Showing 18001 words to 21000 words out of 26224 words
Chapter 7 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf
nan ba har
matsafa suna siyarwa.
Haka Dr Joshi ya yanke shawarar kawai ya kashe kansa akan ya aikata wannan mummunar
aikin da É—aukar alhakin al'umma Gara kawai yakashe kansa,dan yasan Æ´arsa dake gunsu ma
ba zasu barta lfy ba,bama ze kuma ganinta ba,gara kawai yakashe kansa,wayarsa ya É—auka ya
yi video akan duk abinda ya faru da duk wani details akan harƙallar ya turawa wani abokinsa
dake aiki a Dubai,ko minti biyar beyiba saƙo ya shigo wayarsa da sauri ya duba atunanin sa
abokin nasa ne,amma se ganin wani vedio ya yi daya jijjiga duniyarsa.
<><><><><><><>
Kande tana tafiya amma jitake kamar ana binta idan ta waiwaya kuma bata ganin kowa,tun tana
shiru harta ci birki tana faÉ—in "ko wane arne ne yake bin bayana kawai yayo waje na gansa,in ba
hakaba zan ci me É—umama masa tuwo Allah wlh" se mafita take ita kaÉ—ai amma ba wanda ko
gittawa ya yi a hanyar,cigaba tayi da tafiyarta ta nigogi tana masifa,amma still tanajin takun
mutum alamar ana biye da ita,kamar bazata juyo ba tayi kamar bata damuba kawai ta juyo da
sauri aikuwa idonta ya faÉ—a akan wannan mahaukacin yana dab da ita.
Cikin É—an firgita da yadda ya ke dab da ita tace "kai kirezi dan fazaan ka kasha Omo ne iye, y
are u follow me,are u mad?" Sekuma tace jini kuma ina tambayarasa bayan mahaukacin ne.
Daukar wata sanda tayi tace "ware kabar nan dan me dafa muku tuwo agidanku,bar nan kona
maka ɗaukar amarya na jibga a ƙas" bawan Allah ganin ga ɗakko bulala ai aguje ya ruga ya
barta se Bala'i take ita kaÉ—ai
Acen gida kuwa mama ce tazugo umma wai an hana Æ´aÆ´anta su Hafsah haihuwa se cinye
musu ciki ake tanata kuka,aikuwa umma dake ba hankali ne da itaba ta dinga yada magana
acikin gida amma inna bata kulata ba sema É—auko kwanon silbarta data zuba miyar da tayiwa
Hafsatu tayi ta ajiye aƙasa tana kullo kofar sashen ta.
Umma ganin inna tamata banza cikin jin haushi tace "Allah wadaran maye me cinyewa mutane
Æ´aÆ´a" cikin zafin rai inna ta waiwayo ta kwashe fuskar umma da mari dede lokacin da Mudassir
ya sanyo kai cikin gidan.
í ¼í¼¹kANDEí ¼í¼¹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Not edited
Free page:09
Bismillahirrah manirrahim.
Salati Mudassir yasaki yana fizgo umma daga riƙon da inna ta mata se fyalla mata mari
take,cikin ɓacin rai yace "yau base gobe ba zamu bar gidan nan,Ni dama na daɗe da sanin ba'a
son zamana da iyalina acikin gidan nan,kullum se kande ta kama Ikilima ta daka,yau kuma abin
yakoma kan matata to ni bazan É—auka ba,maza Hadiza tafi ki fara harhaÉ—e mana kayan mu".
Turo baki gaba umma tayi tace "nide gsky wnn gidan ko wutafa baka ja mana ba,Allah ya gani
ba zan iya kwana acikin zafi ba,Ikilima ma jikinta baya son sauro kasani"
Mama dake laɓe abayan ƙofar sashen ta tayi tsuki ganin faɗan beyi nisa ba takoma ɗaki.
Umma tuni tayi gaba tabarsu nan suna kayan haushinsu, itade ko gobe idan Hadiza zata dinga
shiga hanyarta to baza ta gaji da gyara mata zama ba itama,a zaure ta haÉ—u da mlm habu
wanda duk abinda ake yana jinsu,har abinda Hadiza tace yana ji, murmushi kawai ya yi don
yasan ko sama da ƙasa zasu haɗe Hadiza bazata iya barin gidan nan ba,sallama inna ta masa
yace mata adawo lfy yabata wani ruwa acikin gora guda biyu yace idan taje ta baiwa ko
waccensu, in Sha Allah inde matsalarsu ba daga Allah bace shafar jinnu ce ko wani al'amari na
Ubangiji to in Allah yaso bazasu kuma ɓarin ciki ba,dan idan be manta ba Hafsatu ɓari na biyar
kenan tayi,ita kuma Maryam ɓarinta biyu wnn ne aketa murna harya kai wata biyar se kuma
gashi naƙuda ta taso mata da alama shima ɓarinsa za'a yi.
Amsa inna tayi ta fice,a waje taga baba Musa tayi masa sallama ya tsare mata napep tana ya
barshi amma seda ya biya me napep É—in,yanata yi mata gdy da sa albarka itada mlm habu,dan
duk sanda irin haka ta samu yaran nasa itace take ƙoƙari dasu,duk shirin umma da
mama,mama bata bari umma taje gidan su Hafsatu ba wanda yasan dalilinta,ita ma umman
bata sani ba,ko a kwalar rigarta ma abin baya damunta dan ita ba mutum bace me son zuwa
unguwa dama,mama ta fake da cewa tunda uwar asugwui na zuwa wai inna take nufi su suyi
zaman su base sunje ba,da wnn mama ta hana umma zuwa gurin su Hafsatu.
Amma ita idan fitar ta ta kamata tana zuwa gidajen Æ´aÆ´an umma batareda ta sani ba.
Kande a hanyarta ta dawowa daga kasuwa tana shirin tsallaka titi amma an tsayar da kowa
daga masu ababen hawa har masu tafiya aƙafa,wasu irin maka makan motoci ne na sojoji
baƙaƙe suketa wucewa aguje, tana tsaye agefe tana kallo,se masifa take wai an hana su
wucewa saboda wasu banzaye masu baƙaƙen kaya,wai su sojoji,wanda tasan yanzu idan zasu
ga bomb ba wanda ze tsaya guduwa za suyi "mtswwww*,taja wani dogon tsuki tana cewa "ai
wlh idan jarumin soja na gaske akeson gani abari nazama soja za aga jarumta, duk wani bomb
ko wata AK47,dasu igwa,dasu gurnet,dasu tiyagas da waye bazasu bani tsoro ba,kai woo ni
woo ni,zaa kand zaa ƙanwar mazaje su ustazu Hamis dasu ya Musa,zaa 1 nd only soja of gidan
ustazu habu me kayan koli yihuuuu cau cau" ta fada tana wani jijjiga ita bata yadda ba itama
namiji ce kuma soja ce, kallonta na kusa ta ita sukayi suka kwashe da dariya.
Ihun mutane suke yi ganin wani mahaukaci ya karto aguje ta cikin jerin motocin nan yanaso ya
tsallaka,cikin rashin Sa'a motar ta bigeshi,ai aguje kande ga saki kayan hannunta aƙasa ta ratso
cikin mutane tana "kai ku kauce" har ta iso gaban mahaukacin nan wanda yake ta juya kansa
daya ɗan fashe ga gwiwar hannunsa ma ta ƙuƙƙuje,saurin tsallaka wa tayi inda mahaukacin
yake zaune se yamutsa fuska yake alamar yanaji zafin ciwon nasa,tsugunnawa tayi ta kama
kan nasa ta É—ago tayi saurin yago gefen burmemiyar rigar jikinta ta É—aure masa kan
nasa,mutane anci dafifi ba wanda ya isa inda suke se kallo ake ana mayarda yacce akayi,gasu
tsakiyar titi ga rana,ga motocin nan dole suka dakata saboda basu gama wucewa ba
mahaukacin ya ratsa har aka buge shi.
Kallonsa tayi tace "kai kirezi ina zaka je ne bakada farin tuwo ne acikin kanka iye?wai
ƙwaƙwalwa ce farin tuwo,kana kallo kowa an saka masa pause saboda lakwaye zasu wuce
amma ka wani taho aguje, inama zakaje ne,ba a area na baroka ba meya kawo nan?kar de
sake biyo ni kayi?aiko gashinan ka samu riba Dilla miƙe kirezius kawai" se masifa take masa
tana turancesa kamar yana fahimtar me take faɗa,kama masa hannu tayi ta miƙar dashi tace
"taho na kaika gefe ka huta".
Wani soja ne ya fito cikin baƙaƙen kaya fuskarsa sanyeda face mask ya rike wata bindiga abar
tsoro yana zare jajayen idonsa yace "hey u bunch of lunatics,bazaku tashi agurin ba?bakwa
gani kun tsare mana hanya ne?"
Juyowa kande tayi tana kallonsa kamar bazata ce komiba sekuma ta tsaya tamasa kallon sama
da ƙasa tace "me i no wasa da ragwayen sojoji lyk U,kuma kaine benci ba ni ba ɗan renin
hankali kawai, É—an wulaqanci ku bige mutum ko sannu baku ce masa ba sannan kawani taho
ciki agaba kamar tankar miyau dawasu idonka kamar gautar É—aci kanaso ka karanta min
nonsenseus,eh r u mara foka living things kawai, ni bana tsoron ka ehe ,i no tsoronka" daga
hannu cikin ɓacin rai ze mareta mutane se kallo akw,wasu ma tafiya suke amma sun tsaya
kallon yacce zata kaya tsakanin wannan yarinyar me shigar maza,dan bazasu ce itama
mahaukaciyar bace duba da yadda take tsaf tsaf,kawai shigar ta ce ta maza.
Tana tsaye ƙiƙam ko gezau batayiba mahaukacin nan kuwa hana tsaye a bayanta se ɓoye
fuskarsa yake alamar tsoro yakeji,ya rirriƙe mata riga ta baya,ganin za'a mareta da sauri ya
kama hannunta yana ja alamar ta zo su gudu amma kande da taurin kai ta fizge rigarta tace
"Dilla cen cikamin rigata,idan tsoro kakeji koma gefe kayi kallo,ko kuma ka hau legediz Benz
dinka ka ja saɓa,wannan kurtin sojan besan ni bane,nima fa banaji Allah wlh, Nima soja ce daka
ganni anan kawai wannan kayan ne bana sakawa",ta fada tana juyowa kan wannan sojan,dede
sanda ya sauke hannunsa caraf aka cafe hannun,juyowa ya yi yaga wanene wannan me rabon
shan wahalar,saurin ƙamewa ya yi yana sarawa wanda ya riƙe hannun nasa,yace "sorry
boss,wannan mahaukatan ne suka tsayar damu,sun shiga kan hanya" yafaÉ—a har lokacin yana
ƙame"
Kallon kande da taja daga wanda ya fito yanzu ya yi,yana sanye cikin wasu irin kaki na sojojin
ciki wato elite force,ya ɗaure gashinsa da band baƙi,fuskarsa rufe da mask iya idon sa ne
abuɗe,kallonta yake yadda take wank hura hanci taja ƙafa ɗaya baya ɗaya agaba ta dunƙule
hannu kamar zata kai naushi, irin tana jiran kora kwana,matsowa ya yi kusada ita cikin wata
exotic voice yace "sorry Æ´an mata,bakuji ciwo ba ko?" "Normal kawai oga,beji ciwoba ai bani
aka bigeba wannan kirezin ne" tafaÉ—a tana wani karkace baki gefe tana hura hanci tare da nuna
mahaukacin wanda har lokacin idonsa aƙasa yana ɓoyewa abayan kande, se wani sunkwi da
kai yake.
Ƙura masa ido general Asim ya yi wanda sunansa yake rubuce agaban rigar kakin jikinsa,har
lokacin be cire mask É—in ba,kallon mahaukacin yake sosai kafin ya juyo kan kande yace "cool
down soja girl yi hkr naga beji ciwo sosai ba ma,amshi wannan ki siya masa maganin ko a
chemist ne" yafaɗa yana mikawa wannan sojan na ɗazu hannu, kuɗi ya miƙo masa masu yawa
ya amsa yana miƙawa kande,amsa tayi tana wani ci cijewa ta ƙirge 5k ta miƙa masa sauran
tace "wannnan ma sun isa,zan siya masa harda abinci ma,1k kuma na siyi waken soya na dana
zubar nasan yadda ake yunwar nan wasu sun kwashe" kallonta kawai yake be amsaba ta ajiye
akan wata mota dake kusa dasu tace "censa yakkaɓai na sara maka,naga kamar kai nagari
ne,mazan fama Allah tsare gaba da bayanka, banda wasu masu neman dukan talakawa,censa
yakkaɓai" yafaɗa tana sara masa,amma wai yakkaɓai zatace masa.
Shide yana tsaye yana kallon ikon Allah tajanyo hannun mahaukaci wanda g.Asim keta ƙarewa
kallo sukayi gaba, mutane se kallon kande ake ana mamakin ƙarfin halin ta,haka ta dinga tsara
mutane tana wucewa janye da hannun mahaukaci wanda yake ta rawar jiki kamar yanajin
tsoron mutane.
Komawa mota su g.Asim sukayi suka ƙara gaba.
Haka kande ta kai mahaukaci wani chemist aka wanke masa ciwo se yatsina fuska yake,kande
na gefe tana yi masa sannu cen tace "Dilla jishi ƙato da kai se wani kwaɓe fuska kake,bawani
zafin kirki nasani, kuma ma wai ina Æ´an uwanka ne suka barka se galantoyi kake layi2
kwararo2,koda yake ma kaida kake kirezi ina zaka sani" haka ta dinga ɓaɓatu me Chemist nata
dariyar yadda take wani buÉ—e kafaÉ—a take ita adole najimi ce.
Ana gamawa ta biya kudin taje bakin masallaci ta siya masa shinkafa da wake me mai,ta siya
masa kifi soyayya ta saka aciki ta sai nasa fanta ta haÉ—a ta kawo masa,ko wanke hannu be
jiraba ya zurma hannu yafara kai loma hannu baka hannu ƙwarya.
Kallon sa take seya bata tausayi tace "oo kirezi anji gumama, kai wlh yunwa arniya ce
baruwanta da hauka ko kai yaro ne,kawai kowa farmaka take,kai yunwa Allah gama mana dake
arniya kawai" idan ba gizo idon ta ya yi ba kamar murmushi mahaukacin nan ya yi,amma se
taga kamar idonta ne,yana gamawa ta zuba masa ruwa ta É—au gorar da ya shanye fanta ta
watsa maganin da me Chemist ya basu ta zuba ruwa ta jijjiga yana narkewa cikin dabara ta
baiwa mahaukacin nan aiko ya amshe ya shanye ba musu ta kalle sa tace "kai kirezi a haka de
kamar me hankali, duk yacce akayi da kai ba wata damuwa,kuma dan Allah duk Æ´an uwanku
aka rasa wanda ze kula dakai,nagade ba ka duka balle suce, yaude nayi aikin lada,dole ma na
faÉ—awa su zakarius".
Seda ta ga ya fara bacci aƙasan bishiyar mangoro da suka zauna sannan ta tashi tace "barin
ware nide,gashi bakada suna to korezi se anjima na saɓe".
Hartayi nisa mahaukacin nan be dena kallonta ba,idonsa cike da hawaye.
Bayan inna ta gama kulawa da hafsatyta mata duk wani abinda yakamata tamata sallama ta
wuce asibitin mlm Aminu Kano gurin Maryam wacce take nan rai a hannun Allah, ta kasa
haihuwar abin dake cikin kula ga haihuwar,duk ta galabaice ta fice a hayyacinta, tana ganin inna
ta fashe da kuma tana rike hannun innar tace "kuyafemin inna mutuwa zanyi,dan Allah kice
mama da baba su yafe min,momy da Abba kuma ku yafe min dan Allah mommy kicewa Aliyu
shima ha yafemin" tana gama faÉ—a tafara salati,da sauri inna ta ciro ruwan addu'ar da mlm
yabata ta kafawa Maryam abaki wani ya shiga wani ya zube haka har tasha kusan rabi,mintinan
goma tsakani tafara wata irin jijjiga kamar convulsion ya kamata da sauri mommy sarakuwar
Maryam ta fita ta kira nurses suna zuwa sukace kowa yafita abasu guri.
Kafin awa daya Maryam ta haifi abinda ke cikin ta ashe twins ne gasunan kamar ƙadangaru
haka aka nannaÉ—e acikin tsumma aka baiwa daddyn Aliyu dan shi Aliyu mijin Maryam baya gari
yana hanyar dawowa.
Tasamu bacci,acen inna ta wuni har dare, koda kande ta koma gida bataga inna ba agurin mlm
ta tare se addabar sa take da sheri kala2 tana masa zancen bazawararsa batula,anan unguwar
take tana mugun son mlm habu,hakan yasa duk inda taga kande yi take kamar ta mayar da ita
cikin ciki.
Se dare kusan taran tare inna ta dawo,koda ta dawo ta samu kande tayi bacci a É—akin Amo.
Zaune take agaban madubinta na tsafi ta saka doguwar rigarta baƙa wacce take sawa idan
zasu gana da bokanya mama,cikin ɓacin rai da murya me firgitarwa mama tace "Zabba'u babu
yadda za'ayi aikin ki ya yi kyau bayan kin zauna kina bacci,an toshe mana duk wasu hanyoyi da
zamu kuma samun galaba akan Æ´aÆ´anki,daga yanzu bazamu kuma samun damar sadaukar da
jininsu wa dodo ba,sannan ƴarki siddiƙa ba abinda zamu iya yi mata,na gargaɗeki akan karki
yadda kowa ya ganki alokacin da kike birne mahaifa da kuma jinjirin karyar nan,kin karya mana
doka saboda haka dole ki karɓi hukuncinki"
Cikin matsanancin firgicin mama take cewa "kitemakeni yake mama Ajuji yaja da zamaninki
yake mama me tukunyar Sheri,wallahi bansan yadda akayi hakan ta kasance ba,bansan wanda
ya ganni ba a sanda nake aiwatar da aikin,seda na tabbatar kafa sun kau kafin na aiwatar da
aikin,sannan bansan taya aka toshe mana hanyoyin baiwa dodo Ajuji jinin su Hafsatu ba,mama
kitemaka min,abani wani aikin komin hatsarinsa inde Æ´ata siddika zata dawo cikin nutsuwarta to
koma meye na amince zanyi".
ÆŠago kai mama bokanya tayi baka iya hango fuskarta sam,se wani abu jaa sosai kamar
garwashi wanda yake nan kamar idonta,cikin muryarta me rarrabuwa tace" babu wani aiki da
zaki aiwatar da ze ceci Æ´arki,tun farko mun gargaÉ—eki amma shashancinki da banzan tunanin ki
yabaki cewa ke kaɗai ce me jiran duhun dare domin aiwatar da buƙatarki,saboda haka a yanzu
de babu abinda zamu iya miki,karki kuma nemana idan ba abu me muhimmanci kika zo dashi
ba"
Jiki a sanyaye mama ta rufe madubin ta na tsafi,kuma ta duƙufa acikin tunanin neman
mafita,tabbas ko ya zatayi seta ga bayan A'isha,tunda suka taso a rayuwa itace matsalarta,
tunani tafarayi rahuwarta ta baya.
FLASH BACK..
Zabba'u mama da A'isha Inna,maƙotan juna ne kafin suyi aure,tun suna yara ba wani jituwa
suke ba Allah be haÉ—a jininsu ba sam,haka kawai Zabba'u ta tsani A'isha batareda wani
ƙwaƙƙwaran dalili ba,irin tsanar nan ta rashin haɗuwar jini marar tushe.
Islamiyyarsu É—aya, Zabba'u ta girmi A'isha,amma A'isha na gaba da ita a makarantar
islamiyya,saboda ƙoƙarin A'isha itace head girl a lokacin,wata rana tana tsaron latti abakin gate
itada ƴan uwanta prefect Sega Zabba'u da tawagar ƙawayenta ƴan salon tsiya kai ba
kokari,haka sukazo kansu tsaye zasu wuce amma prefect din nan sukace dole se an musu
bulalar latti,nan fa faɗa ya ɓarke harda dambe A'isha na gefe duk masifarta bata fiya dambe
ba,dan irin mutanen nan ne masu zuciya da nacin faÉ—a,kuma inda tasaka maka hannu seta fitar
da jini,hakan yasa bata fiya dambe ba.
Tafiya tayi ta sanarda shugaban makarantar alokacin yana meeting da wasu malamai da
alarammomi akan musabaƙar da za'ayi yana basu sunayen ɗalibai masu hazaƙa,acikin
malamai baƙin fuskar da sukazo makaranta harda mlm habu,acikin ɗaliban kuwa harda
A'isha,da sauri shugaban ya tashi ya biyo bayanta, haka ma mlm habu,koda sukaje sun samu
Zabba'u tacire hijab ɗinta se tiƙar dambe take da prefects ɗin,yaranda tama girmesu,aikuwa nan
da nan shugaban makaranta ya tattara su zuwa Ofishin sa, aka tmby meya faru nan fa kowa ya
hayayyaƙo tana bada bayani,kowa nason ace shine me gsky, A'isha na gefe batace komi
ba,buga musu tsawa shugaban makaranta ya yi kafin ya juyo kan A'isha yace "head girl Muna
sauraron ki meya faru?" Nan ta kwashe yadda akayi ta fada cikin nutsuwarta kanta a sunkuye,
nan shugaban makaranta ya baiwa wani malami bulala yace ya zane masa su Zabba'u,aiko
agaban baƙin malaman nan aka zanesu se sharɓar kuka suke amma Zabba'u ko gezau
batayiba duk da yadda bayanta ke raÉ—aÉ—i dan sun