Showing 30001 words to 33000 words out of 52687 words
Chapter 11 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf
Ummhhn.
Ko palonsa basu shigaba saigasa ya fito da wayar a hannunsa zai kaimata.
Kar6a tayi tana cewa,
Let's go zeey,.
Ayeesha ce tai saurin qarasowa ta hawo stairs hu'du dake qofar palon tareda miqawa neesah
ledar hannunta fuska a sake tace,
Inatason ganinki nabaki wannan tsarabace.
Tamke fuska tayi tareda 'fagowa zatai mgn idanuwanta suka sauka akansa yana tsaye yana
kallonsu.
Wata 'yar kwalba Ahmed ya bude batareda neesah ta luraba bare Jamaal dake nesa yayi saurin
zazzage mattacen baqin macijin dake ciki ya juya ya shige palonsa yana cewa,
Antynah gud night dan ni barci nakeji.
Murya a shaqe tace,
Tnx amma ki aje kayanki bana buqata.
OK tace tareda juya zatabar gurin a tsorace da qarfi zeey takira sunan neesah tana nuna mata
qaton baqin macijin daidai ayeesha zata 'dora qafarta
a tsorace cikeda firgici neesah tasa hannuwa biyu ta ture ayeesha da qarfi sbd gudun karta taka
ya sareta
Wani mahaukacin ihu ayeeshar tasaki sbd muguwar faduwar datayi nantake jini ya 6alle mata.
Wani iri mugun gudu dabai ta6a sanin yanadashiba ya fito aguje ya tallafota yana kiran sunanta
da qarfi nanma su ummi suka fito a ru'de sbd sun jiyo ihun
Ahmed ma a ru'den yafito yana tambayar lpia,
Khadija dake zaune cikin rumfar shaqatawar kusada qofar palon Ahmed taga komai kuma sai
ayau ta tabbatarda qiyayayyarta lami ce akan wainnan.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*�
_Don't forget to vote, follow and comments_
[8:31AM, 4/9/2018] �+234 703 593 2228�: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*46-47*
*_I sincerely heart you labibah lawal thank you for all the care_*
*_page 'din na yau naki me_*..
Jinin dake zubane sosai ya tsananta tashin hankali da fargabarsu tuni ummi tafara kiran
innalillah sbd tarigada ta saddaqar da cikin ya 6are.
Sunkutarta yayi duk da jinin dake 6ata masa jiki suka nufi mota ummi da inna rabi suka shiga
yabar gidan da mugun speed.
Qoqarin zubewa takeyi zeey tai saurin tarota sbd sosai take cikin tashin hankali dan Sam ta
manta da cikin da ayeeshar take dashi yanxu shikenan tayi kisa tunda ta 6arar mata da ciki.
Hawayene suka gangaro mata na tausayin ummi yanxu shikenan ta rusa musu farin cikinsu
dasuka kasa samu daga gareta sun samu daga wata tayi musu hasararsa.
Zubewa tayi gurin tareda sakin siririn kuka ahankali sbd har cikin ranta taji baqin cikin itace silar
rasa farin cikinsu.
Ganin tana kukan datake mai tsima rai yasa jikin Ahmed yayi mugun sanyi ya matso zai kamata
yaji an riqe hannunsa a tsorace ya 'dago.,
Khadija ce tsaye idanuwanta taf da hawayen tausayin kanta dana neesah a karo na farko ta
kallesa cikin ido murya a sanyaye tace,
Ahmed karka shiga hurumin Allah sosai sbd samun sassaucin sauran lefukan da ka jima kana
aikatawa.
'Dauke numfashinta tayi tareda kama neesah suka bar gurin.
Kallonsa zeey tayi zatai magana ya watsa mata idanuwansa dasuka kada rai a 6ace yace,
Tabbas danasan haka abin zai kasance dana qi biyewa kafirar baqar zuciyarku saidai na reni
sonta a zuciyata na mutu dashi koba komai zan zama masoyi na haqiqa ko bayan raina zatai
alfahari da ni amatsayin masoyi na haqiqa.
Wani kallon tsana da wulaqanci ta watsa masa kafin tace,
Ko yanxu ma lokaci bai qure maka ba saidai ka shirya kai da neesah ne zaku 'dandani 6acin ran
Jamaal kun 6arar masa da ciki.
Qoqarin damqota yayi tai baya tace,
Don't waste your energy tun yanxu
Save it you gonna need it later,
Da kana nufin ka dakemu ne ka daki banxa to bari kaji lokacin da kake zazzage qaton macijin a
kusada qafar ayeesha kana tunanin ta kareka kar Jamaal ya hango to abinda baka saniba shine
sosai tai seti da yanda ya hangoka tsaf dan haka saika shirya fuskantar 'dan uwanka da
iyayenka.
Wucewa tayi tareda sakin dogon tsuki tana cewa,
Dama bakasan dawa kake wasaba.
Kasa komawa bedroom 'dinsa yayi sbd jirin dake neman 'dibarsa sai kawai ya durqushe agurin
hawayen da baisan dasuba suka fara gangaro masa na tausayin neesah dakuma mummunan
tashin hankalin da gidan zasu fuskanta ta rarrabewar kawuna.
Khadija nakaita 'dakinta ta fice zuwa nata 'dakin ta zube a qasa tana kuka Mara sauti sbd
wannan abun datake gani su ayeesha nayi to tabbas bazata samu Jamaal ba har abada.
Zama zeey tayi kusada ita tareda rintse ido ta dafa hannun neesah dake zaune quryar gado
idanuwanta jajir.
Koda suka isa asibiti aka kar6eta batareda 6ata lokaciba aka tabbatarmusu da cikin ya xube
gaba 'daya dan haka basai anyi wankin Mara bama shiyasa aka kasa gano magani tasha cikin
tuni dama yafara zuba.
Duk iya yanda ummi taso daurewa saida tayi hawayen tausayin Jamaal sbd yanda idanuwansa
suka ka'da jajir ko magana yakasayi sai zama yayi bakin gadon da ayeeshar ke kwance ya riqo
hannunta da wannuwansa biyu ya rintse ido yanajin wani irin zafi a zuciyarsa.
Bata wani jimaba ta farka tana bude ido ta fashe da wani irin kuka.
Bude idonsa yayi tareda riqota yana qoqarin lallashinta
Ummi ma matsowa tayi tana cewa,
Ki kwantar da hankinki ayeesha Allah zai kawo miki wani insha Allah.
Ihu ta qwalla jin abinda ummin ke fada takallesa tace,
Na rasa babyna ko yananan?
Girgiza mata kai yayi yana qoqarin kamota jikinsa ta fasa ihu tana kuka cikin tashin hankali
tareda fusge drip da canola dake jikinta tana rusa kukan daya masifar 'daga hankalinsu.
Qoqarin kamota yake tana turjewa kuka take sosai tana cewa,
Babyna,babynah inason babynah.
Tsuru inna rabi tayi tana kallonta cikeda mamakin kukan datake akan ta rasa cikin fari kuma
agaban uwar mijinta.
Ummi kuwa tausayin ayeeshan da baqin cikin rasa cikin yasa itama hawayen take.
Daqyar ya qanqameta ajikinsa sbd ko magana baya iyayi
tsit 'dakin yayi banda kukanta dake fita ahankali bakajin komai tuni idanuwanta da fuskarta suka
kumbura tsabar kuka kallo 'daya zaka mata tabaka tausayi idanbakasan komaiba.
Har gari ya waye suna zazzaune kuma har lokacin kukan take saidai qarfinta daya qare
hawayene kawai ke tsiyayowa ahankali.
Dr na shigowa da safe ya sallamesu shida ummi ne suka kamota ahankali take takawa harsuka
isa mota.
Tana shiga motar ta fashe da wani sabon kuka ahankali ya shafo kanta yana kallon fuskarta dan
har lokacin baya iya magana.
Da shaqaqqiyar murya tace,
Nidai ka kaini gida gurin ummana.
Girgixa mata kai yayi dan ganin yake idan ya bu'de baki yayi magana wuta zata iya fitowa sbd
wutar bala'in dake cin zuciyarsa.
Ummi ma da ranta ke 6ace dannewa tayi a fuske tace,
Muje akaita gidan idan hankalinta ya 'dan kwanta daga baya sai a dawo da ita.
Har cikin gida ummi takaita gurin ummanta dasai alokacin tasan meke faruwa hankalinta ya
tashi matuqa.
Harsuka iso gida bamai iya magana acikinsu.
Tsit palon ba kowa dukaninsu suna 'dakunansu bawai dan basu tashiba saidan babu mai
kwanciyar hankali da nutsuwa acikinsu.
A palo ya zauna ya rufe idanuwansa dasuke masa wani yaji yaji tsabar Jan 6acin rai.
Ummi kuwa 'dakin neesah ta nufa tana shiga ta tarar da ita zaune tsakiyar gado ta cusa kanta
cikin cinyoyinta ba kuka takeba amma idanuwanta sunyi jajir hakama fuskarta sbd kukan data
kwana tanayi.
Kallonta ummin tayi tabbas tanason neesah fiyeda 'yayanta saidai hakan bazai hana tayi mata
fa'dan abinda tayiba.
Aneesah"" ummi takira sunanta da fuska a 'daure.
'Dagowa tayi zuciyarta na harbawa sbd ummin bata ta6a kiran sunanta ba.
Juyawa tayi fuska ba walwala tace,
Kizo Palo yanxu kisameni.
Jiki a sanyaye ta sauko gadon ta fito palon.
Tana fitowa ya rintse ido yanajin zafin zuciyarsa na qaruwa.
Jamaal "" ummi takira sunansa bai amsaba ya miqe tsaye tareda rintse ido yace,
Ummi bana buqatar sauraron komai dangane da wannan maganar sbd bana buqatar cigaba da
zama da ita and pls ummi karku tirsasani sbd komai zai iya faruwa....
Da sauri Ahmed ya qaraso gabansa zaiyi magana Jamaal ya wanka masa Marika guda biyu a
Jere.
Tasowa ummi tayi ta riqe Jamaal 'din
Cikin wani mugun 6acin rai yace,
Kaida ita wlh badan ummi ba saina nuna muku matsayinku.
Idonsa jajir shima ya 'dago murya a karye yace,
Ko yanxu ka nunamin tsayina zan 'dauka koyayane amma dan Allah ka yarda dani karka
hukunta neesah ba laifinta bane zan dauki kowane irin hukunci nawa da nata.
Takaici da baqin cikin Ahmed 'din ne suka qara rufesa ya fixgo neesar ya jefawa Ahmed din
harsaidata bugu a goshi jini yafara fitowa a hasale cikin karsashi yace,
Kuje can Ku qarata bana bugqatarta bare kai da har abada na cireka cikin jinina.
Kallon Ahmed ummi tayi cikin 6acin rai idonta taf da hawayen baqin cikin dake shirin afko musu
tace,
Gskia ne dasa hannunka dumu dumu a 6arewar cikin?
Ido jajir yana kallon neesah dake kukan dake cin ransa yace,
Sharrin she'dan ne ummi amma dan Allah karkuga laifin neesah...wani wawan Marin takaici
ummi tasakar masa tana huci kafin tayi baya inna Rabi tai saurin riqeta tana hawaye itama sbd
ganin masifar data afkowa gidan.
Rarrafowa yayi yana hawaye murya na rawa kamar zararre yace,
Ure angry ummi and you have every right to be amma
Ummi kuyimin hukuncin komai amma dan Allah kice kar Yaya ya rabu da neesah ummi sonda
nake yiwa neesah yakusa zuwa qarshe dan nasan kasheni sonta zaiyi amma bazan ta6a bari
tarabu da Jamaal ba, ummi inason neesah,ummi sondanake mata bazai bari nabarta ta cutuba
um...
Dukan baqin ciki Jamaal ya rufesa dashi tako ina shikuwa ko motsi yaqi yi sai kallon neesah
dake kallonsa cikin wani irin yanayi na shiga zuciya tana kuka ahankali.
Ummi ma kukan take ahankali takasa koda motsi ga jini dake fita ta baki da hancin Ahmed
amma har lokacin Jamaal yakasa daina dukansa.
Har lokacin idonsa nakan neesah batasan sands ta matso da gudu ta rungumo kansaba dayayi
sharkaf da jiniba ta fashe da kukan sonsa da tausayinsa.
Zuciyarsa ce taqara tunxura da baqin ciki tareda zafin rai ya fixgo qatuwar electric flower verse
ya 'daga a hasale zai qarasasu kowama ya huta da azabar zuciya khadija dake tsaye tuni tana
kuka kamar ranta zai fita ta qarasoda gudu ta gifta inna rabi ma tuni ta riqesa nan ya dafe
zuciyarsa dake shirin bugawa yabar palon yana rangaji dan har lokacin tana rungume da
Ahmed 'din da tuni ya fice hayyacinsa hannunsa gam cikin nata.
Jiri takeji da zazza6in tashin hankali amma haka ta miqe da gudu ta nufi 'daki ta 'dauko key
zeey dake 'dakin tana leqen komai ta taso da sauri ta kar6i key sbd neesan kanta bazata iya
driving ba.
Harsuka fice gidan ummi bata motsaba saima sabon kukan dayazo mata inna Rabi na
rarrashinta jiki asanyaye da tashin hankali.
Baya take taredashi hannunta na riqe da nasa duk da itama tuni tafara ganin dishi dishi kafin
idanuwanta suka rufe ruf.
Wani shu'umin murmushi zeey tasaki tareda qarawa mortar gudu ta nufi hanyar barin gari.
Tafiyar 5 kilomita tayi daga cikin garin kafin ta gangara daji ka'dan shige gate 'din 'dan babban
gidan leloh da yaransa.
Yaran liloh biyu suka shigar mata dasu ciki tabar motar nan takar6i mukullin motar liloh 'daya ta
koma cikin gari a guje.
Qofar gidansu ayeesha ta parker batareda tafitoba takirata awaya ta fada mata tana qofar gida.
Ayeesha da tuni dama ta girgije tun bayan barinsu jamaal ta fito cikin Riga da wando black
tareda blue facingcap da black speck ta fito riqeda handbag ta fada motar dama zeey bata
kashe ba ta Figa da gudu suka bar qofar gidan.
Suna parking motar Habib nashigawo harabar gidan.
Wani kallo yake watsawa ayeesha yana cewa,
Finally dai today is our day of victory.
Cikin farin ciki mara misaltuwa tasaki dariya tareda kar6ar kwalbar hannunta leloh ta kur6a tace,
Yes and all tnx goes to our dearest zeey.
Dariya suka sheqe da ita gaba 'daya suka 'dunguma zuwa palon.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*�
_Don't forget to vote, follow and comments_
[8:31AM, 4/9/2018] �+234 703 593 2228�: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*48-49*
Ahankali tafara bude idanuwanta dasukai mata nauyi dakuma qirjinta dake mata matuqar ciwo.
'Dakin tabi da kallo taga lafiyayyen 'dakine ta lumshe ido tana jin azabar ciwon kai da qirjinta
yana qaruwa.
Dafa bango tafarayi ahankali ta tashi zaune saita hango Ahmed gefenta a yashe bayako
numfashi gabanta ya buga nan take komai yadawo mata ta rarrafa kansa ta girgizashi jikinta na
rawa hawaye na gangaro mata.
Ko alamar rai bata gani atareda shiba a ru'de ta rarrafa gurin qaramin fridge 'din dake 'dakin ta
bu'de bataga ruwa acikiba hasalima ko aiki bayayi ta miqe jiri na 'dibarta ta fa'da mataccen
toilet 'din dake 'dakin daqyar ta samo ruwa da alama ma sun dade dan harsun fara canza kala
amma bata damuba ta 'debo ta zuba masa a fuska.
Sam babu alamun zai motsa ta qara zuba masa amma bai motsaba.
Jikintane yasaki ta zube gabansa tareda rungumo kansa ta fashe da wani irin kuka mai ciwo da
bata ta6ayiba a rayuwarta sbd har cikin tsakiyar ranta takejin sonsa ayanxu.
Kuka take kamar ranta zai fita hartana shaqewa..
Ahankali taji ya motsa kansa yana qoqarin 'dago kansa amma ya kasa.
Dariyar farin ciki da kukane suka zo mata lokaci 'daya ta 'dago ta kallesa hawayen jajayen
idanuwanta na tsananta gudu murya a dashe tace,
Ahmed pls don't leave me...
Lumshe idanu yayi cikin azabar ciwon dayakeji daqyar bakinsa ahankali yace,
Anty neesah pls forgive me,
Son danake miki ne yasa idanuwana rufewa harna aikata abubuwa da dama pls forgive me.
Cikin sheshekar kuka tace,
Ahmed na yafe maka amma pls kar katafi kabarni daidai lokacin da zuciyata take tsananin
buqatarka.
Lumshe idanu yayi yace,
Ina miki so mai tsani Anty neesah shiyasa ko ayanxu bana baqin cikin mutawa ahannunki saidai
baqin cikina zan tafi nabarki cikin tarin maqiya marasa imani su ayee...
Numfashinsane yafara qoqarin sarqewa ga jinin daya qara 6allewa daga bakinsa.
Tashi tayi da sauri cikin tashin hankali tana waiwayensa ta nufi qofar 'dakin ta fita Neman
taimako.
Zaune suke suna tattaunawa cikin farin ciki ga kayan drinks da snacks a gabansu..
Habib da ayeesha suke zaune kujera 'daya duk kusan Rabin jikinta cikin nasa
Sai zeey dake zaune ta 'Dora qafafunta kan table 'din gabansu
Leloh ma qafarsa akan table 'din take yana busa sigarinsa tareda korawa da giya.
Zeey ta 'dau remote ta rage volume tareda kallonsu tace,
Guys time na tafiya muyi abinda yakamata kowa yakama gabansa sbd ni da anbi ta tawa datun
kafin nazo nan dasu zan Parker motar a daji na kunna mata wuta duk su qone kowama ya huta.
Murmushi ayeesha tasaki tareda hararar Habib tace,
Wannan kwa'dayayyen yace saiya cire kwadayinsa akanta ya muka iya.
Liloh yasaki wata yar iskar daria yace,
Kuma nima saina huta da ita bayan yagama sbd kyawu irin nata bantaba ganinsaba dan haka
zan 'dandana na tabbatar idan har ciki haka abin yake.
Koma me zakuyi kuyi dan a qaje nake danaga fitar numfashinta na qarshe bayan nagama ganin
kun wulaqanta rayuwarta kunyi mata kaca.....
Idonta ne ya sauka cikin na neesah kafin ta qarasa maganarta ta miqe batareda wani tsoroba ta
nufeta tana wani shu'umin murmushi.
Duk iya yanda taso danne mamakin da tsoronta kasawa tayi tafara binsu da kallo 'daya bayan
'daya idanuwanta na ka'dawa da mummunan 6acin rai kafin ta tsaida kallonta kan zeey tanajin
wani 6acin rai na shigarta.
Daria zeey tasaki cikin kallon raini zatai magana neesah ta 'daga hannu ta yanka mata wani
gigitaccen mari saiga ha6o ya 6alle mata ta 'dago a hasale zatai magana nesaah ta kuma watsa
mata wasu marika biyu atare.
Atare dukkansu suka miqe suna kallon yanda idanuwan neesah 'din sukai jajir alamun takai
qarshen fusata.
Baya zeey tayi tareda rarumo qatuwar kwalbar giyar leloh ta kwa'dawa neesah a kai tuni
goshinta ya fashe da jini.
Sake 'daga fasashiyar kwalbar tayi ta soka daidai cikin neesah daidai nan Ahmed daya taso
yana bin bango ya kara kwalbar tayi masa kyakkyawar suka a ciki.
Ihu neesah tasaki tareda 'daga hannuwa ta riqosa lokacin dayake qoqarin zubewa amma taji an
damqota ta baya.
Kuka take tana kiran sunansa tareda qoqarin qwacewa sbd ganin ya zube jini na gangarowa
daga jikinsa amma har lokacin idanuwansa ita suke kallo bakinsa na motsawa ahankali tana iya
gano sunanta yake fada.
Hannu take miqawa ta kamo nasa daya ke miqo mata Habib yafara janta yana cewa,
Yaudai duk wani miyau na saina maida akanki kafin ya yayyagaki mu cinna miki wuta harke har
wannan sabon tauraron zuciyar taki.
Janta yake da qarfi yana qoqarin turata 'daki tana ihu tana qoqarin qwacewa.
Lumshe ido Ahmed yayi cikin azaba kafin ya tattaro 'dan qaramin kuzari ya fixgo bindigar
wandon leloh daya hango ya harbi Habib saura qiris yasamu neesah sbd hannunsa dake rawar
rashin qarfi.
A