Showing 1 words to 3000 words out of 26224 words

Chapter 1 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf

🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.






Free page:01

KANO STATE.


*Unguwar kwanar Æ´an dadawa*

Tafe take tana ƙwambo,ta ɗage kafaɗarta ɗaya irin yadda nigogi keyi,jikinta sanye da wata
ƙatuwar riga irinta maza da wando shima ƙato,kanta sanyeda pcap,zariyar wandon harkusada
gwiwar ta,ƙafarta sanyeda wani ƙaton boot na maza baƙi, duk ya tsufa yasha faci,kayan jikinta
kuwa sunyi uban squeezing,se ƙwambo take tana hura hanci,tafiyarta ma tanayi rana ɗage kafa
ɗaya kamar namiji,hannunta riƙeda ƙaramin bucket fari wanda ake cewa fallasa na talla,shaƙe
yake da awara me miya.


Tana tafiya tana É—age kafada irin yadda maza keyi,duk inda ta gitta yara da manya sekaji ana
kANDE mai awara,ita kuma tana É—aga hannu kamar wata Æ´ar siyasa tana faÉ—in "eh mana,dawa
dai, kuhuta kawai".

Tana kawo wa wata chamber samari guri ya kaure da ihu suna faÉ—in zaa kand, zaa
kand,itakuwa se wani ɗage kafada take tana ƙwambo,tana basu hannu suna kashewa kamar
yadda maza ke gaisawa da junansu.

Cikin karkace baki kamar namiji tace "eh maza yane?, ya ake ciki ne eye?,kun haÉ—o min
balance É—ina ko yaya?"

ÆŠaya daga cikin samarin yace "ai tuni na cake miki uwar kuÉ—in ki zaa kand, d one nd only
ƙanwar maza in the ƴan daddawa village" wani juyowa tayi ta kallesa ta karkace baki ita adole
namiji ce tace "zakarius asswear zan bubburma maka hannu a hanci,see zis tsamius want to
read me nonsenseus eh,tsohon waye yake a village din iye? Zakarius zafa mu raba
tawun(town) da kai fa,Allah wlh, Ni kar ka sake cewa unguwar mu village garama kawai ka mata
zigidir ka kirata local getto yafi yawwa", tafada tana wani dire bokitin awarar ta.

Tamika maka hannu tace "giv me zaa yastazey(yesterday)balans",miƙa mata kuɗin yayi,ta amsa
ta gyara p cap dinta ta laƙwato miyau tafara ƙirga kuɗinta.

"Wan,su,siri,foo,fai,sis,sabin,ess,nai,sen" haka ta dinga fillila Æ´an hamsi2 tana kirgawa ita adole
turanci take,samarin wurin sunmata yuuu da ido suna kallon É—an bakinta kamar gidan tsutsa
gashi jajur wai ita anan namiji ce,kaf faɗin unguwar batada ƙawa duka maza ne abokan
hurɗarta,acewarta ita ƙanwar maza ce sbd haka itama namiji ce ba ragguwa ba,ƙawarta ɗaya
ce layuza,itama sbd tsananin haƙurinta da juriya yasa suke ɗasawa,saboda tun suna yara ita
kaÉ—ai ce take jure wahalar bala'in kande shiyasa har suka girma suna tare,kuma bata sauyaba
duk ko yadda suke da mugun banbanci in person. Iyayen layuza sunyi2 suraba wannan abota
saboda yadda kande ke tafiyar da rayuwarta kamar ba mace ba, komi nata a tsaitsaye take
yinsa tamkar namiji kasancewa duk yayyenta su takwas maza ne,ita kaÉ—ai ce mace,se yaran
kawunnanta mata biyu.


Wani siririn saurayi ne yazo chamber yana wani hura hanci,tana tafiya yana kakkaɓe wandonsa
da hankacif,ta inda ta ajiye bokitin awarar yabi ze wuce,be Ankara ba ta finciko rigarsa ta baya
da hannu É—aya tadawo dashi inda take tsaye tace "kai yane? Bakaga manyan guys bane zaka
wani taho siii kamar dodon koÉ—i kana nema ka yimin tamola da bucket of my awaras" cikin
broken english dinsa yace "hey u mara foka, liv my t-shirt alone,wat do you say,i will eat ur fada,
daughter of air kawai".


Cikin ƙaraji tace "hey wat do u nufi iye? Is me ka kira dota of air iye? Hey gayis ku cafa min shi
anan gurin,Ni ze nunawa karyar turanci harda zakigina,kamar ni zaa soja of gidan ustazu habu
me kayan koli,zecewa dota of air,nice Æ´ar iska,dama É—an iska kace dana maka afuwa,gayis oya
ku tara masa na yashi abaka" aikuwa rana rufe baki É—an kanzaginta zakarius ya fizgo wnn
lamushshsem saurayin yafara talle masa ƙeya,yana faɗin "hu are u iye?,do u know zaa soja of
Æ´an daddawa getto iye,zis is zaa kANDE, me awara and zaa one nd only soja of zis tawun".

Dasauri wani saurayi ya taso yana cewa "easy zaa kand, baki gane wnn bane eh?".


Cikin hura hanci ita adole uban daba tace "hey Boris don't firgita me, don't do yawa,kawai ka
bari nasa zakarius da duna sumasa ɓalli-ɓalli a hammata,Allah wlh yanzun nan se nasa su
mayar dashi kangaroo hannuwa aɗage" tafaɗa tana keɓe baki gefe.

Boris yace "dawa de zaa kand wnn fa she is jikan mai unguwa Bello,kin mantashine?, tun muna
yara aka kaishi bauci karatu gurin Æ´an uwansu,baki gane shiba?".su adole se sunyi
turanci,dama haka suke duk Æ´an gang din kande Mayun turancine,dolema kayi turancin nan na
dole inde kana tare da kande.
Se lokacin taƙare masa kallo tace kai "Bello sagalo, innalillahi wai wnn Bello sagalo ne wanda
yake shan majina muna yara, innalillahi yee gurin ya kaure da ihu,Bello sagalo haka akayi ta ihu
ana kashewa,suna tambayar sa yakaratu, yanata zuba musu ƙarya yace ai yagama degree
dinsa a harkar noma,shi yanzu she is piropeshonal farmer ne in d Æ´an daddawa tawun.

Kallonsa kawai suke suna ta ihu yana basu labarin ƙarya bayan ance musu almajiranci aka
kaishi,amma se gashi yana ce musu shi yagama degree dinsa,se zabga musu turanci yake.


Kande ta daga murya tace "oya kip kwayet,oya zakarius É—auko min awarar cen kowa yasiya
kuma yau ba bashi wlh, asawata(mamanta) tace kitty zatakai hospital bcos of she is not
well,sbd haka kowa yau seya biya zeci".


Boris yace "dawa de zaa kand wlh yunwa nakeji kuma banda ko ƙarfanfan yau,yau emti nake
alqur'an,atemaka abani har gobe" kallonsa tayi tace "yawa kake zakarius eh,meye haka
ne,Allah yau sede Kaci tuwon asawarka,kanaji fa nace kitty ba lfy yau Allah no loan of my
awaras".

Nan danan aka wawashe awarar suna tsaka daci Bello jikan me gari yace "kawarmu amma
awarar nan wlh da dadi" cikin jin haushi tace "kai sagalo wlh zansa zakarius yamaka askin rabin
hanci,dan me dafa muku tuwo agidanku wanene kawarku?, ni am soja,zaa one nd only soja of
gidan ustazu habu me kayan koli,ko kace zaa kand,da nayi niyyar nayafe maka kuÉ—in awarar
amma nafasa,kuma wlh dan ma awarar ta shekaran jiyace datafi hk daÉ—i".


Duk kallon ta sukayi jin abinda tafaÉ—a wai awarar ta shekaran jiyace,masu lashe hannu duk aka
tsaya ana kallon.

Sauran guda huÉ—un da ta rage tace zakarius ya É—auka ya cinye tabashi kyauta.

Wato ita kande haka take duk bala'i seta faÉ—i gsky sede a mutu.


Gata da kyauta,abunta baya rufe mata ido sam.


..........


Hanyar gida ta nufa bayan tagama haÉ—a kan Æ´an cinikinta,tana tafe tana wakar bobmali tana
wani buÉ—a kafaÉ—u,duk inda ta gitta zakaji ana zaa kand tana Sa'a de mutanena, tana É—aga
hannu kamar meneman ƙuri'a.

Dede wani gida madedeci yasha suminti taja birki ganin maza na fitowa daga zauren gidan
nasu da alama yanzu aka idar da sallar azahar,dama idan aka aka zauna É—aukar karatu agurin
babanta se anyi sallar azahar sannan ake watsewa, gefe taja tana fito se wani kallo mazan da
suka kasance samari da magidanta harma da tsoffi suke mata,wasu na mata kallon tir da ita
batayi halin ubanta ba wanda yakasance babban malami a unguwar kuma liman.

Yayinda wasu suke mata kallon marar kamun kai kuma marar hankali,wasu ma kallon da suke
mata ma'anarsa aboye take.

Ganin sungama wucewa ne tazo tana bouncing tashige cikin gidan itama,a zauren ta haÉ—u da
babanta mlm babu me kayan koli,tana shiga tace "Sa'a de dagus, zaa imamu sannunka de da
hutawa" kallonta yayi murmushi kwance akan fuskarsa cikin Muryar ustazai yace "a'a ya
kande,ainafin daga gurin tallar ake ne?" "Dawa de dagus,dagacen nake kuma an siyar,duk da
na faÉ—a musu ta shekaran jiyace amma haka suka lamushe suka caken balans É—ina,kasan
innata akwai iya sarrafa hatsi,duk taurin kan hatsi yana tsoron masifar inna,shiyasa kaƙi kara
aure dagus,hehehe Kai dagus nawa,zaa imamu sekayi Allah wlh" tafaɗa tana keɓe baki gefe
tare da sheqewa da dariya ganin yadda baban nata sauke tabaransa yana mata kallon ƙasan
ido.


Cigaba tayi "wai dagus ina zawarar nan taka ne batula iye? Kasan fa cikar nan tana bala'in
ƙaunarka iye, she is love you lodi lodi asswear,yawa kake imamu,kawai karufe ido kayi wuff da
batula,kadena tsoron inna ni na tsaya maka,kalli batula Æ´ar caras da ita eyane" ganin tana
neman gurin zama yasa cikin lallashi yace "ainafin yake uwata kisamu kishiga daga ciki ki kai
kuɗin tallar naki,seki samu ki watsa ruwa ajikin ki ko yaa kande" sheqewa da dariya tayi tamiƙe
ta É—auki bokitinta tace kai innata Allah yasa de Æ´ar aljanna ce,duk ta rikita mana zaa imam da
bala'in ta,imamu guda amma yana tsoron matarsa hehehe" takara sheqewa da dariya tana fito.

Ball take da duk abinda yatari gabanta,tana faÉ—in "asswear Sena saka Æ´an gidan nan adashen
robobi,tunda kun zama non living things,ko Ina se kun karkasa kaya sekace gidan kutare, Æ´an
yawa kawai, Alqur'an inde bazaku zama living things ba sede kuyita siyan sabbin kaya,dan
kullum Sena fasa wanda nagani a tsakar gida", wata matace tafito daga É—akin ta tahau durawa
kande zagi ganin tayi mata fatali da sabon bahonta data jiƙan kayan wanki,gashi se yararin
ruwa yake da alama ya fashe ne.

Ko kallon inda take kande batayiba ta afka ɗakin innarta ko cire takalman ƙafarta batayiba,wani
baƙin cikin ne ya tokarewa umma amaƙoshi ganin ko kulata kande batayiba duk irin manyan
ashariyar datake sauke mata,ga sabon bahonta agefe ruwan ciki yagama tararewa aƙasa sbd
babbar hujewa da yayi,ƙwafa tayi ta juya ɗakinta inda tabar baƙuwarta.


AÉ—akin su kande kuwa, tasamu innarta ta idar da Salla takalleta tace, "uwar masu gida ya akayi
naga bokiti, incede ba bashi kika rabar da awarar ba yauma?" "Ga balans É—inki nan yau ba
arnen dana baiwa bashi,kowa seda yaban ƙudina,kuma na gaya musu awarar shekaran jiyace
datayi cimbi amma dashike hannunki na daurine sunsiye harda lamushe hannu,kai inna hoo
ke,hoo ke ga masifa ga iya girki,ga kyau kamar birin wasa,zaa inna ta,matar imamu,kin mallake
mana liman guda duk masifarki amma yaƙi kara aure,yafita gari ana girmama shi,amma daga
shigo gida seya koma kamar zakaran da ruwa yayiwa bugun dawa,kai inna Allah de yasa
kishiga aljanna" tafaɗa tana shafa ƙatuwar magen dake kwance akan gadon innarta ta,duka
inna ta kaiwa kande ta goce tana dariya tace "zanci ubanki fa uwar masu gida,nikike fadawa
Allah yasa zan shiga aljanna? Yo idan aljannar ta ubankice kice karya sakani".


"Sa'a de inna kema kin san idan aljanna a hannun dagus take da tunkan ki sheqe ma ze wullaki
cikinta,Kodan jarabar ki,ni jiyama batula ta tareni a hanya tace ina imamu nata,harda sabulu
tabani" da gudu inna ta biyo kande aikuwa takwasa aguje se dakin kakarta Amo,kan ta shige
É—akin tasakeyin ball da bahon umma na É—azu aikuwa yarabe biyu,ko waiwayawa batayiba ta
afka É—akin Amo kakarta, cikin ihu irinta bebaye Amo tace "na shiga uku takwara, waya biyoki ne
kike neman kayar dani?".


Acen waje kuwa inna wani aikin takama ta fita batun kande,dan tasan ko giyar wake tasha
bazata fara binta É—akin Amo ba wacce yaran gidan suke kira da gwaggo,dan ko bazata bari ta
daki kande ba koda lefin me tamata balle yanzu da suke ba'a.


Tana cikin haɗe kayan wanke wankenta Sega umma ta fito daga ɗaki ta rako baƙuwarta kallon
banza sukayiwa inna suyi hanyar zaure, umma se sakewa inna habaici take.,

Ko ci kanku inna batace musu ba,sukayi hanyar waje suna ƙus-ƙus,cikin ƙasa da murya umma
take cewa,"dan Allah lami ki tabbatar kinje min gurin nan,wlh kullum na kalli waccen shegiyar
me suffar maza banajin na gamsu,sonake talalace takoma kamar karya,ganin ta ahaka be
isheniba sonake takona magajiyar" takarasa tana kashewa lami ido,shewa sukayi suka tafa.

Koda umma tadawo daga rakiya tasamu bahonta adagargaje wata ashariya me rai ta lailayi
tana sakewa,"wani É—an kaza kazane ya dagargaza mata sabon bahonta,wane tsinanne
ne,ɗebabbe,tanbaɗaɗɗe", tanayi tana karasawa kusada inna,tana zuwa ta duƙa ta dau
fasasshen bahon nata tana bangaje inna ai kafin tayi motsi ba biyu inna ta kwashe ƙafarta Sega
umma aƙasa kamar an juye buhun dawa,ihu tasaki dede Lokacin da ƴarta Ikilima ta sanyo
kai,ganin uwarta aƙasa tana zabga ihu ga inna agefe kamar batasan abinda akeyiba dan ko
kallon inda umma take tule aƙasa bata kallo kamar ba ita ta juyeta aƙasanba.


Aguje Ikilima ta rugo tana faɗin "innalillahi umma sannu,garin yaya kika faɗi,gashi dan baƙin hali
bawanda yatemaka miki" tafaÉ—a tana zabgawa inna harara, cikin kururuwa umma tace "ga
baƙar muguwar data kwashen ƙafa nan,sbd nayi magana akan tsinanniyar ƴarta me suffar
maza,ta fasamin baho,wayyihuhu kashin aguÉ—ina ze balle,yiiiihiii duwaiwaina".

Cikin masifa Ikilima tasani ummanta tayo kan inna tana zage zage da niyyar tureta,aikuwa tana
sakin umman tasake tafiya rijib tazube aƙasa tasake ƙwallah ihu,ko waige Ikilima batayiba
burinta ta ture inna wacce ke tsaye tana kallon yadda Ikilima ta zaburo kamar zatayi faÉ—a da
Sa'arta, tana zuwa gaban inna taja ta tsaya kamar an riketa takasa tureta sbd wani irin kwarjini
da taga innar tayi mata,dede lokacin kande ta fito daga É—akin Amo tagama cika cikinta da fura.

Duk abinda ake tanajinsu, tana zuwa ta kwashe fuskar Ikilima da wani mari, tasa ƙafa fa
kwashe kafar Ikilima tahau jibagarta sekace soja ya kama kwarto,ihu Ikilima keyi da kururuwa
itada ummanta,sunata aikawa kande zagi da jafa'i kala2.


Ihunsu ya janyo hankalin sauran Æ´an gidan aka firfito ana kallon wnn dramar,aka rasa wanda ze
kwaci Ikilima a hannun kande,seda tanata lilis sannan ta kyaleta,inna kuwa aikinsa taci gaba da
yi kamar bata gurin,kande tana gama jibgar Ikilima tasa kai tayi hanyar waje tana buÉ—a kafaÉ—a
da hura hanci.

Seda ta fice sannan aka fara cece kuce, ana mayarda yadda akayi,umma se kururuwar
ankashe mata Æ´a take,tana jifan kande da munanan alkaba'i.


Amo kakar su kande tana É—aki tana kallo batasan ma me ake ciki agidan ba, kasancewarta

bebiya ce,se akusa cinnawa gidan wuta da bala'i batasan anayiba. Kallon da takeyima in za a
kasheta batasan me ake cewa ba,sede tayi ƙuru da ido tana kallon hoto tunda bajin abinda ake
faÉ—a take ba.



Wai wacece kande ne.



_Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daÉ—e suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin
kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma
yakawomu acikin wnn daddaÉ—an labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_


_shin dake akayi daddaÉ—ar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN
YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku
da wani daddaÉ—an labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata
bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_

_zazzafar tafiyace me É—auke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haÉ—i da ban tausayi,tattareda
zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da
surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_


*kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa
wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin
07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret*



Magoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all😘




Share fisabilillahi 🤲

🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.

Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.


Free page:02


Bismillahirrah manirrahim.

Mlm Hamza shine sunan mahaifin malam habu me kayan koli mahaifin kande,yanada mata
biyu Amina da Hafsatu, Amina (Amo)itace uwar gidansa ta DaÉ—e bata haihuba har seda mlm
Hamza yakara aure ya auro Æ´ar uwarsa Hafsatu ta haifi yaro namiji ana cemasa Musa,ko
shekara beyiba Allah ya baiwa Amina ciki, tahaifi namiji itama aka sanya masa Abubakar,
shekarar sa biyar Hafsatu takara haihuwar namiji aka sanya masa Mudassir.


Suna zamansu lfy daga baya Amina tafara wani irin ciwon kai da kunne harya kai tana ficewa a
hayyacinta,idan ciwon ya taso seyayi kwana uku batasan inda kanta yake ba,anje asibiti sun
kasa gano ainahin meyake damunta,haka aka koma na Hausa duk de bata canza zani ba,dg
baya tafara wasu ƙuraje ajikinta kamar ƴan zufa, daga baya aka gane ashe baƙon dauro ne
yakamata, duk da cewa bashida alaƙa da ciwon kanta,amma tunda aka gano baƙon dauro ne
aka tashi tsaye da magani,daga wnn ciwon seya zamto batajin magana sosai,bakinta ma
dakyar idan tayi magana ake gane abinda take faɗa,tun ana zuwa asibiti abu yaƙi sauki har
daga baya idonta ma ya fara wani fari2,seya zamto bataji,bata gani,bata magana,hakan yasa
tabar wasiyyar riƙon Abubakar a hannun Hafsatu,dan ta sakawa ranta ciwon bana tashi
bane,iyayen Amina sunso su É—auketa amma nlm Hamza da Hafsatu suka hana,Hafsatu na iya
bakin ƙoƙarinta da Amina,mlm Hamza yana kan neman magani baya gajiya,cikin hukuncin
Ubangiji aka kwatanta musu wani me maganin gargajiya hardana iska acen kura,datemakon
Allah aka fara samun sauki,idonta ya washe haka tafara magana amma da ƙarfi,kunnenta
yafara budewa ta yadda sekayi magana da karfi sannan zataji.

Wannan shine dalilin zamowar Amina bebiya,daga baƙon dauro takoma bebiya,bayan tasamu
sauki sukaci gaba da zamansu da Hafsatu lafiya har lokacin kuma Abubakar na hannun Hafsatu
ta haÉ—a da Æ´aÆ´anta ta rike.


Kwatsam aka wayi gari Hafsatu ta rasu ba ciwo ba komi,daga baccin dare bata farka ba, Amina
da mlm Hamza sunyi matukar yin baƙin cikin rashin Hafsatu daga baya suka dangana,se rikon
yaran duka yakoma hannun Amina wacce suke kira da Amo.


Musa, Abubakar, Mudassir sun kasance Æ´an uwa masu son junansu,sunada hadin kai
sosai,sam bazakace suÉ—in Æ´an uba bane,saboda suna da haÉ—in kai,manoma ne kamar
mahaifinsu, suna noma da kiwo sosai hakan yasa sukeda rufin asiri sosai.


Sunyi karatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login