Showing 6001 words to 9000 words out of 31350 words

Chapter 3 - FATALWAR DEBORAHBook Complete By Mrs Sadauki.txt

Advertisement

04 Mar 2025

4663

yana kashe min jiki ne ruhina na yin wani sanyi liƙis,ko gama ida rufe ido ban yi ba na ga Deborah a tsaye a cikin mafarkina ta yi kicin-cikin da fuska,ba ta kuma ɗauki dogon lokaci ba ta shaƙe min wuya....
[27/02 15:49] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta


*FCWA*☀️

________________________


07

Ko a cikin miyagu ita Deborah ƙarshe ce wurin iya mugunta,na sha jin labaranta a cikin littafin sirrin Kakata Ayodele na MUTUWARE.Wannan yasa ban ma ɓata wa kaina lokaci ba wurin ƙwatar kaina ta ƙarfi ba,sai dai furucin baki wanda nake feso ayoyin Alkur'ani duk wacce ta zo min wata ma ko ƙarshen ayar ban kai wa nake kamo wata.Amma tsabar taurin rai na fatalwa haka ta daure azabar da nake yi mata domin kuwa karatun Alkur'ani na ƙona ruhinta ne kamar yadda yake ƙona jinnu.

Cikin ikon Allah dai na samu na ci galaba a kanta ta bari na tashi daga baƙin baccin nan.Kan fuskar Uncle na sauke idona wanda ke sharar bacci,a hankali na sauka daga bed ɗin na nufi farantin da ya shigo mana shi don ɗaukar ruwa na sha sai dai ina taɓa gorar da hannuna nan take ruwan suka ƙwafe ki ɗigo ɗaya babu alhalin da idona na gansu.

Ƙishi nake ji sosai,maƙoshina ya bushe kamar wacce ba ta taɓa shan ruwa ba.Don dole na zura hijabi tare da fitowa,wani abin mamaki ne ya faru da ni,a daidai lokacin da na sauke ƙafata daga step ɗin ƙarshe sai duk ƙwayaƙwayin lantarki suka fara disashewa suna wani lummm kamar rana za ta faɗi,ko kafin ƙyaftawar ido kuma suka dinga tarwatsewa ji kake tatatseeee ! Rasss! Duk sun mutu ɗakin ya dawo baƙi ƙirin ko tafin hannuna ban iya gani,iska ne ya soma kaɗawa a hankali-a hankali kafin kuma ƙofae fita falo ta yi wani ƙiiii ta buɗe kanta daidai nan wata murya irin kamar ta wanda ya ɓata ta soma kiran sunana.


“Naf? Naf zo gare ni! Naf zo mana za su tafi da ni” muryar da na ajiye hankali sai na ji ta Uncle ce,kamar wacce ake yi wa jagora haka na soma bin wani hasken jar wutar kyandir har na fita daga gidan baki ɗaya.Tafiyar ƙasa na soma yi a cikin duhun sararin samaniya wanda ya ɗauki wani yanayi kamar lokacin damina,duk taurari sun ɓata sai giza-gizai ke faman gudu.



Ba zan iya cewa ga iya adadin lokacin da na ɗauka ina tafiya ba,ni dai kawai na gan ni a bakin ƙofar shiga wani jeji ina dab da saka ƙafata ciki na ji an jawo ni ta baya.Sai a lokacin kawai tunanina ya dawo jikina,a tsorace na juyo ina kallon shi.Farin dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekara ɗari da wasu ƴan kai.


“Me ya kawo ki wannan wuri?” ya jefo min tambaya cikin wani yare wanda ba nawa ba amma tabbas na fahimci me ya ce.

Samun bakina na yi da irin nasa Yaren na ce “ina ne nan?”

“Keɓaɓiyar duniya ce wacce aka tanada domin ɓatattun ruhika waɗanda suka kasa gane inda za su dosa” ya bani amsa.

“Kana nufin nan ba Zimbabwe ba ne?”

Wani kallo yayi min na wani lokaci kafin yayi ɗan ƙyaci ya ce “wannan duniyar da taku abubuwa biyu ne mabanbanta,iya ruhi kawai ke shigowa a nan amma ke ban san ta ya aka kika zo nan ba alhalin babu wani tabo da ke nuna kin aikata wani zunubin”


“Don Allah ka taimaka min na koma gidana” na faɗa ina hawaye.

Ya ce “dole sai na san wanda ya turo ki izuwa nan”

“Kamar yaya?”
“Ina nufin matsafi,aljani ko bokan da ya cillo ki nan”

“Deborah ce”

Ina faɗar sunanta sai yanayin fuskarsa ya canza ya bayyanar da razani,amma ban san me yasa ba ya kwantar min da hankali wurin cewa “ko ma dai wace ce za ki fita in kin so sannan in kin yi niyya don babu abin da ya fi abin bautar Musulmi ƙarfi ”
Wata ajiyar zuciya na sauke da tunanin a yau zan koma gida amma sai na ji yana mai ci gaba da cewa “za ki biyo ni mu je can gidana in kin huta sai na faɗa miki hanyoyin da za ki bi ki koma duniyarku”
Duk da ban so haka ba amma na yi yadda ya ce ɗin na take masa baya har muka isa wani kogo,ko kafin na kai ga tambayarsa me za mu yi a nan sai na ga ya rikiɗe ya koma maciji .Na yi baya da sauri ina waro ido,yayin da shi kuma ya soma magana “kar ki ji tsoro domin ni ɗin aljani ne ba mutum ba,ki kama kogon gam za ki tsinci kanki a ciki”

Na girgiza masa kai don ba zan yarda na shiga cikin wuri tare da aljani ba.
“Ba ki da sauran lokaci ki yi sauri ki shiga na fara jin ƙamshin Deborah muddin ta tarar da ke nan to shi kenan fa ba zan iya yi miki komai ba” bai gama rufe bakinsa ba na soma jin sawun takunta,jiki na rawa na yi yadda ya ce kamar ƙyaftawar ido sai gani cikin kogon wanda ke ɗauke da abubuwan ban mamaki.
Daga inda nake ciki na ji muryar Deborah na cewa “Baba tsoho ba ka ga wani ruhi yana shawagi ba ta nan wurin?”


“Babu wani baƙon ruhi da ya shigo nan duk yau” ya bata amsa,sai ta yi gaba shi kuma ya shigo yana mai kallona kafin ya rikiɗe ya koma mutum.Wata step ya soma takawa ni ma na take masa baya har muka isa can saman ƙatuwar bishiyar,na waro ido ina kallon duniyarmu ya bil'adama.
Ya tsinko wani fure ya murza shi yana mai furta wasu harufa sai ga gidana ya bayyana,haka yayi ta tafiya da tunanina har muka shiga babban falo Uncle Salem na gani a zaune duk hankalinsa a hargitse,yayin da bokanyar gidanmu ke zuga shi kan cewa babu wani ɓata da na yi akwai dai inda na je na ɓuya abin da ya fi ban mamaki jin wai tana faman cewa sati guda rabona da gida.Baba tsoho kamar ya san abin da ke raina sai cewa yayi “kin yi doguwar tafiya ne shi yasa,kika yi kwanakin nan” bai ida rufe baki ba duk komai ya ɓace daga idonmu wanda na lura yayi daidai ne da shigowar wata baƙuwar fuska a falon wacce alamu suka nuna kuma ƴar aiki ce....
[28/02 08:22] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta


*FCWA*☀️

________________________


08


“Da matsala fa,ina ga Deborah ce ta ɗauki siffar bil'adama ta je gidanki da sunan ƴar aiki” Baba tsoho ya faɗa fuskarsa cike da damuwa.


Cike da tashin hankali na ce “ta ya aka yi ka gane?”


“Ita kaɗai ce mai ƙarfin ikon da za ta iya katse min dubana kai tsaye daga shigowarta,yanzu abin da ya kamata a yi ki je ki kwanta ki huta zan fara binciken hanyar da za ki bi ki koma gida kafin nan da wata uku”


“Wata uku kuma? Ni da nake son na koma tun yau” na faɗa a rikice.

Wani kallo yayi min kafin ya ce “kina tunanin tafiya daga ɓoyayyar duniya zuwa duniyar bil'adama abu ne mai sauƙi? To tsaya ki ji ita kanta Deborah farkon ranar da za ta keta hijabin da ke tsakaninmu da ku sai da ta ɗauki kusan shekara guda currr.In taƙaice miki zancen a ƙaramin misali sai kin yi tafiyar wata biyu kafin ki isa can,shi ma sai in na samu aljani mai matuƙar gudu”


Wani gumi ne ya rufe ni nan take,a duniyarmu na sha jin cewa aljani na iya yin abu kamar ƙyaftawar ido amma a nan ga shi yana yi min zancen watanni biyu.Sam ban yarda da shi ba,don haka na ƙudurta a raina zan fita daga kogon nan na je na nemi hanyar da kaina.

Kan wani gadon ganye na je na kwanta kamar yadda ya ce,na lumshe idona amma ba da niyyar yin bacci ba.Sai da na bari hankalinsa ya ɗauku kan aikin da yake yi jikin wani allon ƙarfe sai na yi saurin sauka daga gadon na je na dafa kogon nan take na tsinci kaina a fili.


Gudu na soma ina waiwaiye har sai da na yi nisa sosai sannan na tsaya yin tafiya,cikin ikon Allah na hangi hanyoyi biyu daga nan ma ina tsinkayen kwalta.Na saki murmushi don kuwa na san in ba a duniyarmu ba babu inda ke da kwalta ina dab da bin ɗaya daga cikin hanyoyin kwatsam wani dodo ya bayyana a gabana.Tsoro ya kama ni ,ga shi ina son yin baya amma tamkar shukar da aka dasa haka na kasa motsi.


“Barka da zuwa hanyar tsirar ruhin da ya ɓata” dodon ya faɗa yana wangale min baki nan muninsa ya ƙara bayyana,hanya ya bani da nufin na wuce.Abin da ya faɗa na maimaita a zuci sai na fahimci eh lalle ina kan hanyar daidai kenan, wannan karon ina cira ƙafata sai ta bar ƙasa haka na bi hanyar nan na soma tafiya duk yadda nake tsinkayen kwaltar amma na kasa kawowa a gare ta.


Ga yunwa ga ƙishi ga gajiya,sai na ɗan sunkuya ina mai riƙe gwiwaina kamar mai yin sallah daidai nan idona yayi tozali da wani ɗan rame kamar gurbin tanda sai ruwa ke ɓulbulowa.Jikina har rawa yake wurin duƙawa na soma sha,sam ban farga ba na ji ni tsundum cikin ruwa na nitse ciki hatta kaina.Ina ɗaga kaina sai na ga wasu ƴan masu mugun kyawu suna wasar kos,yayin da kuma ɗaya daga cikinsu ke gefe tana saƙar hannu.Ido muka haɗa da ita sai ta sakar min murmushi kafin ta yi min alama da hannu na zo,ƙafafuwana a sanyaye na soma tafiya kwacal! Kwacal ! Cikin ruwan har na isa gare ta.


Duk ƴan matan suka maido hankalinsu gare ni,suna masu karon baki wurin cewa “waooo! Bil'adama a duniyarmu?”

“Ku yi min shuru ku ci gaba da wasarku,ke kuma zauna nan” ta dube ni tare da nuna min wani Kunkuru🐢 ni tsoronsa ma ya kama ni ganin yadda yake ziro kai yana maida shi kuma ciki, amma a haka na daure na zauna.

Tsakiyar idona ta kafe da kallo har sai da na ji wani abu na huda fatata yana ratsa ɓargona,a nan take kuma tsikar jikina ta tashi duk gashin da ke hannuna yayi wani tsiri-tsiri da shi ban gama yin mamaki ba na ga wani abu ya soma fita daga hudodin yana zubewa...



Ga waɗanda ke son shiga paid group sai su yi min magana kai tsaye ta WhatsApp numberta +22795045822.

A page 10 zan dakata da free page in sha Allah
[28/02 10:07] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta


*FCWA*☀️

________________________


9_10

★DEBORAH

Ta daɗe tana kwaɗayin dawowa duniyar bil'adama tun shekaru ɗari da ashirin da suka gabata,sai dai ba ta samu ƙwaƙwaran dalilin da za ta faɗawa al'ummarta na ɓoyayyar duniya waɗanda take mulka ba.Sai a ranar da idonta suka yi gamdakatar da Uncle Salem ta ji wata hatsababiyar ƙaunarsa ta shiga ranta,ta yi ƙoƙarin danne muradinta sai dai hutar sonsa sai ƙara azalzala take yi a ranta.Yanayin yadda yake kula da Nafisa shine abin da take so tun lokacin da ta na raye,sai dai babu namijin da ke da jarumtar tunkararta da zancen so ballantana har ya kai ga ririta ta dukkan hatsabiban matsafa da bokaye tsoronta suke.


A ranar da ta zo ta shigar da Uncle Salem faɗa da niyyar dama don ta kasance matarsa ta dare ne a duniyar mafarki,shi yasa ta sanar da shi cewa dukkan komai yana da farashi.

A yanzu da ta faso duniyar bil'adama ba ta ga abin da zai mayar da ita ɓoyayyar duniya ba,farkon zuwanta a jikin Abidah ta yi wa baƙin ruhinta masauki.Cikin shu'umancin da ta saba yi ta juyar da kwanyar Mamar Sadauki ta saka mata kishin Nafisa,don sai in rikici ne ya shiga a tsakaninsu ne za ta samun yadda take so.Korar bayi masu yi wa Nafisa hidima duk tsarinta ne,kuma birninta ya cika duk an sallame su.

A wannan ranar ce kuma ta bazama neman gangar jikin da za ta ɗauka,dole tana buƙatar na cikakkiyar mace mai hankali wannan yasa ta fita tsakar dare neman raunatacen ruhin da za ta nakasa ta ɗauke gangar jikin.
Gida-gida ta dinga bi har Allah ya kai ta gidan Sakina ƙawar Nafisa,tun kallon farko ta gane ta.Tsaye ta yi tana kallon yadda Sakina ke zazzaga wa mijinta ruwan masifa tana cewa “ wallahi sai ka sake ni,ba zan zauna kullum kana tafiyarka daji kana barina a gida ba kamar wata mai gadi .Ka sake ni na je na auri wani wanda ya san mutumcina,ai MIJI GOMA BA UBA GOMA BA NE(littafin Sadiya AbdulRak kenan)”

Cikin rarrashi ya ce “Sakina ki ajiye hankalinki da kyau ki yi wa kanki karatun tanutsu don kar ki je ki yi BONONO(Mom Afra) daga baya ki zo kina cizon yatsa”

“Wa ya faɗa maka ƘWAƘWALWAR KIFI( Emilia) ce da ni da ban san abin da zai fishe ni dare ba?”

Yayi ɗan murmushi don kwantar mata hankali ya ce “ ba ki san kusan duk kowanne gida NAUSHIN WUTA (Ameera Adam) mazajensu ke yi ba?”

“Kar ka yi ɓarnar bakinka don wallahi ba zan yi BIYAYYA(Mai ƙosai) a gidan auren da ake cutata ba” ta yi furucin tana mai banko ƙofar ɗaki ta fito ba tare da ta yi la'akari da tsawon dare ba,FATALWAR DEBORAH wacce tun ɗazu take tsaye ƙiƙam ta yi wuf ta shige gangar jikin Sakina nan take kuma ta ɗauki controling tunaninta,cike da iya tsafi ta ƙarawa jiki da fuskar Sakina shekaru ta yadda ba kasafai za ka gane eh ita ce ba.

Daga nan direct gidan Uncle Salem ta zo,ba ta wani sha wahalar fiddo Mamar Sadauki tsakar gida ba sai kuma ta fara buga ƙofa.Baiwar Allah Mama ta zo ta buɗe mata ,kawai sai ta fashe da kuka tana cewa ta taimaka mata ba ta da kowa.Abin ka da dama an juye ma kwanya haka Mama ta shigo da ita cikin gidan,a washegari kuma ta gabatar wa da Uncle Salem da ita a matsayin ƴar aiki,shi sam hankalinsa ba kwance ba saboda tashi da yayi ya ga Nafisa ba ta kan shimfiɗa har ɗakinta kuma ya je nan ma ba ta nan.


★Nafisa


A hankali duk kambun maitar da ke jikina ya fice na dawo normal,sai dai kafin ma na kai ga yi mata godiya na ji tana cewa “zan ara miki ƙarfin ikona ta yadda za ki yaƙi abin da ya fito da ke daga duniyarki izuwa nan,ban son gardamar nan taki ki riƙe a barki ” ta faɗa tana mai yi min wani kallo na tsakiyar ido kafin ta ci gaba da cewa “ki faɗa min wacce siffa kika fi so? Ina nufin cikin dabbobi me kika fi so?”

“Ban son ko ɗaya” na bata amsa.

“Me kika fi tsoro to?”

“Ƙadangare” na bata amsa.

Sai ta saki wani murmushi kafin ta yi wa ƴan matan nan magana ta aike su wata maƙabarta tana son su tono mata kabarin wani su kawo mata shi.

Babu jimawa suka je suka dawo ɗauke da wani abu cikin farin ƙyalle,kan teburi suka ajiye shi tare da buɗe shi.Gawar wani ƙadangare ce na gani har ya bushe kana iya ganin ƙasusuwansa.


Wasu harufa ta fara lissafowa yayin da kuma ta saka ƴan matan suka yi wani cercle suka kewaye mu suka sa mu tsakiya,wani furucin su ma suke yi cikin salon ɗaga murya yayin da ita kuma nata take yinsa a sauti ƙasa-ƙasa “Lazaaar! Laaazaaar! Ōÿānīÿēmį ” a hankali na ga ƙadangaren yana dawowa ɗanye haɗi da ɗan kumbura nan take tsoro ya kama ni,daidai wannan gaɓar ne kuma ta kama yatsana ta tsaga shi jini ya soma tsirta yana sauka kan jikin ƙadangaren kai kace dama jinin nawa ne yake so nan take ya soma motsi yana buɗe bakinsa.

Kalmar farko da ya furta ita ce “Gimbiya Sarah” a nan ne kuma na san sunanta,sai ta saki murmushi a lokaci guda kuma ita da ƙadangaren suka kalle ni.


Tsoronsa nake ji sosai,don haka da sauri na je bayan Sarah na ɓuya amma ta wani matsa ta yadda dole dai na fuskanci ƙadangaren wanda ke kallona da ƙattin idonsa.

“Shugabata!” ya furta,na waro ido jin wai ni ce shugabarsa.

“Nafisa wannan shi ne Lazar,wata ƙawata ce da muka yi rayuwa da ita duniyar bil'adama ta ƙyarƙyare shi ta hanyar tsafi.Yana da matuƙar power na san zai taimaka miki sosai,abin da nake so da ke dai shine kawai kar ki yi gardama har mu kammala aikin nan kin ji ko?”

Kai kawai na gyaɗa mata,sai ta ƙara bani umarnin na zauna.Jikina na ɗan rawa na yi zaune ,yatsana ta kamo wanda ta tsaga ɗazu.A gaban idona ba mafarki ba ta kamo shi Lazar ɗin ta saka min shi ta cikin ƴar tsakar da ko allura sai an yi da gaske ta wuce amma ƙaton Lazar ɗin ne ya shige tsaf,wani iri na ji bayan ta gama shigar da shi.

“Ki lumshe idonki me kika gani?” Sarah ta faɗa .
Na kuwa lumshe su nan na hangi FATALWAR DEBORAH tana shayar da Abidah wata gubar maita,so take a dole dai sai ta cutar da ƴata.Ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba,abin da na gani ɗin na sanar da Sarah ita kuma sai ta ce “ƙarfin ikon fatalwa yana ƙaruwa ne ta hanyar shan jini kawai, wannan dalilin yasa ta zaɓi Abidah matsayin wacce za ta dinga yi mata farautar rayukan mutane tana kamo kurwarsu ita kuma sai ta tsotse jinin.Yara da yawa Mayu na amfani da su don yi musu bauta,saboda shi yaro sam ba za a zarge shi ba amma hakan tana faruwa ne ga iyaye masu sakaci wurin yi wa ƴaƴansu addu'ar bayan asubah kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi mana umarni da mu dinga karanta musu wannan addu'ar *A'UZU BIKALMATILLAHI TAMMA,MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMA,WA MIN KULLI AYNIN LAMMA* ”


Idona ba su bar fitar da hawaye ba na ce “in kuma mutum bai iya karanta Larabcin ba?”

Ta bani amsa da “ sai yayi da Hausa don Ubangiji yana jin kowanne Yare sannan yana amsar addu'ar bayinsa ”

“To ki faɗa min da Hausar don halin yanzu ma ji nake kamar ban yi karatu ba”

“Ina neman tsari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login