike lafiyar ki ƙalau, meya same ki? Bana son ƙarya"












Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S











Page 16


Ƙura mata ido yayi, a hankali tace "bafa wani abun damuwa bane, radio nake ji aka faɗi wani labari daya bani tausayi, shikenan fa bari in gwada takalmin nan dan tun kan isa na hango ƙafa ta tayi cif a ciki"


Ammar yabi Mufeeda da kallo ba dan ya yadda da abunda tace ba, amma ƙiri ƙiri ta basar da zancen ta karɓi takalmin ta saka, na zaman tsakar gida ne amma kalar pink ne me tudu yayi kyau sosai, ta miƙe ta ɗanyi juyi tace
"yaka gani yayi min kyau kuwa?"
Gyaɗa mata kai yayi,
tace "Nagode mijina Allah ya baka gidan Aljanna"
"Ameen ya Allah"


*****************


"Maman Sadiq maƙociyarki me kallon gidan ki ta shigo miki kuwa? "


Maman sadik tace "Hmm ta shigo min maman Amir ke kin ganta wata 'yar yarinya da ita, amma mijin ta baki ganshi ba ƙato da shi, ni ba dan na ganta kalar wayayyu ba da cewa zanyi a ƙauye ya auro ta"


Ɗayar tace "dan Allah ta shigo muku? Ranar da ta shigo muku ina ga bana nan, kaddai' yar Yarinyar da naga ya sata a a daidaita sahun sa ce matar?"


Maman Amir tace "Wallahi itace maman Nur"


"Taɓɗijan niko zanso in ƙara ganin ta"


Maman Sadiq tace "ke kina ganin ta 'yar Yarinya se shegen ji da kai, watan ta guda a unguwar nan fa sannan ta shigo mana, tana wani jin kai a gurguje ta tafi, nace kin gamin yarinya da kinibibi,' yar da da auren wuri aka min na haifeta"


Maman Nur tace "Kedai bari da mijin nata wata tsiyar ne da shi da ta ɗaga mana kai, amma duk layin nan shi ne matsiyaci ɗan adaidaita sahu ne fa"


Maman Ameer tace "kema dai kya faɗa"


Maman Sadiq tace "Maman Nur ya kamata akaiwa maƙociyar tamu ƙyallen Ankon sunan ki na haihuwa"


Maman Amir tace "wallahi kuwa mu kai mata muga meza tace"


Maman Nur tace "haka za'ayi ɗakko ƙyallen muje"


Suka ɗakko ƙyallen Atamfa suka nufi gidan Mufeeda.


Tana tsakar gida tana aikace aikacenta aka buga ƙofa cikin ƙaramar Muryar ta tace
"waye?"
Suka amsa da "mune".


Ta buɗe musu ƙofa suka shigo, tun daga tsakar gidan suka fara ƙarewa gidan nata kallo basu yi zaton cikin gidan ta yana da kyau haka ba.


Tai musu iso cikin falon ta suka gaisa, ta kawo musu ruwa da ɗan abun motsa baki na garar ta, nan suka dinga ci suna zuba surutu, ita dai Mufeeda sam bata da saurin sake wa da mutane dan haka sedai ta kallesu tayi murmushi kawai.


Can maman Amir tace "yawwa Mufeeda dama ƙyallen ankon sunan Maman Nur ne muka kawo miki ko mai gidan ze sai miki"


Mufeeda ta karɓi ƙyallen ta gani tai murmushi ta miƙa musu tace


"Aikuwa Atamfar tayi kyau sosai, se dai ni da ban daɗe da Aure ba kayan lefe na na nan ko taɓawa banyi ba, sedai ince Allah ya rabaki da cikin lafiya, idan kika haihu zan sako abunda Allah ya horemin in shigo inyi miki barka"


Ɗan buɗe baki maman Nur tayi tace "kodai me gidan ne baze miki ba, amma Atamfar fa babu tsada dubu biyar ce fa"


Mufeeda tace "Anty kenan aike yanzu kinfi buƙatar Addu'a fiye da wannan Atamfar, kuma insha Allah zan saki a Addu'a Allah ya raba ki da cikin nan lafiya"


Maman Sadiq tace "ai insha Allah zata rabu da cikin nan lafiya, duk 'yan layin nan za suyi fa anko zamuyi, mene dan ya miki lefe kwanan nan, ke yarinya bari kiji mazan yanzu ba' a tausayin su, ki zage duk abunda kike so ki sashi gaba seya miki"


Murmushi sosai Mufeeda tayi tace
"to nikam se an jimanku zan shiga kitchen, nagode sosai da shigowar da kuka yi"


Ta tashi ta barsu a falon, suka fito suna mamaki gami da zage zage.


Maman Sadiq tace "yau naga kinibabbiyar yarinya, wani wai kinfi buƙatar addu'a akan anko ji munafuka"


Maman Nur tace "ke niba wannan ba ina mijin ta ɗan a daidaita sahu ne, kawai base naga saman fridge ɗin ta da kayan shayi ba hadda su butter ga biscuits da kayan daɗi, naga dai bata haihu ba amma data buɗe fridge zata ɗakko mana ruwa hadda chocolates a cikin fridge ɗin, wallahi raina ya biya, bari gobe in Allah ya kaimu aikawa zanyi ta sanmin milo"


Maman Amir tace "hmm kedai bari muda mazajen namu suke da sana'oi da suke samun kuɗi rabona da baban Amir ya saimin kayan shayi tun haihuwar Amir yanzu yara na uku, danma ba kiga ɗakin nan na tsakar gida ba ke kinga kayan Abinci kamar a kanti?"


Maman Nur tace "wallahi shiga gidan zan dinga yi nida yara, a dinga shan madarar nan damu"


Maman Sadiq tace "in kinga fuska muma semu biyo ki"


Suka cigaba da gulmar su dai


**********************


Mussaman Jidda ta shirya ta tafi gida, domin ta ziga Umma akan Auren Mufeeda da Ammar.


"Umma wallahi Idan ba'a tsaya akan Ammar ba, wallahi ze zama mijin tace, su Fa'iza basu gaya miki abunda yarinyar nan tayi musu ba"


Umma tace "A'a nidai sunzo nan Halima ta rakasu gidan Sa amma ba su dawo ta nan ba"


"to sun biya gida na, sun gayamin yadda ta dinga musu wulaƙanci"


Halima tai farat tace "Wallahi ƙarya sukeyi, tare fa muka je ba wani wulaƙanci da tayi musu"


Jidda tace "dan ubanki dake nake magana? Ko kuma ƙanwar uwaki ce da zaki goyi bayan ta?"


Tura baki Halima tayi tace "ai ni gaskiya na faɗa"


Umma tace "to ni Jidda na kasa gane inda maganganun ki suka dosa sam, wani irin wulaƙanci ne haka?"


"wallahi Umma rashin mutunci ta dinga yi musu, kuma da naje gidan ta baki ga kayan Abinci ba kamar abun banza, kashe mata kuɗi yake kaman kaman me amma ku nan baya kawo muku, se anyi magana yace ba shi da kuɗi"


Umma tai Murmushi tace "To meye a ciki dan ya kashe mata kuɗi matar sa cefa, kuma Ammar ko be mana a yanzu ba a baya yayi mana balle har yanzu Ammar yana iya ƙoƙarin sa akan kyautata mana, Jidda lokacin da mahaifinku yake da shi na wata ya ya kashe min kuɗi kaman babu gobe, shi ba mace ce ta haife shi ba? Ko kuma lokacin da yake kashe mana kuɗin meyasa ba kiyi complain cewar be kyauta ba? Ina yanzu keda 'yan uwanki kuma' ya'yan wasu kuke aure kuma suke muku hidima, dan me za kuce ɗan uwan ku baze wahaltawa wata ba? Ai abun Alfaharinku ne ace ɗan uwan ku ya auro 'yar mutane kuma yana iya riƙe ta, nikam Alhamdilillah Ammar har yanzu yana ƙoƙarin kyautata mana, kuma ni ina ƙaunar ta, Dukda murɗaɗen hali irin na Ammar duk da yadda bashi da tarin dukiya tace tana sonsa a haka ni ta gama yi min komai ina ƙaunar ta"


(ƙalubale gareku iyaye, haka ya kamata ku zamo masu adalci ga matayen 'ya' yan ku, dukda wasu sirikan basu da kirki, amma da yawan lokuta ƙannen miji da yayye suke jawowa matar ɗan uwansu a gurin iyayen su, su faɗi abunda akayi da wanda ba'ayi ba suce anyi, ku kuma iyaye babu binki ce babu komai ku hau kai ku zauna, Allah ya kyauta)


Jidda tace "Shikenan Umma tunda baki yadda ba, zaki gani da kanki wataran ai"


********************


Ammar ya dawo ya shiga ɗakin sa, ƙaton flower Mufeeda ta zana da sunan sa da Nata, gefe tayi rubutun kalaman Soyayya ta ajiye masa akan gado ɗan girgiza kai Yayi a ransa yace


"sam Yarinyar nan bata rabo da shiriri ta"


Ya fito falo ya tarar da Abincin sa sedai be ganta ba, yayi tunanin ko tana wani abun ne, dan haka ya zauna ya fara cin Abincin sa, sam Abincin baya masa daɗi saboda babu Mufeeda a kusa dashi balle taita masa wannan shirirtar tata, yana gama ci har ya tafi ɗakin sa ya dawo ya duba yaga ko tana lafiya, yana buɗe ɗakin ta ya tarar tayi ɗaiɗai akan gado tana bacci, ta tafi ƙarshen gado wanda idan tayi ƙwaƙwƙwaran juyi zata iya faɗowa, kome ya sata bacci da wuri haka oho?


A hankali yaje gaban gadon nata da niyyar ya gyara mata kwanciyar, yana ɗagota ta firgice ta saka ihu.


Rirriƙeshi tayi tana zare ido, yace
"Ke menene haka? Nine fa"


Ajiyar zuciya tayi ta lumshe ido tace "wallahi ka bani tsoro, wani ɗan jaririn ƙadangare ne ya shigo gidan nan shiyasa na taho ɗaki fa"
tai maganar tana kwanciya a jikin sa.


"Yanzu Jaririn ƙadangaren ne yasa kika dawo ɗaki kika kwanta hadda rufe ƙofa?"


"eh mana idan kuma ya shige min ɗaki fa?"


"Shikenan cikani zanje in kwanta"


Ta ɗan kalle shi tace
"kaci Abinci kuwa?"


"Naci kwanciya zanyi yanzu"


Ta langaɓar da kai tace "nifa yau ban ganka sosai ba"


"Nifa bana son rigima, cikani ki koma baccin ki"


Wani irin kallo take masa, lumshe ido take alamar akwai bacci akan ta sosai amma Ammar gani yake kaman da gayya take masa wannan kallon.


"I love you sweetheart" shine abunda ta furta masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login