Showing 18001 words to 21000 words out of 31350 words

Chapter 7 - FATALWAR DEBORAHBook Complete By Mrs Sadauki.txt

Advertisement

04 Mar 2025

4661

ka zo?”
“ Sai zuwa wani satin Naf,yanzu akwai binciken da zan yi”

Kafin na basa amsa sai da na juya na dubi Inna A'i wacce ta zagaya toilet a karo na uku tun lokacin da na soma waya,ina son tambayarta lafiya amma saukar numfashin Uncle a kunnena yasa na ƙara mayar da hankali wurinsa.
“ To Uncle zan fara lissafin kwanaki tun yanzu”
“Faɗa min me za ki shirya min na special?” tambayar da yayi min kenan wacce na ji wani banbarakwai don har wani salo na daban amon muryarsa ke fitarwa.Kamar zai yi kuka na ji yana cewa “ Please Naf faɗa min mana kar ki ji kunyata ” hakan kuwa ya ƙara ɗaure jijiyoyina na rasa amsar da zan basa,daga can toilet na soma jiyo saurin nishin Inna A'i cikin azaba babu wani tunani na kashe kiran Uncle ɗin tare da nufar toilet ɗin ina tambayar lafiya.Ba ta bani amsa ba sai ƙofar toilet ɗin da ta buɗe ƙiiii da kanta,daga inda nake tsaye na hangi Inna A'i zaune kan wc tuni ta fita hayyacinta don da alamu gudawa ce take ta yi.
Tsakaka na gani kan katanga tana saukowa kamar za ta faɗo bisa kanta da mugun sauri na ɗauki takalme ina kiran sunan Allah na kashe tsakar,ta kuwa faɗo ƙasa bindinta ya rabu da gangar jikinta da mugun sauri kuma ta bi ta ƙafafuna shuuu ta fice ta bar guntun bindin wanda sai motsi yake.

Daidai nan Inna A'i ta soma kelaya amai kamar hanjinta za su faɗo,ba tare da tsantsani ko ƙyanƙyaminta ba na taimaka mata ta yi wanka ,bayan nan na sa abin kwashe shara na saka bindin tsakakar sannan na wanke toilet ɗin na rufe ƙofa.Ina zuwa tuni Inna A'i ta yi bacci,ni ma sai na raɓa gefenta na kwanta.
Washegari bugun ƙofar ɗakinmu ne ya tashe mu,yadda ake jijiga ƙofar kamar za a ɓallata yasa muka kalli juna kafin na miƙe na je na buɗe,da sauri na yi baya ina kallon shugaban makarantar da mamakin abin da ya zo nema a yanzu ko ƙarfe shidda ba ta yi ba.Yadda kuma yake yi min wani kallon tsaf yasa na sha jinin jikina......


Ga mai son shiga paid group 500 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

Sai ya turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________

6-7


Na haɗiye wasu yawu muƙut, Allah na gani ba na cikin mutane masu mugun tsoron nan don za a iya kirana jaruma kai tsaye amma kallon idon headmaster kaɗai sai da suka hautsana hanjin cikina.

“ Barka da warhaka shugaba!” na samu bakina dakyar ya furta.
Ya saki wani murmushi wanda kana gani ka san ba na jin daɗi ba ne kafin ya ce “ lafiya! Ina son duba toilet ne don ganin ko gyaran da aka yi yayi” ya faɗa cikin wani irin amo.
Kamar na ce masa wane gyara kuma amma sai na basa wuri ya shigo,cike da girmamawa ya gaishe da Inna A'i wacce ke zaune har yanzu a inda na bar ta kafin ya shiga cikin toilet ɗin na take masa baya kuwa.Dube-dube na ga yana yi kamar mai neman wani abu amma ban kawo komai ba don na yi tunanin ko gyaran ne a gaske yake dubawa .

Fuskarsa duk ta nuna alamun ƙin jin daɗi har zai fito sai kuma ya tsaya cak yana cewa “jinin mene ne can?”
Inda ya nuna na duba sai na ga daidai wurin da na kashe katsakakar jiya ne,amma ai na wanke toilet ɗin sosai ta ya aka yi jinin bai fita ba.

Yadda ya watso min idonsa masu matuƙar dafi yasa na soma inda-inda,“ dama...dama jiya ne da Innarmu ta shiga ta ga tsakaka...” da sauri ya katse ni “ kenan ita ce ta buge mata bindi? ”
Tsuru-tsuru na yi don ina tsoron kar ya kore ni ya ce ba zan koya ba,ya ƙanƙance ido ya ce “mu nan garin ba a kashe ƙwari ban san daga wane wajen kuka fito ba” sai kuma ya fita ni ma na take masa baya,ina kallon yadda ya bi Inna A'i da wani mugun kallo kafin ya fita.


Ɗakin na rufe bayan na gama kallon yadda har a wajen sai da yayi ta dube-dube.
Ko da na juyo sai na ga tuni ta shiga toilet,sai na jira ta fito sannan na shiga ni ma na yi alwala na fito na yi sallah sannan na zauna na yi Azkhar ɗin safe.

“ Ina kwana Innarmu? Ya ƙarfin jikin naki?” na faɗa bayan na gama komai.
“ Alhamdullah ai na ma warware,ina ga kajin jiya ne suka buga min ciki don na yi doguwar tafiya” ta bani amsa .
Na ce “ ai kuwa dai ,yanzu ki kwanta ki huta dai zuwa an jima sai ki yi mana girki”
Ta ce “ a'a na fa warke yanzu zan shiga kitchen“ tana gama faɗa ta miƙe kuwa,ni kuma na ɗauki wayata nan na ci karo da miss call ɗin Uncle Salem ya fi goma duk yayi su ne bayan na kashe kiransa na jiya.Ɓangaren saƙo na duba sai na ga text ɗinsa yana bani haƙuri tare da alƙawarin ba zai sake ba.


Kiransa na yi sai dai sam lambar ba ta shiga,duk sai na ji babu daɗi haka na kunna data na soma yin shat ban ajiye wayar ba sai da na ga ta kusa mutuwa sannan na saka ta caji.Ina shirin shiga wanka na ji ana shelar ana son ganin dukkanin malaman da suka zo a ɗakin meeting da ke cikin makaranta da misalin ƙarfe takwas da rabi .


★Uncle Salem


Cikin kaɗaicin son kasancewa da Nafisa ya soma bijiro mata da sabbin abubuwan da za ta fahimci shi mijinta ne amma da dukkan alamu ya ga sam ita a iya uban kawai ta yi masa matsuguni.Jin ta kashe masa waya yayi tunanin kunya da kuma fushi ne yasa ta datse kiran,hakan yasa yayi ta jera mata su da ya ga ta ƙi ɗauka sai ya tura mata text tare da kashe wayar ya rungume pilow.Zuwa yanzu haƙurinsa da juriyarsa sun yi ƙasa sosai,yana matuƙar son kasancewa da ita a duk cikin sati ranar juma'a da asabar kawai a bai yin azumi duk don kare mutumcinsa.Sau ɗaya tak ya taɓa neman auren wata wacce dama ita ce take haukan sonsa,amma an zo yin auren aka fasa saboda bai da wani asali.


Idonsa sun kaɗa sun yi jajur saboda abu biyu da suka haɗe masa, feeling da kuma fushin Naf wanda a duniya in akwai abin da yake guje ma to bayansa yake shi yasa a kowane lokaci yake yi mata abin da take so.Ko da kuwa iyayenta sun so nuna masa illar gatan da yake yi mata sai ya ce musu har yanzu Naf yarinya ce.Sai dai a jiya da Daddy ya ce masa ya ci a ce ta tare da kuma yadda ya ga surarta cikin doguwar rigar da ta lafe jikinta duk ta fitar da shap ɗinta sai yake ji a ransa eh za ta iya ɗaukar nauyin buƙatarsa.

Juyi yayi ta yi a daren,da ya ga dai sam baccin ba fa zai zo ba sai ya miƙe ya je watso ruwa tare da zama kan dadduma yayi ta lazumi bayan raka'o'i biyu da yayi.Sai daf da asubah ya samu bacci,amma duk da haka ana kiran sallah sai da ya je masjid da ke nan cikin Company ya dawo ya ƙara komawa bacci.Bai farka ba sai wuraren ƙarfe goma na safiya,wani wankan ya sake tare da shirya wa cikin wando tree quater na sojawa da kuma rigarsa t-shirt ita ma ta kakin soja.Bai ɗora hulla ba ya dai saka farin gilashi kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ta aiki da kuma wayarsa.Sai da ya fito a hanya ne ya kunna ta,bayan ya shiga mota ne ya ga saƙon cewa Nafisa ta so kiransa amma ba ta same shi ba.Ya ɗan saki murmushi yana jin zuciyarsa ta yi sanyi ko ba komai yana da tabbacin ta sauko daga fushin da take.Kiranta yayi har sau biyu,a na uku ne Inna A'i ta ɗauka ta shaida masa ta fita.



★ƘWARGWAM


Ko da na fito daga wanka tuni Inna A'i ta soya min dankali da kuma ƙwai,na yi zaune na ci na ƙoshi kafin na jawo kayan kwalliyata na shafa mai da turare har da hoda.Bayan nan na zaɓo doguwar riga ta tambaya ƴar côte d'ivoire,sosai ta amshe ni sai na zaɓo hijabi da jaka da kalmi duk waɗanda za su hau da ita.


Ina shirin fita ita ma Inna A'i ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kwanon miya na jiya,ta ce “ ashe ba ki ci abincin nan ba dubi yadda duk yayi tsutsotsi ya lalace”

Na dubi cikin kwanon na ga babu kyawun gani manyan tsutsotsi ne ke ta yawo suna shige da fice cikin ragowar naman kajin.Da mamaki na ce “ amma kuma abincin har ya isa lalacewa haka?”

“ Ni ma haka na ce,ko ƙila zafi” Inna A'i ta faɗa .
Na ce “ kawai ki zubar ki wanke kwanukan sai ki mayar musu ,ga key nan in za ki fita ki rufe ɗakin na tafi sai na dawo”
“Allah ya tsare hanya”

Na ce Amen ina mai yin addu'ar fita daga gida.Kamar yadda ƴan magana ke cewa in ka yi boko to ƙauyancinka ragage ne hakan yasa duk da ban san ko ina na makarantar ba haka na dinga karanta duk wani allon sanarwa da na gani har na dace da ɗakin meeting.


Da isa ta sai na tarar duk kamar ma kowa ya zo ni ake jira,sallama na yi tare da samun wuri na zauna kusa da wata wacce na ga tana sanye da hijabi saɓanin sauran matan da ke wurin duk sun ci uban ado an ɗora mayafi.
Babu jimawa kuwa manyan namu suka suka shigo,duk muka miƙe tsaye don nuna girmamawa kafin mu zauna.


Ɗaya daga cikinsu ne ya soma yin magana ,su biyar ne huɗu maza sai mace ɗaya.
“Yawwa da farko muna yi wa baƙin malaman School Ƙwargwam Barka da zuwa,kamar yadda kuka sani duk faɗin garin nan wannan ita ce kawai makarantar da ake koya karatun boko da sauransu...” sai yayi wani murmushi wanda yake ɓoye wata manufa kafin ya ci gaba da cewa “ Ƙauyen Ƙwargwam na zagaye da ƙauyukan maƙota guda huɗu,shine a tsakiya sannan dukkan sauran ƙauyukan nan a wannan makaranta tamu mai farin jini suke zuwa ɗaukar darasi.Kar dai na cika ku da surutu,ina son waɗanda za su koyawa ƴan sakandari su koma layin nan duk su zauna” ya nuna wani layi,nan duk wasu daga cikinmu suka ware kansu nan ne na fahimci wato ba iya primary ba ce kenan school ɗin.

Kamar kuwa ya karanci tunanina sai ya ce “ makarantar ta kashi gida uku ne,da farko Sakandari sai ya nuna layin malaman kafin ya ce wannan shi ne Principal ɗinku ku da ɗalibanku,ƴan primary kuma ga naku shugaban headmaster sai ya nuna mutumen nan na jiya da ya kawo min abinci shi kuwa har da yin wani murmushi.Ina so duk ku basu girmansu,ni kuma mai yin magana ni vice headmaster,wannan kuma vice principal ya nuna ɗayan namiji ,daga ƙarshe sai wannan kuma ita ce Grand Maa mai makarantar ce ofishinta shine dogon nan mai jan penti in kuna da wata matsala ko wani abu da ya shige muku duhu ita ce za ku je ku yi wa magana” bayan duk ya gama nasa jawaban su ma ɗaya bayan ɗaya suka yi nasu kafin su faɗa mana fatansu da kuma tsarin makarantar wanda tun da nake ban taɓa jin irinsu ba amma haka na ja bakina na yi shuru.


Bayan an gama meeting sai wasu matasa suka shigo suka soma rabon coffe mai shegen ƙamshi.Ana bani na karɓa ina kallon ruwan coffe ɗin waɗanda a tsakiya aka shatin zuciya,na dubi na maƙwabciyata na ga ita ma nata haka yake.


Na yi shuru ina tunanin ko sai yaushe zan fara soyayya oho.
“Madam Nafisa ” Muryar headmaster ta katse min tunanin na ɗago muka haɗa ido,ya sakar min murmushi kafin ya ɗaga kofin hannunsa kamar yadda Turawa ke yi mai nufin Bismillah.
Na ɗan murmusa kafin na soma kurɓa ina ganin lokacin da ya saki murmushi ,a baki coffe ɗin har ya fi daɗi kan kyawunsa a ido.

Bayan mun gama sha ne aka rabawa kowa ajin da zai koya ,sai kuma duk muka miƙe Grand Maa sai ƙara jadadda mana take gobe tun ƙarfe bakwai na safe kowane malami ya tsaya bakin ƙofar ajinsa.

Muna fitowa na cewa wacce muka zauna kusa da juna,“mene ne sunanki?”
“Adama,ke kuma fa?”
“Ni kuma Nafisa”na bata amsa nan muka so yin masayen lambobi sai dai ni na bar wayata can gida tana caji a dole ni na bata tawa na ce sai ta ɗago min hannu.

Ina zuwa bakin ƙofar ɗakina sai na tarar da shi a rufe.Sai na zauna kan ƴar matakalar da aka yi bakin ƙofa na tsaya jiran Inna A'i don babu tantama gidan headmaster ta je.Ni kaɗai ce a wurin amma haka nake jin ana magana kusa da ni irin sosai ɗin nan,da na waiga ko ina kuma babu wanda na gani.Shuru na yi ina tunanin ko dai kunnuwana ne amma abin mamaki sai na ji ana dariya,da sauri na dubi inda sautin ke fitowa wani ɗan rame na gani irin na gidan tururuwa tabbas a ciki nake jiyo sautin amma sai aka yi tsit na wani lokaci.

Ni kuwa da son jin ƙwaƙwaf na duƙa tare da kai kunnena ƙasa ina saurara,ƙafafun mutum na gani tsaye kusa da ni.Da sauri na tashi sai na ga headmaster ne,yayi min kallon nan nasa kafin ya ce “me kike yi haka a waje?”
Na ƙaƙalo murmushin yaƙe na ce “na zo na tarar Innarmu ba ta nan ne shine na tsaya jira har ta dawo”
“Kuma kin yarda za ta dawo ɗin?” ya jefo min tambayar wata iri,ni kuma da yake ba wani damuwa na yi ba na ce masa “ eh za ta dawo ai ita ce za ta zauna da ni har mu koma”
“Hum!” ya ja wani ƙyaci kafin yasa key ya buɗe min ɗaki,na yi masa godiya tare da shigewa ciki.

Har zan shiga wanka na soma jin ƙaurin ƙonewar abinci,da sauri na shiga kitchen na kashe gas ɗin .Bayan na yi wanka na fito na yi mamakin da ban ga Inna A'i ta dawo ba,wayata na cire a caji na duba sai na ga Uncle ya kira ni sai na mayar masa ya ɗauka.Muka fara gaisawa kafin na ce “ Uncle ina ne za ka je na ji kamar kana driving?”
“Wurinki mana ko ba ki so?”
Cike da murna na ce “ wai Uncle da gaske?“
“ Na taɓa yi miki ƙarya? Ke dai kawai ki shirya tarbena don na kusa zuwa sai an na iso” yana gama faɗa ya kashe,ni kuma cike da zumuɗi na miƙe na soma gyara ɗakin na shiga kitchen na fara duba abubuwan da duk muka zo da su na haɗa masa lemun zoɓo na jona ƴar ƙaramar frigine ɗin da ke nan a kitchen na saka.

Haka na zauna na yi ta yin abubuwan da na san yana so kafin isowarsa.Aikin da na duƙufa shi ya mantar da ni wani cewa Inna A'i ta fita,haka na wuni ni ɗaya sai dab magrib ne Uncle Salem ya kira ni ga shi ya iso ni na je na tarbo shi can fara isa makaranta.Gidan gaba na shiga ya tuƙo motar yayi parking nata daidai ɗakina,nasa sabon key ɗin da headmaster ya bani na buɗe sannan muka shiga .A gajiye yake wannan yasa ya soma shiga wanka,ko da ya fito tuni an soma kiran sallah da sauri na ɗauke idona ganin ya fito babu riga daga shi sai farin towel ya ɗaura a ƙugu.
A ɗan daburce na ce “ Uncle ga kayan buɗa bakinka”
Bai ce komai ba sai gefen katifa da ya zauna haka nan ya ƙi saka kayan,da kansa ya zuba zoɓon don dai ni ba zan juri kallonsa a haka ba na shige toilet na ɗauro alwala .

Da zan fito sai da na ɗan ziro kai don ganin ko ya saka riga sai dai karaf muka haɗa ido da shi,yana nan kuma a inda na barsa.Ya sakar min murmushi yayin da ni kuma na fito cike da kunya,kaina sunkuye na ɗauki dadduma na soma yin sallah ko kafin na gama ya canza kaya ,a nan ɗaki shi ma yayi sallah gefena kan nasa daddumar.

Hannuna ya kamo da nake ta yin Azkhar ɗin yamma da ban samu na yi bayan sallar asar ba.Wani irin sanyi ne nake ji yana ratsa ni ga tuwon tafin hannunsa sai wani matse min nawa yake .

“ An gama yi wa Uncle ɗin fushi?” ya tambaye ni yana murmushi mai sauti.
Na ce “ ni ban yi fushi ba”
“ Kalle ni” ya faɗa ,a hankali na dube shi ɗin idonmu ya sarƙe cikin na juna ina son kawar da kai amma tamkar wacce ya yi wa dabaibayi na kasa.A hankali na soma sauke ajiyar zuciya ,tsawon lokaci muna a haka kafin ya buƙaci in zuba abin da na dafa mu ci.Jiki duk a sanyaye na zuba muna ci muna aukin kallon juna har muka gama,ana kiran sallar isha'i na miƙe don gabatarwa amma ya katse ni “je ki yi ɗahara ki sake alwala”

Ban musa masa ba don ba ya daga cikin halayena yin gardama a gare shi.Da mamakina kuwa da na shiga toilet alwalata ta karye iya ɗan kusanci da muka samu kawai,amma sam ban kawo shi wai don wannan niyyar yasa ya ce na je na sake alwala shi yasa ko da na fito ban wani ji kunyarsa ba na haye dadduma,shi ma sai da ya sake yin wata alwala kafin ya yi sallah.


Hira muka soma yana tambaya ta meeting ina basa amsa cike da sakewar fuska kafin na soma jin cikina na yin ciwo,tun ina daurewa har na kasa.
“ Je ki kwanta” cewar Uncle ,ina cije leɓe na haye katifa tare da yin rairan ina duban sama dafe da cikina.

Jakar da ya zo da ita ya buɗe sannan ya ɗauko wasu kwalabe yayi wani haɗi cikin kofi ,kafin ya cika bakinsa da ruwan ya zo ya ɗora shi kan nawa.Na buɗe bakina na dinga haɗiye ruwan maganin a hankali ina lumshe idona har na shanye duka,ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login