Showing 30001 words to 31350 words out of 31350 words
Chapter 11 - FATALWAR DEBORAHBook Complete By Mrs Sadauki.txt
mana gari wanda ya koma na matsafa” ta bani amsa.
“Ya ake gane matsafi?” na tambaye ta,ba ta bani amsa ba sai ido da ta tsura min har sai da na tsargu na ce “ Mama ya kike kallona haka sai ka ce ni ma dai MATSAFIYA(MRS SADAUKI) ce”
“Wane ne matsafi Naf?” ta jefo min tambayar.
Kai tsaye na ce “mai shan jini”
Sai ta girgiza kai ta ce “a'a ba ita ce amsar ba,a duniyar Ruhaniya sun fassara matsafi cewa duk wanda zai iya juya wani matakin iko ko kuma ya iya karantar tunanin wani to matsafi ne.Sai dai matsafan sun rabu kashi biyu,tsarkaku da kuma masu mugunta.Misali ni da ke ai kin ga aikinmu shi ne ceto al'umma,yayin da kuma tsohuwa mai kifi take muguwa”
“Ni da ke kuma? A'a ni ba matsafiya ba ce,Mama faɗa min ita tsohuwa mai kifi matsafiya ce ko mayya?” na tambaya sai dai ko kafin ta bani amsa Inna A'i ta fasa wani uban ihu tana cewa “wayyo idona”
Da wani mugun sauri duk muka miƙe tsaye,Mama ta ce “dama ai zuwanki nake jira shi yasa ban tafi gida ba.Ki bayyana kanki kafin na binciko ki ”
Na dube ta na ce “Mama ke da wa kike magana?” dariyar da aka ƙyalƙyace da ita ne yasa na samu amsata,na waro ido duk da ina son labarai da kuma horror film amma ai ban taɓa ganinsu a zahiri ba wannan yasa tsoro ya kama ni ashe hakan kuma shine babban kuskurena.Saboda ina firgita duk tsikar jikina ta tashi wannan kuma ya bayyana ɓoyayyar siffata wacce ban san da ita ba sai gani na yi akaifuna na ƙara yin tsayi suna yin tsini daidai nan kuma tsohuwa mai kifi ta bayyana a gare mu.Sai na rasa da wacce matsalar zan ji,dukkan jikina rawa yake.
“Hahaha! Ƙaramar matsafiya har ke ce za ki wani je tare ma wani faɗa?” tsohuwar ta faɗa tana kallona kafin ta mayar da dubanta ga Mama ta ce “ oh! Uwar Sadauki ko kashe ni za ki yi irin wannan hassala?” jin furucinta yasa na juya na dubi ɓangaren Mama,wani uban ihu na fasa tare da rugawa can kusurwar ɗaki ganin Mama ta juyar da idonta sun koma farare tasss kamar madara.
Nan dambe ta kancame a tsakaninsu har suka iso inda nake , tsohuwa mai kifi ta kama ƙafata ta gantsara min cizo ban san lokacin da na fasa wani mahaukacin ihu ba.Cike da jin haushi na caka mata yatsuna gefen wuyanta,zoben hannuna sai ya soma fitar da wani haske kafin can tsohuwa mai kifi ta ɓace ɓat.
Hannuna ya dawo normal sai dai inda ta cije ni ya fasa,da sauri Mama ta nufo ni tare da cire kallabinta ta ɗaure min ƙafar.
Ƴar ƙaramar jaka ta buɗe ta fata ta fiddo wasu abubuwa waɗanda na sha ganinsu wurin Uncle Salem.Hawaye na soma saboda ban son shan maganin nan,ina ji ina gani ta sa wata ƴar ƙaramar wuƙa ta tsaga ƙafata na ƙwalla wani uban ihu ina kiran sunan Uncle haka ta saka min magani kafin ta naɗe min ƙafar,sai ta bani maganin nan da ke kashe min jiki yana jefa ni duniya biyu mabanbanta.Baccin na gama ɗaukata kuma na tsinci ruhina a ɗakin darasi na matsafa,ina shiga sai na ji lamba ɗaya na cewa “ƴar rainin hankali sai yanzu kika damar zuwa?” ban kula shi ba na je na zauna kan kujerata na maida hankali kan darasin da Grand Maa ke yi.Yau kuma zane ta yi a jikin allo na wasu halittu maras kyawun gani kafin ta ce “a yau zan nuna muku yadda ake mayar da abin da ba yiyu ba a zai tabbata,sai dai ku sani hakan a iya ɓoyayyar duniyarmu da kuma masu irin ido uku kawai za su iya ganin abubuwan nan.Ba komai ne wannan abin ba sai fitar da abin da ka zana da hannunki izuwa wannan duniyar,wato ka mayar da zane gaskiya ta hanyar saka masa RUHIN ALJAN(MRS SADAUKI) bari na nuna muku kan wannan zanen” ta faɗa tare da taɓa wani zanen maciji tana faɗar formula na tsafi,sannu a hankali kuwa macijin ya soma yin motsi kafin kuma ƙyaftawar ido ya sauko ƙasa yana buɗe baki .Grand Maa ta ɗauke shi da hannu tana dariya kafin ta ce“kun gani babu wuya ko? Principal raba musu takarda da biro kowane daga cikinku ya zana abin da yake so” haka a raba mana takardu kowa ya shiga zanen abin da yake so,ni sai na rasa ma me zan zana can kuma na soma yin zanen ina murmushi ba tare da ni kaina na san mene ne zan zana ba a haka har na kammala.
Wasu takardun aka sake raba mana masu ɗauke da harafofin tsafi,Grand Maa ta ce su ne za mu karanta domin kawo abin da muka zana izuwa duniya.Bakina na soma motsawa ina kafen zanen da ido kamar yadda ta koya mana,kamar almara kuwa haka na ga ya soma yin motsi sai dai fa ya ƙi yin sauri kamar na kowa tun da tuni suka fara yin shewa suna jin daɗi wasu har sun fara yi min dariya.
Grand Maa ta ce “lamba uku ki nutsu da kyau ki aje esprit ɗinki wuri guda don aikin na son nutsuwa” ba tare da na ɗago na dube ta ba na jinjina kai tare da ci gaba da yin fafutukar fiddo shi amma ya ƙi,hakan ya hassala ni na ɗaga murya ina karanto harufan “huhannn!” zanen yayi wani irin kuka da yasa na zabura yayin da ajin yayi tsit.
Kowa ido ya buɗe da baki yana kallon abin da ya fito cikin zanen da na yi,yayin da Grand Maa tsabar tsoro ta ƙanƙame principal.
Da sauri na lumshe ido jin Dragon 🐲 ɗin ya soma lasar fuskata yana yin wani kuka kuma,na buɗe idon tare da kai hannuna na soma shafar saman kansa.
Headmaster na gani da sauri yana goge dukkan zanen da aka yi kan allo.Yadda na kafe shi da ido ƙila shi yasa Dragon ɗina kallon wurin,yana ganin sauran zanen da ba a goge ba ya fara yin wani kuka da yasa duk halittun da ƴan uwana suka zana suka soma ɓuya yayin da kuma Ajin ya soma girgiza takardu na tashi sama.
Headmaster jiki na ɓari ya bar jikin allon ganin my dragon ya soma feshin wuta yana ƙona dodannin da ke jiki.Kafin daga ƙarshe ya soma feshin wuta ta ko ina babu shiri duk suka shiga guduwa yayin ni kuma na yi tsalle na haye bayansa kawai sai ya tashi da ni sama yana shawagi.
“Nafisa? Nafisa?” na ji muryar Inna A'i na tashe ni,na buɗe ido dakyar ina kallon ta kafin na ce “lokacin sallah yayi?”
Ta ce “ina fa ! Gobara ce aka yi can cikin makaranta shine headmaster ya ce a tado ki”
Na miƙe ina kallon bakin ƙofa sai na gansa a tsaye sai gumi yake,na ce “to ni da ba namiji ba mene ne kuma abin tada ni kai agajin kashe gobara?”
Wani kallo ya watso min irin yana cike da takaicina ɗin nan,kafin ya haɗiye wasu yawu har sai da na ji ƙarar muƙut .Ya ce “ki zo mana Malama Nafisa duk kowa fa ya fito ke ake jira”
Ina shirin yin magana aka buɗe ƙofar toilet sai na ga Mama ta fito hannunta riƙe da bokitin ruwa,ta miƙa min shi tana cewa “ki dai je ai taimako babu ruwansa da mace” na karɓi bokitin na zura takalmina ko hijabi ban saka ba haka na fita zuwa can inda wutar ke ci ,abun mamaki a wuri guda take sannan duk ƙoƙarin kashe ta da suke ta ƙi raguwa amma ina watsa ruwa ɗaya da bokiti ta soma mutuwa ko minti biyu ba a yi ba kuwa duk komai ya tsaya cak sai biɗiɗin hayaƙi da yake tashi.Da yake ni har yanzu doluwa ce sam ban ga abun almara ne ba koma wanda hankali bai ɗauka,sai ma murna da na yi wutar ta mutu.Na juya zan tafi na ji muryar Grand Maa na cewa “ina za ki je? Kin ɗauka haka za mu bar ki ne ki tafi bayan duk uwar asarar da kika yi mana”
Da mamaki na ɗago ina dubanta,sai kuma na ga dukkan sauran malaman sun zagaye ni kowane yana murmushin mugunta....