Showing 6001 words to 9000 words out of 26224 words

Chapter 3 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf

bamu basa damar guduwa ba.

Shine wanda ya fara bayyana ajikinta sakamakon ruwan addu'a da aka shafa mata, seda muka
tabbatar kun ƙonasa da ayoyin Allah ta yadda baze ƙara moruwa ba kafin muka barsa ya
fita,fita ta har abada bakuma ze ƙara gigin shafarta ba".


Se yanzu ta sauke numfashi idanunta arufe,cikin sanyin jiki malam yace in Sha Allah babu
abinda wani mahaluki ya isa ya yi agaremu face abinda Allah ya tsara mana.


Tabbas munji daÉ—i kuma muna gdy bisa kariyar da ka kasance kana baiwa Æ´armu,amma kasani
mudin bil adama ne babu wani haÉ—i tsakanin mu daku, muna godiya matuqa amma dole zaka
bar jikin wnn yarinya,idan kayi duba da ƙarancin shekarunta sbd haka ina gamaka da Allah
akan kayi haƙuri ka barta".

Ido rufe kuma cikin wata murya wacce ta fi ta farko ƙarfi da firgitarwa tace "wannan ne kuma
bazamu iya yi muku alqawarin aikatawa ba,zamu tafi yanzu,bazamu kuma bayyana ba,kuma
zamu É—auki mataki dede gwargwadon abinda aka aikata wa goÉ—iyar mu,sannan zamu aikata
wani al'amari atareda goÉ—iya wanda muka tabbatar shine kariya agareta kuma zaman lafiyar
kowa aciki harda ku,duk abinda zata aikata kar wanda ya ƙalubalanceta akai,tabbas komi
yanada lokacinsa, kuma idan lokacin da muka dibarwa hukuncin da zamu yanke ya kai to
tabbas komi ze bayyana.

Mlm Abubakar bin Hamza tabbas kaiÉ—in mutumin kirki ne,ka kasance me aikata alheri akoda
yaushe,kuma me saka sharri da alheri,saboda haka karka ce zaka É—auki wani mataki akan
hukuncin mu,zamu tafiiii amma kusani muna tare da goÉ—iya akoda yaushe,domin nauyin kare ta
yana rataye a wuyan ahalinmu,wannan alƙawarine.
NATAFIIIIIIII...., KUMA ZAN DAWOOO...."




Wata babbar hamma kande tayi kafin ta tafi yaraf ta kwanta kamar ta mutu, wani nannauyan
bacci ne ya yi awon gaba da ita.


A lokacin sallar isha'i ake kira,jikin malam habu amatuqar sanyaye yatashi tasake tofe kande ta
addu'o'i,wacce banda gumi ba abinda take,dukama wanda yake É—akin ya haÉ—a uwar zufa.


Se a sannan inna da Amo wanda idonsu yajiƙe sharkaf da hawaye ya kumbura suka saki
junansu,kaka Amo kamar abin tsafi duk abinda ya wakana taji raÉ—au kamar ba bebiya ba.

Zuciyoyin duka wanda suke cikin É—akin É—auke da tambayoyi masu yawa amma kowa ya bari har
lokacin daya dace kafin ya furta.

Haka mazan suka fito daga É—akin jiki a sanyaye,akan idon mlm habu yaga gittawar mutum da
gudu ya yi hanyar waje.

Girgiza Kai kawai mlm habu ya yi dan sarai ya gane ko wanene,kawai shiri ya yi,kuma yasawa
ransa koma menene da yaddar Allah baza ayi nasara akansu ba.

Haka kande ta share kwana biyu batasan inda kanta yake ba,kullum se malam yamata tofi
aruwa ashafe mata jiki.


Yau kamar a mafarki inna tana sallar azahar taga wani abu kamar inuwar mutum ya tsaya
adede kan kande.




🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.

Free page:04


Bismillahirrah manirrahim.

Kafin inna ta karasa setaga kamar wannan inuwar ta faÉ—a ajikin kanden.

Saurin miƙewa tayi bakinta ɗauke da addu'o'i ta nufo inda kanden take akwance,tana zuwa
dede lokacin kande ta buÉ—e idonta wanda sukayi jajir jini ya kwanta acikinsu kamar an zuba
mata,baka ganin farin cikin idon ko kaÉ—an,tana gani tar amma idon yayi mata nauyi.


"Alhamdulillah" shine abinda inna ta furta tana kama hannun kanden datake miƙa mata.


Jikinta yayi mata nauyi sosai bata iya motsa ko ɗan yatsan ta,kuka inna keyi ƙasa ƙasa,ta janyo
wayarta keypad tana dannanwa mlm habu kira, alokacin shi kuma ya shigo cikin gidan
hannunsa É—auke da wata gora ta ruwan addu'a, Kasancewar an idar da sallar ya sallami
É—alibansa masu É—aukar karatu,tare suka shigo da twins wanda suka dawo sbd ciwon kanden.

Dasauri mlm habu yakarasa shiga É—akin yana tofa mata addu'o'i,ahankali yace "mamana",
bakinta yamata nauyi sosai amma ta É—aga idon ta wanda yake nan gwanin tsoro sbd yadda ya
koma ta kallesa,hakan yabashi tabbacin ta dawo cikin hankalinta,


Sake tausasa murya ya yi bayan ya janyota daga kwance ya mayar jikinsa ta jingine dashi ya
sake cewa "kingane wacece wnn?" Yafada yana nuna inna dake durƙushe kusada gadon tana
hawaye,ganin yadda fuskar Æ´ar ta ta ya kumbura sosai bakinta abushe idonta babu daÉ—in kallo.

Jinjina kai tayi a hankali alamar ta ganeta, "waÉ—annan fa?" Ya nuna su twins wanda suma
hawayen suke,dan akwai shaƙuwa me tsanani tsakaninta dasu kamar ba saƙonnin ta ba,duk
ma yayyen ta maza suna matuƙar ƙaunarta,sake jinjina kai taji a hankali,amma ba magana.


Hamdala mlm da inna sukayi,gorar ruwan addu'a mlm ya É—akko ya yi bismillah ya kafa mata
gorar abaki,ba musu ta amsa ta fara sha da sauri, sefa tayi rabi kafin ya cire mata ta
huta,sannan ya sake miko mata ta amsa seda ta shanye tas,kaÉ—an ta bari ya zubaa hannu ya
shafa mata afuska sannan ya ajiye gorar.

Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fara yinƙurin amai,da sauri inna ta miƙo mata
wani ƙaramin baho aikuwa tafara sheqa wani irin amai baƙiƙirin dashi,harda wasu abubuwa

kamar kwalba, aman babu kyan gani,ga wasu abubuwa kamar tsutsa se motsi suke,seda
takusa yin rabin bahon kafin aman ya tsaya mata,takoma jikin mlm tana sauke wani wahalallen
numfashi,ba jimawa wani baccin ya sake kwasheta.

ShimfiÉ—eta mlm yayi yasake tofeta da addu'a kafin suka sake fita.


Seda takai la'asar tana bacci kafin ta farka,cikin ikon Allah koda ta farka idonta ya fara washewa
kuma harta iya tashi da kanta ta zauna, Amo na gefe se zare ido take,dazarar taga kande zata
kallo ta setayi maza ta ƙara damƙe carbin ta,murya asama take istigfari,dan wlh tsoron bala'i
kanden ke bata,ganin take har yanzu al janun na nan basu tafi ba.

Inna ce tashigo ta kamata suka shiga toilet takai mata ruwan zafi wanda mlm ya yi mata tofi
aciki,inna tayi mata wanka dan har lokacin jikinta babu ƙarfi.


Tea me kauri inna ta haÉ—a mata da ruwan addu'a wanda mlm ya yi mata shi dayawa komi nata
inde naci ne ko nasha to da wnn ruwan za'ayi mata amfani,har wanka.


Duk wannan abin da ake yi umma bata leƙo sashen ba ko sau ɗaya,mama de ta shigo sau ɗaya
ta tsaya daga bakin ƙofa tace Allah y kafa afuwa tayi gaba,ko takalma bata cireba balle tashi
É—akin.


Duk da inna taji zafin abinda suka mata amma taji daÉ—in yadda mama tazo ta duba jikin
ƴarta,koba komi de tazo,tafi umma wacce ko bakin ƙofar sashen bata leƙo ba.


Seda kande ta shafe sati É—aya kafin ta fara magana, maganar ma me ban mamaki dan kamar
wata namiji haka take magana tana wani karkace baki gefe,da farko abin dariya ya baiwa inna
hartana cewa "haba uwar masu gida,daga buÉ—e baki kuma se shegan taka,meye haka kamar
namiji?" TafaÉ—a tana murmushi.

Cikin cijewa kande tace "yo inna da mecece ni É—in,ai ni namijice kawai totally,kallifa duka
yayyena maza ne" tafaÉ—a tana nuna su Hamza da su Hamis da twins dasuka kalli juna., saboda
haka nima namiji ne kuma soja zan zama in Sha Allah.

Ya Musa yace "haba auta ke mace ce,kuma kyakkawar yarinya,Æ´ar autar inna da malam,jikar
Amo kallifa ji sumarki me kyau da ita ga tsayi".

Kallonsa tayi tace "Allah ko ya Musa,wannan gashin shiya sake saka wa nake kama da mata
ko? To yau base gobe ba zan askesa,Sena je an aske mini shi".


Kamar wasa tafara acting kamar namiji,duk kayan da inna ta É—akko mata ta sanya setace sam
bata sonshi, ita sede anemo mata riga da wando su zata saka.


Tun Inna na kallon abun a matsayin wasa har tafara jin haushi,cikin fusata tace "zanci ubanki
fa,ki tashi ki saka kayanki,tun ɗazu kin sauna da ɗaurin zani,karki bari raina ya ɓaci", se mafifa
inna take.


Nan take idon kande ya cenza tayi tsaye ƙiƙam taki motsi ta sunkuyar da kanta gashinta ya
zubo ya rufe mata fuska,inna tayi magana har ta gaji amma shiru babu amsa,ganin hakan yasa
ta sakko ta fara lallashi da ban baki,amma shiru kamar tanayi da dutse.


Matsowa inna tayi ta dafa kande tana yimata waƙa kamar yadda take mata idan tayi fushi,
amma ko alamar zata motsa babu,janyota inna tayi da niyyar rungumeta amma taƙi janyu
wa,sema ji tayi kamar ba mutum take jaba, kamar gini haka ta maƙale agurin, cikin tsoro inna ta
saketa taja da baya,aguje ta ruga zuwa zauren gidan tana ƙwalawa mlm kira, jikinta banda rawa
ba abinda yake.


Arikice ta fada zauren inda mlm ke tsakiyar karatu da É—alibansa,da sauri ya tashi yana
tarota,cikin sauri kuma ya janye ta sukayi cikin gidan yana tambayar ta meya sameta harya
firgita ta haka,inna banda rawa ba abinda jikinta yake se nuna masa hanyar É—akinta take,ta
kasa magana hawaye se zuriya yake akan fuskarta.

Hanyar É—akin ya nufa da ita,amma ta cije a waje taki shiga,baiwar Allah Inna banda rawa ba
abinda jikinta yake.


Sakinta mlm ya yi yashiga É—akin yaga kande a halin da take,bakinsa É—auke da addu'a yake
nufarta,haka mlm ya shafe tsawon lokaci aÉ—akin kafin ya fito yana sharce gumi.


Yana fitowa Sega kande abayansa tana faÉ—in "inna yunwa nake ji wallahi,dan Allah kiyi mana
É—an wake", jikin inna be dena rawa ba ta kalli malam,jinjina mata kai ya yi alamar bamatsala.

Cikin ɗari2 inna tace "to auta in Sha Allah,zoki amso mana fulawar", inna ta fada tana miƙo
mata naira dubun da mlm ya bayar,cikin murna ta yi hanyar waje daga ita se ɗaurin zani a ƙirji
ko É—an kwali babu akanta,ga dogon two color hair dinta dakenan har kusada mazaunanta
yanata tashi iska na kaÉ—a mata shi,kamar ba Æ´ar hausawa ba,da sauri mlm yace "a'a uwata
kawo na bayar a amso muku", haka tundaga wannan ranar kande ta koma me siffar maza.


Bawai jikinta bane ya koma siffar mazan, a'a,tana nan a yadda take,kawai de gabaki É—aya
yadda take gudanar da al'amaran rayuwarta ne ya koma na maza,inna batasan ya akayi ba se
ganin kan kande tayi an aske mata rabin sumarta, normally sumarta ta kai har É—uwawu amma
kawai se wayar gari akayi an yanke Mata fiye da rabi yakoma kamar na namijin ba indiye.

Shigarta da komi nata sak namiji, school ma ta dena zuwa,ɗan karatun ta da ake taƙama dashi
aka nemeshi aka rasa,bayan fatiha babu abinda kande ke karanta wa daidai,a fannin boko
kuwa É—um,kai ya koma kamar na kifi bata gane komi,tunrancin da yazamewa bakinta kamar
yaren ta na usuli shima aka nemesa aka rasa,komi nata kamar an juya mata shi,tamkar yadda
ake juya riga daga Dede takoma baibai.

Ada ta kasance me yawan son turanci,har bayan samun matsalar ma bata dena son yin turanci
ba,amma fa kafurin broken english take kwaɓawa,baƙaramin ciwa turanci zarafi take ba,idan ta
kwaɓa wani turancin se dariya ta kusa kashe mutum,amma ita ko ajikinta,ta fuske,ita adole
turancin gaske take.
Ga baki daya rayuwarta tayi juyin waina acikin tanda,yayyenta maza abun ya yi musu ciwo
sosai,gashi sun kasa samun wata gamsashshiyar amsa daga iyayen nasu,sude sun san tun
sa'adda tasamu matsalar jinnu din nan bata kuma samun kanta ba,kullum da abinda zata fitar
sabo arayuwarta.

Tun ranarda sukayi ƙungiya sukayiwa inna ƴar tsure tare da jefa mata wata nannauyar tmby
wanda yakusa zautar da jin ta,har girgizar da tayi sanadiyar tambayar su ya bayyana afili,nan
take ta fatattakesu sbd rashin gamsashshiyar amsar da zata baiwa Æ´aÆ´an nata.


Hakan yasa suka juya tmbyr izuwa kan mlm,tabbas shima ba ƙaramin jijjigashi tambayar tayi
ba,amma dayake namijin gaske ne shi be nuna ya firgita da tmbyr ba.

Cikin dakiya mlm yace "Hamza me kace?,me kuke son sani gameda lalurar Æ´ar uwarku
ne?bayan komi akan idon ku ya faru,kuma duk abinda aljanin yafada kunji da kunnenku".


Maimaita tambayar Hamis ya yi cikin kwantar da murya yace "am mlm dama cewa

mukayi,menene gaskiya akan abinda muka ji aljanin kan auta ya faÉ—i?shin wanene Abu
Rayyan,menene dalilin da ya sanya gabaki É—aya rayuwar auta ya cenza,kuma munga baka
É—auki kowanne mataki ba,kamar ma abinda take yi yanzu baya damunka,gashi mutanen
unguwa harsun fara gutsira zantuttuka akan sabon tsarin rayuwar da ta É—akko a yanzu,sam
sekace ba Æ´arka ba,komi nata ya sauya,mlm dubi yadda takoma sak namiji,kuma ma dakanka
ne kabata kuÉ—i tasai irin tufafin da maza suke sakawa,wanda kaine ka koyar damu cewa duk
namijin da yake kamanceceniya da mata to yanada babban zunubi agurin Allah (s.w.a),haka ma
ga macen ta take kamanceceniya da maza,harfa yanke gashin kanta tayi,wanda yin hakan a
addini shima haram ne,gashi yanzu bata tsoron kowa,shekaran jiya nan naga ta kama Ikilima
tamata shegen duka seda ta yimata targaÉ—e a hannu,mlm dan Allah kafaÉ—a mana menene
asalin abinda yake faruwa wanda mu bamu sanshi ba,kuma wanene ABU RAYYAN* a iya sanin
mu kune iyayenmu,kuma aduk cikin kakanni mu bamusan wani me suna abu Rayyan ba,mlm
kai masani ne wanda Allah yabashi baiwar ilimummuka me tarin yawa,kuma abinda take yi Sam
ko a addini be dace ba,idan ma sbd aljanun kanta ne ai Allah ya baka sani ta yadda zaka
magance komi batareda an bar wani aljani ya sauya mata rayuwarta hakaba,ka gafarcemi mlm
idan na faÉ—i abinda ya sosa maka rai,bada nufi bane ".


Dogon numfashi mlm yaja kafin yace "duk naji abubuwan da ka faÉ—a kuma tabbas maganganun
ka gaskiya ne,amma abunda nakeson ka sani,duk wata cuta Allah be halicce ta ba har seda ya
fara saukar da maganinta, sannan idan ka lura gaba ɗaya rayuwar auta maƙiya ne a kewaye da
ita wanda nasani kuma kun sani,tun kafin bayyanar wannan aljanin atare da ita ansha neman
nakasta rayuwarta wanda ku ƙila a yau kuka san wannan,akwai aljanun da zaman su atareda
mu bil adama babu alheri wanda hakan kesa muke yin duk yadda zamuyi araba wanda suka
shafa dasu,akwai kuma nau'in aljanun da zaman su atareda mu wata kariya ce daga Ubangiji*

Tabbas rayuwar auta ta sauya kuma babu wani wanda hakan kewa daÉ—i daga Ni har
mahaifiyarku,kuma duk yadda zakuji ciwon sauyawarta baku kai mu ba tunda mune muka
kawota duniya,kuyi hakuri kubata lokaci,idan kun lura harda kuruciya a lamarin uwata,in Sha
Allah komi ze dedeta da izinin Allah*
Ni nasan abunda baku saniba,wanda in Sha Allah idan lokacin kusani ya yi tabbas ba makawa
se kun sanshi,rayuwar auta akwai wasu manyan sirrika wanda lokaci ze bayyana su,kuyi hakuri
ku bata lokaci,kuma ina roƙon ku kar wanda ya hanata abinda take ko ta nema,inde befi ƙarfin
ku ba ina neman alfarma abata,sannan Abu Rayyan bakowa bane kawai zancen aljanin
ne,nagama magana kutashi kuje Allah ya yi muku albarka".

Sam mlm be basu damar yin wata magana ba,kuma tabbas sunajin cewa akwai abinda mlm be
faÉ—a musu ba,amma kamar yadda yace komi lokacine suna fatar lokacin nan ba anesa yake
ba,dan duk wanda yasan auta ada yarinya me hankali ga ƙoƙari ga son karatu,to ba ze yadda
itace ta koma yadda take a yanzu ba,yarinya ƙarama me shekaru goma zuwa sha ɗaya,sam
kamanninta ya sauya,babu wata cikakkiyar nutsuwa atare da ita,ga rashin kunya,duk wani ilimi
da take dashi yanzu babu ya gudu,takoma kamar jaka, bata da mutunci sam,ga ƙarfi kamar ba

mutum ba,ba wanda ya isa ya É—aga mata yatsa ko ya É—agawa innarta,duk mutanen gidan yanzu
shakkar ta ake, ƙaramar yarinya amma ta addabi kowa,musamman umma da ƴarta Ikilima
wanda suke nuna sam basuda alaƙa da ita,mama de dama ba shiga shirgin kande take ba,tun
bayan da É—anta Abdullahi yakoma sashen ta shikenan burinta ya cika,dama ba dan Allah ya
barshi a gurin inna ba, barazanar da mlm Musa mijinta yamata ne yasanya ta kyaleshi
acen,amma yanzu tunda ya dawo gurinta ba abinda ya shalleta dasu.


Abdullahi ya gudu shashen uwarsa mama ne tun ranar da kande ta tayarda aljanu, yaji tsoro
sosai ya kwashi kayansa yakoma sashen uwarsa wanda har yau wata na biyu da faruwar abin
be dawo ba,tun Inna na magana da mlm har suka hakura,mlm Musa ma be ce ya koma ba
hakan ya yi wa Mama daÉ—i kuwa, É—an ta ya dawo gare ta.


Tun daga lokacin kuma Abdullahi ya fita harkar kande ya dena kulata,itama bata damu ba ta fita
iskar sa.


Dama acikin unguwar mace ɗaya ce ƙawarta layuza maƙota ne dasu inna,layuza tanada haƙuri
sosai bata cika yin fushi ba,duk masifa da bala'in kande tana shanye wa, Allah ya É—ora mata
ƙaunar kande,hakan yasa suke ƙawance,.



Tunda É—abi'un kande suka sauya iyayen layuza suka hanata hulÉ—a da kande anna ta kafe ta
ƙiji,kusan kullum tana hanyar zuwa gidansu kande,.


Layuza tana tallar dafaffen dankali, kasancewar basu kai su kande hali ba,hakan ke burge
kande sosai,ita tallah mugun birgeta yake,a ƙa'idar gidansu mlm habu yaro baya tallah,saboda
sunada rufin asirin su,amma rana tsaka kande ta tayarda bala'i ita tallah zata fara,tun mlm da
inna suna ganin abu wasa har ta fara kuka tana tirje tirje ita se an yimata sana'a ta fita tallah.

Haka mlm badan yaso ba ya goya mata baya,seda ta zaɓi abinda zata dinga tallar ma,awara ita
kadai take so,haka mlm yabata kuÉ—i taje tasiyo rabin mudu,inna tayi mata awara,ranar da ta
fara É—auka taci wankanta jikinta sanye da wasu riga da wando Æ´an dai dai na maza tasha cover
shoe dinta babban size wanda yafi ƙarfin ƙafarta,ta ɗauki bokitin ta fito tana ƙwambo tana buɗa
kafaɗa dede umma na baiwa Ikilima sako a ƙofar shashensu da alama aikene ake bata,wata irin
dariya suka kece da ita kamar zararru,yi suke sosai suna nuna kande wacce ta tsaya sororo
tana kallonsu fuskarta a murtuƙe,dake sashen umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login