Showing 99001 words to 102000 words out of 105124 words

Chapter 34 - WATA KISSAR BY BOOK AISHA HUMAIRA .txt

05 Jun 2024

18969

Mufeeda a kaina, A yanzu idan na tauye haƙƙin ta nayi miki se Allah ya tambayeni, balle kuma bani da shi"


Abun ya nemi ya koma musu faɗa suka yi baran baran ta koma ta zage Mufeeda tsaf, Ammar yana tare mata, da haka ta bar gidan.


Ammar yaita rarrashin Mufeeda yana bata haƙuri akan irin abubuwan da Jidda take mata, Mufeeda tace
"Bakomai Yaya Ammar, ai wataran se labari nasan ze wuce"


"Yawwa 'yar Aljanna, ɗazu bayan fita ta Amina ta turo kuɗin nan, amma dubu Ashirin da biyar ta turo'"


Mufeeda tace "Eh munyi waya da ita, wai a ribar data samu ne nima ta sanmin, seka bani dubu goma ka siyomin ruwan leda, se in rubuta maka kayan lemon da nake buƙata, in sanar da mutane na fara saida kayan sanyi"


Ammar yayi murmushi yace "Shikenan, Allah yasa Albarka, Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zan shiga kasuwa ana sauke kaya daga trailer, inje abunda na samu in ƙara da kuɗin hannu na se in siyo ko Omo ne da Sabulu a hannun 'yan sari in fito bakin kasuwa in siyar"


Idon Mufeeda fal ƙwalla tace "Yaya Ammar zaka iya wannan aikin me wahala kuwa?"


Murmushi yayi yace
"Nifa namiji ne, da aikin soja zan tafi dan dai Baba baya so ne, karki damu zan iya kije ɗakin tsakar gida na siyo miki nama kici, ki ƙara haƙuri Mufeeda Insha Allah komai ze wuce"


"Yaya Ammar seda ka siyo Naman nan"


"Eh mana nasan kina so, kin daɗe baki ciba"


Allah sarki Ammar, harda fruit ya haɗa ya siyo mata, duk yadda tayi dashi yaci ƙi yayi, Amma yaji daɗin ganin murmushi a fuskar ta, sanadin wannan Nama data ci.


Tun Ammar yana sintiri akan Napep ɗinsa har ya haƙura,
Kullum da sassafe yake tafiya kasuwar singa, haka ze zage yaita sauke manyan buhunhunan kayan Abinci, abun da ya samu haka ze haɗa da kuɗin hannun sa ya sai ƙanan abubuwa kamar Omo da su Sabulu a hannun 'yan sari ya fito bakin kasuwa ya siyar.
Ammar duk sana' ar daya san zeyi ya samu kuɗi babu ruwan sa yin abarsa yake, wataran ya samu riba wataran ya faɗi amma hakan baya hana gobe ma ya fita.


Kamar wasa Mufeeda ta fara Saida kayan sanyin nan, dama kafin su fara seda taita gayawa Allah, abu kamar wasa wuni ake zuwa siyan ruwan sanyi da lemo, randa babu wuta ta bayar a siyo mata mai ta kunna inji, Sosai take ciniki.


Ranar da taga ta samu riba da yawa bayan Ammar ya dawo ya huta tace
"Yaya Ammar ya kamata ka siyo mana banki, kullum mudinga ajiye ɗari biyu, duk sati dubu ɗaya, zasu temaka mana wataran"


Ammar yace "hakane kin kawo shawara Jaririya ta, Insha Allah zan siyo mana mudinga ajiyewa"


Duk wannan hali da suka shiga Babu wanda suka gayawa, tare suke ta faɗi tashin su, randa suka samu suci me kyau randa babu suci abunda ya samu.
Allah yasa musu Nasibi akan sana'ar, Mufeeda tana daga gida amma tana cinikin ta sosai.


Kwana biyu Ammar beje gida ba saboda bashi da kuɗin daze musu alheri idan yaje, ranar wata Asabar yasa Mufeeda ta shirya suje, su fara zuwa gidan su Ammar idan yaso da Azahar, se suje gidan su Mufeeda.
Haka kuwa aka yi, suna Zuwa gidan su Ammar suka tarar da Abba a tsakar gida, suka gaisa.
Abba yace
"Aikuwa Halima tana Islamiyyar safe, ita kuma taje wata barka nan ƙasa amma yanzu zata dawo, Ina A daidaita sahun naka ne?"


Ammar yace
"tana gurin gyara, Amma zan karɓo Insha Allah "


Abba yace "To Allah ya dafa, 'yata fatan kuna lafiya?"


"Lafiya ƙalau Abba"


"Masha Allah, tunda Allah yasa yau kinzo kafin ku tafi kya je kiga dabbobin ki"


Mufeeda tace "To Abba nagode sosai Allah ya ƙara girma"


Abba yace "Bakomai Mufeeda, Allah yayi muku Albarka, ni zan fita nasan ba daɗewa zata yi ba, zata dawo"


Ammar yace "Shikenan Abba adawo lafiya"


"Allah yasa Ammar" Abba ya fice


Mufeeda da Ammar suka zauna suna Hirar su, ɗakinsa na gwauranta dake cikin gidan ya buɗe musu suka shiga, Mufeeda tace
"Yaya Ammar wannan ƙatuwar katifar fa kamar ta Amarya?, bari in kwanta akai"


Ammar yace "Yi a hankali karki lotsamin katifa da wannan ƙaton cikin naki"


"Sena lotsa ɗin, ai da bani da nauyi, kaika mayar dani me nauyin"


Dariya yake mata yazo ya kwanta a kusa da ita yace
"Allah sarki Jaririya ta, ta kusa zama Mum koya zata yi raino"


"Ai baka tuna ni Jaririyar bace, ka haɗani da aiki"


Hirar su suka dinga yi cike da ƙaunar juna, wani lokacin Ammar yana kallon yadda cikin yake motsawa mussman idan tana bacci, ya ɗora hannun sa akan cikin nata, yana jin yadda yake ɗan motsawa, Da haka bacci ya ɗauke su.


Koda Umma ta dawo tayi mamakin ganin gidan a buɗe ba kowa, tana shigowa ta tarar da ɗakin Ammar a buɗe ga takalma a ƙofar ɗakin, tai magana kusan sau uku taji shiru, ta ɗaga labule, bacci suke sosai Umma ta sauke labulen tana ɗan murmushi.


Aikace2 ta shiga yi, Ta ɗora girki Amma duk su Ammar basu san tana yi ba, Mufeeda bata samun bacci sosai, tana raba dare gurin Ibada da kaiwa Allah kukan su, sannan idan tayi sallar Asuba bata komawa bacci saboda Ammar da wuri yake fita, wani lokacin shida da rabi ya bar gida, da rana ta ɗan ɗaga kuma an dinga sintirin siyen ruwa da lemo kenan, dan haka basa samun ishashen bacci, mussman Ammar da yake Aikin ƙarfi.


Jiddace tayi sallama idon ta Jawur kamar wadda aka koro, Umma ta kalleta tace "Jidda lafiya kuwa?"


Fashewa da kuka tayi, tace


"Umma na shiga uku, Baban su Haidar wai Zainab ze Aura ashe? Ɗazu na samu labari, na shiga uku Umma, ta gama sanin Sirri na ta shisshige min, na yadda da ita Amma taci Amana ta, Nusaiba na taje har gida ta mata rashin Mutunci baki ga dukan da da baban ta yayi mata ba, na shiga Uku Umma.








Wata ta biyo ni private tace "Gaskiya baiwar Allah kin fiye tsananta masifa"
🤣 🤣 🤣 🤣 🤣 Sorry labarin ne yazo a haka. Ina godiya da Comments da shawara.






Ina Masoya na, lokaci yayi da zaku min kara ku nunamin ƙauna, kamar yadda kuka sani na shiga Gasar Matasan marubuta 2021, A gobe in Allah ya kaimu Asabar, 31 ga watan July rukuni na 7,wanda shine rukunin da nake ciki zamu saki litattafan Gasarmu, masu ɗauke da kalmomi 2500.
Na shiga gasa da littafi na me suna BAƘIN TABO, ku kasance dani domin ji ya taka ya a cikin wannan gajeren labari, ina fatan idan lokacin zaɓen labarin Gasar Yayi, zaku zaɓi labarina na BAƘIN TABO,
https://chat.whatsapp.com/J3lB9LvDu174M3yeR56BoK Mata kawai banda maza


Ina Alfahari daku Masoya a duk inda kuke.






Domin Sharhi Gyara, ko Shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨


( *Sai Mata* )


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app 07063065680


Gmail Www.ayshertadam@gmail.com


Please follow me on Wattpad, vote and Comment


ELEGANT ONLINE WRITER'S


NOT EDITED


Page 30


Hargowar Jidda ce tasa Ammar ya farka, yai shiru yana sauraron abunda Jidda take faɗa, rungume Mufeeda ya sake yi a jikin sa yana tunani, a ransa yace
"Allah nagode maka da ba Zainab na Aura ba, da ita na aura nasan tabbas ba zata iya haƙuri da halin da nake ciki ba"
ya cigaba da shafa kan Mufeeda yana kallon ƙanƙantar ta, Amma akwai haƙuri da hangen nesa, tana yiwa Ammar so na gaskiya da zuciya ɗaya.


A hankali Mufeeda ta fara motsawa itama sakamakon kukan Anty Jidda, ta kalli Ammar tace
"Yaya Ammar su Umma sun dawo"


Ammar yace "tun ɗazu suka dawo ai"
"amma me yasa baka tasheni ba? Yanzu an gan mu tare muna bacci, yanzu ya zamuyi mu fita?"
Murmushi yayi yace
"Ya zakiyi ki fita dai, ni ficewa ta zan yi"
Ta kalli agogon dake ɗakin ta ɗan zare ido tace
"Yaya Ammar lokaci ya ja fa, kalli Azahar tayi"
Ammar yace "Eh tashi muje muyi salla"
"Yaya Ammar kunyar fita nake ji, Amma kamar muryar Anty Jidda nake ji fa"


"Eh ita ce" ya bata Amsa


Mufeeda tace "Kamar kuka fa naji ta nayi"


Ammar bece komai ba ya miƙe, ya basar ya fito tsakar gida, ya gaida Mama yai alwala ya fice masallaci.


Da ƙyar Mufeeda ta fito cike da jin nauyi, Jidda na ganin ta, wani baƙin ciki ya tokare mata zuciya.


Mufeeda ta durƙusa tace "Umma ina wuni"


"Lafiya ƙalau Mufeeda, kin tashi ashe?"


Cike da jin Kunya Mufeeda tace"Eh Umma"


Umma ta fuskanci Mufeeda nauyin ta take ji sosai dan haka tace "to yi salla kizo kici Abinci"


Mufeeda tace "to Umma, Anty Jidda ina wuni"


Banza Jidda tayi da ita, Mufeeda ta tashi ta tafi yin Alwala.


Umma ta kalli Jidda tace "Ke kina jin matar ɗan uwan ki tana gaishe ki amma baki amsa ba"


"Umma ba dole in mata banza ba, yarinyar nan ta cuceni ba dan Ammar ya Santa ba da tuni Zainab ya aura, Amma yanzu kalli ya Aure ta, ni kuma zata Auremin miji na shiga uku Umma"


"Haba Jidda, da bakin ki kike cewa kin shiga uku? Ki fawallawa Allah lamarin ki mana, sannan kija girman ki, karki shiga sabgar ta balle inya aurota ta raina ki"


"Haba Umma ya kike wannan maganar, yarinyar Zainab nan ba sirrina da bata sani ba, wataran a gida na take wuni, kawai seta ci Amana ta"


Duk haƙurin Umma seda ta ƙule tace
"to Ubanwa yasa kike gaya mata sirrin ki? ashe har yanzu baki da hankali, kina girma kina shiga dawa, waya gaya miki ana haka? Ai koni da nake mahaifiyar ki ba komai yakamata in sani ba game da zaman Auren ki, Amma kinje kina gayawa wata sirrin Auren ki, watanma bazawara, yanzu kinzo kinamin kuka, ai kinyi kuskuren da baze taɓa gyaruwa ba, kuma karki ƙara zargin Mufeeda ba ita tayi miki ba, dama can Allah ya rubuta Ammar ita ze Aura"


Mufeeda ta fito daga banɗaki tazo ta tada Salla, ana haka Sega Yaya Maryam tazo, tana zuwa ta tarar da Mufeeda ta idar da salla suka shiga Hirar su, tamkar bata san halin da Jidda take ciki ba, suka cigaba da hira hadda Umma suka ƙyaleta.


Jidda tace "Wai Maryam baki san hakin da nake ciki bane?"


Maryam tace "koma na sani mezan iyayi akai? Tun farko ni dama wannan Zainab ɗin ba tayi min ba, na baki shawara shaƙuwarki da ita tayi yawa, Amma kika ƙi ji, Abunda haƙuri be baki ba rashinsa baze baki ba, kuma wallahi in baki nutsu ba Abba yaji labarin yadda kike ɗagawa mijin ki hankali kin san sauran"


Sallamar Ammar ce ta hana su ci gaba da Hirar, ya shigo ɗakin ya zauna, ya kalli Yaya Maryam
yace
"Sarakan yawo, daga Yaya Jidda tazo shine kema kika taho ko?"


Anty Maryam tayi dariya tace
"A'a zuwan ta daban nawa daban, kawai mun haɗu ne, Ai bansan tare kuke da Mufeeda ba, banga babur ɗinka a waje ba"


"Eh yana gurin gyara ne"


Ya kalli Umma yace "Umma me kika dafa ne, muna jin Yunwa fa, daga nan wani gurin zamu tafi"


Jidda tace "Ammar shine kazo ka kula kowa, Amma ni ka shareni kamar baka ganni ba, balle ka tambayi halin da nake ciki, koda yake ba abun mamaki bane, tunda ka fi ƙaunar matar ka a kanmu, damuwar ta itace damuwa 'yar gwal"


"Wallahi tafi gwal"
Ammar ya bata Amsa kai tsaye cike da basarwa.


"Ni kake gayawa Matar ka tafi gwal ko?"
Shiru yayi mata yaƙi bata Amsa, a fusace tace
"Ai dama nasani, ba yau kasaba wulaƙantani ba akan Yarinyar nan, ƙiri ƙiri naje gidanka da buƙata amma kaƙi saurara ta, ko Abinci ya gagara a bani a gidan ka, kuma kana kallo ba kace komai ba"
Shiru Ammar yayi yana mamakin wani irin hali ne haka da Jidda.


Yaya Maryam tace "Haba Yaya Jidda, kema fa ɗan wasu kike Aure, kuma Yayan wasu, sannan ƙanin wasu, shekaru Ashirin da biyu yana miki bauta ya wahalta miki kamar besan ciwon nema ba, shikenan ke kuma wata ba zata mori ɗan uwanmu ba? Mu yiwa kanmu Adalci mana, me Ammar yake dashi wanda yake wahaltawa Mufeeda da har kike iƙrarin ya tare a gurin ta? Ita kin san halaccin da take masa? Kin san ita ɗawainiyar da take da shi, ai macen ma da zata iya Zama da ɗan uwan mu da irin halinsa na Fushi da zuciya, Yabo ya kamata ta samu"


gaba ɗaya Mufeeda ta takura taji babu daɗi abubuwan da suke faruwa duk a dalilin ta, Umma kuwa ta hau yiwa Jidda Faɗa, jiki a sanyaye Mufeeda ta bar ɗakin dan bekamata ta cigaba da zama ana rigima a kanta ba.
Tana fita Ammar ma ya miƙe yabi bayan ta, Abinci ya zubo ya jata ɗakin sa suka zauna yana bata, sedai sam hankalin ta ba'a kan Abincin yake ba.


Yana bata yana mata hira, Amma sam taƙi sakin Jiki, ganin haka yasa Ammar yace
"Shirya muje kiyi musu sallama, mu tafi"
Ta jinjina masa kai, haka aka yi jiki ba ƙwari Mufeeda taje tayi wa su Umma Sallama, ta zaci Umma zata canza mata Fuska ko wani abun, Amma taga saɓanin hakan.
Mufeeda tasa hannu a Jakarta ta ɗakko dubu uku tace "Umma ga wannan, ki ɗau dubu ɗaya a ajiyewa Abba dubu biyu"
Girgiza kai Umma tayi tace "A'a Mufeeda, Nagode Allah yayi Albarka, Amma ai sunyi yawa, ki riƙe Abun ki, ga hidima tana tunkarar ku Allah ya raba lafiya"


Kunya ce ta kama Mufeeda, dan ba tayi zaton Umma ta gane tana da ciki ba, saboda bata cire hijjabin jikin ta ba.
Ammar kam ba kunya caraf ya amsa da "Ameen ya Allah Umma"
Mufeeda a ɗan Shagwaɓe tace "Amma Umma meyasa idan Yaya Ammar ya baki kike karɓa? Nawane bakya so ko?"
Gaba ɗaya Jidda ta tsani yarinyar nan, duk wani salon bariki ta iya.
Umma tai murmushi irin na manya tace "Aishi wannan ƙyale shi, suyi ta nemowa suna bamu muna cinyewa"
Ammar yace "yau dai na ganku a rana keda Umman"
Mufeeda tace "Dan Allah Umma karfa yayi mana dariya, Anty Maryam kisa baki mana"
Anty Maryam tace "Gaskiya Umma kar kisa Yayi mata dariya mana"
Da ƙyar Umma ta karɓa, tana ta mata Addu'a dasa Albarka kamar ta bata duniya, suka yi Sallama suka tafi.
Seda suka shiga Ammar ya nuna mata dabbobin ta, suna ta hayayyafa gwanin sha'awa, Sannan suka tafi.


Bayan fitar su Mufeeda Anty Maryam ta bawa Umma labarin abunda su Fa'iza suka yi wa Mufeeda, da yadda ta zauna a gurin ta bayan sun samu Saɓani, Abun ya daki zuciyar umma, tayi tayiwa Ammar faɗa idan Fa'iza tazo tace ya mata wulaƙanci.


Maryam tace "Wallahi Jidda ba kowace mace bace zata iya abunda Mufeeda tayi ba, na haƙuri da Ɗan uwan mu, Muddin kikayi dalilin kashe masa Aure wallahi kin cuce shi, kuma baze manta ba, nan ma Umma tai kan Jidda da faɗa, da taga alamun babu me goya mata baya, ta miƙe tai haramar tafiya, ranta a ɓace.


Ammar yaji daɗin Abunda Mufeeda tayi, dan be san zata basu ba, suna tafe a hanya yace
"Mufeeda Nagode sosai, Amma kuɗin da kika bawa su Umma yayi yawa, karki kwashe jarin naki fa"


Wata uwar harara tai masa wanda hakan ya shashi yin shiru, suka tari abun hawa zuwa unguwar su Mufeeda.


Suna yin Sallama ta tarar da Baba ze fita, ai da gudu ta tafi ta rungume shi, seda Ammar yaji tsoron karta jiwa kanta rauni, ko nauyin cikin bata jiba take wannan tsallen.


"Autar Baba naga kin zama ƙatuwa, Ammar me kake bata ne? Ta cinye maka tuwo ko?"


Murmushi Ammar yayi suka gaisa da Baba, Baba yace
"tunda 'ya' ya na sunzo bari in zauna muyi hira"
Ammar yabi Baba ɗakin sa, Mufeeda ta ƙarasa gurin Mama, Ta tarar da Yaya Fadeela, Yaya Fadeela ta hangame baki tana bin Mufeeda da kallo, Mufeeda ta rungume Mama tana Shagwaɓa.


"Mamana ina Missing ɗinki sosai"


Fadeela tace "Auta wannan ƙiba haka? Ke kuwa me kike ci haka?"


"Abunda kike ci mana"


Hira suka shiga yi, Fadeela tace "Auta a cire hijjabin mana, kowani salon ne kuma haka?"


"bazan cire ba ɗin"


"Autar Baba kodai kodai"


Hararta Mufeeda tayi tace "Kodai me?"


Ammar yai sallama a falon Mama suka gaisa, sannan yace ze tafi bayan la'asar zezo su tafi.
Mufeeda ta tashi ta tafi rakashi, suna fita Fadeela tace
"Mama kinga abunda nagani kuwa?"
Mama tace "A ina?"
"Kamar ciki ne da Yarinyar nan fa"
"Hmm Fadeela kenan, nagani mana se fatan Allah ya raba lafiya"


Mufeeda ta dawo falon suka cigaba da hira, tunda Mufeeda ta cire hijjabin ta Fadeela taga cikin Mufeeda har ya fito, ta dinga tsokanar ta.


"Mufeeda ni zan miki wankan Jego fa in kin haihu"


"Allah ya kiyaye, wallahi ba zaki minba"


"Ohh ni Fadeela, wai Mufeeda da ciki"


"Eh ya ranki? Shiyasa nake raina ki takuramin kike"


Haka Mufeeda suka wuni suna hira, Fadeela tana ta tsokanar ta, duk lokacin da Mufeeda tazo gida idan tana hira Mama tana fuskantar Mufeeda na cikin kwanciyar hankali, Ammar ya isa da gidan sa, ta dinga tuna lokacin da take ƙoƙarin hana Auren nan, yadda mazan yanzu suke se a hankali samun kamar Ammar se an tona.


**********************


Wata ɗaya da sakin Saima Jabir yana ta shirin Aurensa, Saura Sati biyu a fara biki, Amma Ammar, da Aminu sam basa goyon bayan Auren Jabir, dan haka sam besa su shirgin Auren sa ba.


Saima kam tana murmurewa, ta siyo form

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login