Showing 3001 words to 6000 words out of 105124 words

Chapter 2 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

18982

jikin ki kike dariya? Kinyiwa kanki ranar bikin se dai ki bar gidan nan, inda na gode Allah bani na sai miki ba uban kine ya siya, shashasha mara hankali"


Indai faɗan Mama ne Mufeeda ta saba shansa, dan haka ko a jikin ta, ta shige ɗakin su, wani irin farinciki ke ratsa zuciyar ta wanda bata san dalilin hakan ba, tasan dole Ammar ya dawo saboda kayan da ta bari da gangan a Napep ɗin sa.


Kwana Mufeeda tayi mafarkin Ammar, da tuno shi se ta saki murmushi.
Yayar ta ta kalleta "professor Autar Baba wai farincikin me kike haka? Mama se faɗa take kin bar kayan ki a ɗan sahu, amma baki damu ba? Yanzu me zaki saka ranar bikin?"


"haba Yaya ke an isa ayi bikin ki bani da kayan sawa ne? Ko naki sena saka, ina Addu'a insha Allah nasan me Napep ɗin ze kawomin abuna"


"ya akayi kika san hakan?"
"jikina ne ya bani".
Inma be kawomin ba baba ze saimin wasu.
************


Wasa2 kwana biyu Ammar be dawo ba, yauma tana makaranta sam bata walwala, Fati tace "Muffy wai yana ganki haka?"


"ke barni har yanzu Yaya Ammar fa be zoba"
"to mezezo yai miki?"
"wallahi fati so nake kawai in kuma ganin sa ya haɗu, a Napep din fa nabar ɗinkuna na, Amma har yanzu be dawo ba"


"kayan naki kika bari a Napep, gaskiya baki da kai, yanzu idan be kawo miki ba fa?"


Mufeeda ta taɓe baki "ke nifa bata kayan nan nake ba, Baba baze bari ayi biki bani da sabon kaya ba, ni kawai shi nake so in kuma gani"


Tsaki fati tayi tai bar gurin dan ba ƙaramin ƙular da ita Mufeeda tayi ba.


************


Bayan magariba Mufeeda na kwance tayi shiru tana ta tunanin Ammar, ji tayi ta gaji da kwanciyar, ta miƙe ta fito tsakar gida, Maman su haushin ta take ji, sam bata shiga sabgar ta saboda batar da kayan da tayi, shirye shiryen biki kawai sukeyi.


Yaro ne yayi sallama yace "wai ana sallama a waje, inji wani"


Mufeeda bata tsaya jiran meza'ace ba, ta zari hijjabi tai waje, kaman yadda ta zata Ammar ne a tsaye a gefen Napep ɗin sa.


Da sauri ta ƙarasa inda yake
"Yaya Ammar kaine? Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, dama nazo in tambaye ki ne, ko kune kuka manta kaya a Napep ɗina, tun shekaranjiya nake yawo da su"


Ajiyar zuciya tayi "Kayan ɗinki nane Yaya, na shiga damuwa sosai, zuciya ta ta bani zaka kawomin dama, dan na yarda kai me amana ne"


"Seki kiyaye gaba, idan kin shiga abun hawa ki dena surutu, in ba haka ba wataran dake za'a tafi"


Ya Ɗakko kayan ya miƙo mata
Bata karɓa ba ta tsaya tana kuma ƙare masa kallo, murmushi ta sakar masa tace


"bana surutu a abun hawa ai, ranar ma dan kai ne, nagode sosai Yayana, Allah ya ƙara Arziki, ya kiyaye ka daga sharrin maƙiya, Allah ya azurta ka da halal ya nesan taka da haram, Allah ya sakawa iyayen ka da Alkhairi Addu'ar su da tarbiyar suce ta sa ka zama mutumin kirki "


Ammar yana mamakin yadda yarinyar ke sarrafa harshen ta. Ba ta karɓi kayan ba tace
" Dan Allah ina zuwa"


Ta koma cikin gida, ba tafi mintuna biyar ba ta fito hannun ta ɗauke da leda, ta miƙawa Ammar.
Ya kalleta yace "menene wannan?"


"Yaya Ammar yaba kyauta tukuici, bani da abunda zan biya ka, kawai dai na baka ne"


Girgiza kai yayi "bazan karɓa ba, ungo kayan ki, ina sauri zani wani guri ne"


Kallon sa tayi "zaka zance ne? Idan baka karɓa ba zan barka da kayan sedai ka koma da su ko ka barsu anan dan wallahi bazan karɓa ba"
Tai maganar tana kallon cikin idon sa, dagaske take abunda take faɗa.


Hannu yasa ya karɓa, sannan ta karɓi kayan ta, cikin iyayi tace
"yauwa ko kaifa Yayan Mufeeda"


A ransa ya maimaita "Mufeeda"
Tace "ungo wannan invitation ne, bikin yaya ta za'ayi a wannan satin dan Allah kazo kaji Yaya na"


"ban miki Alƙawari ba gaskiya, Amma Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya"


Wani irin kallo take masa wanda ya kasa gane kallon menene haka?


"Idan ba kazo ba bazanji daɗi ba, kuma zanga kaman kamin wulaƙanci ne, ko kuma maybe... Shikenan dai nagode ka gaida Mama, Allah ya kaika gida lafiya, ya tsareka daga sharrin maƙiya"


Ta juya ta nufi gate ɗin gidan su, yai shiru na ɗan lokaci ya shige baburin sa ya tafi.


Ɗakin Baban su ta nufa, tana zuwa ta tarar da yayyen ta na gidan Aure sun cika falon baban su da mahaifiyarsu suna ta hira ana shirye2.
Tana zuwa taje gaban Maman ta ta ajiye mata kayan ɗinkin tace


"Mama ga kayan nan, me Adaidaita sahu ya kawo min, seki dena haɗemin rai"


Wani daga cikin yayyen ta ya kalle ta


"Ahh kaga professor, kuma Autar Baba da Maman ta"


Mufeeda Ta ɗan tura baki "Autar Baban dai, Mama tafi son Yaya akaina, kuma na fasa zama professor ana aurar da Yaya nima Aure zanyi"


Dariya suka dinga mata, Babbar yayar su tace "kiji min yarinya da rashin kunya, kin fasa zama professor kafin kiyi auren?"


"Na fasa dan Yaya na barin gidan nan Mama zata kasheni da sa aiki, dama kaman bata sona nima Aure zanyi"


Mama tai murmushi tace "naji bana sonki ɗin, nafi son Amina ke kam baki da nutsuwa ga wauta, tunda babanki yana sonki ai shikenan, waye ma ze aure ki a haka, baki iya komai ba, se son jiki da rashin kunya, ko Saurayi baki da shi"


"Wallahi na samo Saurayi, me Adaidaita sahun da yakawo min kayana nake so"


Yanayin yadda tayi maganar ne kanta tsaye da confidence ɗin ta yasa ta bawa kowa dariya, suka ɗau maganar tata shirme.




Domin gyara, sharhi, ko shawara
07063065680


Kuma yaseen ba comments se Allah ya kaimu September zan cigaba da typing.
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )





Page 2


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com






"ke bama son shirme, ubanwa ze miki wani aure, tafi kije kici Abincin dare ki kwanta" cewar Yayan Mufeeda


Baba yace "kaga Abubakar ku ƙyalemin professor auta, yadda take so haka za'ayi, tunda gidan su ne, ku yanzu duk ba 'yan gidan nan bane ba' yan karo ne"


Mufeeda tace "Yawwa Baba gaya musu, dan Mama tafi sonsu, yanzu idan muka ga dama duk korarsu zamuyi kowa ya tafi gidan sa"


"sosai makuwa Auta na"


Haka Baban mufeeda ya ci gaba da zigata tana ta zuba taɓarar ta.


*************
Mufeeda se rawar kai take tana iyayi, anata shirye shiryen biki, sati guda ta dauka ta dena zuwa makaranta se yawon rabon Katin gayya ta, komai da ita ake yi, yayin da gefe guda kullum cikin tunani take yi, zuciyar ta na son sake saka Ammar a idon ta.


Mufeeda duk kayan gyaran fatar da Amarya take yi itama se tayi, tare suka je ƙunshi da gyaran kai, komai angone ya biyawa Mufeeda yadda ya ya biyawa Amarya, gidan su mufeeda su takwas ne, huɗu maza huɗu mata, daga Yaya Amina se Mufeeda, shekaru biyar ne tsakanin Amina da Mufeeda.


Angon Yayar Mufeeda yasan Mufeeda sosai, saboda ba ƙaramar gudunmuwa ta bashi ba lokacin da yake neman Auren yayarta, ita ta taya shi campaign gurin Yayar ta, duk saurayin da Amina za tayi indai beyi wa Mufeeda ba in ta dinga kushe shi se Amina taji bata son mutumin nan sun rabu.
daga tace wancan be iya sa hula ba yana da ƙaton kai, ko kunnuwan sa sun fiye tsayi, se tace wancan ƙatuwar ƙafa ce da shi idan ta aure shi zata haifi ɗan se an je kamfani za'a masa takalmi, se tace wancan kwaɗayayye ne kullum yazo aka bashi abu se ya karɓa, harta kai ta kawo idan Amina tayi Saurayi se tace
"Mufeeda zo kiga wannan saurayin yayi kuwa?"
Mama taita faɗa tana "Amina baki da wayo, kina zaune ƙanwar bayan ki, shekara kusan biyar kika bata, Amma ita ke zaɓa miki Saurayi ki biye mata haka zakiyi ta zama a gida ba aure"


Mufeeda bata da jiki sosai, tana da hasken fata, ba doguwa ce can ba, Amma tana da kyau dai dai gwargwado, kana ganin ta kaga yarinya, Amma akwai baki, ga iyayi da rawar kai, dan kusan duk tafi yayyen ta baki, yayyen ta ba ruwan su da hayaniya a nutse suke, basu da yawan magana, Amma mufeeda ta fita zakka, ita akwai baki da neman rigima ga rashin haƙuri, shiyasa sam basa shiri da maman ta.


****************


Ammar yana zaune a tsakar gida dashi da 'yar Yayar sa Halima, Halima itace Babbar jikar gidan su Ammar, daga Yaye Umman sa ta riƙe ta.
Halima ta gyarawa Ammar ɗakin sa ta fito da invitation a hannun ta tace


"Uncle Ammar, waye ya gayyace ka biki ne?"


Seda yaga katin ya tuna, ya ɗanyi tsaki yace
"wallahi wata fitinanniyar yarinya ce ta bani wai bikin yayarta, yadda shi kawai"
"haba Uncle baza ka bikin ba? Ba kyau fa a gayyace ka walima kaƙi zuwa, Amma gayamin ko Anty na ce?"


Haɗe rai Ammar yayi yace "ke bana son shashanci, yarinya ce fa ƙarama kin girme ta"


"Amma ya akayi harta baka invitation? Wallahi uncle seka ga 'yan yaran fa munfi iya soyayya"


"kunfi iya hauka dai, koke baki isa Aure ba, ina zanje ina kula' yar da da aure nayi da yanzu na haife ta"


Dariya Halima tayi
"Allah ya ja da ran uncle ɗina, to ai da haka da haka"
Haɗe rai Ammar yayi kaman bashi ke hira ba yanzu
"Ke rufemin baki, yaushe na fara wasa dake?"
"Allah ya baka haƙuri"


Gyaran murya suka ji a soro, alamar za'a shigo, mahaifin Ammar ne ya shigo ya kalli Ammar yace


"kai dai kam kaji kunya wallahi, Allah Ammar da kai mace ne masallaci zanje in samu duk wanda yayi min in Aura masa kai sadaka, ace mutum ba zuciya duk sa'aninka da ƙannen bayan ka sunyi Aure amma kai kana zaune, se anyi magana ka kama wani kai se 'yar shekara talatin kai bazaka auri yarinya ba, dama wace yarin ya ce zata aureka, duk ka tsofe a titi ka zama tuzuru, tun wuri kayiwa kanka faɗa kafin ayi da kai kai kake yi da kanka, in ba sokake daga ga shiga guri mutane su fara kaffa kaffa da yaran su mata ba, saboda ka tsofe ka zama tuzuru ba Aure, wanda da kayi Aure tuntuni da yanzu kaima nan da 'yan shekaru zaka aurar da' ya"


Ture Abincin da yake ci yayi, dan ji yayi yana tsaye masa a wuya Ire2 wannan faɗan na mahaifinsa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba, ba dama ya shiga cikin gida ya zauna mahaifinsa ya dinga masa mita kenan akan maganar Aure.


Mahaifiyar Ammar ta fito daga ɗaki tana faɗin "dan Allah malam ka dinga haƙuri, Shifa Auren nan lokaci ne, kuma Alhamdilillah tunda rashin auren besa yana ɗakko maka magana a waje ba, ba ruwan sa da 'yar kowa, kuma yin Aure ai se mutum nada ƙwaƙwƙwarar sana' a ko?"


Mahaifin Ammar yace "ai dama ke kike goya masa baya yake ƙara sangarcewa, kalli kowa gidan nan yau faten wake ya sha amma shi kinyi masa girkin sa daban, shi bazeci faten wake ba, yace se ya gama karatu degree biyu yayi, yace seya samu sana'a wannan babur ɗin da yake ja be isheshi ba indai ba ƙarya ya ɗorawa ransa ba, ni anya ma ba Aljana ce ta aure shi ba?"


Ammar kam ya kai ƙarshe a ƙuluwa da irin wannan faɗan na baban sa, dan haka ya miƙe ya bar Abincin, Mama tace "Ammar Abincin fa?"
na ƙoshi ya faɗa a taƙaice yai waje
Mahaifin sa yace
"Eh haka dai, daga nan kuma ze wuce gurin bautar yahudu, gurin ƙwallon ƙafa aikin sa kenan, shi wace mace ce ma zata iya jure wannan baƙar zuciyar tasa, komai abun fushi ne a gurin sa"
Haka mahaifin Ammar ya ci gaba da faɗan sa har ya gaji yai shiru.


Ammar be koma gida ba se gurin ƙarfe tara na dare, ya zauna suna hira da mahaifiyar sa, tana ta ƙara yi masa Nasiha kan ya dinga haƙuri da halin mahaifinsa
Ammar yace "Umma wallahi na rasa me yasa Abba kaman baya son ganina? Sa ya ganni seya fara faɗa"


"Ammar ba sonka ne ba yayi ba, gaskiya yake gaya maka, a duniyar nan kafin ayi da kai kake yi da kanka, kai namiji ne kuma dukkan lafiyayyen namiji a shekarun ka ya kama ta ace ya ajiye iyali"


"Umma baƙin Aure nake ba, yanzu fa zamanin mu da naku ba ɗaya bane ba, da yawa 'yan matan yanzu me kuɗi suke so, ni kuma bani da su, ga kwalin karatu amma babu ƙwaƙwƙwarar sana' a, haƙurin da kuke dashi ku iyayen mu, matan yanzu ba haka bane a gurin su, ba kowace yarinya ce tasan menene zaman aure ba, zama ne na haƙuri wadda zata fuskanci yau in akwai gobe babu, wace yarinyar zata yadda ta aureni ina tuƙa babur ɗin sahu?"


"Ammar duk lalacewar zamani akwai na Allah Ammar akwai matan ƙwarai"


"Hakane amma duk da haka nafi son in samu macen da ta gama hankali ko bazawara ce, danni bazan auri yarinya ƙarama da bata gama hankali inzo ina fama da shashanci ba"


Girgiza kai Maman Ammar tayi tace "yaro dai yaro ne"


****************


Gidan su Mufeeda ya fara ɗaukar harami, baƙi daga sassa daban daban sun hallara ana ta shirin fara Shagalin biki, duk inda Amarya da ƙawayen ta suka saka ƙafa nan Mufeeda take maida tata, ko aike Mufeeda ƙin zuwa take balle asa ran zata taya aiki.


Aka fara Shagalin biki, kowane ranar event Mufeeda ta sha kwalliya kaman itace amarya, taji a ranta inama ace Yaya Ammar zega kwalliyar nan tata data ji daɗi, nan ta fara tunanin yadda zata samu lambar sa tare da addu'ar Allah yasa kafin agama bikin nan ko taro ɗaya ya zo mata.


Ranar ɗarin Aure aka ɗaurawa Yayar Mufeeda Aure, gida ya cika da jama'a anata shiga ana fita.


Maman mufeeda ta bata kaji da snacks akan faranti tace maza taje ta bawa wasu 'yan uwan baban su yanzu zasu juya su tafi.


Mufeeda ta fito da tray a hannun ta, anata tsokanar ta, suna ce mata professor Mufeeda sarkin rigima, da yake ƙofar gate ɗinsu an buɗe ta gaba ɗaya, hakan yasa kana hango masu wucewa, gidan su Mufeeda yana da kyau, ba babba ne can ba amma yana da tsari, yanayin Abincin da'ake shiga ana fita da shi ze nuna Akwai rufin Asiri a gidan.
Idon ta ta sauke akan Ammar, ya saka yadi Ash da baƙar hula, yana ƙoƙarin kunna babur ɗinsa.
"Kenan yazo amma be nemeni ba?"
Ai dire tray ɗin tayi bata san ma wa ta bawa ba, ta fyalla da gudu tai waje tana faɗin
"Yaya Ammar ɗina"
Juyowa yayi yana kallon inda take tahowa, purple ɗin shadda ta saka, ta sha surfani tun daga sama har ƙasa, hannun ta ya sha lalle, ga zobuna da abun hannu, tayi ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashin ta da keta sheƙi, tayi kyau matuƙa kaman itace Amarya.


Ta ƙaraso inda yake se nishi take, ya kalleta yace
"ke bakya jin kunya kike gudu a gaban mutane?"
Ajiyar zuciya tayi tace "haba Yaya Ammar yanzu da tuni ka tafi bamu haɗu ba, harna fidda ran zakazo" tai maganar a ɗan shagwaɓe
"hmm to ai gashi nazo, ya taro?"
"Alhamdilillah"
"Allah ya basu zaman lafiya"
"Ameen Yaya Ammar, Amma ba har tafiya zakayi ba, kaci Abinci kuwa?
" No bashi nazo ci ba, nazo an ɗaura aure nayi Addu'a" yai maganar tare da shiga babur ɗin sa ze kunna, hannu ta sa ta riƙe makullin tana kallon sa.


Haɗe rai yayi yace "Ya haka? Cika min ina sauri ne"


Dukda wani uban kwarjini da yayi mata musamman daya haɗe rai, bata nuna masa ta tsorata ba ta dake tace "kai kullum cikin sauri kake ne? Ni gaskiya idan baka shigo ba bazanji daɗi ba, ya za'ayi in gayyace ka kuma ka tafi baka ci komai ba?"


Ammar yace "ke wai haka kike? Cikamin key ɗina zan tafi"


Ƙwalla ya gani a idon ta, tana zumɓura baki, tana karya wuya kaman za tayi kuka, ta ƙara riƙe key ɗin gam, ji yayi kaman ya balbaleta da masifa amma yaga ta wani nutsu ta koma kalan tausayi. Ɗan gajeren tsaki yayi yace "muje"
Murmushi tayi tareda cewa "ko kaifa"
Amma still ta cire mukullin ta riƙe a hannun ta dan karma yace ze tafi.


Cikin gida ta shiga dashi har falon baban ta, yana zaune yana gaisawa da baƙin sa tace "Babana ga Yaya Ammar wanda ya kawo min kaya na dana bari a mota na kawo maka shi ku gaisa"
Ammar ya durƙusa suka gaisa da mahaifin Mufeeda, yai masa Allah ya Sanya Alkhairi.
Baba yace
"Masha Allah, Yaya Ammar mungode fa, dan saura ƙiris Auta ta sha duka a hannun Mama, Allah ya saka da alkhairi, mungode sosai"
Ammar yace "bakomai"


Ya miƙe suka fito yace "ke bani key ɗina zan tafi"
Ta marairaice tace "dan Allah kayi haƙuri saura Mama ku gaisa ba dan hali na ba dan Allah"
Haka ta kuma Jan Ammar inda mahaifiyarta take, ya gaishe ta ya musu Allah ya Sanya Alkhairi, Nan ma Mama tayi masa godiya.


Mama tace "Mufeeda kawo masa kayan ɗaurin Auren shima"
Ammar yace "A'a a barshi yana sauri ne"
Mama tace "Ai ba'ayi haka ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login