Showing 12001 words to 15000 words out of 31350 words

Chapter 5 - FATALWAR DEBORAHBook Complete By Mrs Sadauki.txt

Advertisement

04 Mar 2025

4660

bandeji.
“ Wani ne” ya bani amsa,da ido na ƙara kafe hoton don kuwa ni dai yayi min kyau sosai har ban san lokacin da na ce “ yana da kyau sos...” yadda Uncle ya ƙware ya shiga yin tari ya hana ni ƙarasa abin da nake son faɗa,da sauri na je na kawo masa ruwa ya karɓa tare da rufe system ɗin ya soma sha kafin kuma ya miƙa min kofin ya je ya kwanta kan kujera mai zaman mutum uku yana wani jan numfashi tuni na tsure wuri guda ina kallonsa....
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________

03

Jikina na ɗan rawa na isa gare shi ina mai zube wa ƙasa daidai kusan kansa na ce “ Uncle?” shuru yayi min bai ce komai ba haka ya ƙi buɗe idonsa,hakan sam ba ƙaramar barazana ba ce a gare ni don gani nake na yi masa laifi ne har ya sa shi ƙwarewa amma ban san taƙamaimai mene ne ba.

“ Uncle?” na ƙara faɗa wannan karon ina mai kai hannu ina gwale fatar idonsa a dole so nake ya buɗe su ya kalle ni,na kuwa ci nasara ya buɗe su sai dai yadda suka yi ja sosai har sai da na ji tsoro na ɗan ja baya.

Murya a disashe kamar wanda ransa zai fita yana kokowa da numfashinsa ya ce “ Nafisa me na faɗa miki? Ban ce kar na saki ko da wasa kin ce wani namiji yana da kyau ko kuma ki kalle shi ba?”

Na ɗan ja ajiyar zuciya tare da matsowa na ce “ ka yi haƙuri Uncle ba zan sake ba,amma saboda me Uncle? Ka ga fa duk ƙawayena suna da samari ni amma ka hana ni kuma...kuma kamar mai baƙin jini maza sun tsane ni ” shaaa hawaye suka zubo min tuna yadda ko a makaranta ƴan ajinmu ba su shiga duk abin da ya shafe ni,kusan kuma malamanmu maza ma haka ba kasafai suke saka ni yin wani abu ba,in an zo nan ta wurin ƙannaina da kuma mazan da suka zo karatu a gidanmu su ma duk hakan ce ke faruwa.


Ba tare da ya ce min komai ba ya tashi zaune haɗi da ɗan duƙewa ya dafe saitin zuciyarsa,ina ganin haka sai na miƙe da sauri har ina tuntuɓe na nufi bedroom ɗinsa na ɗauko masa maganinsa.Na cika kofi da ruwa tare da ɓallo ƙwaya biyu na miƙa masa ya karɓa tare da sha,cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yin wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ ki je ki haɗa kayanki,zuwa jibi sai na kai ki can ƙauyen da za ki koya”

Duk ƙuncin da ya cunkushe min zuciya ne ya tafi ban san lokacin da ƙawa zuci ya ja ni ba kawai na rungume shi ina cewa “ na gode sosai my Uncle,kenan har ka yi magana da Daddy ya amince wayyy!” na yi ihun murna ina jijiga bayan Uncle da na rungume tsam a ƙirjina kafin kuma na sake shi da gudu na bar falon.


Ina shiga ɗaki na tarar da family na cin abinci,ɗakina na nufa na shiga sauko da akwatina ko taimakon masu aiki ban nema ba na soma shirya kayana ina yi ina murmushi ina jin daɗi na luluɓe min ruhi.Sai hoton kaina nake gani a cikin aji ina koyar da darasi wa ɗalibaina,ban zauna ba sai na haɗa duk kayana na jiki da kuma jaka da takalma.


Takardu da littafaina ma trolly daban na ware musu kafin na miƙe ina yawo cikin ɗaki ina magana ni ɗaya kamar irin yadda malamai ke yi.A hankali na soma jin ciwon kan da ya zame min aboki tun na ƙurciya na ziyartata,tun ina daurewa har na kai na kasa jurewa na haye bed na kwanta.Mafarkin da na jima ban yi ba tun shekaru kusan uku shine na soma yi kamar ana jirana.


Tsaye nake kan ƙafafuna na mage ina juya idona masu matuƙar haske da hange nesa tamkar na Alhuduhudu. Manyan-manyan dabbobin daji ne a tsaye a gabana suna buɗe min bakunansu masu manyan haƙora yayin da ni kuma ke ankare da kowanne daga cikinsu kafin mu soma yin dambe ina jibgarsu duk na yi musu jina-jina da jini kafin wata halitta mai siffar babban sauro ta caka min bakinta daidai cikina .Azabar da ta ratsa ni ce yasa na saki wani razananen ihu,daidai nan na farka sai dai abin mamaki daidai wurin da aka cake ni ɗin har a zahiri ciwo yake yi min.


“ Lafiya Nafi?” Ammy ta faɗa wacce ta shigo yanzu hankali tashe,ido na soma juyawa amma na kasa faɗa mata don ko na ce zan faɗi abin da na gani a mafarki kamar abin tsayi sam bakina ba zai iya furtawa ba.

Hawaye kawai nake yi,sai shi ma Daddy ya shigo yana tambayar lafiya.Kai kawai na girgiza masa ,ya zo ya kamo hannuna ya ce “ kina ji na Nafisa faɗa min mafarkin me kika yi?” da sauri na janye hannuna daga cikin nasa,na diro daga kan bed na nufi ƙofa.
Sai kuma na yi tsaye ganin Uncle shi kuma zai shigowa gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala ce yayi.
Haɓata ya tallabo ta yadda zai iya kallon fuskata da kyau ,tsakiyar idona ya dinga duba yana wani motsa baki kafin ya ce “kin kuwa yi Azkhar yau?”

Idona na soma juyawa ina son kauce kallon nasa da ba ƙaramin takura min suke ba,sam babu daɗi ji nake kamar yana zuƙo raina ne.
“ Kin yi Azkhar na ce?” ya sake tambayata.
Kai na girgiza alamun a'a,don kuwa ban yi saboda tun asubah na samu saƙon cewa sunana ya fito a jerin waɗanda za su je bautar ƙasa wannan zumuɗin ya shagaltar da ni yin Azkhar kamar yadda na saba.


Ya sake ni kafin ya ce “ biyo ni” sai ya juya,haka na take masa baya ina waiwayen su Daddy muka fita zuwa can sashensa da yake waje.
Ɗakin Uncle Salem ciki biyu ne da falo,ɗakinsa guda na bacci guda kuma wanda yake zuba kayan maganin aljanu na ruƙiya.Direct ɗayan ɗakin muka shiga,kaina ne ya juya da na shaƙi warin magani iri-iri yayin da gefen cikina daidai inda aka soke ni ya soma motsi har sai da na danne wurin.

“ Zauna a nan” Uncle ya nuna min wata doguwar kujera,babu muso sai na zauna ɗin.Wata kwalba ya ɗauko tare da zuwa kusa da ni ya zauna kafin ya buɗe ta,tun kafin ya ce min na sha na soma hawaye don ni kaɗai na san irin abin da nake ji a duk lokacin da ya bani ire-iren maganin nan.

Bakina ya taɓe tare da ɗura min maganin,jikina ya ɗauki rawa kafin cikin fitar hayyaci na soma basa labarin mafarkin da na yi tiryen-tiryen.Kwantar da ni yayi yana mai jan doguwar rigar jikina sama,da sauri na rumtse ido lokacin da ya janye hannuna ya ɗora nasa a daidai wurin da ake ta yi min motsi.


Teburin da ke ɗauke da tarkacen da shi kaɗai ya san na mene ne ya jawo,ina ji ina gani da raina Uncle Salem ya soma tsatsaga fatata da reza.Banda wani zaɓi banda hawaye don tuni maganin da ya bani ya kashe min dukkan jijiyoyin jiki sai kaina da ke faman juyi tamkar an jefa ƙwarya a ruwa.



Wata kwalba ya ɗora daidai wurin ya soma tatsar jinina har ƙarar fitarsa kake ji,kamar minti biyu kafin ya cire kwalbar ya ajiye ta kan teburi.Wani magani ya shafa min a daidai ciwon mai bala'in zafi,har sai da raina ya kusa fita kafin da sauri ya cika bakinsa da wasu ruwa ya zo ya fara shayar da ni su.Duk ɗigo ɗaya na ruwan da zan sha to tamkar ana warware azabar da yake jikina ne , wannan yasa nake shan maganin cike da zalamar da ta haifar min da soma shan yawunsa da kuma laɓansa.


Jikin Uncle Salem ne ya ɗauki wata irin rawa jin Naf ɗinsa na sumbatarsa kamar za ta cinye leɓensa,duk wani tsohon feeling nasa da yake faman yin ƙasa da shi a kowacce safiya ya soma taso masa.A daidai gaɓar da ya soma mayar mata da martani kuma tuni bacci ya ɗauke ta,idonsa na fitar da wasu irin hawayen jaraba ya soma sunsunar wuyanta yana jin tamkar ya mayar da ita cikakkiyar mace ko zai samu salamar ruhi.


Dakyar ya rareashi kansa ya janye daga jikinta,daɓas ya zauna yana duban yadda take baccin wahala . Ƙonannen jinin mai tattare da guba yayi baƙi ƙirin a cikin kwalba,sai ya ɗauke shi ya je ya zubar toilet ya wanke kwalbar.

Sai da ya je ya sake wata alwala sannan ya nufi masjid,a can ya samu Daddy bayan sun yi sallar sun fito ne Uncle Salem ya dubi abokin nasa ya ce “ Abdul Hameed ban san me yasa ka zaɓi ka ɓoye min rufaffen sirrin Nafisa ba,amma hakan bai da wani amfani don kusan na fahimci matsalar junun da ke jikinta ya samo asali ne daga can tushe ba wai gamo ta yi da su ba”

Cak Daddy ya tsaya yana kallonsa, Uncle Salem ya jinjina masa kai ya ce “ tabbas ko yau sun ziyarce ta,saboda sakacin addu'ar da ba ta yi ba”

Daddy ya ce “ mu je can gida zan yi ma bayani” haka suka wuce suka isa,a keɓaɓen falon Daddy duk suka zauna tare da yin shuru Uncle Salem ya matsu ya ji labarin yayin da shi kuma Daddy ya rasa ta ina zai soma.Can ya nisa tare da furzar da huci kafin ya ce “ to da farko dai kamar yadda na faɗa ma ni ɗana ga sarauniya Ayodele Ayush,kafin zuwan Musulunci a Victoria Falls suna bautar ababen bauta iri-iri ,yin tsafi kuma sai ya zama adon garin.Sai dai sannu a hankali duk komai ya canza saboda yadda mahaifina sarki Ameer ya taka muhimmiyar rawa ganin ya kawar da duk wani fasadi sai dai kash zuwana duniya kuma aka tsiro da wasu sabbin canfi wai alamomi sun nuna za a sake yin maimaici wato daga cikin tsatsona za a samu wacce za ta jagoranci mulkin ƙasar.Amma tabbas ni ba magajin sarki ba ne,sosai na ji tsoro da jin haka don tamkar karatu haka ake biya min maganar nan har na mallaki hankalin kaina”

Uncle Salem yayi saurin katse shi da cewa “ haba aboki ta ya za ka yarda da wani canfi?”

Daddy yayi murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ya ce “ dole na yarda mana,duba da tun ina ɗan shekara ashirin a duniya na ajiye iyali saboda yadda kullum nake kasa bacci ina harin neman abokiyar rayuwa wacce zan jefar wa da ƙwan haihuwar shugabar gobe ko zan samu sukuni ”
Uncle Salem ya ce “ kana nufin wai Naf?”

Daddy ya jinjina kai ya ce “aboki tun lokacin da na yi aure zan ce ma wannan larurar da ka san ni da ita ta mugun feeling ta kau,shi ma tun a daren farkonmu.Sannan kana dai ganin yadda lamarin aurena ya kasance a sirrance sai daga baya iyayena suka sani,har bisa yanzu sarki fushi yake da ni saboda na ƙi yarda na zauna a can Victoria Falls ni kuma ina gujewa Nafisa ƙalubalen da za ta fuskanta ne in ta zama shugaba”


“To amma mene yake baka tabbacin cewa hakan za ta kasance?” Uncle Salem ya tambaya .
Daddy ya ce “ saboda kama take da wata goggon Mamana ita ce mace ta biyu da ta mulki Victoria,to yadda ka ga Nafisa ita ma haka take kai kace tsaga kara ne aka yi.Hakan kuma babbar matsala ce domin zai iya kasancewa ita ta dawo duniyar nan a gangar jikin Nafisa ”

“ Wai ko sarauniya Deborat?” Uncle Salem ya tambaya,don kuwa ita ɗin ba ɓoyayya ba ce a duniyar nan duk kusan labarinta ya karaɗe ƙasashen duniya saboda shahararta wurin iya yin tsafi,sai dai ko kafin Daddy ya ce wani abu tuni tv ɗin da ke manne jikin bango ta soma yin wata tsaga “ƙiiiii!” kafin kuma ta faɗo ga ƙasa ,sai iska kuma mai ƙarfi wacce ta haifar da fashewa ƙwan lantarki ji kake ɗuuu haskensa ya ɗauke sai labulaye suka soma tashi sama suna wulwulwul....
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________


04


A cikin duhun ɗakin ne Daddy da Uncle Salem suka hango wata mace sanye da fararen kaya wanda ko tantama babu likafani ne.A tsaye take jikin window sam ƙafafunta ba su taɓa ƙasa ba sai wani lilo suke kamar wacce aka rataye,farin gashin kanta kuwa sai yin sama yake iska na naɗa shi.

Cikin muryarta wacce kana ji ka san ba ta ɗan adam ba ce ta soma yin magana,“ ko kai ko abokinka babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake,Yarima Abdul Hameed ban sani ba ko ka san cewa sunan Deborat ya haramta ga duk wanda yayi hijira ya bar gidansu domin guje abubuwan da allolinmu za su zartar,ka sani cewa Nafisa jaruma ce ba mu zaɓe ta ba sai da sanin za ta iya.Sannan ka godewa Allah da ya kasance aikin alkhairi ne za ta gudanar ba wai na cutar da al'umma ba,sannan kai kuma da kake ta ƙoƙarin dakatar da mu ziyartar ta ka sani akwai lokacin da maganinka ba zai yi aiki a jikinta ba don haka gara ka baiwa kanka lafiya ka bar matarka ta yi aikinta yadda ya kamata.A tunaninka hatta auren naku ba mu sani ba? Mun sani sarai saboda kai ne za ka yi jinyarta a lokacin da ta kammala aikinta na farautar azzalumai ” tana gama faɗa kawai ta bi ta window ta fita yayin da kuma komai ya dawo normal hatta hasken ƙwan lantarki rasss ya koma yana yi .


Daddy da Uncle Salem sai suka fara ƴar kallon-kallon ba tare da sun cewa juna komai ba.
Can Daddy ya kasa yin shuru ya ce “ aboki ka yarda da fatalwa?”
“ Na yarda mana saboda ni ma ita ce ta raine ni” Uncle Salem ya basa amsa .


“ Ban gane ba”
“ Eh kamar yadda na faɗa ma ni kaina ban san iyayena ba domin a titi aka tsince ni to Inna Delu ta raine ni ta bani dukkan tarbiyya da kuma kulawa ta uwa,sai bayan na mallaki hankalin kaina ne ta sanar da ni ita wace ce saboda za ta koma makwancinta“

Daddy ya ce “ wai kana nufin dama Inna fatalwa ce?”

“ Eh sosai ! Bari na je na duba na ga ko Naf ta tashi” ya faɗa tare da miƙewa ya fita ,hankalinsa da tunaninsa na kan fatalwar Deborat wacce kusan duk dare Inna Delu na yi masa gatanarta.
Ko da ya shiga ɗaki ya tarar Nafisa na ta yin baccin gajiya ,ya dubi agogo ya ga lokaci sai tafiya yake ga shi kuma ba ta yi sallah ba.Sam bai son ya tashe ta amma sanin sallar asar ma nada ƙurarren lokaci yasa ya soma shafar fuskarta da tafin hannunsa mai taushi da sanyi.




Cikin bacci na soma jin sanyi na ratsa min kumatu,ga taushi kamar auduga.A hankali na ware idona na sauke su kan kyakkyawar fuskarsa,ban ida warkatsewa ba ya ce “ lokacin sallah Naf”

Jin ya ambaci sallah na yi saurin tashi hankali tashe don na tsani na makara,ya ɗan ja da baya yana mai ci gaba da kallona kafin kuma ya fita.Ni ma fitowa na yi na wuce can sashenmu sai da na fara gabatar da sallar sannan na yi wanka na saka riga doguwa marar hannu na ɗaura kallabinta sannan na fita.

Yunwa nake ji hakan yasa direct kitchen na shiga,Ammy ce da A'i mai aiki ke ta faman yin girki da dukkan alamu yau sarautar ta Daddy ta motsa shi yasa Ammy ke aikin da kanta.
“Yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,A'i ta yi dariya ta ce “ oh shagwaɓarki Nafisa ko auta albarka ”
Ammy ta ce “ bar ni da ita dai ta ci gaba da sakalcin in ta je can ƙauyen ai na ga wacce za ta yi wa”

Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai aiki wacce nake kira da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai daɗi” A'i ta washe baki don sosai take jin daɗin yadda Nafisa ta ɗauke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa gare ta,haka kuma ita ce ta raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan.


“ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai zuba min kunun gyaɗa a kofi.
Na ce “ wai Innarmu ba za ki je ba?”
A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin daɗi na ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne.


Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda da shi .

Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen tafiyata ne.

Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki” sai ya zaunar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login