Showing 3001 words to 6000 words out of 31350 words

Chapter 2 - FATALWAR DEBORAHBook Complete By Mrs Sadauki.txt

Advertisement

04 Mar 2025

4664

su san abin da kalmar ma take nufi ba,sannan Mama da Inna A'i sam ba za su taɓa tada zancen ba”


Ƙirjinsa na soma duka da dukkan ƙarfina kafin na soma magana cikin ɗaga murya har jijiyoyin wuyana na tashi,“kasancewar tasu yara yasa na fi damuwa,don za su iya fitar da maganar su ce sun ji Abbansu ya cewa Mamynsu Mayya.Kenan me za ka ce in ƴan unguwa suka fara guduna? ”


Ƙara riƙe ni yayi gam na soma zillewa ina son raba jikina da nasa,ya ce “don Allah Naf ki yi haƙuri wallahi na san Abdallah ba zai taɓa faɗar haka ba ballantana Mohamed da ko magana bai iya ba”


“Shi kuma zargina da ka yi ka ce ni na kama ruhin Abidah?”

“Naf ki fahimce ni na faɗi haka ne saboda ke ma farkon ciwon jinnunki haka suka fara nunawa,tun gwajin farko na gane kina ɗauke da kambun maitar aljanu amma na yi ta fafutukar ganin na toshe duk wata ƙofa da za ta iya yin galaba a kanki har ki fara aiki da ita.Ina son ki Naf, wannan dalilin yasa duk wani lokacina na ƙarar da shi wurin kula da ke.Na san na yi kuskure a ɗazu amma ki yi haƙuri ki yafewa Uncle ɗinki”


Kalamansa sosai suka daki zuciyata,amma ba zan sauko da wuri ba na fi son na nuna masa zunubinsa mai girma ne don ko kowa ya kira ni da sunan mayya shi bai kamata furucin ya fito bakinsa ba.

Na goge hawayena da bayan hannu kafin na ce “na ji yanzu dai ka cika ni ”

“Sai kin ce kin yafe min kin haƙura”


“Zan faɗa amma ba yanzu ba”

“Don me?”

“Sai na yi tunani” na fara tare da ci gaba da yin mutsu-mutsu ina son ya rabu da ni.Ya na sakina na yi saurin yin gaba na shige bedroom,kan bed na haye tare da yin rub da ciki har yanzu hawaye na zubo min.Na kasa gane me ake nufi da Maitar aljanu sam,ta gado ce ko kuwa jinnun ne ke Mayu sai su liƙawa mutum? Ban sani ba!


“Tashi ki ci abinci ”na ji muryarsa bayan ɗan lokacin da na ɗauka a haka.Ina jin yunwa hakan yasa na tashi zaune,a halin yanzu kuma Naf ɗin Uncle ce kawai na wai matarsa ba haka nake ji wannan yasa na shagwaɓe masa kamar tun can farko da muna gidan Daddy kafin aurenmu.


Murmushi ya saki mai sauti kafin ya zauna gefena ya soma ciyar da ni da kansa har sai da na ƙoshi.Ina shirin komawa na kwanta amma ya taro ni tare da kafe ni da ido,na turo baki gaba na ce “ni ka bar kallona da jajayen idonka”


“Irin naki ne ai” ya faɗa tare da kaiwa lips ɗina sumba,da sauri dai na janye don ban son abin yayi nisa.Ƴar dariya yayi tare da miƙewa tsaye yana cewa “da dukkan alamu wata dai tsoron haihuwa take shi yasa take gudun mijinta”

Na yi masa hararar wasa na ce “su waɗanda na haifa ai na ga kai ka riƙe ni suka faɗo”

“Har da faɗan magana? Zan kama ki ne haba yarinya”
“Ni ce yarinyar?” na faɗa cikin jin haushi,ya ɗaga min gira yana mai cewa “ko ba ita ba ce?”


“Ita ce” na basa amsa ina shirin kwanciya sai na ga wani ƙaton ɓera kan dressing mirror yana kallona ƙuri.Gabana ya bada wani irin sautin dasss,na zabura zan sauka amma ɓeran ya ruga.Na ja ajiyar zuciya ina mai cewa kaina ‘ kai Nafisa ki cire tunanin matsafan nan a ranki,ki bar shirme’

Uncle kuwa tambaya ta yayi “mene ne?”
Na ce “babu komai ” kawai sai ya fice ya bar ni a nan .

Duk yadda na so ture tunanin ɓera sai dai abin ya cuttura don kuwa da zarar na rufe ido shi nake gani yana yi min murmushin mugunta.Na shagala sosai a duniyar tunani barkatai sai na ji an dafa kafaɗata, na zabura ina ɗan ihu sai dai ban ga kowa ba amma tabbas na ji ɗumin tafin hannu.Babu shiri na zuro ƙafafuna ƙasa da niyyar sauka,amma sai na ji na laɓa wani abu mai taushi kuma mai gashi na yi ƙara tare da koma kan bed sai na leƙo ƙasa.Ɓeran ɗazu ne dai na gani,yanzu ma muna haɗa ido ya ruga ya shige ƙarƙashin gado.Wannan karon kam na tabbata ba zargi nake ba,kawai zahirin gaskiya ce ta fito .Wani irin tsalle na yi na diro daga gadon tare da falfalawa da gudu sai dai ina kai wa ƙofar fita daga falo ta rufe kanta ruf tare da motsa kanta tana saka key wanda a gaban idon handle ke juyawa da kuma gidan key kafin daga ƙarshe key ɗin ya ɓata gaba ɗaya.


Wasu Mayun idanuwa na ji suna kallona,cike da tsoro na juya bayana a hankali nan na yi arba da wata mummunar siffa sanye da fararen kaya waɗanda ba su rufe ƙafafunta irin na ƙofaton doki ba.

Wani irin luuuu ruhina da ke can cikin ɓargon jikina yayi,ko tantama babu FATALWAR DEBORAH ce a zaune a kan kujerata tana yi min wani kallo mai cike da tsana da kuma son kawo ƙarshena.....
[27/02 02:13] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta


*FCWA*☀️

________________________

In ba ku manta littafin MAKARANTAR MATSAFA ainahinsa ci gaban book ɗin MUTUWARE ne,sannan tun a can yayi magana kan DEBORAH wacce ke babbar hatsabiyaya.In mutum yana so zai iya karanta iya FATALWAR DEBORAH in kuma yana son sanin duk abubuwan da suka shafe ta ne sai ya koma ya samo littatafan farko wato MUTUWARE da kuma MAKARANTAR MATSAFA.

05


Ban taɓa ganin fatalwa ba cikin siffarta ba sai yanzu ,ko Andre da na gansa yana cikin siffar mutum ne sannan sam jikinsa bai fitar da warin gawa ita kam wannan har wani iska marar daɗin shaƙa jikinta ke fesar wa.


Kamar ƙyaftawar ido haka gangar jikinta ta ɓata sai doguwar rigarta kawai da ke zaune kan kujera.Daga bayana na ji shuuu ,da sauri na juya sai na ga wayam.Dariya na ji daga can sama ,ina ɗaga kai sai na hange maƙale da fanka ashe duk jikinta ƙwarangwal ne rigar ce ta rufa masa asiri.

Bakinta ta buɗe ta shiga dalalo da yawunta wasu koraye kafin ta soma magana cikin wata shaƙaƙiyar murya wacce kana ji ka san ta matattu ce.


“Wajen ƙarni uku ya shuɗe,amma har yanzu ba a yi jaruma irin DEBORAH ba,ni ɗin ta daban ce.In na so na mayar da ruhina mai kyawu ko akasinsa,kin ga zamanin Kakarki Ayodele muguwa ce Ni amma ta iya sarrafa kambunta ta kuɓutar da al'ummarta sannan duk yadda na so na ɗauki mataki a kanta ban yi galaba ba.Ke kuma lokacin zamaninki haka na fito a salihata amma kika kasa taɓuka komai sai mijinki ne yayi, wannan babban abin kunya ne kika tabka kin fita zakka a kaf sarakunan da Victoria Falls ta samu.Wannan dalilin yasa na yi tattaki tun daga ɓoyayyar duniya na zo nan,ki sani daga yau an fara ƙirga kwanakin ƙuncinki da wahalarki.Sai na kawar da duk wani farin cikinki,hatta shi mijin naki zan mayar da shi nawa Hahaha ! Ya iya soyayya ba? Zan zama karuwarsa Hahaha ” ta ƙarashe maganar tana wata irin dariya wacce ta saka fankar fara juyawa da ita yayin da kuma amon muryarta duk ya hargitsa dodon kunnena.



Rigarta ce ta wani miƙe tsaye tare da soma yin tafiya kamar wani mutum sai faman wuwulniya take tana doso ni,ni kuma ina ja da baya har na dangane ga ƙofa.

Sai a lokacin kuma siffarta ta bayyana cikin rigar,sai na ga ashe ta fi muni in tana kusa.


“Ni zan tafi ba za ki sake ganina ba,amma shi mijinki iyeee! Iyeeen! Za mu dinga soyewa” sai ta wani tashi sama ta fice ta rufin ɗaki.Ƙiiii! Ƙofa ta buɗe kanta,a wahalce na fita ina dafa bango har na sauka ƙasa ina mai ƙwala kiran sunan Mama ya fi a ƙirga amma babu ko ɗaya da ta amsa alhalin tana zaune daram a falo.


Ina isa na ƙara marairaice murya na ce “Mama yanzu nan ...” saurin katse ni ta yi “don Allah ban tambaye ki ba,kin ga ki yi rayuwarki yadda kike so tun da hakan kike gani daidai ne.Sai dai ki sani ni kurwar ruhina ta fi ƙarfinki ko kin kame ta sai kin sake ta,saboda ɗaci ne da ni shi dai tun da ya zama malaho sai ya je can ki ci gaba da juya shi” tana gama faɗar haka ta ajiye kofin madarar hannunta ta tashi ta bar min wurin.


Ji na yi kamar na ɗora hannu a kai na ƙwala ƙara haɗi da kuka,bayanta kawai na bi da ido har ta shige sashenta.
Inna A'i wacce shigowarta kenan ta dube ni ta ce “auta lafiya?”

Hawaye masu ɗumi suka zubo min na ce “babu komai Innarmu,daga ina kike?”


“Gidan Dijo na tafi,kin san ba ta jin daɗin jikinta ɗazu da mai aikinta ta kawo ɗan wake ta sanar da mu shine na je.Na yi tunanin ma ko ciki ne da ita ashe zazzaɓi ne kawai”


“Allah ya bata lafiya”

“Amen! Faɗa min meke faruwa na ga uwar sadauki kamar ranta a ɓace”

Na sunne kai kawai don ban san me zan ce mata ba, Uncle Salem yayi sallama yayin da kuma Abdallah da Mohamed ke yin dariya suna biye da shi.Kallo ɗaya kawai na yi musu na janye idona,ko zama bai yi ba sai ga Mama ta fito fuskar nan a murtuƙe ta ce “in ka gama abin da kake ina son yin magana da kai”

“Ba na yin komai Mama” ya faɗa yana mai miƙo min leda,ina ganin yadda Mama ta bi ledar da ido kafin ta koma ɗakinta.Uncle ya dube ni ya ce “me kuma aka yi ? Na ga kamar Mama na fushi da ke, sannan su wannan hawayen na mine ne?”

Ban basa amsa ba sai Mohamed da na jawo wanda tuni an yi masa wanka an canza masa kaya.“Ina kuka je yarona?” na tambaye shi,dariya yayi ya soma yi min surutu yana sanar da ni sun je wani Mall Abbansu ya saya musu abubuwa masu daɗi.


“Naf da ke fa nake” Uncle ya faɗa ,na ɗaga kai na dube shi na ce “Mama na kiran ka”

Matsowa yayi kusa da ni ya wani kamo ni kamar wata yarinya ya ce “ki faɗa min don Allah kafin na je”
“In ka dawo za mu yi maganar” na faɗa ,“ok na ji bari na je” ya faɗa tare da yin gaba na bi bayansa da kallo ina jin tausayin kanmu ganin wata masifar na tunkaro mu ta uƙubar uwar miji.



Uncle Salem na shiga ɗaki ya tarar da Mama a zaune ta cika fam kamar za ta fashe,gefenta kuma Abidah a zaune yanzu ta tashi daga bacci.

Cike da girmamawa ya gaishe ta tare da cewa “Mama ga ni ” sai kuma ya samu wuri ya zauna.
Cike da izza ta ce “dama tambayarka nake son yi wace ce uwarka?”

“Subahallah! Mama wacce irin tambaya ce wannan?” Uncle Salem ya faɗa yana jin wani iri a zuciya .

Mama ta ce “eh ai gwara na ji da bakinka wace ta haife ka ni ko Nafisa?”
Kansa ne ya soma sarawa,cike da ladabi ya ce “Mama don Allah ki yi haƙuri duk da ban san laifin da Naf ta yi miki ba”

“Ai ita ba ta laifi matar gwal ce,ina ce duk abin da ta yi daidai ne ta mayar da kai malaho sai abin da take so ake yi a gidan nan tana ƙaryar ita jinin sarauta ce an wani kawo bayi suna yi mata ayyukan da ita ce ta dace ta yi su.Ko kunya ba ta ji ƴan aiki ne ke yi wa mijinta girki yana ci ita kuma tana can tana yawon ta zubar tana gogayya da ƙatti da sunan aiki.To daga yau in dai ni ce uwarka to ya zama dole a kori bayin can daga gidan nan,a bar iya A'i”


“Mama kar ki manta Inna A'i ko can ba ƴar aiki ba ce,kuma Nafisa yarinya ce ba za ta iya yin ayyukan gidan nan ba ita ɗaya a bar ko mutum ɗaya ne sai ya dinga kama mata”


“Ba dai a cikin bayin Victoria Falls ba,ka sallame su ni nan da kaina zan nemo ma ƴar aiki ka tashi ka tafi Allah yi ma albarka”

Ya miƙe yana mai cewa “amen” kafin ya fice....
[27/02 02:52] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta


*FCWA*☀️

________________________

06

Ina nan zaune tare da yara Uncle Salem ya fito,a yanayin fuskarsa kawai na fahimci ba abu mai daɗi ne Mama ta sanar da shi ba amma na basar na ci gaba da fitar da chocolat da ke cikin ledar da ya bani ina nunawa Abdallah shi kuma yana karanta sunayensu.
Bai ce komai ba yayi sama,ni ma na ƙi tanka shi na yi zamana dukkan sallolina ma a ɗakin Inna A'i na yi su har isha'i.Abinci kuwa kasa ci na yi sai su Abdallah da na saka gaba suka ci na kuma umarce su da su wuce can ɗakin kakarsu tun da a can suke kwana,na yi Inna A'i sallama na fito.


Tun da na soma taka step nake jin tamkar ana take min baya har wata guguwa-guguwa nake ji haɗi da wani numfashi kamar na kumurci,amma a haka na daure na haura sama direct kuma ɗakin Uncle na shiga.

Kiciɓis muka yi da shi ya fito daga bedroom ɗinsa ƙugunsa ɗaure da towel yana goge kuma sumar kansa da ɗan ƙarami.
Na ɗan ja ajiyar zuciya kafin na je na karɓi towel ɗin na zauna da shi ina goge masa ruwan.


“Naf!” ya faɗa can ƙasan maƙoshi,na ce “uhum!”

“Mu je ki yi wanka” ya faɗa tare da tashi tsaye ya ja ni muka shiga can uwar ɗaka,sai da yayi mana addu'a sannan muka shiga toilet ɗin.Ruwan ɗumi ya cika min bahon wankan da su na shige,sai a lokacin ya fita ya bar ni na soma wanka ina ayyana abubuwa da yawa a raina har na gama na fito ɗaure da towel ɗinsa.


Bayan na shafa lotion da turare na saka kayan baccin da ya fitar min,sai a lokacin ya rufe laptop ɗinsa yana tsokana ta.“A zo a sama wa Mohamed ƙanwa”

Murmushi kawai na yi , ya rungumo ni tare da ja na muka yi baya muka zube kan bed.“Wai kin san da ina mahaukacin son ki?” yayi min tambayar da bai bani damar basa amsa ba saboda bakinmu da haɗe wuri guda yana kissing a hankali kuma yake shafar cikina zuwa ƙasa.Dakyar na aro jarumtar fitar da duk damuwata na ajiye hankali muka faranta ran juna,a yau ma Uncle ya ƙara dasa min wani sonsa na musamman a zuciya .A ɗan kunyace na yunƙura zan tashi amma ya mayar da ni tare da yi min raɗa a kunne,a shagwaɓe na daki ƙirjinsa na ce “uncle kana ƙara girma amma kana abubuwan yara” wata shu'umar dariya yayi ya ce “au kar dai a ce kallon tsoho kike yi min? Baby duka nawa nake da ba zan kasance da ke sau biyu ba?”



“Ni dai a bar ni na huta bacci nake ji” na faɗa ina ƙara ƙoƙarin tashi amma ya ɗora hannunsa kan cikina yana mai cewa “ki jira na haɗo miki lafiyayen abinci dai baby sai ki ji ƙarfin kula da mijinki”

Yana gama faɗar haka ya tashi ya kimtsa tare da fita,ni kuwa na lafe cikin blanket ina murmushi.


Uncle Salem kuwa shi kansa yunwar yake ji don kalaman Mama kasa barinsa sukuni suka yi ballantana har yayi tunanin cin abinci.
Ƙasa ya sauka tare da shiga kitchen,tray ya samu ya soma ɗora duk abin da za su ci yana tsaka da yin aikin gabansa Mama ta shigo hannunta riƙe da na Abidah.
A ɗan kunyace ya ce “Mama fitowa kika yi?”

“Eh Abidah ce tace min yunwa take ji shi ne na zo kitchen don sama mata abin da za ta ci” ita ma Mamar ta faɗa tana mai kallon trayn da ya zuba fruits kamar yadda Abidah ke kallo.

Shi kuwa ƙaramin plate ya samu ya soma yayanka mata yana mai farawa da Bismillah kamar yadda abin ya zame masa jiki babu abin da zai yi ba tare da ya ambaci sunan Allah ba.
Yana miƙawa Abidah amma ta ƙi karɓa a ƙarshe ma dai cewa ta yi ba ta jin yunwar,da Mama ta kama hannunta don su koma sai ta tsira kuka tana mai cewa “ni wurin Abba zan tafi”

Uncle kuwa sanin halin da ya baro Nafisa ,sannan da wanda shi kansa yake ciki na larurarsa sai ya kuwa ya murje ido ya ce “Mama ki tafi da ita ki rarrashe ta za ta bari,Abidar Mama ki bar kuka kin ji ko ? Gobe zan saya miki zuma” ya faɗi haka ne saboda duk rigimar da take in ambaci zuma tana yin shuru.
Da wani irin kallo Abidah ta bi bayan Uncle,wanda kuma a zahiri ba ita ce ɗin ba ruhin DEBORAH ne ke juya gangar jikinta.Ta so ace ya tafi da ita can ɗakin don hana shi ƙara kusantar Nafisa,amma babu yadda ta iya dole ta haƙura ta bi Mama.



Ina nan yadda ya bar ni ya shigo,jikinsa har rawa yake kamar kullum muddin dai yana da buƙatar kasancewa da ni to duk wani control rasa shi yake.

Fruits ya soma ciyar da mu,sai ya saka a bakinsa yana ɗura min kamar wasu tantabaru ko kuma ya saka a bakina sai ya dinga sha yana gamawa da sumbata ta a haka muka ƙara shiga wani shauƙin soyayyar muka samawa juna nutsuwa a karo na biyu.Duk yadda na so kuma na kwanta bacci Uncle bai bari na zauna da najasa ba sai da muka tsabtace jikinmu,a shagwaɓe nake yi masa mita sai ya ce “Baby babu kyau fa kwana da janaba,in mutum bai iya yin wanka to Manzon rahama ya ce ko alwala ce ka yi kafin ka kwanta don nisanta kanka daga sheɗanu”

Ambatar sheɗanu da yayi shi ya dawo min da tashin hankalin ɗazu na gamdakatar da na yi da FATALWAR DEBORAH,cike da tsoro na ƙanƙame shi ina shigewa ƙirjinsa haɗi da ɓoye fuskata shi kuwa karatu na ji ya soma yi min yana min wata irin shafa wacce ta mayar da tsikar jikina da ta tashi.

A hankali na soma lumshe ido saboda karatun da yake yi min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login