Showing 60001 words to 63000 words out of 105124 words

Chapter 21 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

18988




Page 19


Binta da ido Ammar yayi, a fusace yace


"baki da hankali ne? Meye hakan kikayi? Ɗazu kin jefomin waya na ƙyale ki yanzu kuma kin fasamin waya kin kyauta kenan? Wace irin Yarinya ce ke haka? Wane irin hali ne wannan? "


Ta ɗago manyan idanun ta ta kae shi tace
"Nice bani da hankali ko? Nagode bani da hankali na Yadda"
ta juya da sauri tabar masa falon, binta yayi da kallo yana mamaki, ta masa laifi kuma tayi fushi


(Nikam nace ashe babu daɗi, mutum yayi lefi ya maze ya ɗorawa abokin zamansa laifin da gangan"


Har Ammar ya kammala shirin sa ya fice be kuma ganin ta ba, shima da ya fita be dawo gida ba se bayan magariba, bayan magariban ma daya dawo bega Mufeeda ba, ta ajiye masa duk abunda ya kamata wanda ze buƙata, amma bata falon.


*************


Washegari bayan fitar Ammar sannan Mufeeda ta fito falon, ta kammala ayyukan gidan ta zata ɗora girki amma taga bata da kayan miya, gashi bata kula Ammar ba balle ta gaya masa babu kayan miya, shiryawa tayi ta fita yin cefane, tunda ta fito kan babban layin taga Wata ƙatuwar Mota tana binta, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya.


Taje gurin Sa'idu me kayan miya domin Siyayyar kayan miyan, Sa'idu yace
"ko kece Amaryar kusa da gidan Maman Nur?"
"Eh Nice" ta bashi amsa a taƙaice.
"Allah sarki, da alama naga ke ba irin halinku ɗaya ba, kina da nutsuwa da hankali, amma yakamata ki kula sosai kiyi taka tsantsan dasu dan basu da kirki sam basu san ciwon kansu ba"
"to ni jna ruwa na? Ko tambayar ka nayi?"
"A'a naga kina da nutsuwa ne, shiyasa nace bari in miki magana kiyi hankali da su"


"Malam dan Allah bana buƙatar jin wannan maganganun naka, ka sallameni in tafi dan Allah"


"to shikenan, amma ni gaskiya na gaya miki"


Tsaki Mufeeda tayi ta karɓi kayan miyan ta tace
"Riƙe gaskiyar ka bana so" tai gaba abunta.


Biyo bayan ta me motar nan ya ci gaba dayi yana mata horn, juyowa tayi domin ganin dalilin da yasa ake mata horn bayan ta bashi hanyar daze wuce.
Parking me motar yayi, me ya buɗe murfin Motar ya fito, Babban Mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in da biyar, ya ƙaraso inda Mufeeda take yana wani ƙarama ta kallo yana murmushi, Sanye take da dogon Hijjabi tun daga Sama har ƙasa, ya gyara tsayuwar sa yace


"Baby tun ɗazu nake binki, ina ƙoƙarin yi miki magana amma ban samu dama ba"


Banza tayi masa tana ƙoƙarin wucewa, Ya kuma shan gaban ta kaman zasu haɗe yace "Haba 'Yar kyakywa, ya ina miki magana kinƙi saurara ta, ki tsaya kiji dame nazo mana"


"Malam meye hakane? Nifa matar Aure ce ka dena bi na dan Allah"


Kallon ta yayi daga Sama har ƙasa yace"Ke ɗince matar Aure? Nima ai mijin Aure ne, dan Allah ki bani lokacin ki two minutes kawai Beb, Akwai saƙo me girma da nake ɗauke dashi daga zuciya ta zuwa gare ki dan Allah ki saurareni mana, Kyakywar Baby kamar ki nasan bazaki wuce your sixteen age ba, baki dace da tafiya a wannan ranar ba"


A fusace ta kalle shi tace "Tir da Wannan saƙon naka, mara mutunci Ka kiyaye ni na gaya maka ina da Aure dan me zaka dinga bina haka? Wallahi zan maka tijara in taraka mutane a gurin nan na gaya maka, dalla ban hanya wuce dattijon banza kawai, wanda be san darajar Aure ba"


Ganin Mufeeda ta haƙiƙance ne yasa ya bata hanya karta tara masa jama'a, aikuwa da gudu2 sauri2 ta ƙarasa gida se haki take.


Duk abun nan daya faru akan idon Sa'idu me kayan miya, riƙe baki yai yana jinjina kai, Yace


"Au dama duk ustazancin nata na ƙarya ne, ance me Napep ne mijin ta me kuma ya haɗa ta da wannan me motar? Taɓɗijan mata na abunda suke so a duniya, Fuska biyu da rana tsaka lallai yau akwai zazzafar Jarida a majalissa" Nan ya ci gaba da ƙanan surutan sa.


Koda ta koma gida, mita ta ci gaba dayi da mamakin maganganun wannan shashashan mutumin mara mutunci, Seda tayi salla ta huta sannan ta ɗora girki, loka2 idan ta tuna abunda mutumin nan yai mata ta kan yi tsaki.


Sosai take missing ɗin Ammar, tayi kewar murmushin sa, da sauran Nishaɗin da yakan sata, amma idan ta tuna abunda Zainab ta dingayi masa ranar, da kuma Yadda take kiran sa a waya se haushi ya kamata.


Yauma ya gaji sosai bayan isha'i ya dawo gida, gaba ɗaya kwanakin nan da Mufeeda ta watsar da shi se yaga gidan yayi masa faɗi, gidan baya masa daɗi, kosan fitowa falon ba yayi ko Abincin ya fara ci se yaji baya masa daɗin ci, gashi yanzu duk wanda ze bashi Abinci inba na gidan sa ba ba yajin daɗin sa.
Abunda yake ƙara bashi mamaki be wuce Yadda take takatsan tsan gurin kiyaye ɓacin ransa ba, Amma ƙiri Ƙiri tayi masa laifi amma ta maze tana fushi, to zuwa ze ya rarrashe ta ko kuwa?
Wata zuciyar tace "kai aikuwa daka faɗo wannan 'yar Yarinyar zaka bawa haƙuri, ita fa tayi maka laifi"
Wata zuciyar kuma tace masa "But at least ya kamata kasan halin da take ciki" haka yaita saƙe2 a ransa.


Seda yayi Sallar isha, har ya zauna ze ci Abincin ya fasa ya miƙe ya nufi ɗakin ta, ya tarar da ita tana zaune a tsakiyar gado tana wasa da gashin kanta data tsefe, yai Sallama ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, tunda ya shigo ɗakin yaji yana tashin wani sasanyan ƙashi me daɗin gaske.
Ya tako a hankali ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, yayin da ta maze ta basar dashi kaman yadda yake mata a wasu lokutan idan yana fushi da ita.


"Wai Fushin me kike yi hakane?"
"Bakomai" ta bashi Amsa
"Kin min laifi kin koma kina fushi, Allah ya shiryeki, tashi muje kici Abinci"
"Ni na ƙoshi"
Haɗe rai yayi ya ƙura mata ido, juyawa tayi ta sakko daga kan gadon tana tura baki, ta fice falo.
ɗan girgiza kai yayi yabi bayan ta.


Ammar ya takura ta ta dinga cin Abincin nan badan ranta yana so ba dan har ƙwalla tayi, yace idan tai masa kuka ze ɓata mata rai sosai.


Suna cikin haka Wayar sa ta fara ringing, Idonta ya sauka akan Sunan Fa'iza da ke screen ɗin ƙaramar wayar sa, miƙewa Yayi ya tafi ɗakin sa Amsa wayar.


A ɗan hasale ya ɗaga wayar yace
"Ke lafiya kike kirana yanzu? Meye hakan kikayi?"
"Bakomai Yaya Ammar bugowa nayi in kwashi gaisuwa kawai, Sannan kwana biyu baka zo gidan mu ba"
"Abunda zaki gayamin kenan ya hana ki kirani tun rana?"
"to ai nasan lokacin kana aiki"
"Yanzu kuma ina hutawa ne, karki ƙaramin haka na gaya miki" yayi tsaki tare da kashe wayar sa yace
"Wannan wace irin takura ce? Mutum yayi Auren ma be huta ba? Da suke damuna da kira ni ina naga halin kuma Auren wata macen? Yanzun ma inji da rigimar wadda nake tare da ita mana" yai ta mita ya fito falo


Koda ya dawo falon ya tarar bata nan, Kwanukan yadda ya tashi ya barsu haka itama ta barsu a gurin, shi ya tattare Kwanukan ya kai kitchen, ya tsaya yana wankewa dan ya lura bata barin ko cokali ya kwana bata wanke ba.


Yana kammala wanke wanken akan ɗauke wuta, harze wuce ɗakin sa ya ƙyaleta ya jiyo sheshsheƙar kukan ta ta Window.


Ƙofar ɗakin ta ya tura ya shiga, ya kunna fitilar ƙaramar wayar sa ya haske ta, duk tayi jifa da fulullukan dake kan gadon ta, ta baje gashin kanta se sheshsheƙar kuka take, haushi ne ya kama shi, daze balbaleta da Masifa se ya tuna tunda suke bata taɓa masa makamancin haka ba, idan har ya ƙyaleta a haka be kyauta ba gata Yarinya ƙarama.


(Gareku Maza, ya kamata a dinga yiwa Mata Uzuri a wasu lokutan, idan har ya kasance mace tana kaman ta kyautatawa, wani lokacin ta birki ce saboda ɓacin rai ayi haƙuri a kai zuciya nesa, kar kace zaka hau ka ƙara mata tension, ka danne taka damuwar hankalin ta ya kwanta tukuna)


Ammar yaje ya kwaso fulullukan da tayi watsi dasu a ƙasa ya mayar da su kan gadon sannan ya hau gadon.
zuba mata idanu Yayi yana haskata yama rasa ta ina ze fara.
Gajiya tai da kallon da yake mata, ta zame ta kwanta ta juya masa baya, kashe fitilar wayar Yayi shima ya kwanta ya matsa kusa da ita dai dai Kunnen ta Yace
"Waike wace irin rigimammiya ce haka? Kinmin laifi baki bani haƙuri ba, kika fasa min waya bayan baki san da wa nake waya ba"


Gaba ɗaya jinta tayi wani iri Yadda suke kwance a guri ɗaya yake mata magana.


Ta dake tace
"Nasani mana, da 'yan mata kake waya"
"Shine kike fushi dan nayi Waya da
'yan Mata? Ai bani na kira su ba, su suka kirani fa"
Banza tayi masa ta ƙara matsawa gaba.
Aikuwa Ammar ya ƙulu yasa hannu ya fizgota yace
"Ni kike wa wulaƙanci dan ina lallaɓa ki, ranar da nake Waya da Maryam nake magana, kije kiyi abunda kika ga dama"
Jiki a sanyaye ta riƙe Hannun sa


"Yaya Ammar ɗina, Nasan nayi maka laifi amma ban san a wannan karon me yasa na kasa haƙuri in karɓi laifina ba, Yaya Ammar ina shiga damuwa idan naga wata ta raɓeka, ina iya jure komai amma banda wannan, dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba, Wayar ka ma dana Fasa kayi haƙuri please, ka karɓi tawa kasa layin ka seka bani ƙaramar in riƙe, kayi haƙuri kaji "


" bana son wayar ki, ai bani na sai miki ba"


"Eh nidai naji ka karɓi tawa please"
Shiru Yayi bece mata komai ba yama rufe idon sa, miƙewa Zaune tayi tace


"Dan Allah Yaya Ammar badan halina ba, kayi haƙuri Insha Allah ko dawa zakayi waya bazan ƙara maka haka ba, yanzun ma sharrin sheɗan ne"


tai maganar tana riƙe hannun sa, ɗisar Hawayen ta yaji a hannun sa ya ɗan kalleta, dukda a duhu ne tayi kalar tausayi, tayi regretting har zuciyar ta.


A hankali ya janyo ta jikin sa yana taɓa gashin kanta dake matuƙar birge shi, amma bece mata komai ba.


"Yaya Ammar ka haƙura?"
Shiru ya kuma yi mata.
Cikin Muryar Shagwaba me cike da Yarin ta tace
"Dan Allah kace ka haƙura"
Still bece uffan ba, shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ji tayi gaba ɗaya ta takura da yadda suke ɗin nan, Yanayin ya mata wani iri banbarakwai, dan haka ta Yunƙura zata miƙe taji ya riƙe ta gam, a hankali taji yace
"Turaren wa kika shafa?"
"Turare na ne"
"Hmm ba irin wannan kike sawa ba" Yai maganar a hankali tare da Ajiyar zuciya
Ɗan tura baki tayi tace
"Yaya Amina ce ta bani ranar da ka kaini gida"
Jinjina mata kai Yayi.
Cikin shagwaba tace "Yaya Ammar bacci nake ji"
"to yi mana ai ba hanaki nayi ba"
"to ka cikani mana ka tafi ɗakin ka"


Ɗan Murmushi yayi yace
"Ni kike kora? To ai gida nane a inda nake so anan zan zauna"


Ammar yana jin yadda zuciyar ta ke harbawa da sauri sosai, gaba ɗaya ya takura ta.


Gajiya tayi da ƙoƙarin barin jikin sa tai shiru, amma ta kasa bacci tana jin Yadda yake sauke Numfashi ta ɗauka bacci yayi.
A hankali ta kai hannun ta ta taɓa gemun sa dake matuƙar birge ta, ji tayi ya riƙe hannun ta, ɗan zaro ido tayi tace
"dama idonka biyu wai?" bece komai ba se ɗan murmushi da yayi yace "Yau hankalin ki ya kwanta ko? Gobe zan aske shi"
"Idan ka aske ko hmm ni nasan me zan maka".


A hankali bacci me nauyi ya ɗauki Mufeeda, bugun zuciyar ta ya koma normal, Tunda Ammar ya shiga ɗakin ta zuciyar sa ke saƙawa tana warwarewa, ya rasa abunyi gaba ɗaya, wani gefen na zuciyar sa yace "Yarinya ce tayi ƙanƙanta"
Amma Cikin bacci Mufeeda taji abunda bata saba ba dan haka da ɗan ƙarfi tace
"Yaya Ammar meye haka ne? Nifa bacci nake ji, dan Allah ka koma ɗakin ka"
Ƙarshe Ammar be gama yanke shawara ba, se bayan da komai ya lafa ya dawo hankalinsa, dafe kai Yayi tare da faɗin
"Subhanallah, what the Fucking shit i did"
Yama rasa me ya kamata Yayi, ya dafe kansa yai shiru, Yayin da kukan Mufeeda ke fita ƙasa2, ta shi Yayi a hankali ya kunna fitilar wayar sa ta dunƙule a cikin bedsheet tana kuka, gaba ɗaya tausayin ta da haushin kansa suka kama shi, wai yau shi ne ya kasance da wannan 'yar mitsilar Yarinyar da yake wa kallon me ƙuruciya.


Ya miƙe ya fita, yaje ya kunna gas ya ɗora ruwa, Allah ya temake shi aka dawo da wuta, ɗakin ya dawo ya same ta yadda ya barta, yama rasa me zece mata.


A hankali yace "Can I help you? Ga ruwa can na kai miki toilet"


Sanin Halinsa yasa ta ɗan juyo ta tashi zaune tace masa
"bakomai zan iya kula da kaina"


Ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet tana taka wa a sannu a hankali ya riƙe ta har ƙofar toilet,


Ammar yace
"but do you know how to take the ritual bath?"


Juyowa tayi ta Harare shi a ranta tace "Sekace da shi yake min?" Amma a fili tace
"An ko yamana a Islamiyya"


Seda ta shiga toilet Sannan Ammar ya canza mata zanin Gado ya fita da wancan.


Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya yaji kamar ya koma ya kuma duba ta, kuma se yayi tunanin karta raina shi, wani kallo zata yi masa idan ya koma?
( Yo Yaya Ammar raini na nawa kuma? 🤔🤔 bayan..... 😜)


Ya nemi guri ya kwanta.


Wani irin farinciki ne ke ratsa Ammar wanda ya rasa na mene ne? A zahiri yana matukar raina Mufeeda yana ganin ƙanƙantar ta amma ta bashi mamaki fiye da yadda yake zato matuƙa, lokaci lokaci se ya ɗanyi murmushi wani lokacin kuma yayi tsaki a hankali zazzaɓi ya dinga rufe shi, tare da wani bacci me daɗi yayi gaba da shi.


Da ƙyar Mufeeda ta iya bacci, dan har bacci ya ɗauke ta kuka take tana kiran wayyo Mama a hankali.


***************
Da safe wata uwar makara yayi, dan bayan Yayi sallar Asuba har goma da rabi bacci yake, a hankali ya buɗe idon sa da suka yi masa nauyi ga kansa na sarawa, Ya miƙe ya shiga toilet ya wanke bakin sa ya fito.
tunani yake idan ya fito ta ina ze fara haɗa ido da ƙanƙanuwar Yarinyar da ya kasa controlling ɗin kansa a kanta.
Ita kuwa Mufeeda gajiya tayi da kwanciyar, dukda Jikin ta babu ƙwari tashi tayi ta sake wanka ta sha kwalliya ta shiga kitchen.


Ga mamakin Ammar yana fitowa yaji ƙamshin Abinci, tana kitchen tana aikin ta, lallai Yarinyar nan wani lokacin akwai ƙarfin hali sannan ya jinjinawa juriyar ta, a hankali ya taka zuwa ƙofar kitchen ɗin, ta bawa kitchen ɗin baya dan haka bata san yazo ba.
Ƙura mata ido Yayi yana kallon ta.
Waya take yi da Yaya Amina, tasa wayar a hansfree ta ajiye tana waya.


Mufeeda tace "Yaya Amina wai dan Allah wani irin turare kika bani ne?"


"Turare ne kawai Amma meya faru?"


"A'a bakomai tambayar ki kawai nake"


Dariya Yaya Amina tayi tace
"Kai Auta ki labarta min mana"


"Uban me zan labarta miki? Keda Allah kawai Yaya Amina"


Dariya sosai Yaya Amina take, suka yi sallama ta ci gaba da aikin ta.


Seda Ammar yayi dariya mara Sauti da yaji tace wa Yaya Amina ita da Allah.


babu tsammani ta juyo taga Ammar ta ɗan razana ta ce
"Haba Yaya Ammar ni gaskiya ka bani tsoro, ban san kazo ba fa"
Ya wani maze yace
"Kingama girkin ne? Na makara zan fita"
"yi haƙuri saura kaɗan" ya jinjina mata kai ya koma falo, dama ita tasan za'ayi haka, mazewa ze tayi kamar be komai ba.


Har Yanzu da ta taho kawo masa kayan breakfast a hankali take tafiya tana yamutsa Fuska, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, amma shi sam gani yake idan ya buɗe baki yai mata magana akan abunda ya faru koya mata sannu zata raina shi.


Yana lura da ita Abincin ma bata ci ba Sosai, kaɗan taci ta barshi, seda ya gama ta miƙe zata kwashe kwanukan Kaman an masa dole cikin basarwa yace
"Yi zaman ki kawai"
Da yake yasan yayi aika aika, duk wani aiki na gidan shi yayi, amma ya buɗe baki Yace mata Sannu ya gode ne baze iya ba.


Har Mamaki Halayen Ammar suke bata wani lokacin Yana dai ta kula da dukkanin Moves ɗin ta.
Mufeeda ma kuwa ta nuna masa kaman babu abunda ya faru tunda haka yake so, har wani respect na musamman ta shiga bashi ko da wasa bata nuna masa sauyi saboda abunda ya faru jiyan ba.


Wuni yayi a gida beje ko ina ba, Duk shi ya dinga ayyukan gidan, duk da shima baya jin daɗi, Mufeeda kam bakin ta yau mutuwa yayi, wuni sukayi kaman kurame, kusan akan kujera ta wuni gaba ɗaya jikin ta babu daɗi ciwo yake mata, Amma sedai Ammar ya kalleta ya ƙi ce mata komai.


Daddare tea ya dafa mata ya sha Madara da Milo ya kawo mata, ɗan yamutsa Fuska tayi za tayi magana ya haɗe rai yace
"ki karɓa ki ci Abinci kawai"
Tana tura baki taci Abincin seda ya tabattar ta ƙoshi sannan ya sata a gaba ta tafi ɗakin ta ta kwanta, shima ya tafi nasa.


Wayar ta ta ɗauka ta tura masa saƙo
"Yaya Ammar bani da lafiya fa"
"Meke damunki?" yai mata reply


Emoji ɗin kuka ta tura masa tace
"Ai kafini sanin meke damuna"


"Ai ba jikin mu ɗaya ba da zan san meke damunki, ki gayamin mene ne, idan ya kama muje Asibiti semu tafi"


"Shikenan tunda haka kace, Seda Safe have a nice dream Hubby, I love you"


Juya message ɗin nata yaita yi, wani irin tausayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login