Showing 51001 words to 54000 words out of 105124 words

Chapter 18 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

18964

a hankali.


"Naji, karki manta gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri zamu fita"


Jinjina masa kai tayi tana lumshe ido, ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita sosai akan filo ya fita ya koma ɗakin sa.


Daya koma ɗakin ma tuni ta dafa masa ruwan wankan sa kafin ta kwanta, da zafi sosai ya haɗa ruwan yayi wankan, sannan ya samu guri ya kwanta, tunani yake da ƙoƙarin sama wa kansa mafita akan zaman sa da Mufeeda, baze yuwu su ci gaba da zama a haka ba dan ba ƙaramin cutuwa yake ba, yana mata kallon Yarinya ƙarama amma a lokuta da dama kasancewar su tare yana ƙara jefa shi cikin wani hali, lallai salon da take amfani da shi yana matuƙar tasiri ga zuciyar 'yan mazan.


Haka yaita tunani har yayi bacci.


Da safe Mufeeda tana ta ɗoki zata fita, watan ta biyu a gidan nan amma sau ɗaya taje Asibiti sekuma maƙota data shiga, Suna gama breakfast ta saka Ammar a gaba suka ware kayan Abincin gara da su rarraba da wanda zasu tafiwa da su Umma, har na su Yaya Maryam seda da su Jidda seda ta ware masa, ta rarraba kayan zaƙin nan na alkaki ta warewa kowa nasa hadda wanda ze bawa abokan sa su Jabir su bawa matan su.


Ammar ya kalle ta yace "Ai wannan kayan da kika rarraba sunyi Yawa, saboda ke aka kawo be kamata ki kwashe ki rabar ba, wanda zaki bawa su Umman ma ya isa nagode"


"Abunda kaci kashi ne wanda ka bayar shine rabon ka, ka sani ko dalilin bayarwar da mukayi Allah ya ninka mana, ai abun duniya ko ka bayar ko baka bayar na seya ƙare"


"Amma babu wanda zaki bawa a family ɗin ku? Be kamata ace kin rabar da kayan nan haka ba"


"Ai kowa seda aka bashi kafin a kawomin, kaga wannan ai ya ishemu kaima kwana biyu seka huta, Allah dai ya ƙara maka buɗi babban mutum, ciyarwa ba aikin rago bane, kana ƙoƙari sosai seka huta kafin su ƙare"


"maganar hutu ai babu shi tunda na riga na ajiye ki, dole in fita in nemi abunda zan riƙe ki, kaman yadda yake a shari'a"


Miƙewa tayi tsaye tace "kana ƙoƙari mijina, Allah ne kawai ze biyaka ladan ɗawainiyar da kake, Allah ya ƙara Arziki, bari inje in shirya karmuyi rana"


Ya jinjina mata kai, ta koma ɗakin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, tayi to match da mayafin ta da Jakarta, Mufeeda akwai Gayu, da ta fito falo Ammar be fito ba ta bi shi ɗakin sa, tana zuwa ta tarar ya shirya yana ƙoƙarin saka links ɗin hannun rigar sa.
Da sauri ta ƙarasa inda yake, ta fara ƙoƙarin saka masa tace


"Babban mutum kayi kyau sosai kaman in sace ka in gudu"


Kallon ta kawai yake ba tare da yace mata uffan ba, amma itama tayi kyau sosai, amma sam ba tayi kama da matar Aure ba.
Ta ɗakko turare ta feshe masa jikin sa, tace
"Allah ya barni da abun sona har ƙarshen Rayuwa ta" ita dai duk wani motsi da zata yi se tayi masa Addu'a kokuma tayi masa kirari, kota nuna masa irin soyayyar da take masa, lokuta da dama har mamaki take bashi.


Haka ya shiga gaba tana binsa a baya, suka kulle gidan suka fita, Ammar idan ya fita tare da Mufeeda baya ɗaukar passenger.


Seda tasa Ammar ya tsaya suka saiwa su Abba Fruit sannan suka tafi, Basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar, Mahaifin Ammar yana tsakar gida yana jin radio suka shiga da Sallama.


Abban Ammar yana ɗaga ido, Mufeeda ya fara kallo ganin su tare da Ammar yasa ya gane itace Sirikar sa, Murmushi yayi yace
"barka da zuwa Yarinyar kirki sannu da zuwa sirika ta"


Har ƙasa Mufeeda ta durƙusa tana murmushi ta gaida Mahaifin Ammar, shima cikin dattaku ya amsa mata, yace
"Zauna mana sirika ta" gefen tabarmar Abba ta zauna


Ammar ya ɗanyi gyaran Murya yace "tunda ni baka maraba da zuwa na, bari in koma"


Abba yai Murmushi yace "ni ai ka daɗe muna tare, ni nayi 'ya dama ba a Auta da namiji babarka tayi Auta da kai, ni yanzu ga auta ta nan"


Ammar yace
"Aikuwa zaka ga halin Auta kam"


Murmushi Mufeeda tayi tace
"dama shima ɗan auta ne?"


Abba yace
"ƙannensa uku ne suka rasu, kinga kuwa shi ne ɗan Auta"


Dariya Mufeeda tayi, Umma ce ta fito daga ɗaki hannun ta ɗauke da carbi, alamar sallar walha ta yi, tace


"Yau Allah yayi an kawo min Mufeeda kenan? Tun ina magiyar har na gaji"


Nan ma cikin girmamawa Mufeeda ta gaida Umma, ana haka Halima ta shigo daga aiken da aka yi mata, tana ganin Mufeeda ta fara murna tace


"Anty Mufeeda ashe zaku zo ɗin tun ɗazu nake kallon hanya"


"Yaya Halima ni na makarar damu ai, Amma ai gashi munzo"


Duk rashin saurin Sabon Mufeeda yadda iyayen mijin ta suka karɓeta ba ƙaramin yi mata daɗi yayi ba, sun nuna mata karamci da dattako, jinsu take kaman iyayen ta, sosai ta sake suna hira, anan Har hira ta kawo Abba yake gaya mata yana kiwon dabbobi a kangon jikin gidan sa, nan suka shiga hira sosai har Mufeeda take nuna sha'awar ta akan kiwo.


Yadda take hira da iyayen sa cikin mutuntawa kaman iyayen ta ba ƙaramin burge Ammar yayi ba, Ammar ya miƙe yaje Napep ɗinsa ya kwaso kayan Abincin da suka zo dasu da Yadda aka kasafta kayan.


Abban Ammar yace
"A ina ka samo wannan kayan haka Ammar?"


"Dama kayan garar Mufeeda ne"


Abba yace "gara kuma Ammar? Ina fatan ba zuwa kayi kace se an maka gara ba, dan nasan halin ku matasan yanzu akan gararar nan se kuyi wa mace gori dan abin kunya" Abba ya ɗanyi maganar a hasale.


Wato Abba halinsu ɗaya da Ammar, sam basa son aga gazawar su, musamman akan abunda yake haƙƙin su ne suyi shi.


Mufeeda tace "A'a Abba, da cewa yayi ma baze karɓa ba, Baba ne ya kawo haka yake yi duk wadda ya aurar ya bata gara, Amma dan Allah kayi haƙuri ba shi yace a kawo ba"


Abba ya kalleta ganin kaman ba taji daɗin yadda yayi wa Ammar ɗin ba, yace "Hmm zaki kare mijinki ko? To ni a yanzu yamin laifi zan iya zane shi ma"
Sunkuyar da kai Mufeeda tayi tana murmushi, daga nan yayi musu Nasiha da Addu'oi.


Seda Mufeeda tabi Abban Ammar ya nuna mata yadda dabbobin sa da yake kiwo suke, a cikin maganar sa zaka gane tsohon ɗan boko ne, Ga Mufeeda da shegiyar tambaya, duk abunda ta tambaye shi se yayi mata bayani dalla-dalla. .




Bayan tafiyar Mufeeda Abba yace "Ammar kana surutan cewa Kai tayi maka Yarin ta, to a manyan da kake hange da wuya ka samu Yarinya me hankalin ta, dukda nagani tana nuna ƙuruciyar wasu lokutan amma ka bita a hankali Yarinya ce me biyayya, ina jin nauyin ta ne amma ba dan haka ba seka koma da kayan Abincin nan, ka kula da matar ka, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta da yake kanka"


Ammar yace Insha Allah suka yi Sallama da Abba ya bar Mufeeda a gidan su.


Bayan tafiyar Ammar ya kira Halima a waya, tana ɗagawa yace
"kiyi wa Mufeeda kitso kafin in dawo ɗaukar ta"
Ta amsa masa da "to"


Mufeeda da Halima ne suka zage suka tsiri alkubus, Yadda Mufeeda take aiki ba ƙyuya babu ganda ba ƙaramin bawa Mahifiyar Ammar mamaki tayi ba.


Da azahar suka kammala girki, suka gyara ko ina, aikuwa sunyi santin girkin nan sosai, Halima tayi wa Mufeeda kitso ƙanana masu kyau ba tare da ta gaya mata Ammar ne yace ayi mata ba, Bayan sun gama kitson Kuma tai mata jan lalle, kaman wata amarya tayi kyau sosai.


Ta samu food flask ta ɗibarwa Ammar Abincin, ta ajiye masa se bayan sallar isha'i sannan Ammar yazo ɗaukan ta, taji daɗin wuni a gidan su Ammar dan sun mata kara suka nuna tamkar su suka haifeta, sosai suka karrama Mufeeda.




Da zasu tafi Abba ya kira Ammar ya nuna masa Akuya Aure ɗaya da kaji masu ƙwai yace ya bawa sirikarsa, za'a cigaba da kula mata dasu anan.
Ammar yace "ba shakka an gode, to ni wanne ka bani?"
Abba yace "kai sau nawa ina baka dabba, idan kaza ce ka yanka ka cinye abarka, ai bazan kuma baka ba"


Mufeeda tai murmushi har ƙasa ta durƙusa tana yiwa mahaifin Ammar godiya.
Abba yace "bakomai 'yar Auta, Allah ya baku zaman lafiya ya ƙara muku ƙaunar juna, muma mungode sosai"


Umma ma seda ta haɗawa Mufeeda su tsintsiya da manyan jakar omo, sannan suka yi sallama.


Seda Ammar ya biya da ita gidan Yaya Maryam ta gaishe ta, taita mita akan meyasa be kawo ta da wuri ba se a daren nan, suka bata nata kayan da suka kawo mata sannan suka tafi gida.


Suna komawa Mufeeda ta gabatar masa da Abincin da tazo dashi, seda Ammar ya kwashi girki ya ƙoshi sannan yace
"waye yayi girkin nan?"
"Nice" ta bashi amsa


Ya basar yace "shiyasa beyi daɗi ba"


Ta kalle shi tace "Abba dai yace yayi daɗi"


"Ai dan karki ji babu daɗi ne yasa shi cewa yayi daɗi, amma babu daɗi"


Seda yaga ya ƙoshi ya wani fara beyi daɗi ba, tattare Kwanukan ta fara yi tana tura baki, se yanzu ya lura da hannun ta da yayi Jawurrr da lalle, ƙurawa hannayen ta ido yayi, ta kwashe Kwanukan ta, ta kai kitchen ta wanke tai tafiyar ta ɗaki.


Ƙin zama tayi a falo, shi kam Ammar dariya ma ta bashi, ita a dole fushi take.


Har ƙarfe goma Ammar yana falo yana kallon wani Film a Bollywood, ba zato babu tsammani yaga Mufeeda ta ɗare cinyar sa, shi a zaton sa tuni tayi bacci, se ƙamshin turare take, rigar ta ta bacci iya gwiwar ta, kanta babu ɗankwali se bakin ta da take shan sweet.


Ammar yace "Ya haka?"


"Na kasa bacci, kuma naji kana kallo shi yasa na fito"


Ammar kaman ze kuka yace
"kinga ɗagani banyi shafa'i da wuturi ba"


"in muka gama kallon base kayi ba"


"waike baki san yanzu lokacin sanyi bane? Ba'a son yawan taɓa ruwa ba?"


"to ba se in dafa maka ruwan alwala ba"


A ransa yace "wannan 'yar yarinyar in banyi dagaske ba yauma seta hanani bacci"


Dan haka ya haɗe rai yace
"Malama ki ɗaga ni"


Maimakon ta ɗaga shi, sema ta gyara zaman ta ta miƙe ƙafafuwan ta akan nasa, kaman yadda yayi ta jingina bayan ta a ƙirjinsa ta ci gaba shan alawarta da zuwa yanzu bakin ta ya zama ja jawurrr saboda kalar alewar.


Daskarewa yayi a gurin ya kasa magana balle ya motsa, lallai yau ya ƙara tabbatar da tsagwaron yarinta akan Mufeeda, Ammar yayi ƙam dashi kaman gunki, sun kusa mimtuna goma a haka, ko a jikin ta kallon ta kawai tame.


Ta fara taune alawar nan a bakinta, sekuma ta janye ƙafafuwan ta ta juyo ta kalle shi tace
"Au naman ta ban maka bismillar alewa ta ba gashi na taune ta, bari in tafi dan na fara jin bacci"
Ta miƙe da nufin ta tafi amma ba zato ba tsammani Ammar ya janyo ta.


Abunda yayi ne yai matuƙar bata mamaki, dan ko a mafarki batayi zaton hakan ba.


Seda Ammar yasa baki ya shanye alawar da ta tauna a cikin bakin ta tsaf, sannan ya cika ta ya miƙe kamar beyi komai ba ya wani maze ya haɗe rai yai tafiyar sa ɗakin sa


(🙄🙄 to su Yaya Ammar manya)










Ashe dai kuna son littafin nan haka? Ai ban sani ba seda nayi tsallaken update na rana ɗaya nasha tambaya.
To yaseen in ba Comments posting se Allah ya kaimu Monday.
Ina godiya masoya da addu'oinku da kuma shawarwari.


Domin gyara, sharhi ko shawara ƙofata a buɗe take
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )








*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com





ELEGANT ONLINE WRITER'S











Page 17






Binsa tayi da kallo har ya shige ɗakin sa, tashi tai ta koma ɗakin ta, tana ƙara mamakin abunda Ammar yayi mata.


Da safe harta tashi ta gama breakfast be fito ba, tana ƙarasa gyara gida ne ya fito yana wani basarwa, Mufeeda ta kalle shi tace
"barka da Safiya Babban Mutum"


Be amsa ba se jinjina mata kai da yayi, ya nemi guri ya zauna, ya fara breakfast ɗin sa yana wani mazewa, murmushi take yi tasan abunda ya faru jiya ne yasa yake ta wannan basarwar.


Seda ya gama ta koma kusa dashi tace "Hubby kalli lalle na yayi kyau kuwa?"
Kallon hannun yayi da zuwa yanzu ya fara zama maroon, ya gyaɗa mata kai, amma bece komai ba.


Ta kawo masa breakfast ɗinsa ya fara yi, yanayi yana wani mazewa gaban sa taje ta zauna ta zuba masa ido ya ɗago idon sa ya sauke a nata yace


" Se kinsa na ƙware kike min wannan kallon haka?"
"A'a bazaka ƙware ba, kallon Soyayya ne sedai ka ƙara jin daɗin Abincin, A bani a baki mana duk randa ka ciyar da ni da hannayen ka masu tarin Alkhairan nan nafi ƙoshi fa"


Hararar ta yayi yaci gaba da antaya loma, tayi ƙasa da murya tace
"haba Autan Abba mijin Autar Baba, ba dan halina bafa kaga ni Yarinya ce zanyi maka kuka fa"


"ga guri nan maza zauna kiyi kukan, tunda ke a rayuwar ki Kuka kamar jin daɗin sa kike yi"


Tura baki tayi ta riƙe hannun sa


"dan Allah baby ka bani a baki, nice fa Jaririyarka ce seka barni da yunwa?"


Kallon ta yake yadda take ta zuba taɓara.


Ammar ya haɗe rai yace
"kinga idan baki bari ba zan tashi yanzun nan in bar miki gidan"


"Allah in baka bani ba zanƙi cin Abincin yau"


"to karki ci mana cikina ko naki?"


"cikina ne, Amma ni bazan iya zama ina kallon abun ƙauna ta beci Abinci ba, dama nasan baka sona"


"Dama na taɓa cewa ina sonki ne?"


"Baka taɓa cewa kana sona ba, Amma nasan ana sona ko ba a gayamin ba na riga na sani"


Kallon ta yayi ta ɗago itama ta kalle shi tare da kashe masa ido.


"Ni dai bance ina so ba, saboda a yanzu dai raino kawai nake yi, ni banga abun so a gurin ƙwaila ba, banda rawar kai da Yarinta babu abunda kika iya"


Ta gyaɗa kai tace "Shikenan nagode, Nikam har zuciya ta idan nace ina sonka, to ina nufin abunda na faɗa"


Ta miƙe ta koma kan Kujera tai shiru, ƙarshe ma ta kwanta ta rufe idon ta, Yanayin yadda yaga ta yine ta ɗan bashi tausayi, Amma dai bece mata komai ba ya kammala breakfast dinsa, kaman ya miƙe yaje yai haramar Fita, se yaga be kamata ya tafi ya barta tana fushi ba duba da Yadda take shiga damuwa idan taga baya walwala.


Hannunsa ya Miƙa ya ɗan ja yatsan ƙafar ta, a hankali ta buɗe ido ta kalle shi,
"Sakko in baki Abincin, kar inje kice bana baki Abinci"


Ba tace komai ba ta Sakko tazo gaban sa ta zauna, Yanayin Fuskarta ya nuna ƙirirs take jira tayi kuka, dan ba ƙaramin haushin abunda Ammar ya faɗa taji ba.


Ya haɗa mata abun karyawa ya kalleta yace "dawo nan" ya nuna mata inda zata zauna daf dashi, ta matsa ta zauna ya fara bata Abincin a baki tana ci.


Ya ɗan girgiza kai yace "Rigumammiya kawai se kace 'yar Yaye"


Tura baki tayi tana sosa gefen fuskarta, tamkar irin shagwaɓaɓɓun Yaran nan.


"Na ƙoshi fa"


"kin ƙoshi wa kike nufi ya cinye ragowar ki?"


"To ai na ƙoshi cikina ya cika"


"ɗan wannan Abincin ne kika ƙoshi, oya buɗe bakinki ki cinye sauran"


"Allah in kace se naci zan iya yin Amai"


Haɗe rai Yayi yace "kenan ɗan wannan Abincin kikeci shiyasa ba kya ƙiba, sekin cinye"


Hannu tasa ta ɗaga rigarta tace "kalli fa cikina ya cika sosai"


"Nagani rufe" ta sauke rigar ya ɗan ƙura mata ido sannan yace
"Allah ya shirye ki"


"Mekuma nayi?"


"A'a bakomai Addu'a kawai nayi miki"


Ƙarshe Ammar ne ya tattare Kwanukan, dan yau rikici take ji sosai.


Yana shirin fita ne yaro yayi Sallama da yake yau gidan a buɗe yake, Mufeeda ta amsa ta fito tsakar gida, ta kalli yaron tace


"Ya akayi ne?"


Ya miƙo mata kofi yace "wai gashi inji Umman mu wai dan Allah ki ɗan zuba mata madara da milo zata sha tea, idan kina da Butter ki ɗan san mata taci bredi"


Mufeeda tace "ayya ka koma kace mata dan Allah tayi haƙuri, bani nake siyan kayan ba, me gidan ne yake siya kuma bana bayar da abu seda izinin sa"


Yaron yace "to" ya juya ya tafi.


Ta koma falo tana tsaki,Ammar da yaji yadda suka yi da Yaron yace


"Meyasa baki basu ba? Kefa kikace abunda ka bayar shine rabon ka"


"hmm Yaya Ammar kenan, ina sane na hanasu, kai baka san wannan rainin hankalin na wasu matan ba, ranar suka shigo nan suka nemi su rainamin hankali dan sun ganni ƙarama, Yanzu dana basu shikenan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login