Showing 3001 words to 6000 words out of 26224 words
Chapter 2 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf
boko zuwa matakin secondary,daganan Abubakar yakoma cikin kasuwar Æ´an kaba
yana sana'ar hatsi da kayan lambu da kayan koli,Allah yasanya masa albarka aciki,Abubakar
wanda akasuwa ake kiransa da mlm habu me kayan koli yanada tarin ilimin addini,É—an izalane
na gaske,hakan yasa da dare yake koyarda magidanta harma da samari agida,da karancin
shekarunsa aka basa limami.
Shida Æ´an uwansa suka sake gyare gidansu suka mayar dashi sashe huÉ—u inda kowansu yayi
aure,aka barwa Amo da mlm Hamza shashe É—aya,mlm habu duk yafi Æ´an uwansa hali,hakan
yasa yake temaka musu sosai,duk rabin É—awainiyar gidan shine,sbd mahaifinsu yanzu baya
aikin komi, zaune yake agida sbd jikin girma,sun bude masa shagon hatsi anan cikin
unguwa,baya zuwa ko ina kullum yana shago kusada gida.
Matar mlm habu me suna A'isha mace ce me kirki da faram2,amma masifaffiyace sosai ta
gaske inde aka shiga harkarta to ba mutunci,tanada kyauta sam bata da munafunci da shiga
abinda be shafeta ba, itace ta fara haihuwa acikin gidan ta haifi namiji aka sanya masa sunan
mlm Hamza,akwai kishin sauri sosai tsakaninta da matan su Hamza da Mudassir,sam basa
sonta sun haɗe mata kai,kullum cikin zuga mazansu suke akan sun zauna basuda ƙwaƙƙaran
aiki se noma,gashinan habu ya amshe girma da ragamar komi,sugasu su biyu shikuma shikaÉ—ai
amma yafisu arziki,akan haka Musa yataɓa sakin matarsa Zabba'u, wacce takasance sumumu
kasau, batada hayaniya sam amma muguwa ce,ko alama bazata nuna fushi ko ɓacin rai
afuskarta ba amma seta bada mamaki ta hanyar abinda zata aikata,batada mutunci,amma sam
ba a ganewa,tunda aka mata saki É—aya sbd iyalan mlm habu dashi kansa daga nan seta cenza
takunta, ganin faÉ—an zahiri ba riba seta koma yi ta bayan fage.
Seta zuga matar Mudassir Hadiza,dake ita Allah yamata bakin tsiya,batada kunya ko
kaÉ—an,idan faÉ—a yahado ku duk abinda ya fito abakinta faÉ—a take yi kanta tsaye,sam bata ganin
girman A'isha,ta tsani A'isha ga jan faɗan tsiya duk yadda ka kaiga hkr seta ƙureka ka tanka ta.
Hakan yabaiwa Zabba'u damar aiwatar da yaƙinta ta hanyar Hadiza.
Abangaren Mudassir tun baya É—aukar zigar matarsa Hadiza hartaci galaba akansa ya fara
adawa da ɗan uwansa,sam baya ganin ƙoƙarin mlm habu akansu.
Gashi su har lokacin Allah be basu Æ´aÆ´a ba,seda A'isha ta haifi maza shida ajere, sannan
haihuwa ta tsaya mata,Hamza,Hamis, Ibrahim, Musa, Mudassir,dan sefa yayiwa Æ´an uwansa
takwara sannan Aminu,bayan Hadiza matar Mudassir tasaka an riƙe bakin mahaifar A'isha ta
hanyar asiri acewarta dan ita komi nata ba sirri,idan ranta yaɓaci seta furta mugun alkaba'i tare
da cewa mutum seya gani,hakance ta kasance tacewa A'isha seta gani akan sunyi faÉ—a ranar
sunan Aminu.
Alokacin ne kuma matar Musa ta haifi mace aka samata sunan Hafsatu,wata shida tsakani
Hadiza ta haifi mace itama,Musa yayi2 da Mudassir yasaka sunan Amina amma Æ´aki,sbd
Hadiza tace muddin ya yarda aka sakawa Æ´arta sunan amo to sede ya saketa kuma ba inda
zata da Æ´ar sede ya kaiwa Amo bebiya da akayiwa takwara ta shayar da ita,shikuwa ba wacce
yake ƙauna aduniya bayan Hadiza da ƴarsa,haka aka sanya wa yarinyar suna Hulera sunan
uwar Hadiza kenan.
Alokacin ne mlm habu yarasu yayi ciwon kwana biyu yarasu.
Kwatsam Sega A'isha da ciki,hakan ya firgita Hadiza matuƙa dan tayi tunanin A'isha tagama
haihuwa,a tunaninta A'isha bazata kuma haihuwa ba har ta mutu,hakan yasa ta sakankance
kawai sede suka farga da tsohon ciki ajikin A'isha,haka tasake haihuwar Æ´an biyu maza,
alokacin ne akayi tashin hankali dan kiri kiri su Hadiza suka nuna baƙin cikinsu afili wai da
gangan take haihuwar maza sbd ta cinye dukiyar gidan, alokacin ne suka raba gari tadena
mu'amala dasu kwata2 bayan ta sauke musu kwandon hauka da shika-shikan rashin
mutunci,dan Æ´an uwanta masifaffu ne suma haka akayi baram baram,sam malam habu bayajin
daÉ—in wnn rashin jituwar ta matansu,daga lokacin A'isha bata shiga harkar kowa acikin su,sbd
akan fuskarta suka fada mata basa ƙaunarta itada mijinta da ƴaƴanta kuma in Allah ya yarda
seta gani,hakan yasa ta tayarda bala'i sede mlm habu ya cenza mata gida sbd abinda
facalolinta sukace, shikuma yace bame rabashi da Æ´an uwansa, duk abinda yasamesa ko
Æ´aransa daga Allah ne bawanda ya isa ya cutar dasu se abinda Allah ya tsara masa.
Dama shine yake taka mata birki take rage wani abun,amma dan ta ita kullum se anyi bala'i
agidan,ƙiri ƙiri se a dokar mata yara amma mlm habu yahata magana,ranar da ƴan biyu suka
rarrafa sukaje sashin mama suka zubar mata da gasara kashesu ne kawai Hadiza batayiba,
dake tana sashen itama, A'isha na sallah sede ta dinga jin ihunsu ga ƙarar duka alamar
dukansu ake,tana zuwa mama dake bakin ƙofar shashen tashige toilet da sauri, Hadiza ko
bataga zuwan A'isha ba tayi nisa se zabga musu tsintsiyar kwakwa take a hannu,aikuwa kamar
walƙiya A'isha tayi wani irin tafiyar yaji da Hadiza, duk kibarta seda A'isha ta kaita kasa tanata
jibga, daƙyar aka raba wnn faɗan lokacin Hadiza tayi laushi se kuka take an fasa mata baki da
hanci, se bayan anrabasu sannan mama tafito daga toilet tana sallallami, ko kallonta A'isha
batayiba ta kwashi yaranta wanda suke ta ajiyar zuciya.
Aikuwa aranar Hadiza bata kwana agidan ba dan wani ƙaton macijine yashige ɗakinta kan gado
ya fasa kai se huci yake.
Daga kan twins inna bata kuma haihuwa ba, kullum addu'ar ta Allah ya bata mace,tanason Æ´a
mace arayuwarta, gashi ba halin ta É—auki yaran facalolinta yanzu se suce tanason ta kashe
musu Æ´aÆ´a.
Ahaka Zabba'u takara haihuwar mace aka sanya mata siddiqa se Maryam, Hadiza kuwa bayan
Hulera ta kara haihuwar Asiya, se Ikilima.
Mama kuwa daga baya Allah yabata namiji,kusan tare suka kara haihuwa da A'isha wacce
batasan tanada cikiba har seda yayi girma ajikinta,bata faÉ—awa kowa ba segashi sun haihu tare
da Zabba'u wacce yaran gidan suke kira da Mama,aranar Hadiza har suma takusa yi saboda
baƙin ciki.
Zabba'u bata wani damuba ganin ta haifi namiji itama,amma sam aƙasan zuciyarta bataso
A'isha wacce yara ke kira da inna tasake haihuwa ba,amma bakomi zasu gani,Hadiza de ita
nata baƙin cikin afili yake amma bawanda yasan me mama take ciki tunda ita mijin nata yaƙi
É—aukar zuga.
Kasancewar inna a asibiti ta haihu wnn karon daga ita se mijinta, dan Æ´an uwanta ma seda aka
sallamota sukaji haihuwar, ba wanda yasani har uwar mijinta Amo hakan yasa seda suka dawo
snn Æ´an gidan sukasan ma haihuwa tayi kuma mace,Æ´an uwan A'isha Æ´an bala'i ne basuda
mutunci haka suka dinga kiÉ—e kiÉ—e suna shewa da guÉ—a an haifi kANDE,ranar suna yarinya taci
suna Amina,anyiwa Amo takwara ba zaman lfy lols,seya kasance kamar ba suna biyu akeyi
ba,ƴan uwan Aisha sun cika gida an kashe kuɗi anyi ɓarna sosai da kuɗi da abinci da nama,
sam bazakace wai ana wani suna a sashen Zabba'u ba,dan da gayya Æ´an uwan Aisha suke
wani abun dan niyyar su ana tankasu se sun ci uwar mutum.
Wannan yaƙara girmama baƙin cikin Hadiza kuma taci alwashi sosai akan seta lalata rayuwar
ahalin A'isha,inda mama Zabba'u ko ajikinta tunda de ta haifi namiji to ai angama komi,yaro yaci
suna Abdullahi.
Tare kande da Abdullahi suka taso se suka tashi kamar twins, sam basaji ko kadan tare suke
zuwa makaranta Arabic da boko kullum se ankawo kararsu ko sun daki yaran mutane ko sunyi
wani abun,gasu da ƙoƙari amma sam basaji,kullum mlm habu na hanyar makarantar
su,shekararsu biyar amma sam basaji,a lokacin umma takara haihuwa ta haifi Ikilima,daga
lokacin se haihuwa ta tsaya musu duka matan gidan.
Kande irin yaran nan ne da ake kira gifted, duk abinda aka karanta mata sau É—aya yashige
kanta kenan ba maimaici,nan take take É—auke abu a kanta,tanada zuciya sosai batason
reni,gata yarinya amma ƙoƙarin ta har tsoro yake baiwa inna da mlm, shekararta biyar amma
tana iya karanta duk ayar da aka janyo acikin Kur'ani,sbd idan mlm habu na koyarwa a zaure
itada Abdullahi suna gurinsa,hakan yasa duk yadda wasa ze dauke mata hankali baya hanata
É—auke abinda taji an karanta koda ba ita ake gayawa ba.
Kande ta tashi cikin tsananin soyayyar uwa da uba,ga yayye maza kowa kande, sunan da
kakarta tasaka mata kenan Amo,itace take kiranta da kande ko kuma tace takwara,A'isha (inna)
kuma tace uwar masu gida,wnn suna yana ƙonawa umma da mama rai,gabaki ɗaya sun tsani
yarinyar ganin duka ƴan gidan kowa yana son kande, hatta ƴaƴansu ba wanda ya dakko baƙin
halin uwarsa.
A cikin yaran Zabba'u siddiqa ita tafi kowa sanyi,yarinyar batada hayaniya sam,ga ilimin addini,
baruwanta.
Yaran umma kuwa kusan dukkan su basu da hayaniya bakamar itaba,Ikilima ce kawai tayo
halin uwarta.
Matan kusan duk sunyi aure, Hafsatu, Maryam,yaran Zabba'u duka sunyi aure, siddika ce kawai
ta rage se Abdullahi autan mama.
Yaran umma ma Hulera da Asiya duk sunyi aure suma.
Kaf unguwar ansan gidansu kande gidane na Æ´an izala masu ruko da addini,dan su Hamza
daga malamin islamiyya se alaramma,se wanda ke kasuwa gurin kasuwanci,suka sunada aikin
yinsu,bame zaman banza, twins kuwa suna jami'a.
Ko daga waje duk wanda ze shigo gidan to ina kande shine abinda ze furta,duk ta dusashe
tauraron sauran yaran gidan,tun mama na damuwa harta gaji ta saki,umma ce kullum cikin
wahala, batada aiki se jifan kande da inna da mugayen alkaba'i,inde akan inna ne bata furta
alheri.
Haka baba Musa komi ya samu kande,ko yace wnn na uwar masu gidane, Abdullahi ko kamar
bashi ta haifeshiba ganin tasa tazo É—aya da kande hakan yasa yaron ya tattare kayansa ya
koma É—akin inna.
Ankai ruwa rana sosai da mama, dan ta kafe akan É—anta baze zauna agurin innaba, duk Æ´aÆ´a
maza da Allah yabata amma se É—an gudalenta za a É—auka awani baiwa inna,hakan yajanyo
baba Musa yace idan takara tayarda zancen abakin aurenta,dan shi yana ƙaunar ɗan uwansa
mlm habu,kuma sam baya É—aukar wargi, hakan yasa baya iya hanasa É—an uwansa duk abinda
ya nema,duk da cewa bashi ya nuna yanason ya rike Abdullahi ba amma ganin yaron nason
zama agurin inna yasa yake jin nauyin amsarsa,dan gani yake kamar idan Abdullahi yabar gurin
inna mlm habu zeji ba daÉ—i.
Mama tanaji gana gani aka rabaga da É—anta,bata wani damu sosai ba dan tasan inna ba
maƙetaciyar mutum bace,dan kular da ze samu agunta ko ita wacce ta haifeshi se haka.
Kwatsam wata rana aka baiwa kande scholarship daga makarantarsu zuwa babbar makarantar
nan ta m.m. Haruna English academy, alokacin shekararta goma,tagama primary zataje
secondary,dan jumping aka dinga yimata, ga haddar izu talatin akanta na Kur'ani.
Haka akayi ta murna agidan ana tayata farin ciki,inna kuwa har sadaka seda tayi.
Yayyenta maza kuwa kowa seda yabata kyauta.
Ranar ta ta farko a school.......
í ¼í¼¹kANDEí ¼í¼¹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:03
Bismillahirrah manirrahim.
Tun ranarta ta farko a makarantar tayi kawaye yaran masu kuÉ—i,tasaje da yaran masu kuÉ—i
itama saboda irin kalarsu gareta,farace sosai,tanada tsayi ba lefi,gata da hanci da manyan
ido,idan tana magana bakinta kamar bashi ke motsi ba,siraran lips ne da ita,fuskarta oval
shape,sumar hanta tana da tsayi sosai,ga saje daya biyo ta gaban kunnen ta,tanda 1 side
dimple, kyakkawar gaske ce,yarinyace amma jikinta a murje yake sosai,fatarta tanada matuqar
kyau,snn gashin ta ba baƙi bane wuluk,akwai ruwan golden brown aciki hade da baƙi suffarta
daban take kamar ba É—iyar hausawa ba.
Ga ƙoƙari kamar alhuda-huda,komi aka fada mata sau daya ya zauna akanta kenan koda ba a
ajinsu bane,hakan yasa satinta uku aka fara shirin yimata promotion zuwa j.s.s. 3,ranarda
takoma gida tana murna tare da takaddar gayyata izuwa ha mlm habu,koda su umma sukaji
labari nanfa bala'i ya tashi akan sede asaka Ikilima da saddiqa da Abdullahi a m.m. Haruna,duk
da cewa siddika tana shekarar ƙarashe ne amma haka umma ta dinga bala'i,mama de uffan
bata cewa,tagaji da yiwa inna hassada tunda kullum Sa'a a gefen inna da iyalanta yake.
Kwatsam rana tsaka aka dawo da kande dg school tafaÉ—i,sunkaita clinic na makaranta an
dubata har drip ansaka mata amma sam taƙi ta farfaɗo,hankali tashe inna ta shinfiɗe ta,anata
shafa mata ruwa taki farfaÉ—o wa, Amo kuwa banda ihun kuka ba abinda take,murya a sama
irinta bebaye take faÉ—in,duk wanda yake son ganin bayan jikarta karya bari ta ganosa dan seta
yi masa rashin mutunci,haka taketa zabga bala'i tana ihu irin ta kurame.
Haka mlm habu yadawo ya samu autarsa unconscious,addu'a kawai yake tofa mata,haka ya
karanta wasu manyan surori aruwa yace inna ta shafe mata jiki,yin hakan ko keda wuya ta
farka,kamar robot haka ta miƙe tsaye batareda jikinta ya lanƙwashe ba,a tsorace inna ta matsa
tana zare ido cike da faÉ—uwar gaba,duk yayyenta dake É—akin ba wanda be tsorata ba ganin
yanayin da ta farka aciki.
Fuskarta tayi kore sosai,jikinta ma haka,idonta yakoma ɓaki duka ko ƙwayar fari babu,cikin
buÉ—aÉ—É—iyar murya kamar ta maza tace "lahuhu irmati gidigam gam,abukanwatur fadurma gim
gam" kamar wata bokanya haka take furta wasu irin dalamisai,jikinta banda jijjiga ba abinda
yake,bakinta har wani hayaƙi yake fitarwa, nan take dakin ya fara jijjiga kamar ze ruguje,cikin
ɗaga murya mlm habu ya fara karatun suratul baƙara,yi yake da karfi, nan take su Hamza suka
É—auka,da karfi suke karatun, Amo na gefe se tsandara ihu take kamar ana yankata, ta tsula
fitsari yakai sau biyar,sun rungume itada inna se kuka suke, Amo se ihu take tana gwalanci wai
nan addu'a take.
Ihu kande tafara yi tana jijjiga kamar ba mutum ba,cen tayi wata irin gigitacciyar ƙara wacce duk
maƙotansu seda sukaji,gashi marece ne anata kiraye-kirayen sallar magrib, ihu take tana susar
jikinta kafin takara yanka wani ihu me karfin da yafi na baya tazube aƙasa ta zauna kamar ƴar
bori, still su mlm habu basu dena karatunba sema wasu manyan ayoyi da suke sake janyo
wa,kamar a mafarki tafara rera karatun tare dasu,idan suka cenza aya itama tacenza har suka
yi shiru,amma ita seda takai ƙarshen aya.
Zuciyar mlm habu akarye cike da firgicin wannan sabon al'amari daya riskesu yau,amma Cikin
dakiya ya buɗa muryarsa babu wasa yace "wanene kai? Me kake yi ajikin ƙanƙanuwar yarinya
irin wnn? Ko ta yimaka wani laifin ne da ka zaɓi shiga cikin jikinta,kuma ga dukka alamu sun
nuna cewa kai É—in musulmi ne".
Cikin wata babbar murya marar hayaniya akace "Assalamu alaika ya Imam Abubakar bin
Hamza,Tabbas ni muslumi ne kamar yadda kaji,kuma sunana Muhammad Arun É—an Sarkin
aljanun baihak,ni musulmi ne,kuma ni É—in na kasance ajikinta tun tana cikin cikin
mahaifiyarta,sannan ni ne wanda nake bata kariya bisa umarnin kakana muzgar".
Jikin inna da Amo banda rawa ba abinda yake,yayyenta ma dauriya kawai suke,domin abin
babu daɗin gani kwata kwata halittar jikinta ya sauya kamar wani ƙaton gardi, ga wasu jijiyoyi
sun ratsa mata a damtsen hannunta,gashi daga ita se vest da leggins.
Jinjina kai Malam habu ya yi yace "tabbas nagani kuma naji kai É—in musulmi ne,amma shin me
wannan yarinya ta aika maka,ko ta cutar da kai ne dayasa ka bayyana akanta ko kuwa?".
"Babu É—aya daga cikin biyun tambayoyin ka,wato zancen gsky naso nayi zamana shiru
batareda na nuna wata alamar cewa ina tare da itaba,amma hakan baze taɓa yiyuwa ba,anyiwa
goÉ—iya wani mummunar sihiri wanda akaso bayan tagama wulaqanta tayi mummunar mutuwa.
An sadaukar da jini ga baƙaƙen aljanu an tura su jikinta da mummunar niyya,kuwa hakan
yakusa yin tasiri sakamakon bama tare da ita a lokacin ,munyi wata doguwar tafiya zuwa ƙasar
misra domin gabatar da wani yaƙi acen tsibirin asgarul mundal, sannan mun nasaka fararen
rauhanai a domin bata kariya da kuma gadinta kafin mu dawo,amma se akayi rashin Sa'a
baƙaƙen aljanun da aka turawa goɗiya sunfi ƙarfinsu,hakan yasa sukayi nasara akansu har
suka raunatasu,duk da cewa mun bar wani kariya ajikinta hakan yasa sukayi kwanaki bakwai
suna fama kafin su sami nasarar shiga jikinta ta hanyar wacce tayi mata turensu,tabata É—an
wake taci,acikin É—anwaken akwai wani magani wanda ya karya garkuwar da muka bari atareda
ita,a jiya ne muka sami nasara akan baƙaƙen aljanun da suka addabi tsibirin da mukaje
yaƙi,cike da azama muka dawo gareta kwatsam se mukayi arba da shugaban baƙaƙen aljanun
da muka nema muka rasa a fagen yaƙi, yana shirin ɗaukar rayuwar goɗiyarmu,wanda da hakan
ta kasance to tabbas da sede mu mutu atare da ita, domin rayuwar mu gaba É—aya sadaukarwa
ce ga ahalin goÉ—iya.
Kakan goɗiya ya taba temakon kakana alokacin da yayi ɓadda kama amatsayin ɗan Adam
kuma almajiri, lokacin kakana ba musulmi bane,amma karamcin da kakanta yayi masa yataɓa
zuciyarsa,har ya amshi musulunci,a dalilin haka yasa yake bibiyar ahalinsu.
kakanta ya temaki kakanmu, yana saurayi a lokacin batareda ma yasan cewa aljani yatemaka
wa ba,a hannun kakanta Abu Rayyan kakana ya amshi musulunci,hakan yasa kakana ya tara
iyayenmu yabasu labari kuma ya umurce su da amsar musulunci tare da faÉ—a musu lalle su
kasance masu baiwa ahalin Abu Rayyan kariya har ƙarshen rayuwarsu.
Mun kasance tare da mahaifin goÉ—iya kafin faruwar wani babban al'amari, daga baya kuma
muka koma gareta tun acikin cikin mahaifiyarta,.
Tabbas makashinku na tare daku, tabbas anaso a salwantar da rayuwar goÉ—iyarmu hakan yasa
muka riƙe baƙin aljani Gandamul arzu bawai dan bazamu iya galaba akansa ba, a'a sedan
munaso ya bayyana ajikinta akan idon ku,yaso tserewa tun da sa'ar da mukayi arba da juna
aɗazu,amma na riƙesa sakamakon munaso kufara hukunta sa da kanku da ayoyin Allah,ya yi
iya yinsa dan ganin be iso nan ba,sbd yasan karonsa da mlm ba zeyi masa kyau ba amma sam
bamu basa damar yin hakan ba.
Niyyarsa ya aiwatar da abinda aka aikosa yakama gabansa batareda ya iso gidan nan ba
amma