Showing 3001 words to 6000 words out of 52687 words
Chapter 2 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf
hankalinta yakasa kwanciya da abubuwan
dake faruwa.
Zubewa yayi gabanta ya riqo hannayenta cikin tashin hankali yace,
Umma dan Allah kadaki yankewa neesah wannan hukuncin sbd zai lalata rayuwarta data
iyayenta
Umma yakike tsammanin mutane zasu dau zancen ace neesah ta 6ata kuma anfasa aurenta
Mutane 'dauka zasuyi wani abin banzar ta aikata har aka fasa aurenta kinga daganan samun
miji zaiyi mata wahala kuma ma ba duk wannan ba Umma wlh ina son neesah kamar
numfashina dan Allah kadaki rabani da farin cikina.
'Dauke kai tayi cikin tunanin abinda yafada to amma idan ta yarda ya auri neesah za'ariqa
gulmar 'danta akan ya auri wadda ta gudu yawon banxa daren aurenta
Nasa mai sauqi ne duk yanda yakesonta bayan kwana biyu zai hakura ya nemi wata.
Girgiza kai tayi da sauri ta miqe tsaye cikin tamke fuska tace,
Tahir idan har ni ce na haifeka to tabbas bazaka auri neesah ba kuma wlh nagama magana
yanxu kawunka zaije yasanar musu cewar mun fasa.
Quryar 'dakinta tashige tana gama fadar hakan tabarsa zaune yana rintse idanuwansa dasukai
mugun ja.
_11:00am_
Ahankali ta bude idanuwanta dasukai mata nauyi ga kanta datakejin yayi mata wani nauyi.
Da qyar ta tashi zaune zaune tana kallon 'dakin tana lumshe ido sbd har lokacin basu gama
bude mataba.
Gabanta ya fadi da qarfi sbd tuno abinda faru hartazo nan.
Jikinta takalla taga komai nata na jikinta head ne kawai babu
Ta tashi a hankali ta sauko gadon amma jiri ya hanata tsayuwa sbd jinta take kamar abuge ko
tsayuwa bata iyayi ga idanuwanta suma sun kasa gani sosai.
Bango tafara bi tana tanga'di hartakai qofa takama handle da qyar ta bude tafito palo.
Zaune yake a palon yana kur6a wine a hankali yana waya da Umma tana sanar masa yazo
maza dashi da Kawu zasu gidansu neesah su fada musu anfasa auren.
Wani shu'umin murmushi yasaki zaiyi magana sai ganinta yayi tafito tana bin bango.
Kashe wayar yayi tareda aje cup 'din hannunsa yataso yana murmushi yace,
There she comes my beautiful charming baby..
Hannu yakai zai rungumota ta 'daga hannu zata maresa amma takasa sbd ko gani batayi sosai
hakama jikinta a mugun mace yake.
Sheqewa yayi da wata muguwar daria yana cewa,
Baby kadama ki wahalar da kanki bazaki iya komai ba you can't even stand dan haka
kidaina qoqarin yin wani Abu.
Qara 'daga hannu tai amma sai hannun yakasa kaiwa.
Da qarfi ya fixgota jikinsa ya matse yana shinshinata yana lumshe idanu wani 'dadi na shigarsa.
Rigarta ya fara qoqarin zamewa ta tattaro wani 'dan qarfi ta turesa tana qoqarin zubewa sbd layi
ta
Damqarta yayi sbd ransa daya fara 6aci gashi zata 6ata masa time harsai Umma tasake
kiransa.
Matseta yayi ajikinsa yana qoqarin kai bakinsa anata.,
Zubewa tayi qasa cikin baqin ciki hawaye nafitowa idanuwanta sbd ko kadan batada qarfin
qwatar kanta.
Binta yayi qasa ya cicci6eta ya yanufi bedroom da ita cikin zaquwa dan jin yake idan baiyi
gaggawar kusantarta ba yanxu zai iya rasa ransa.
Zip 'din rigarta ya bu'de yafara shafar lallausau fatarta yana lumshe ido harya gangaro kan
qirjinta yana 'dora hannu akan qirjinta yaji nutsuwarsa ta qara kwancewa jikinsa yadau rawa
yafara qoqarin rabata da rigar ta tattaro qarfi daqyar ta turesa amma ko motsi baiyiba sbd
qarfinsa da nata ba 'daya ba.
Lasarta yafarayi tako ina
Jin yana qoqarin rabata da pant 'dinta ta 'daga hannunta daqyar ta lalubo bedside lamp ta
'dagota da qyar ta kwada masa akai.
Wata raza nanniyar qara yasaki tareda zubewa gefenta a sume.
Fadowa tai qasan gadon ta rarrafa ta fito Palo da qyar takai kanta bakin fridge 'din data hango
palon ta budesa da qyar ta lalubo robar ruwa
Bata tsaya la'akari da sanyin ruwanba ta bude robar ta juyewa kanta har fuskarta sbd tunanin
ko zata rage jin mayen kota samu qarfin gudu.
Sanyin ruwa ya shigeta sosai ta girgiza kanta taji wani 'dan qarfi yashigeta hakama mayen ya
rage.
Miqewa tayi da sauri ta nufi qofa ta fice daga gidan tafara sauri tana waiwaye gashi ko 'dankwali
babu akanta ga rigarta saija da qasa take sbd yanayin 'dinkin bridal gown.
A firgice ya tashi ya dudduba yaga tabbas ta gudu
'Daki yakoma da sauri yashirya dan gwara yaje gida su sanarwa iyayen neesah sun fasa data
rigasa ta tona masa asiri gwara yarigata.
Da mugun gudu ya isa gidan ko zama baiyiba suka 'dunguma zuwa gidansu neesah.
Tahir kuwa tunda garin ya waye bai fitoba yana 'dakinsa ya rufe kansa banda zubar hawaye ba
abinda yake.
Mamuh馃拫
[3:19AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )
_By_
_Mamuh geee_
*8-9*
Saida tayi tafiya sosai cikin qarfin hali sbd har lokacin qarfin jikinta bai gama dawowa ba ga
rigarta datai mata wani irin nauyi sai ja da qasa take.
Jiri taji ya fara 'dibarta kanta ya fara jujjuyawa ta sulale qasa daidai wani mai napep yakawo yayi
saurin tsayawa
Itakuwa tattaro qarfi tayi ta fa'da cikin napep 'din tana fada masa inda zai kaita cikin qarfin hali.
Sosai su Abba suka razana da zancen janyewar dasu tahir sukai,
daddyn Lagos ( _dadyn Jamaal_ ) kuwa ransa ne yayi mugun 6aci ya kalli su kawun yace
amma dai wannan harkar qaranta sosai kuka nuna dan banga dalilin fasa aureba kuma tsabar
wulaqanci saida yarage awa biyu 'daurin aure zaku fasa ance muku baza aganta bane ko kuwa
duk cikin son zubar mana da girma.....
Alh hakuri dai shine abinda zan kuma baku sbd nima nasan hakan tozarcine gareku yi muku
hakan amma wlh uwar yaron ta kafe akan aure dai baza'ayiba.
Abban neesah kuwa tsabar takaici da baqin ciki ko magana ya kasa yimusu sai kallon takaici
dayake aika musu dadyn Lagos ne kawai keta faman fada.
Mota ce qirar landcruiser 2018 baqa ta parker qofar gate din gidan nesa kadan sbd motacin
dasuka fara cika layin na 'yan 'daurin aure.
Saurayine kyakkyawa ajin qarshe 'dan kimanin shekaru ashirin da Biyar zuwa da shida.
Ba baqi bane hakama ba fari bane saidai hutu dajin dadi tareda kwanciyar hankali yasa fatarsa
haske tareda wani irin sheqi.
Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda sky blue light mai laushin gaske,
Hakama hular Kansa blue ce sai diamond Rolex watch dake daure a hannunsa da black half
cover shoes na kamfanin _gorge phelex arman_ _Jamaal muh'd abdallah._
Babban amininsa yuseef daya 'daukosa daga airport yafito cikin motar shima cikin nasa adon
na 'daurin auren.
Cikin gidan suka nufa kai tsaye,
Ahmad dake harabar gidan tareda wasu baqi yayi saurin qarasowa gurinsa yana cewa,
Yaya Jamaal sannu da hanya.
'Dan sakin fiska yayi ya amsa tareda wucewa kai tsaye Palin Abba dai dai fitowarsu gabaki
'daya daga palon.
Tsayawa yayi yagaidasu abban suka amsa kowanne rai ajagule kafin su qara wata maganar
saigasu ummi da mamy sun iso gurin.
Ahmed ma matsowa yayi ya tsaya ganin kamar dukkanin iyayen nasu cikin wata damuwar
bayan ta 6atan neesah.
Habib ne ya kuma bude baki yace to mu zamu tafi Allah ya hada kowa da rabonsa hakama
Allah ya shirya muku 'yarku dan gskia abin da mamaki saidai kawai muce Allah yasa ta gane
idanma wani ne ke hure mata kunn.......
Wani mahaukacin mari yaji yasauka a fuskarsa saida yayi baya kamar zai kife ya 'dago da sauri
idanuwansa jajir ya kalli Wanda ya kwada masa Marin.
Cikin takaici yake kallon Jamaal amma sai yaga yayi masa wani irin kwarjini ya juya afusace zai
fita ba zaro yaji saukar wani Marin yana 'dagowa yaganta a tsaye tana tsoyayar hawaye,
Ba Wanda ya lura da zuwanta saidatai marin ummi tayi wurinta da sauri ta cikin ga farin ciki ga
baqin ciki.
A hasale ya kallesu 'daya bayan 'daya yace,
A haka kuke son a auri yar tashar 'yarku?
Yarinyar data gudu ta kwana gidan namiji a daren 'daurin aurenta
Hakama ta 'daga hannu ta mari babba agabanku amma baku iya 'daukar mataki ba,
To tabbas wannan marin wlh saikinyi dana sanin yinsa arayuwarki dan saiya zamar miki masifa.
Kaima kuma kasan baka mari banza ba,
Sannan bazansan kunji haushin fasawarmu ba saikun samar mata miji a yau kun 'daura mata
aure koda yake wane me juyewar qwaqwalwar ne zai auri ragin wani...
Hannu Jamaal yakuma 'dagawa zai kai masa wani marin abban neesah ya riqe hannunsa cikin
takaici da baqin cikin ga zuciyarsa datai masa nauyi ya dafe tareda girgizawa Jamaal kai.
Mudai bamayi akaiwa wani idan kuma gskia ne ga 'dankunan mai zafin kai saiku 'daura masa
mudai mun fasa.
Ficewa sukai daga gidan hannunsa nakan kumatunsa har lokacin.
Kukan baqin ciki mamy da neesah suka saki lokaci 'daya kafin neesah ta sulale ta zube qasa a
sume.
Ummi ce takamota jikinta a tsorace kafin tasa ahmad ya daukar mata ita suka kaita sama 'dakin
mamy.
Jamaal kuwa fitowa yayi shida yuseef suka bar gidan yana mamakin yanda Sam wani lokacin
mata basada tunanin komai girmansu
Yanxu ita wannan taje tahau wata soyayya da Wanda Sam familynsa basada tunani bare
mutumci,,,
Unbelievable "" yafada ahankali yana yamutsa fiska.
Sosai gidan ya qara kaurewa da hayaniya ga 'yan 'daurin aure tuni suka cika layin da anguwar.
Tsit su Abban sukai a palon cikin jimami da kunyar yanda zasu sanar da jama'ar dasuka taru
cewar anfasa 'daurin auren.
Jiniyar isowar gwamna da tawagarsa tacika anguwar suka kalli juna Abba cikin sanyin murya
yace,
Alh kaje kasanar da jama'ar an fasa 'daurin auren kada mubarsu suita jira.
Mamy najin haka ta fashe da wani kukan Anty mamee ta dafata itama cikin tsananin damuwa.
Jiki a sanyaye dadyn Lagos yafito cikin jama'ar yana gaggaisawa da mutane
Manyan senators da members, ga gwamnoni da manyan alqalai ga maroqa tako ina waqa
suke,
ji yayi sam bazai iyaba ya juyo zai dawo cikin gidan saiga Jamaal yadawo yi musu bankwana
zai koma tunda aure yafasu,
Kwarjininsa da cikar zatinsa da dakakkiyar shigarsa tasa
Maroqa na ganinsa suka zageyesa sunai masa kirarin ango sbd tunanin shine ango.
Kallon da baifi sakan gomaba da tunani yasa dadyn sakin ajiyar zuciya ya nufi cikin gidan.
Kallon abban yayi yace,
Justice insha Allah nasamar mana mafita kafito yanxu afara gabatarda 'daurin aure lokaci
na tafiya.
Abban baice komaiba ya miqe suka fita sbd yasan dadyn komai yaza6arwa neesah daidai ne.
_DAURIN AURE_
2:00pm
Abbah shiyayi wallicin ango yayinda babban amininsa former justice rufai yayi waliyi Amarya
neesah aka fara gabatarda 'daurin aure.
Babban sarkin maroqa yafara yadawa a loudspeaker
Yau ranar asabar sha biyu ga Satan biyu an 'daura auren _jamalu muh'd abdallah_ da
_aneesah justice sanda_ akan sadaki naira dubu 'dari.
Yuseef ne yaji abinda maroqin me fada ya juyo yana watsawa Jamaal kallon mmamaki yana
cewa,
Amma wlh gayen nan ka rainamin hankali,
Dama aurenka ne za'a 'daura ka rude da cewar na neesah ne.
Wayar dayake tun 'dazu da ayeesha ya kashe yana kallon yuseef cikin lumshe fararen oily eyes
'dinsa yace,
Uhummm me kake fadane?
Harararsa yayi yace,
Kaga rainin wayon ya isa hakanan kuma......
Moroqane suka yanyamesu kafin yace wani Abu.
Kirari suke bakin rai yuseef ya fara yi musu 6arin kudi cikin farinn ciki batareda ya nuna
damuwar komaiba.
Kallon mamaki Jamaal yatsayayi kafin shima dai yafidda kudi sosai yabasu batareda yasan
meke faruwa ba.
Mamuh馃拫
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*10-11*
Maroqa cikin jin dadi suka cigaba da watso kirarinsu sbd ganin yanda Jamaal da Yusuf ke musu
6arin nerori.
Wayarsa ce tai ringing
Da kamar bazai duba ba saiya 'dago yaduba.,
Siririn tsaki yaja kafin ya 'daga wayar tareda barin gurin ya nufi cikin gidan.
Part din dayake amatsayin nasa duk lokacin dayazo gidan can ya nufa.
Komai fes sai qamshin rose air freshener da sanyin ac dake tashi ga dukkan alama Ahmed
qaninsa anan ya sauka.
Zama yayi a sofa tareda crossing legs yana amsa wayar cikin rashin fahimtar me ayeeshar ke
fada ahankali yace,
Calm down pls ayeesha sbd I don't understand a single word acikin magananki.
Wani sabon baqin ciki da takaici suka taso mata amma gudun 6ata ransa saita danne tace,
Captain I just got a massage from a friend cewan kayi aure,I mean wai an 'daura aurenka
yau.
Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya yace,
Eshaah,,,,
Jiki a sanyaye ga wani bala'i dake cinta amma ta danne itama cikin sanyin muryar tace,
Uhumm captain,
Eshaah me kikeson nafada miki yanxu?
Inaso kafadamin idan gskia ne ko sa6anin hakan.
Ayeesha you know me,koda auren nayi banga wani dalilin qin fada mikiba sbd I have every right
nayi abinda nakeso so pls kadaki kuma jin irin silly talks 'dinnan kifadamin,okay?
Batareda hankalinta ya kwantaba tace,
Insha Allah captain.
Yaso janta da fira amma jin duk tayi sanyi sai kawai ya kashe wayar daidai shigowar Yusuf yana
sakar masa dariyar qeta yace,
Ango zakasha maifa.
Batareda ya 'dago ya kallesaba yace,
So u are the good friend da ayeesha ke fada kenan?
Zama Yusuf yayi yana shafo sumar kansa bayan ya cire hularsa cikin dariya yace,
Eh to kusan hakan ne duk da dai bansan me kake fadaba amma dai ni ina bayan ayeesha
sbd bazan iya da rigimammiyar amaryarka ba dan ko kai da kake angon bansan ya zaku
qareba.
Still bai 'dagoba yana daddana wayarsa yace,
Yusuf can you pls stop talking bcoz I'm reading sumtin hia and ure disturbing.
Daria Yusuf 'din yasaki ahankali sbd sosai ya hango yanayin zaman dasu Jamaal 'din zasuyi,
A yanda yasan Jamaal miskili mai sanyin hali da ko oho da abu
Ga neesah mai masifar jin aji da ganin ita babba yarinyace uwa uba ga son girma Wanda hakan
yasa Sam ko gaisawa basayi da Jamaal sbd tana masa kallon 'dan rainin hnkali da girman kai
yayi masa yawa tunda ko kallo bata ishesaba dukda tana matsayin wadda ta girmesa.,
Sosai ya hango rikicin zaman gashi alamu sun nuna Jamaal baimasan da aurenba.
Wayarsa ce tayi qara yaduba yaga ayeesa ce.
Kallon Jamaal yayi yaga har lokacin hnkalinsa nakan wayarsa.
Hello ayeeshan captain.
Daga can 6angarenta Murya a sanyaye tace,
Yaya Yusuf pls ka taimaki zuciyata daga halinda take shirin fadawa kafadamin gskiar zance
pls Yaya Yusuf.
Tausayinta Yakama Yusuf sosai sbd shi shaidane akan irin tsananin son da ayeeshar ke yiwa
Jamaal duk da shima yanayimata soyayya mai sanyi.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali yace,
Ayeesha ki kwantar da hankalinki dan auren Jamaal na tabbatarda bazai hanasa aurenki ba
sbd yana sonki,
So ki kwantarda hankalinki sbd shima auren a bazata yazo masa.
Kuka tasaki mai cin rai tanajin wani qaton baqin cikin Jamaal 'din matar daya aura koma
wacece.
Kuka take sosai Yusuf na rarrashinta a wayar qarshema kashe wayar tayi tareda wurgi da ita
tana fasheewa da wani sabon kukan baqin ciki.
Kallon seconds biyar Jamaal yayiwa Yusuf cikin nazarin kalamansa sbd kallo na karantar
yanayin mutum 'dabi'arsa ce.
Alamar haqiqanin gskia ya karanto a fuskar Yusuf ya aje wayarsa tareda fuskantar Yusuf
idanuwansa na qoqarin 6oye 6acin ransa ya bude baki zaiyi magana Ahmed gashigo palon da
sallama yakalli yayansa cikin jinjina alamarin shima yace,
Ya Jamaal su dady na kiranka.
Lumshe idanuwansa yayi ya bude dan zuwa lokacin idanuwansa sun fara canxa launi.
Tsaye ya miqe tareda zuba hannayensa a ajihun wandon shaddarsa ya nufi qofa batareda ya
kalli Ahmed da aka aikoba.
Qasan maqoshi sallamarsa ta fito sbd sosai yaji 6acin rai na shigarsa duk da baisan dalilin
kiranba amma yafara zargin maganar Yusuf da ayeesha gaskia ne,
Danne yanayinsa yayi ya qarasa kujerar nesa dasu dadyn batareda yace uffan ba.
Abban neesah shikansa yayi shakkar wannan hadin na Jamaal da neesah da dadyn yayi sbd
sarai yasan neesah da taurin rai da kafewa akan Abu gashi Sam dama bawai wani kula juna
sukeda Jamaal dinba,
Shima Jamaal duk sanyin halinsa akwai taurin rai da kafiya akan Abu gashi Sam baya wasa da
kowa sbd bayason shirme ko raini a al'amuransa
Shiyasa yake hango ru'du sosai a zamanta kewar auren nasu.
Dady ma yasan da duk wannan saidai a ganinsa dole 'dayansu zai aje kafewar da girman kan
yabi 'dan uwansa idan lokaci yaja.
Gyara murya dady yayi fuska a 'daure yace,