Showing 15001 words to 18000 words out of 26224 words

Chapter 6 - kANDE BOOK COMPLETE BY SADIKA IBRAHIM MOMSANI-.pdf


zuba min guba a cikin abinci,wanda na tabbatar wancen abincin ma akwai same poison a
cikinsa, naso sakinki in a peaceful way Amma abinda kika aikata yanzu yasaka nacenza
ra'ayina,Sena hukuntaki dede 1da abinda kika aikata mini"kallon guards din ya yi yakaÉ—a musu
kai,sake kwashe su sukayi suka fita dasu,Meera se ihu take tana roƙon ya yafe mata, wa Sherin
sheɗan ne amma ko kallon inda take beyiba sema sake busa hayaƙin sa ta yake.


KIAMBA ISLAND PHILIPPINES.


Wani irin ƙasurgumin daji ne dake gaɓar tekun phillipines,daji ne me matuƙar haɗari wanda ƴan
daba suka ƙwacesa suka mayar dashi sansanin aikata miyagun ayyukansu.


Cikin wani underground building suke zartar da meeting É—in nasu,mutane ne wanda kallo É—aha
zaka musu ga tabbatarwa manyan mutane ne su É—in,sbd shigar dake jikinsu, tattaunawa suke
akan yadda ake samun gagarumar riba a harka smuggling da safarar mata da yara,babbar me
kawo ribar kuwa sune kidnapping da human part trafficking.

Babbar me hannu jari a cikin wannan harƙalla kuma me kaso hamsin a duka wannan harƙallolin
itace *Annabella de'cruz* ƴar nan ƙasar ta phillipines ce,matashiyar mace ƴar kimanin shekaru
arba'in,afuskar duniya itadin Æ´ar kasuwa ce me manyan hannun jari a companoni da dama a
ƙasar,ko wannan dajin na KIAMBA ISLAND ma itace jagorar amshe shi yazama mallakin ƴan
daba.


Acikin wannan underground building din Allah ya yi yawa da munanan ayyukan da ake aikatawa
aciki,komi na Anna na ƙasar phillipines anan ake yinsa,duk wani mummunan abu acikin kiamba
dark island ake yinsa.



Agurin ana ƙera duk wani nau'i na muggan makamai,miyagun ƙwayoyi,har asibitin da take
safarar sassan jikin É—an Adam da jarirai a wannan tsibirin yake.


Bayan sun gama tattaunawa akan ribar da suke samu sekuma aka koma kan yadda sabon
jami'in hana sha da fatauci miyagun ƙwayoyi ya musu karan tsaye acikin garin,duk wasu
manyan yaran Anna dake jigilar yimata aiki acikin garin manila ya damƙe su,hakan yasa kowa
ke kawo shawarar yadda za'a ɓullo masa,sbd yanada kafiya, da dagewa akan aikinsa,Asalinsa

ɗan ƙasar Dubai ne,ya yi karatunsa a Dubai har ya zuwa matakin aikinsa a yanzu, kasancewar
mutum me gsky da dagewa akan aikinsa yasa aka dinga masa sauyin gurin aiki har Allah ya sa
aka kaisa ƙasar phillipines agarin manila.

Tunda ya fara aiki yake yiwa ƴan daba manya da ƙanana ɓarna,har sanda aikinsa ya faɗa kan
babbar kura Annabella de'cruz,the red dragon,shine takenta a duniyar miyagu.


KANO NIGERIA.



Wanka kande ta fito,yau wani irin nishadi take ji ta siyi sabon kaya a gwanjo, wani wando ne
3quater me faɗin gaske,se wata rigar polo irin ƙatuwar nan,da alama ta ƙaton mutum ce,tsaf
tagama shirinta,ta ɗakko sabon covershoe ɗinta kauce buba ta ƙwama,ga wata pcap,fara amma
Takoma brown ahakan ma tasha wanki ne agurin Amo dan ita keyiwa kande wanki,guga ne
bata iya ba kuma kande batayi,ahaka take burma kayanta duk squeezing É—insu,wata doguwar
Zariya ta ɗakko ga ɗaure ƙugun wandon dan ya mata yawa,idan kaga yadda tayi dressing seka
ɗauka wani ƙaramin mahaukaci ne,zaka rantse batada gata acikin gidan Kano.



Fitowa tayi tana ƙwambo se karkaɗe jiki take ita adole yau ta yi wankan sabon kaya.


Kallonta inna tayi kamar tayi dariya amma ta maze tace "a'a auta wannan gayun fa,se ina
haka,amma kin yi kyau" cikin shan ƙamshi tawani cira kai gefe tana karkace baki tace "Sa'a de
inna ta,zaa tufar idon mlm habu me kayan koli,seke inna Allah wlh" murmushi inna tayi tana
juye miyar data gama soyawa akan awarar, É—aukan bokitin tayi tana tafiya tana kallon wankan
data ɗauka yau,yau dolene ma tayiwa su zakarius ƙwambo,a zaure ta tsaya ta kalli mlm wanda
har É—alibansa sun fara zuwa,tace "Sa'a de dagus,dawa de zaa imamu,Ni zan ware eh,kawai se
na dawo asa mana albarka" "Allah ya miki albarka ya shiryeku keda Æ´an uwanki mamana,Allah
ya bada Sa'a kinji? Dan Allah banda faÉ—a da doke doke".


"Dawa de dagus,Allah bar mana kai zaa imamu namu,Amin Amin tsoho ni na shige,see you in
zaa aftanu(afternoon)tasa kai fa fita, É—aliban mlm se kus kus suke suna mamakin yadda akayi
malami kuma liman kamar mlm habu amma ya haifi irin wannan Æ´ar.



Tana fitowa waje ta sake cenza yanayin tafiyarta,har wani É—age kafa É—aya take tana zauÉ—ewa
gefe É—aya,wasu yara ne sukace zaa kand me awaraaa,kallonsu tayi tace "saa de yara kuhuta

kawai,kai kutaho yau ko inna zata tabo gajimare ne Allah sede na saka mata lada,Alqur'an yau
sadaka zanyi" aguje yara suka taso da almajiri haka ta dinga raba musu awarar nan,gashi tayi
kyau tayi manya tasha miyar jajjage amma haka kande ta dinga kyautar da awarar nan,tana
cikin baiwa yara se masifa take tana zata yayyarfawa yaro hannu a ƙeya batason
turereniya,wani hannu ne taga ya miƙo shima abashi bin hannun tayi da kallo tace "aaa dawa
de kirezi man,kaima kasan yunwa ashe,hhhh yo ai na É—auka mahaukata basa cin food, Allah
yasin kuwa,kai atafawa yunwa raf raf", yara se tafi suke suna ihu,ta dakko awara ta baiwa
mahaukacin wanda yake ta kallonta kamar ze cinyeta,ganin yaƙi tafiya yasa ta kallesa tace
"yade kirezi ko ta mama kaÉ—an ne?" Jijjiga kai ya yi alamar eh, amshe ta hannunsa tayi tace
"bar nan dan asawarka,bari gobe idan akayi wata Sena ƙara maka idan da kuɗin ka acikin jarin
awarar É—an dusa da tsaki kawai".



Seda ta rabe awarar tas sannan tabaiwa wani yaro bokitin awarar tace ya kaiwa innarta.


Chamber su ta wuce,tana zuwa tun daga nisa ta cenza tafiya tana "yoo yoo maza,ya ake ciki
ne,hi gayis y me news ne" ihu suka É—auka ganin ta da wata sabuwar shiga kuma basu santa da
kayan ba,se wani juyi take tana breakinh dance tana faÉ—in "yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I
am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta kawai se kicibis suka haÉ—e da wannan
mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii
birki agaban sa tace ......




🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free

And now
# kANDE paid.

Not edited


Free page:08


Bismillahirrah manirrahim.

"yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta
kawai se kicibis suka haÉ—e da wannan mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon
ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii birki agaban sa tace "arna yane? Kai kirezi r u in zaa ur
hankali kuwa? Tun dazu na lura da kai se folowin É—ina kake,yane iye hw market ko kaima
wankan ya maka ne?" TafaÉ—a tana tsaresa da manyan idonta.


Juyawa kawai ya yi yawuce yana tafiya yana waiwayenta, zakarius ne yace "zaa kand wannan
ai ya kwana2 a unguwar nan,kusan kullum yana unguwar nan ya daɗe sosai, kawaide baki taɓa
ganinsa bane" taɓe baki tayi kafin tace " wai ina sagalo ne yau bezo cika chamber ba Wetin
hapin dashi ne eh?"
Duna ne yace "dawa de zaa kand,wai bakisan cewa ƙojensa yana asibiti ba?,ai shekaran jiya
tsohon sa yaje yasha tamasa over kawai yazo yasamu babar sagalo ya sauke mata rabin bulo
atsakar baya,ai yasin baban sagalo bulkumi ne,shi har yau beyi hankali ba,tun muna yarafa
yake kwalɓewa har yau be dena ba,kullum idan yashawo kayarsa seyazo ya tarawa babar
sagalo gajiya,arne kawai, ga babar sagalo 50inch shine kawai ta fara nuna masa itama fa
arniya ce,yadda yake wani figigi kamar taliya Æ´ar murji Allah É—aukar amarya kawai tamasa ta
dinga maka arne da ƙasa kan azo akawo masa agaji ya wulla second barzahu arne kawai".



Dariya kawai kande ke ƙyaƙyara,dan ita har ga Allah babar sagalo ta birgeta data sumar da
baban,tun suna yara yake shaye2 daga su wiwi abun ya yi yawa har giya sha yake,kuma idan
ya dawo gidan ya kwara mata amai haka zata wanke tana kuka,amma bawan Allahn nan ba
wacce ya rena irinta,abu kaÉ—an duka,badama tayi magana seya zare belt ya yita laftar baiwar
Allah,gata irin matan nan ne masu jiki da tsawo sosai gata fara dan ita Bello sagalo ya
biyo,baban Bello kuwa baƙi ne wuluk,gashi kamar taliya ƴar murji ta bakin duna,sirirne
sosai,auren gida aka musu da babar sagalo baya sonta shiyasa yake wulaqanta ta,ansha
zugata tadena zama yana dukanta abanza amma setace bakomi wata rana ze dena,haka za
ata zugata amma bata ɗauka,ko agaban su Bello da ƙannensa ne seya mata duka ba abinda ya
dame shi,ansha kai ƙararsa gurin babansa me sunguwa yasa akamasa aɗaure amma take

tayita kuka tana bada haƙuri wai asakesa ita ta yafe masa,haka me unguwa yashe cewa ze
raba wnn auren taje ta auri wanda yasan darajar ta amma tayita kuka tace ita abarta da mijinta
tanason sa,wannan dalilin yasa me unguwa ya É—auke Bello yakaishi bauci gurin yayan baban
su Bello,dake shi makamin tsangaya ne,se aka kai Bello domin ya yi karatu yadena ganin
wannan taladdancin da babansa yakewa uwar amma har kawo yanzu be dena ba.



Shekaranjiya cikin rashin Sa'a yadawo abuge yazo yafara jibgar ta,to dama tafara gajiya kuma
tafara É—aukar shawarar mutane na cewa tadena zama yana dukanta agaban yara,idan ba haka
ba zasu ɓatawa yaransu tarbiyya tunda dukansu mazane,haka zasu tashi kamar yadda sukaga
ubansu,aiko yana fara lafta mata belt cikin zafin rai ta warto gaban rigarsa tayi sama dashi
kamar ta É—aga Æ´ar kaza ta haÉ—e shi da bango ta dinga makawa,tun yana ihu har ya fara bata
hkr, amma ina tayi zuciya seta ta fasa masa kai taga yadena motsi sannan ta yasar dashi
aƙasa,ko ajikinta tasaka hijabi tafita ta kira me napep tasakashi takaishi asibiti tace musu
santsin ya kwashe shi yafaÉ—i.


Tunda takaishi tabari asibitin takoma gida,shine ta tura Bello da kuÉ—in magani da komi shine
yake jinyar babansa ita taƙi zuwa,dalilin rashin ganin Bello kenan.



Seda tagama dariyar sannan tace "yakamata muyiwa sagalo solidarity muje muga jikin lamison
tsohonsa hhhhhh", tasake sheqewa da dariya se dariyar halin gidansu sagalo suke yi.



Washe gari haka fa sake É—ibar wani wankan wanda yafi na jiya ban dariya,ta shafe fuskarta da
basilin se shining take kamar takaddar tsire,tayiwa inna da mlm sallama ta tafi asibiti zasuje
itada su duna su gaisar da baban sagalo daganan zata wuce kasuwa tasiyo waken soyar
awararta.

Itama innar shiri take zata tafi gidan Hafsatu tayi miscarriage,Maryam kuma tana asibiti tana
naƙuda cikinta be isa haihuwa ba watanta biyar kenan,amma naƙuda fa taso mata me
tsanani,shine inna take shirin tafiya dubasu.


Awaje kande taga su duna suka fada mata an sallamo baban sagalo yana gida,gidan suka tafi
suna sake dariyar abinda ya faru,sallama suketa har ita duk sunƙi shiga su adole maza
mazansu faÉ—a gidan mutane haka kawai ba.

Ƙanin Bello ne yafito yace wai yaya yace su shigo kawai dan yanaji muryarsu ya gane su.


Shiga sukayi kande ce agaba se wani É—age kafada take tana baje baya da burma burman
kayanta ga fuska se shining take gwanin ban dariya tasha p cap ga sumarta data yanke tabarta
dede kafaÉ—a ta tattare ta cusa cikin p cap É—in,bayan su gaisarda babbar su Bello kande tace
"dawa inna kina wuta alqur'an, ashe kinyiwa zaa fazaa lamiso dukan dawa?kai inna kin birgeni
Allah wlh,yo dama inna yadda kiken nan da arnen kyau a kamata ya yi ace fazaa yana biye
dake sau da ƙafa kamar yaron aikin ki Allah kuwa,Kinga inna ta alqur'an dagus tsoron ta yake"
tajuyo kan baban su sagalo dake kwance an laulaye masa kai da bandeji tace "ahh cau cau
fazaa ka daku alkur'an, innalillahi irin wannan rawani haka kallifa yadda aka mayar dakai kamar
sarki kasha rawani amma na bandeji wayyihuhu inna tamu dawa de inna kincikawa fazaa aiki
alkur'an Kinga kema kinyi free da duka kamar masara,da seki zauna ya yita miki jibgar
dawa,amma yanzu ai kinsamu lafiya kema kai cau cau inna Sa'a de inna Allah bar mana ke
alkur'an" dariya kamar ga kashe su zakarius dasu duna tun suna kumshewa har suka fara yin
abunsu har Bello dariyar yake kamar ba iyayensa akewa iskanci ba,babarsu Bello itama dariyar
take,dama ita tun ainahi kande birgeta take,duk yadda ake tsinewa halin kande ita batayi
yarinyar birgeta take sosai gata kyakkawa ga ƙarfi kuma zamanta dasu sagalo besa sun lalace
ba daga su har ita,hakan yasa ita se kawai Allah ya É—ora mata son yarinyar,baban sagalo kuwa
da kande ta saka masa fazaa lamiso yana kwance se wurga idanuwa yake ga fuska a suntume
baya iya magana sbd ya jibgu,ya yi gum da baki.

Kallonta tayi tace "kande ina innarki ne? Yau ba tallar awarar ne?" Keɓe baki gefe kande tayi
tace "inna anacen gida nabarota tana shirin zata tafi ashibanci yi ashibanci mana waifa su yaya
Hafsatu ne sukayi ɓari shine taketa shirin zuwa gaishesu harda kama agwagwarta ta yanka
tayiwa yaya Hafsatu miya wai tamayarda kwaÉ—ayi kijifa inna da iyayi,duk da de yaya Hafsatu da
yaya mero basuda damuwa amma ai mama ba godewa inna zatayiba,sede ma azageta ita
kuma yaya Maryam tana asibiti tana naƙuda kuma batakai lokacin haihuwar ta ba"
"Assha subhanallahi abu beyi daÉ—i ba Allah yabasu lfy" "amin" kande ta amsa tana ciro É—ari
biyar tabaiwa inna tace asiyawa fazaa lamiso lemu,ta cewa su Bello ita zata ware kasuwa zata
tafi,tamusu sallama ta fito,babar sagalo har zaure ta raka kande tana dariyar shigar da yarinyar
tayi da yadda take tafiya ita bata yadda ba itama namiji ce.


AGRA INDIA.

SITHABARAN HOSPITAL.

Dr Joshi shine in charge na duba duk wata mace me ciki,ya iya aiki sosai ya kware sosai akan
sanin abinda ya shafi mata musamman masu ciki.

Zaune yake a office ɗinsa yana rubutawa wata mace me ƙaramin ciki magani,wayarsa ce tayi
ƙara cikin faduwar gaba ya ɗauki wayar yana miƙa wa matar takaddar taya gama rubuta mata
maganin da zata je pharmacy ta amsa, nan da nan jikinsa ya jiƙe da gumi,yana picking call ɗin
hoton ƴarsa ya bayyana an saka mata wuƙa awuya cikin tsananin firgita yake baiwa mutumin
haƙuri akan karya cutar da yarinyar duk abinda suke so ya amince ze yi,dariya ƴan daban suka
kece da ita wanda yasawa yarinyar wuƙa a wuya yacire yana cemasa ya kalli babban screen
din dake bayan su, wani mutum ne ya bayyana wanda aƙalla ze iya yin shekaru hamsin da
takwas,amma sbd kuÉ—i da suka zauna masa hakan yasa yake kama da Æ´an 30y.


Fuskarsa da kansa dake da farin gashi ne kawai yake nuna ya manyan ta amma jikinsa amurje
yake kamar matashi, yanada kyau sosai,jikinsa sanyeda wata irin suit se walwali take kamar an
shafa mata gold,yana zaune agaban wani babban teburi aÉ—akin taro,kallon Dr Joshi ya yi
yasaki wani wild smirk yace cikin harshen indianci "idan kana buƙatar ƴarka ta dawo gida safe
nd sound dolene ka yarda da deal É—in da muka kawo maka,dole ne kayi mana gwajin
magungunan mu akan mata masu juna biyu,dole kuma duk cikin da yakai wata biyar kasan
yadda kayi ya lalace domin wannan jinin miscarriage ɗin muke da buƙata a tara mana,idan kayi
hakan ina me tabbatar maka seka zama shararren me kuÉ—in da duk fadin india babu me
irinsa,namaka alkawarin wannan,sannan zan saka asibitin ka yazama lamba É—aya da duk
duniya zata san da zamansa,kaide kawai kabi sharaÉ—in da zamu gindaya maka,ina binka da
lalama ne kawai saboda ƙwarewarka a aiki shine jarinda nakeson amfani dashi a wannan
harƙallar,amma ba dan hakaba da kota ƙarfi Sena saka kayi abinda nake da buƙatarka".


Banda gumi ba abinda yake zuba ajikin Dr Joshi,Amma ba yadda ya iya inde yana buƙatar
zaman lafiyar iyalansa dole ya aikata abinda suka so.

Yana cikin wannan tunanin wasu manyan manyan mutane suka shigo sanyeda kayan likitoci
suka ajiye masa wasu akwatuna suka juya suka fice.


Kallon wayar yayi inda yaji ana masa magana "wannan sune allurorin na baƙin case sune muke
buƙatar ka gwada su akan duk wata me tsohon ciki,su kuma na jan case din sune magungunan
da zakana basu suna sha,se farin case suma allurai ne,duk macen da ka tabbatar cikinta ya kai
wata biyar ko shida to akansu ne zaka yi amfani da wannan allurar,sannan zamu riƙe ƴarka
dake gurin mu,har seka aiwatar da aikinmu na tsawon shekaru daya kafin musaketa" kafin ya yi
wata magana sukayi saurin disconnect na kiran bisa umurnin na cikin babban screen din wanda
ko sunan sa Dr Joshi be sani ba.


Wani irin kuka Dr Joshi keyi,ƴar sa shekararta goma sha huɗu,yarinyace ƙarama kuma ita kaɗai
yakeda,tabbas bayason ya rasata, haka kuma bayason aikata wannan mummunar aikin da
suka sanya sa akan al'ummar da basu ji ba basu gani ba,sbd yasan allurorin yasan haÉ—arin su.

Su wadanda akace ya yiwa masu tsohon ciki illarta shine zata sakarwa jaririn cikin cutar kansa
me hadari,wanda zata iya illata har uwar ba wai yaron kadai ba,idan akayi babbar Sa'a shine za
a haifi cikin amma baze zo da lfy ba, daganan se su kawo wani magani wanda shine maganin
cutar wannan shine kasuwancin da suka kulla da asibitoci da dama a faÉ—in duniya,wani kuwa
tun aciki yake mutuwa kokuma daga uwar har yaron su mutu,kuma se sun zaƙulo babban likita
me cikakkiyar ƙwarewa da sanin kan aikinsa sannan suke kai masa wannan farmakin,duk kuma
wanda ya bijire ko masa barazanar za akasheshi ko kuma akashe wani nasa da haka wasu
suke yadda wasu kuma tayin farko idan sukaji maƙudan kudade kai tsaye suke amincewa.


Ita kuma ta masu cikin wata biyar itace wacce zata lalata cikin har se an kwashe musu,to jini
ɓarin ake siyarwa wasu kamfanoni masu yin mayukan fata dana bleaching,ba iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login