Showing 21001 words to 24000 words out of 26224 words

Chapter 8 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf

daku, kuma shugaban makaranta ya fi ga
musu faɗa harda ce musu manyan kawai,da ƙannen bayansu suke faɗa,A'isha na gefe tana
murmushi, Zabba'u kamar ta tashi ta shaqe A'isha har lahira,bada ita akayi faÉ—an ba amma duk
t fi jin haushin A'isha akan kowa.



Bayan sati ɗaya aka fara zaban ɗaliban da zasuje musabaƙar state,A'isha ce farko acikin list
É—in,bayan an watse daga assembly Zabba'u tasamu shugaban makaranta tace masa itama tana
son shiga,haka ya sanya sunanta aka haÉ—asu da wasu malamai wanda bana makarantar ba
suna musu rehazal da testing É—in karatunsu don jin wanda ya zama colified aje dashi
musabaƙar,A'isha ta haye tare da wasu maza biyu,dama mutum biyar ake buƙata,amma
Zabba'u ko zango na farko bata wuce ba,gashi ta nace seta yi abinda A'isha tayi sbd sanya wa
rai wahala,duk wannan abin da takeyi ustaz habu farin malami me zazzaƙar murya tare da
cikakkiyar ƙwarewa akan iya sarrafa karatun Alkur'ani shine yatafi da imanin Zabba'u.


Duk wannan naci da fafutukar shi take wa,amma kamar ma besan tanayi ba,dan ko kallon
fuskarta bayayi.

Haka Zabba'u tazama discolified a cikin masu zuwa musabaƙar nan, antafi kuma makarantar su
itace taciyo wa Kano ta É—aya,har kyautar maka da kuÉ—aÉ—e masu yawa A'isha ta samo,haka aka
dinga murna aka shirya walima akaci aka sha,A'isha ta baiwa abbanta kyautar kujerar hajjin da
aka bata.


Kawayen Zabba'u babu wacce batasan irin mugun son da take wa ustaz habu ba,har kirari
mata tare da canza mata suna,ZAHAB shine sunan da tamayar wa kanta,ba wanda ya fahimci
abinda ake yi,daga É—alibai har malamai balle shi kansa uban gayya mlm habu,kwatsam aka
kawo cingum da alawa anata raba wa É—alibai wai anyiwa ustaz habu baiko da A'isha head
girl,....


Aranar har wata iskar bala'i Zabba'u ta hau,aguje ta damƙi wuyan A'isha wacce take zaune a aji
se tsiya ake mata wai dama soyayya suke da ustaz habu amma ba wanda yasani,ƙawayenta
sun sata agaba da zolaya ita kuma se sunne kai take tana dariya,ba zato Zabba'u ta shaqi
wuyanta,anyi anyi arabasu amma abu yaci tura,se ihu É—alibai keyi, wasu kuwa aguje sukeje
sukazo da shugaban makaranta,kamar haÉ—in baki sefa ustaz habu shika yazo makaranta
kasancewar ba ana yake koyarwa ba,aikuma wani irin karfi ne yazo wa A'isha tayi wani irin
kukan kura ta ɗaga Zabba'u sama duk da girman jikin ta amma A'isha sefa ta kaita ƙasa,haka
tasamu sa'ar Zabba'u ta dinga naushin baki da hancinta seda ta zubar mata da jini bana wasa
ba,koda shugaban makaranta da ustaz habu suka ƙaraso ai Zabba'u ta dena iskoki ta koma
ihun neman agaji,ihu take iya ƙarfinta tana faɗin arabafa da A'isha mahaukaciya ce,dakyar da
bala'i ustaz habu ya sanya hannu ya fizgo A'isha daga kan Zabba'u wacce tayi laushi,fuskarta ta
haÉ—e da jini,bakinta hanci,idonta duk sun kumbura suntum.


Se fizge2 A'isha keyi tana sake kaiwa Zabba'u cafka amma mln habu ya riƙe hannunta
sosai,har seda ta gaji dan kanta ta tsaya tana mayarda numfashi fuskarta tayi jajur,se huci
take,haka aka ƙara tara wani taron a ofishin shugaban makaranta,anyi anyi da Zabba'u wacce
keta rusa kuka ta faɗi abinda A'isha ta mata harta sameta da faɗa amma taƙi faɗa se kuka take
rafsawa.



Wani mlm ne yaje ajinsu Zabba'u da nasu A'isha ya kira mutum uku2,Æ´an ajinsu A'isha aka fara
tmby meya haÉ—a Zabba'u da A'isha fada,sukace sude suna zaune kawai sukaga Zabba'u aguje
ta damƙi wuyan A'isha ta shaqe ta,sunyi sunyi su raba amma sun kasa shiyasa sukazo suka
kira shugaban makaranta.

Ƴan ajin su Zabba'u aka tmby ko sun san abinda ya faru,nan fa kowa ya fara zare ido,seda
shugaban makaranta ya daka musu tsawa kafin suka fara inda inda, shugaban makaranta yace
wa malamin É—azu ya É—akko bulala ya zane masa su,cikin tsoro sukace zasu faÉ—a.


Babbar ƙawar Zabba'u Hairatu itace tafara bayani,"um dama wai,am um mlm wallahi tsaya
kaji,dama Zabba'u ce take son mlm habu,shine yau kawai se muka ji wai an musu baiko da
A'isha".



Dumm haka gaban kowa ya buga harda Zabba'u wacce ta dunƙule agefe se gumi take,ga kuka
tana kan yi.

🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.

Not edited


Free page:10


Bismillahirrah manirrahim.

Tunda aka faÉ—i abinda ya haÉ—asu kunya ta kama Zabba'u,duk setaji ta muzanta,ace tana faÉ—a

akan namijin da bemasan tanayi ba, mlm habu kuwa tashi kawai ya yi ya bar makarantar ma
gabaki ɗaya,A'isha kuwa wani irin tuƙuƙin baƙin cikin ne ya kamata wato akan masoyinta ma
aka mata wannan renin wayon ko,shi kuma harda wani tashi ya fita kamar munafuki ai zezo
gida anjima ya sameta.

Haka shugaban makaranta de ganin ba wani abin arziki bane ya janyo faÉ—an se son rai irin na
Zabba'u da kuma Sherin zuciya,hakan yasa ya tilasta Zabba'u ta baiwa A'isha hakuri ko kuma
tazo da iyayenta gobe,ai da sauri ta bata haƙuri,don gidansu ba wanda ze goyi bayanta idan
sukaji abinda ya faru,wata kila ma asaka wani malamin ya kuma zaneta.

Sallamar kowa shugaban makaranta ya yi,ya rage daga shi se Zabba'u se malamin da aka tura
kiran ɗakibai ɗazu,nasiha sosai shugaban makaranta yamata,tarefa ƙara lurar da ita
muhimmancin kamewa agurin mace,duk da cewa dan taso wani ba lefi bane amma abinda tayi
na jan faÉ—a lefine,idan kuma ta duba shi wanda take faÉ—an dan shi bemasan tanayi ba.

Godiya ta masa kamar abin kirki,duk taji ta muzanta,tun daga ranar bata kuma zuwa makaranta
ba,har aikawa shugaban makaranta ya yi akace lafiyar ƙalau,kuma tace ace ita ta haƙura da
makarantar gaba É—aya.



Haka akasha bikin A'isha da ustazu habu, watansu biyar da aure,Musa ya yi aure shima,se
bayan ankawo amarya ne A'isha taga ashe Zabba'u ce,itama Zabba'u data ga A'isha amma
seta nuna kamar batasan inda A'isha ta fito ba,dafarko A'isha tayi binta da lalama tana
girmamata matsayinta na matar wan mijinta amma daga baya ta tattara ta dena tunda taga abin
na Zabba'u ba hankali aciki.



Baran ma da Mudassir ya yi aure,mama ta janye Hadiza matar Mudassir suka haÉ—e kai iskanci
ba wanda A'isha bata gani,har kawo yanzu bata canza zani ba.


Sauke dogon numfashi tayi afili tace "A'isha kin aikata babban kuskure na shiga rayuwata da
zame mini katanga da duk wani cikar burina, kuma zan nuna miki kin aikata babban kuskure, Ni
dake shega ka fasa.



*_Bayan wata huÉ—u_*

Kande ce take tafiya tana ƴan waƙe waƙenta,tasha wata burmemiyar rigar me botira agaba,yau
kam Amo harda guga tamata,ta fesa turare se tafiya take tana ɗage kafaɗa,hannunta riƙeda
kuɗi da wani ƙaramin bakko zata kasuwar ƴan kaba, yau komai na kayan miya basu
dashi,waken soyar ta ma ya ƙare shine aka ɗau na agwagwa za'a tafi kasuwa siyyya.

Gitfa wasu Æ´an mata tayi,suka kalleta suka kwashe da dariya, É—aya tace wa sauran "Allah na
tuba,yanzu wannan wai mace ce amma duk ta lalata jikinta da tafiyar maza,ita adole namiji ce",
É—ayar ma tace "waifa soja take kiran kanta"hhhhhh suka kuma sheqewa da dariya,ta ukun kuwa
tace nide birgeni take wlh,ga kyau,wannan idan zata nutsu wallahi mace ce me zati da diri" ta
farkon ta kuma cewa ke dilla cen matsa,ina wani kyau anan wacce kullum take wuni cuÉ—anya
da maza,mtwsss" ta biyun ma ta kuma cewa "kyau iya kyau amma na banza ba mashinshini,ni
wnn anya ma akwai nonon arziki aƙirjinta kuwa?" Ta fada tana kama haɓa, wata dariyar suka
kuma sheqewa da ita suna tafawa.




Juyowa kande tayi afusace ta nufosu tana wani irin huci,tsayawa sukayi dan ganin me zata
musu ita kaÉ—ai sukuma har rai uku,tana zuwa ba wata2 ta haÉ—a kansu guri É—aya dukansu,da
wacce ke tsakiya da waÉ—anda ke gefe da gefe ta haÉ—e musu kai ji kake gub,agigice ta tsakiyar
ta yanka ihu ta kwasa aguje kamar ta gigice, sauran biyun kuma suka tsugunna ko wacce tana
dafe kanta dan sun gumu ba lefi, kallonsu tayi a sheqe ta nuna É—ayar tace "kikace ko akwai
nonuwa akirji na ko?, to maza miƙe ko laluba kiji" tafaɗa tana finciko hannun budurwar wacce ta
fasa ƙara tana bawa kande hakuri,fadi take "dan Allah dan Annabi kiyi hkr wlh Sherin sheɗan
ne,dan Allah kiyi hkr,ni wlh bazan kuma shiga harkarki ba dan Allah kiyi hkr ",kande kuwa ta rike
hannun budurwar chaf tace aifa seta taba kirjin taji ko akwai nono.


Seda budurwa nan tagalabaita saboda kuka,fuskarta duk tayi kace2 da kuka sannan ta saketa
dan ɗayar tuni itama ta cikawa bujenta iska,tace "arniya ƙaramar ƴar iska kawai" ta juya ta tafi
gun aikenta.


Tana tafiya tana tuna yadda Æ´an matan nan suka rikice musamman wacce ta ruga aguje kamar
ta gigice se murmushi take ita kaɗai,abin ya bata nishadi,shafar ƙirjinta tayi wanda take mance
ma wai akwai wata halitta agurin, rintse ido tayi jin ta taɓa wasu halittu masu matuqar
laushi,madedeta dan sunfi ƙarfin hannunta,amma yanayin yadda jikinta yake bata da faɗi ta
sama se ta ƙugu ga yacce take tafiya a ƙobare hakan yasa bakowa ne ze iya gane yanayin
cikar halittarta ba,uwa uba kuma shigarta,amma duk wannan abin bisa tilastawar inna yasa take

saka half vest acikin burma burman kayan nata,wnn ma yaƙara temakawa gurin ɓoye cikar ƙirjin
nata,wanda idan ba ido kasanya mata ba ma sam bazakace tanada su ba.

Hura hanci tayi ta daki ƙirjin nata tace "munafukan abubuwa arnaye me zanyi daku ma,ni dama
baku fito ba yasin,bakkuda wani use agun soja" ta wani cuno baki gaba,tana sake yin doro da
bayanta irin karma akuma lura akwai su agurin.


Sam kande ita a yanzu halittar mata akanta bata birgeta,zata iya rantse wa tana mantawa ita
mace ce se idan tazo kama ruwa ko yin wanka,dan tunda Allah ya sa ta girma ta cika mace
bata taɓa yin jinin al'ada ba,shekarunta ashirin da ɗaya,zata iya rantse wa ma tamanta mata
suna wani abu wai al'ada,dan idan inna tana al'ada ƙaryar mutum yagane,ko lokacin sallah ya yi
seta waske,mlm habu ne kaɗai ze iya sanin tana cikin halin rashin tsarki,hakan ya ƙara sanya
wa kande ta manta da wata aba wai al'ada,balle a yanzu da inna ta dena yi kwata2.


A dede wani lungu wanda ze sada kande da kasuwa taga wani me baro a kwance aƙasa yanata
sheqa amai,jikinsa banda rawa ba abinda yake,da sauri kande ta matsa kusa dashi tace
"subhanallahi sannu mlm, bakada lfy ne?" Be iya ce mata komi ba, ya jingine da bangon gurin
yana mayar da numfashi,jikinsa se rawa yake idonsa ya yi ja sosai,daganinsa yanajin jiki,ga
barronsa a gefe,da sauri ta tashi taje gaban bore hole É—in dake kusada su ta É—ebo ruwa a wani
bucket data gani agurin ta kawo masa tana masa sannu,ya amsa ya wanke fuskarsa ya zuba
akan sa,duk ya bata tausayi,a ranta tace oo Allah neman halak da wuya,kalli wannan babban
mutum dashi amma yana na barrow,ko lafiya bashida ita amma ya fito neman halalinsa,* kande
mutum ce me tsananin tausayi,ita kanta batasan tana da tausayi ba,wani abin ma bata sanin
tanayi.


Gdy mutumin ya mata ya miƙe bayan yaɗanji karfin jikin sa,yaja barrow dinsa harya fara tafiya
Jiri ya É—ebesa yafaÉ—i agurin a sume,da gudu ta tashi ta ruga ta isa inda yake a kwance ta na irin
kiran bawan Allah,wasu masu barrow ta hango a tsallaken titi ta tallafo kansa tana bubbuga
kumatunsa tana kiran bawan Allah bude idonka amma baya cikin hayyacinsa, tashi tayi ta ruga
tsallaken ta kira masu barrow nan tace ga wani É—an uwansu cen ya faÉ—i ya suma kamar ma
bashida lfy ne,da sauri kuwa suka biyota zuwa inda yake kwance aƙasa a sheme,suna zuwa
suka gansa da sauri ɗaya ya tsare musu napep suka kamashi daƙyar suka sanya aciki,dake
sunada yawa se mutum uku suka shiga napep É—in biyu abaya suka rikeshi se É—aya ya shiga
kusada direba suka tafi asibiti,sauran kuma suka zauna suka ajiye wa wanda suka tafi asibiti
barrow ɗinsu,kande tana tsaye tana kallonsu har suka ƙulewa ganinta,jiki a sanyaye ta tashi ta
shiga kasuwa tayi siyayyarta ta juyo hanyar gida,har lokacin fuskar mutumin nan me barrow
bata bar idonta ba,duk tausayinsa dama talakawa ya rufe ta,ita de tasan su bamasu kuÉ—i
bane,amma sunada wadatar da abinda zasuci daa na bukatar yau da kullum be gagaresu
ba,harma wani kan iya jingina dasu shima ya wadata.

Tana tafiya tana tunanin halin tsadar rayuwa da yadda talaka kullum yake shan wahala,kamar
ance ta É—aga kai kawai idonta ya faÉ—a cikin na mahaukacin ta data sanya wa suna kirezi.


Ta daÉ—e bata ganinsa,kusan sati biyu rabon da ta gansa,amma da kullum yana biye da ita duk
inda zata to seta gansa agurin, ta danganta hakan da kila dan tana bashi abinci ne,se kuma a
ka É—auki sati biyu bata gansa ba se yau.


Suna hada ido aikuwa ya sinne kai kamar ya yi rashin gaskiya,tsallaka titi tayi tashareshi ta nufi
hanyar gida,kamar yadda tayi tsammani kuwa yana bayanta yana binta a hankali,amma suna
da nisa da juna,wata kwana tashiga,ta ɓoye ta ɓace masa,ai kuwa aguje ya rugo ya biyo
kwanar shima yana dube dube alamar ita yake nema.

Be ganta ba kawai ya kwaɓe fuska ya ɓata rai ya juya ze wuce kawai ya ganta a bayansa tace
masa "woooooo" ,kamar ba mahaukaci ba seda ya firgita dan babu zato ya ganta akusa
dashi,dariya ta fara ƙyaƙyata wa ganin yadda kirezi ya firgita se zare fararen idonsa yake,a sace
ya saki murmushi shima se kuma ya kwaɓe fuska ya sauke kai alamar fushi yake,dariya take
seda tayi me isarta yatsare ta da manyan idanuwansa yanata kallonta,baƙaramin kyau tayi ba
yadda take sheqa dariyar,1 side dimple dinta kamar a zuba abu aciki ya zauna tsabar yadda ya
loɓa, kallonta yake sosai ya shagala,ji yake kamar ya shafa kyakkyawar fuskarta,gashi ta ta
sharɓa basilin ga hasken rana yana haske fuskarta se wani walƙiya take kamar wacce take
amfani da glowing products.

Gimtsewa tayi tace "hi kirezius Ina ka shige ne?,2 sleep I no see u,were u go, eh" na sha ma
Æ´an uwanku ne suka kwalfeka,ashe de har yanzu kana nan a layi kana gararamba".

Ko mi be ce mata ba se sunkuyarda kai da yayi,kama hanya tayi tace "kai kirezi yau banda ko
asi kawai ka ware nima nayi nan",ta kama hanyar gida,kirezi kuwa yau duk inda kande ta saka
ƙafa shima seya saka,tayi2 ya tafi yaƙi,duk inda ta wuce se an kauce ganinta da mahaukaci,ko
ita kaɗai ba me tarar hanyarta balle yau an ganta da mahaukaci,har gida ya bita,a ƙofar gida
Ikilima ta fito taci kwalliya da alama fita zatayi,se yauƙi take tana wani gyatsine,tayi kyau abinta
itama fara ce kyakkawa,yanzu ta gare shiga shirgin kande tauda de taga ba riba,koda yaushe
idan ta haÉ—o su itace take shan wuya,kuma ba wani mataki da ake É—auka shiyasa tayiwa kanta
karatun ta nutsu.

Ai tana hango kande da wani rusheshen mahaukaci ta tsallara ihu aguje ta koma cikin gida tana
ihu,malam dake zaure da dalibansa da sauri suka fito waje dan ganin abinda ya tsorita Ikilima
haka,ai kwa darewa suka farayi suma ganin kande da wani ƙaton mahaukaci.

Tsayawa tayi tana cewa "kirezi tsaya anan barin gani ko inna ta gama tuwo,kuma kana cinyewa

ka kama gabanka tom", kamar me hankali yako tsugunna agurin,mlm habu yana tsaye yana
kallon ikon Allah.

Juyowa tayi zata shiga gida taga mlm da É—alibansa sunyi cirko2 suna kallonta.

Sallamar É—aliban mlm ya yi bisa dole,kafin ya janyo hannun kande yashiga da ita cikin gida,É—aki
ya kaita ya nemi guri ya zauna ya ƙura mata ido,kallonta yake sosai itama kallonsa take cikin
ido,kallonta mlm yake yana karanta wasu addu'o'i itama kallonsa take ido cikin ido,sosai mlm
yake addu'o'in nan,idonta ne yafara tara jini nan take idonta yakoma kamar an zuba nuna mata
jini,saurin rintse ido tayi gumi na karyo mata ta ko'ina.

Cikin buÉ—aÉ—É—iyar murya ta fara magana hankali kwance,tace....


# 🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.

Not edited


Free page:11


Bismillahirrah manirrahim.

Cikin buÉ—aÉ—É—iyar murya ta fara magana hankali kwance,tace "malam Abubakar bin
Hamza,meyasa ka kasance me gaggawa ne a wasu lokuta? Tabbas kai É—in cikakken É—an Adam
ne, gaggawar ka ta kuma tabbatar mana da hakan,idan baka mantaba abaya shekaru sha É—aya
da suka shuɗe mun taɓa faɗa maka akwai sirri dunƙulalle a tattare da goɗiya,to a yanzu sirrikan
sun fara bayyana tabbas wannan mahaukacin ba mahaukaci bane, cikakken mutum ne me
hankali,kuma ba ƙaramin mutum bane,sannan ta dalilinsa ƙofar sirri zata buɗe,mun baka
gajeren haske,sauran kuma kaine da kanka zaka nemo,tabbas kai É—in ubane na gari,kuma
kaso abinda bakada alaqa kota kusa bare nesa,tabbas zakaga sakamako,mahaukaci sunansa
A'ZAM(ma'anar sunan the greatest),ka tunkaresa kai tsaye kuma ka nuna masa kasan yanada
hankali,tabbas zakasan duk wani abu da kake da buƙatar sani,dukkan wani sirri ze
bayyana,amma ko ka sani lokacin bayyanar sirrin wa goÉ—iyar beyi ba,kai kaÉ—ai kake da damar
sanin wannan sirrin,.. malam Abubakar bin Hamza tabbas zakaga sakamakon alherin ka,ka bar
damuwa da yanayin rayuwar goɗiya,tunda kayi hkr na tsawon shekaru to haƙiƙa ribar ka akusa
take,komi ya kusa zuwa ƙarshe,sannan sirrin cikin gidan nan ma ya kusa bayyana,duk ka zuba
ido zakayi kallo kuma zakayi mamaki,abinda ka sani da wanda baka sani ba duka zasu fito
fili,Ni zan tafiiii,kuma zan dawo kamar de yadda aka saba".



Hamma me tsayi kande ta yi kafin ta lumshe idonta a hankali kuma ta kwanto a jikin mlm, maida
hannunsa ya yi ya rungumeta idonsa na zubar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login