Showing 24001 words to 26224 words out of 26224 words
Chapter 9 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf
hawaye masu zafi,tabbas shi yasani dole
wata rana abinda yake gudu ze faru,amma be ɗauka abin a kusa yake ba,ji yake kamar
bayason wannan ɓoyayyen sirrin ya bayyana,inama wannan abin da suka binne ze iya zama
sirrin da har abada baze bayyana ba,inama inama,amma ba yadda ya iya,shi yasani dole ne
abinda yake gudu seya faru,yasani wata rana dole hakan zata kasance.
Kallon kyakkyawar fuskar ƴar tasa ya yi wacce ta jiƙe sharkaf da gumi,jikinta duk ya saki,juyowa
ya yi ya kalli inna wacce ta takure se sharbar kuka take,tunda aljanin kande ya fara magana ta
shigo ɗakin,dan ta zaga ne sanda mlm ya shigo hannunsa riƙe da kande, fitowar ta ne ta gansu
acikin yanayin da kande bata hayyacinta.
Itama taji duk abinda kande ta faɗa ko ace iskanta ya faɗa.
Shimfiɗera mlm ya yi,seda ta kai kusan magrib tana bacci kafin ta tashi a gajiye, jikinta duk ya
mutu,akasalance ta kalli inna da Amo wanda suke zaune akan ta hannun Amo da carbi,se ja
take tana zare ido,duk a tsorace take,kamar ace kyat ta fece aguje.
Inna kuma hannunta riƙe da wayarta keypad ta kunna kira'a sun ajiye a gefe.
Da sauri kande ta tashi zaune,tace subhanallahi inna karfe nawa ne,kallon juna inna da Amo
sukayi kafin inna tace "karfe Shida da hamsin ne auta, ya akayi ne?,me za'a kawo miki kici?",
saurin miƙewa tayi tana faɗin "innalillahi,inna garin yaya nayi bacci me yawa haka kuma baki
tashe ni ba,wlh wani mahaukaci ne yaketa bina, kullum duk inda naje seya bini,ko dan ina bashi
abin ci ne,yau ma har gida ya biyoni,nace zan duba ko kin gama abinci in bashi,ashe kwanciya
nai, kai innalillahi,Allah sarki kirezi kilama ya tafi" tayi maganar a shagwaɓe kuma sak muryarta
tun tana yarinyar ta kafin ta haɗu da lalurar iska.
Kallon Amo inna tayi,itama haka,duk da cewa Amo bataji me kande ta ce ba sbd
kunnenta,amma yadda kanden ta kwaɓe fuska cike da shagwaba yabata mamaki,balle inna da
ta ji abinda tace da kuma yanayin yadda muryarta ta fita,cikin ɗan murna wacce ta fara kama
inna tare da tunanin ko addu'ar su ce ta karɓu ta ce "mahaukaci kuma auta a ina kika samo sa
ke kuwa?" Kamar an mintsineta tace "Allah wlh kuwa inna,wani kirezius ne ya mini ta kaska,duk
inda na dire legediz dita seya ɗora tasa agun,bansan shi bafa, amma ya nanemin,duk inda naje
yana biye,shine yau ya biyo ni harnan da alama tsumagiya ce ta fyaɗosa,dan be taba biyoni har
gidaba se yau," ta dubi inna wacce jikinta ya yi sanyi murnar ta ta koma ciki ganin yadda ta
kuma komawa kanden ta me kamar maza,ta kuma cewa "ya ake ciki ne tuffar dagus akwai
tuwon ne na ɗan sanmasa ya lomata shima?,kila ma ya tafi yaganni shiru kamar an aiki bawa
garinsu, Allah sarki kirezius" ta fada tana sakkowa daga kan gadon.
Acen waje kuwa bayan mlm ya fita,da sauri ya leqa waje dan tabbatar da abinda aljanin kande
yace,wayam ba kirezi ba alamarsa, jinjina kai Malam ya yi,tabbas wannan mahaukacin akwai
ayar tmby akansa,amma tunda yake bibiyar yarinyar sa yasan dole da manufa,kuma dole ze
dawo,yanzu dole shima yasaka ido sosai akan ƴarsa.
* Niger state minna*
_mariga way_
Tafiya suke amotar sunata mayarda zance akan yadda sace sacen mutane yazama ruwan
dare,kawai se a ɗauke mutane ayi daji dasu kamar dabbobi,wasun su suna ganin lefin gwaunati
ɗari bisa ɗari kan taɓarɓarewar tsaro,ga tsadar rayuwa kullum rayuwa daɗa ƙunci take,kullum
talaka shine a wahala amma dan ɓacewar basira da rashin lissafi da talakan de za'ayi amfani
asakasu su yaƙi junansu,su kashe junansu,hallau acikinsu ne ake samun waɗanda sunfi ma
masu garkuwa da mutanen bala'i wato informants.
Wasu suka suna ganin kawai mafiya aksarin kidnappers son zuciya da dogon buri ne yake
sanya su faɗawa cikin harkar,sunyi nisa sunata tattaunawa akan matsalolin rayuwa,ba zato
sukaji direbansu yaja wani wawan birki yana salatin duk da yazo bakinsa, faɗi yake "yau
munshiga uku tamu ta ƙare kowa yayi ta kansa,se a sannan kowa ya lura da abinda ke faruwa
agurin.
Motoci ne iya ganine hange,duk an fitar da mutane an tarasu aguri ɗaya kamar shanaye,wasu
mutane ne sun rufe fuskar su da baƙin abu,jikinsu sanyeda kayan sojoji,mashinansu kusan
guda hamsin fake agefe daya,wasu mahaukatan bindigogi ne ahannun su,se fitar da mutane
suke daga cikin motocinsu suna tattara su gefe ɗaya,cikin sanɗa direban wannan motar ta
saulale ya fice daga motar yabar fasinjoji sunata sallallami,direban nan yana sanɗa acikin ciyayi
yanason ya samu ya gudu,ba zato yaji bindiga akansa an ɗana masa ana cemasa ya miƙe ko a
harbesa.
Cikin tsananin firgita ya miƙe tsaye yana haɗa me bindigar da Allah karya kashe shi,wlh yanada
iyalai da marayu wanda suka dogara da shi,kaɗashi akayi tare da sauran fasinjojin da ya kwaso
har inda aka tara mutanen da aka fara kamawa,yana juyowa idonsa akan wanda ya sanya
masa bindiga,cikin tsananin mamaki yaga ɗaya daga cikin Mutane da ya ɗakko ne, wanda
dashi akayi ta zancen ƴan garkuwa da mutane,ashe shima ɗaya daga cikin su ne.
Kusan duk motocin da aka kama acikin fasinjojin akwai kidnapper aciki,sune suka Sanar da ƴan
uwansu nakan hanya cewar motoci sun taso da yawa,kasancewar ranar cin kasuwar mariga
ne,har sukayi nasarar kame mutane da yawan gaske,mafiya yawancinsu ƴan kasuwa ne,wasu
da kayan da zasu kai don cin kasuwar,wasu kuma da uwar kuɗaɗe ajikinsu don zuwa cin
kasuwa,amma cikin hukuncin Ubangiji duk anyi garkuwa da su.
Seda ƴan bindigan nan suka haɗa mutane masu yawan gaske,kafin suka kaɗasu zuwa
daji,bayan sun amshe musu kuɗaɗe da kayan abinci,haka suka tasa ƙeyar jama'a da dama.
Ga tafiya ba karama ba,wasu a hanya sukayi ta suma,wasu harbinsu akayi saboda sunyi
yunkurin guduwa.
Seda sukayi tafiya me nisan gaske wacce ta shafe awoyi da yawan gaske kafin su isa wani
ƙaramin gari inda ƴan bindigan sukeda zama,haka aka dinga amsar numbobin iyalan bayin
Allahn nan ana kiran su ana sanar musu anyi garkuwa da ƴan uwansu,duk wanda akayi cinikin
sa haka za'a waresa gefe,haka suka dinga cinikin mutane kamar dabbobi.
Wadanda ba a samu cikakken bayani agurin ƴan uwansu ba,da waɗanda sukace su basu da
kowa suma aka waresu gefe,su nasu hukuncin na daban ne,mafiya yawansu saida sassan jikin
su ake,wasu kuma kashesu ake,wasu kuma se ajuyar da tunaninsu suma su koma ƴan bindiga.
*******
_United Arab Emirates _
DUBAI.
_Durah jungle _
Dubai special force vanguard.
Wasu manya manyan sojoji ne da hukumar soja ta dubai suka ware waɗanda ake baiwa horo
na musamman,a wuri na musamman,durah jungle wani sansanin soja ne dake nesa da garin
sosai,su waɗannan sojojin bakowane lokaci ake fita dasu aiki ba,duk wani aiki me mugun haɗari
shine aikinsu,kamar shiga ƙungiyoyin manya manyan daba irinsu, ISIS, mafias,ko kuma
manyan sindicates wanda suka gagari duniya,irin wannan aikin ake tura su domin kawo
ƙarshensa,chief commanda RAYYAN RAHMAN,shine tsaye yana kallon yadda atisayen ke
wakana, tabbas lokacin da yake jira ya kusa ƙaratowa,shi da wasu zaƙaƙwuran sojoji irinsa
wanda suka wahala kuma suka bautawa ƙasar su,sune suka fitar da wannan reshen na sojojin
sirri tare da goyon bayan shuwagabannin kasar na ƙwarai.
Ofishin sa ya koma ya fara fitar da list na sunayen waɗanda za'a tura domin zama ɗaya daga
cikin ƙungiyoyin dabar da sune a jadawalin su a yanzu,su waɗannan ƙungiyoyin sun gagari
duniya ta fannoni daban daban,a kuma ƙasashe mabanbanta,acikin ƙasashen da za'a tura
waɗan nan sojojin akwai Dubai ɗin kanta se phillipines,China,south Africa, Russia,Ghana da
kuma linjeriya kasarmu ta gado.
_Nigeria,Kano state_
*Sannu kaji mamuda, jiki ya yi kyau ai alhamdulillah,kaida muka kawoka ranga ranga kamar
zaka sheqa, baka fa san waye akanka ba,Allah sarki wata yarinya ce me shigar maza shigar ta
ta gwanin ban dariya,ita ce tazo tace mana ga wani me baro cen ya faɗi,shine fa muka rankayo
aguje ashe kaine,ai yarinyar nan ta temaka wlh,da wata ce guduwa zatayi taga mutum a
kwance kamar bashi da rai,uhum kaide mamuda Allah ya kara afuwa,wai nace mamuda bakada
ƴan uwa ne,ni har yau kwananka biyu amma banga kowa yazo da sunan dubiya ba da ga fanni
ka?"
"Wlh jabir kacika ɗan banzan surutu,haba mutum yana kwance bashida lfy amma ka sanya shi
agaba se famar ratattako batu kake babu birki,sekace an buɗe dam din ruwa,haba dan Allaha"
"Kaiko lurwanu daɗi na da kai kenan ka cika saka ido da yanƙwana mutum,haba kalli fa yadda
ƴan matan cen suka kakkallo ni, se wani faɗa kake min acikin jama'a dan na tambayi mamuda
ƴan uwansa,naga ai gsky na faɗa,tunda muka kwaso shi ranga ranga muka kawosa nan
bawani daga nasa da sukazo da sunan duba jikinsa,kuma dan na tambaya shike nan nayi lefi
haba du Allah du Annabi lurwanu".
Se cecekuce samarin suke a tsakaninsu,wanda aka kira da mamuda kuwa yana kishingiɗe
akan gadon marasa lafiya ya lumshe idonsa,ƙala be ce musu ba amma duk abinda suke fada
yana saurare,har suka gama faɗan nasu kuma suka koma fira.
..... Moscow, Russia....
Wani irin gidane cable front acen cikin wani guri wanda ya yi nesa da cikin garin Moscow
ɗin,kusada wani madedecin tafki,wasu manyan security ne suke shawagi agurin,duka ƙofofin
gidan masu password da thumbprint ne,wasu manyan motocine kusan guda goma sha ɗaya
suka parker a waje gidan,biyar agaba biyar abaya,se wata golden lemo a tsakiya,kusan atare
ƙofofin motocin suka buɗe banda ta tsakiyan wacce ta kasance lemo.
Kusan mintuna asirin kafin aka buɗe daya daga cikin ƙofofin lemo din,wani ingarman namijine
ya fito daga cikin motar,jikinsa sanyeda wasu simple Pakistan wear farare tas,se wani
madedecin makawuya daya naɗa akan hular kansa wacce take baƙa, ƙafarsa sanye cikin
takalma sau ciki baƙake,hannunsa sanyeda wani danƙareren agogo me matuƙar tsada,fararen
yatsunsa sanyeda wani zobe baƙi me fuskar zaki,ya riƙe wata sanda kamar da gold me shegen
kyau se walwali take,saurin buɗe masa lema akayi saboda snow ɗin da ke sauka agurin.
Fuskar mutumin kadai idan ka kalla seka kuma kallo,mutum ne majiyi ƙarfi, ingarman namiji ne
sosai,fatarsa har wani yello take,fuskarsa cike da beard me ɗaukar idon me kallo,yanada kyau
me suna kyau*wild king Rolex*kenan,tafiya ya fara cikeda izza irinta maza majiya ƙarfi,duk inda
ya gifta se securityn wurin sun rungume hannunsu ɗaya a ƙirji tare da sunkuyarda kansu.
Yana zuwa gaban main entrance na shiga gida kofar tayi scanning na idonsa,bakinsa ɗauke da
fito ya danna kansa cikin falon wanda ya ɗauki ɗumi me daɗi da ƙamshi,wata matace zaune
fara me dogon gashi ta juya baya,hannunta ɗauke da wata ƙatuwar mage fara me kyau.
Takawa yake yana nufar inda take zaune,bakinsa yana fito,yana isa inda take gaban wasu
duwatsu masu ci da wuta irin room heater ɗin nan na jikin bango amma wannan wasu irin
duwatsu ne masu kyau da sheqi kamar normal dutse suna fitar da zafi de ɗumama daki.
Hannu yasa yana shafar dogon gashinta me kala biyu baƙi da roɗi roɗi kamar fari kamar milk,ko
gezau bata motsa ba,ya cigaba da shafar sumarta har zuwa dogon wuyanta,hannu yasa ya juyo
da kanta da ƙarfi ya juyo da fuskarta...ba zato wayar ɗauko rahoto ta faɗi saboda ganin fuskar
matar nan..
Jama'a kande ce faaaaa, a Moscow
End of free pages kuma book 1.
*************************
Shin menene ainahin asalin kande?
Wanene wannan mighty wild king Rolex din?
Wanene chief commander RAYYAN RAHMAN?
Wani lokaci yake jira?
Wanene mamuda me barrow wanda ke kwance a asibiti?
Wanene general Asim?
Wanene mahaukaci kirezi?
Wai ma suwanene mlm habu da inna?
Wani sirri suka sani akan kande,wanda aljanin kanta yake yawan nanatawa?
Meye alaqaar da aljani yace akwai tsakanin kande da kirezi?
Wani mission ne RAYYAN RAHMAN ze tura special force ɗinsa?
*Duka wannan amsoshin suna dunƙule acikin littafin kande kashi na biyu wato book 2.*
# love
# hate
# crime
# black money
# soccery
# betrayal
# illegal trafficking
# smuggling
# comedy
# romance
# momsani✍️
_Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daɗe suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin
kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma
yakawomu acikin wnn daddaɗan labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_
_shin dake akayi daddaɗar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN
YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku
da wani daddaɗan labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata
bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_
_zazzafar tafiyace me ɗauke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haɗi da ban tausayi,tattareda
zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da
surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_
*kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa
wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin
07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret*
Masoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all