Showing 1 words to 3000 words out of 107121 words
Chapter 1 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
[27/03, 17:48] Elhajj
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
1
By
Asmabaffa
Masoyana naga sakonku sosai na yabo da jinjina kan novel dina na maraicin rahma,ban
San Kalmar da zanyi amfani da ita ba wajen gode muku,na gode kwarai Allah ya bar
kauna,Allah ya biya muku dukkanin bukatunku na alkhairi.
LONDON na nufa a 80 jirgi ya saukeni da kyar na hada kudin zuwa ma sabo da jin
dadinku readers bazan bari ya wuce Ku ba,wani gida Wanda ya amsa sunansa gida ko a kasar
ba duk gida ba,ko ina ya tsaru wani handsome na hango narke a 3seater yana latsa wata
dankareriyar iPad ga wata computer new design itama iPad a gefe yana ta aiki ciki hade da
danna waya,tun daga yatsunsa nasan kudi da Hutu hade da jin dadi sun ratsashi,don guy
karshene wajen haduwa da kyau OMAR MOHD OMAR kenan dan kimanin 35yrs sunan
kakansa yaci.Baban sa mohd Omar Ibrahim shahararren dan boko ne kuma dan kasuwa kuma
dan siyasa,shi kadai tilo iyayensa suka Haifa kafin rasuwarsu,yan asalin jahar gombe ne,fulanin
gombe,babansa ya tsaya masa yayi karatu kafin rasuwarsa,yanzu kam mohd Omar sai yan uwa
da suke gombe kawai suka rage masa,yana musu alheri da ziyartarsu, dattijon kirki yayi aikin
gomnati kala kala,ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau
daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka
ambassador ne na Nigeria a Russia.ga kamfanoni da yawa,harkar business iri iri,ya Tara dukiya
kadarori barkatai,a takaice dai hamshakin me kudine na gasken gaske dake zaune a abuja
birnin tarayya.yana da mata biyu hajia amina itace uwar gida tana da yara uku dan Allah bai
bata haihuwa da yawa ba,Omar shine na farko,sai abdullah dan 18yrs sai autarta suleim
yar9yrs.matarsa ta biyu hajia rahina yaranta duk matane guda 5 sadiya 27yrs,Aisha
25yrs,zainab 23yrs,naja 21yrs sajida 15yrs autarta.hajiya amina yar kauyen gombe ce,dan haka
batayi karatu ba iyakacinta secondary shima bayan mohd Omar ibrahim ya aureta ya sata
tayi.ita bata aiki bata zuwa ko ina ta rike yaranta ta basu tarbiya tare da mijinta,
Rahina kuwa da yaranta uku manya duk suna aikin gomnati sunyi degree,kullum sai iyayi a hau
mota fuuuuuuu ko wacce ta tafi aiki,in salary yazo ai ta gasa da juna. Baffa yayi yayi su fito da
miji tunda sunyi degree amma sunki,shi yasa gidan ya Tara mata rida rida.gashi na bangaren
amina sune sukafi kowa kyau,musamman Omar,shi yasa suka kara tsanarshi.
Basa zaman lfy ko kadan, dan hajiya rahina bata kaunar hajia amina da yaranta,dan amina
tana da maza ita bata dasu,ganinta zata fita cin gado,gashi alhaji mohd yafi son amina da
yaranta musamman Omar,da wannan yasa rahina dagewa lallai yaranta mata baza suyi aure ba
sai ko wacce tayi degree tana aikin gomnati,suma yaran nata a akidar haka suks taso kuma
halinta kaf suka dauko,ga karya,rashin mutunci da nuna su wasu ne,a junansu ma basa zama
lfy,daga munafunci sai fada a titi,sai gasa da junansu ko wacce naso taga tafi kowa,gasu da bin
malamai uwarsu ta dorasu,ita kuwa Allah sarki haj amina mutuniyar kirki ce mace ta gari,abin
duniya bai dameta ba,ga hakuri da addini.addua kawai take zabgawa kanta da yaranta
musamman Omar dan sunfi kishinsa,shi kam Sam baya shiga harkar kowannensu sai iya nasu
dan yaga kannen nasa ba tarbiya.
Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal
ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba
zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi
normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya
tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara
dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma
kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi
yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai
taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da
birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke
ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya
kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau,
Ta bangaren halaye kuwa Omar kusan 95% yake,baya shan komai,baya ko saurarar mata
duk yanda suke rubibinshi, yama tsani yan mata shi,basa gabansa,baya shiga harkar kowa,bai
damu da matsalar wani ba,sai in ka nemi taimako wajensa zai baka,matsalarsa akwai zucia da
saurin fushi,ga girman kai,da rashin fara'a dan baya daria ba komai ke sashi murmushi ba.yana
da tausayi in yaganka cikin masifa amma shi baya shiga rayuwar wani bare ya kai masa agaji
sai ka nema zai maka,baya son surutu da hayaniya.yayi karatunsa na degree a London ya
karanta economics,yanzu yayi masters tuni.bangaren addini kuwa ba a cewa komai yana da
haddar ya kai izu 40,banda sauran wasu littafai na addini daya haddace,kuma ba laifi yana aiki
da ilminsa,yana kuma addini sosai,baffa ne ya matsa masa kan lallai sai yayi aure,yana 30yrs
ya nemo masa auren yar gidan wani governor wato sahar,yar boko ce itama dan medicine ta
karanta tana aiki a wani babban hospital dake abj,tana da private nata guda biyu..
Sahar kyakyawace ba laifi chocolate ce amma tsabar body cream ta dawo fara tas,ga daukan
wanka ammafa in zataje aiki.bata ganin kowa da mutunci ganin tana juya naira,motocinta 4 laba
laba,duk ma'aikantan gidansu tsoronta sukeyi,sabo da cin mutunci,bata da tarbiya,ba kamun
kai,dan a wurin aiki har tafawa take da maza,give me five saleem bam kaji sun kashe.
Haka maza suyi ta yaban kyanta da turarenta gaskia kin hadu,mijinki ya more,tayi ta zancen
batsa da mazan aiki.wasu kamilallun matan ma'aikata sunsha bata shawara amma taci musu
mutunci,
Tsiyar sahar bata tsaya nan ba har kan mijinta Omar bata ganinsa da gashi ko kadan,bai San
mene aure ba,bai San dadinsa ba,bai San love ba bai tabayi ba,dama baffa ne ya lika masa
dole,
Sahar addini bai dameta ba,ita kawai kudi da aikin gomnati,ga kawaye marasa tarbiyya,a
rana sai ta fita sau biyar kullum bata gida,da anyi magana tace aikinta.
Taki yarda ta haihu Sam tace ina bata shirya ba,bataso ta lalace,Omar ma sabo da kudinsu ta
yarda ta aureshi,dan ita burinta kudi.Omar gajiya yayi da bakin cikin halinta ya tafi London ya
huta,ita kuwa ko a jikinta,ya mata fada da nasiha taki ji,bata bari ya kusanceta sai in bukatarta
ce,ko tana son karbar kudi wajensa,shi kuwa baya sonta bashi da feeling a kanta yanayi ne don
sauke hakkin dake kansa,shi yasa ma yake tunanin anya yana da lafiya kuwa danshi bai taba
jin sha'awar matarsa ba Sam,mata kuma ko inda suke baya kalla bare ya gano matsalarsa.
Amma babban abokinsa sultan yace dan baya son matarsa ne shi yasa,duk ranar daya hadu
da real love dinsa zatayi busting dinsa sanannan zai tabbatar lfy yake.Omar kuwa gani yakeyi
karyane kawai.yaki yarda kwata kwata,yaje hospital da dama a turai sunce lfy lau yake. Wannan
kenan kadan daga the most handsome and sexy OMAR.
Ku biyoni readers yanzu akafara Taku har kullum
Asmahbaffa.
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
2
By
Asmabaffa
Nigeria na dawo abuja garin da ake ji da naira.wajen gari na fita gidajen masu
rangwamen gata,wanda suke kaiwa da kyar suna yar sana'a,da suke haya a wajen abuja Kafin
a karasa cikin garin abuja,dai dai gefen titi na hango wata yarinya tana saida apple da dafaffen
kwai,a titi take bi tana mikawa ta window na mota,apple and egg tana bi mota mota a round
tana dagawa masu mota domin su siya,
Kallonta nayi sosai yarinya ce yar kimanin 15yrs ta hada gumi sakamakon ranar da ake
zabgawa,sanye take da wata yar doguwar Riga ja da kadan ta wuce gwiwarta,rigar taji jiki ta
kode ta jeme,ta fita daga hayyacinta da dankwalinta baki,amma kana kallon yarinyar fes da ita
rigar kar kar ba dirty,da gani gidansu da tsabta,
Yarinyar na kurawa ido na kasa dauke idona sabo da tsananin kyau da tsarin sura na
wannan yarinya,kerarriyar yarinyace me cikar zati,dan kana kallonta Kazan ta hada jinsi da
larabawa basai an fada ma ba,da gani nan gaba za ayi mashahuriyar budurwa,duk motar data
wuce sai ta kalleta wasu har tsayawa sukeyi suce suna sonta,
Santala santalan kafafunta na kalla na jinjina kai,sama nayo naci karo da makeken hips dinta
da tudun mazaune wasu das dasu,nan nace to fa yarinya karama kenan nan gaba fa za asha
kallo,ina yin gaba naga idon garin wato boobs dinta suma dai basu girma ba kananu yanzu
suke tasowa nan gaba suma uhmmm...wuyanta na kalla naga wasu yan digo digo baki sun kai
biyar Wanda ake Kira tawadan Allah, wuyanta mul dashi kadan ake ganin kashi,
Fuskarta na tafi sawa ido,bakin nan na hango light pink dan cut,lips masu matukar
kyau,hakora kanana tas farare,hancinta na kalla me kyau da tsayi gami da tsini amma ba mai
yawa ba,da digon baki dis a kan hancin Wanda ya kara kawata fuskarta,idanu dai dai ba manya
ba ba kanana ba farare tas kamar madara,
Gashin kanta Wanda yayi luf har gaban goshinta ga saje kadan yala yala baki sidik,bata da
girman goshi lol,gashinta ta tubke jelarsa har ya wuce tsakiyar bayanta,
Sa idona bai tsaya nan ba readers sai Dana kai kallona wajen kunnenta kanana masu kyau,fara
ce kar,rana da wahala ma yasa ta danyi duhu a hakan.tallanta kawai takeyi a titi bata sauraran
kowa,wasu dan kyanta suke siya,wasu dan ta kulasu su sami damar lalata mata rayuwa,shi
yasa bata kulasu sam,dan haka tana zuwa talla take siyarwa,
Wata yar yarinya na gani baza ta wuce 9yrs ba me kama da me tallan apple da egg ita
amma sai dai a kirata da light chocolate dan ba fara kar bace,hannun me saida apple ta kamo
tana anty IKLAS kizo inji ummi tallan ya isa,wai yunwa mukeji ki dafa mana abinci,
Hannun yarinyar iklas ta rike tana murmushi ok suhaila dama yanzu zan dawo gida,ya
schl?normal anty,ance ban biya kudin books din da akace mu siya ba,ranar Friday za a rufe.
Sorry baby akwai kudin zan baki gobe never mind,botikinta ta dauka dan tuni egg ya kare
apple saura Leda biyu,gida suka wuce ita da kanwarta,nima na rufa musu baya,tafiya sukayi ba
wani nisa da titi wani gida suka shiga Wanda zai iya zuwa na 3 a lalacewa kaf gidajen dake
unguwar suna cikin mafi rangwamen gata.
Gidane na bilon siminti amma kamar kango tsabar lalacewa,daki biyu ne,sai toilet Wanda
rabin katangar toilet din na karfen langa langa ne,sai kitchen dinsu suma na langa langa
ne,gidan ko ina da simintinsa a dabe yake,dakinsu kuwa duka ledar tsakar dakice kusan
sabuwace ma,abin mamaki wani bed na gani na gaske kalar na kasar waje yasha katuwar
katifa,ga wata spare katifa jingine a bango,gefe guda wasu kayan kitchen ne dana cin abinci na
gaske masu tsada a katon kwali har biyu,gefe can wata sip ce itama kalar bed din da gani
ansha wuya wajen shigarta dakin,rabin sip din kayan sawarsu rabi kuma suke boye kayan
abincincinsu da sauran tarkace,Duk a daki daya,daya dakin kuwa Leda ce da center carpet me
kyau kuma da gani me tsadar gaske ne,nayi mamaki,wasu kujeru na gani na alfarma 3 seater 2
seated da 1seater,da badan ginin marar kyau ba da palon yafi haka kyau,wata TV na gani
katuwa me kyau kamar plasma tsarinta girke a kan wani glass TV stand,
Gidan ko ina kal kal yake sai kamshin turaren wuta ke tashi,wata dattijuwa na hango a zaune
tsakiyar tabarma tana fere doya,na kare mata kallo wannan sai dai a kirata kakarsu amma ba
ummi ba da naji sun fada,jikinta suka zube wash ummi tsohuwa me ran karfe,mun gaji,ko
wacce tana ta dakuna tsohuwa tace dalla Ku dagani zaku karasani,sai warin rana kuke,ke
faratu tashi ki mana girki,kiyi wanka ki huta,gashi na rage miki hanya.na fere doya,na miki
jajjage,to ummi na gode,bari nayi sallah tukun.
Sallah tayi ta shiga kitchen.faten doya ta yi musu sannan sukaci,wanka tayi ta shirya kanwarta
suhaila ta rike hannunta sukawa ummi sallama ummi mun tafi islamiyya daga can zamuje
kasuwa domin saro apple zamuje ma gidan gona siyo kwai sabo da siyarwa gobe,addua ta
musu suka wuce.
Wai wace IKLAS NE
Babansu abdurrahman saddiq dan asalin kasar libiya ne,balaraben libiya a can wani kauye
a yankinsu,ruwan sama aka musu mai matukar yawa Wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a
yankin,da kyar aka samu aka ceci mutane ba Sufi 10 ba,wasu kuma mutum biyar suka
taimakawa Kansu da rakuminsu suka yo hanyar Nigeria,su kwana su tashi a sahara har Allah
ya kawosu Nigeria,har suka sauka a jigawa state da rakumansu,maza ne su biyar,haka suke
fadi tashi a kauyukan jigawa,ciki harda abdurrahman saddiq babansu iklas kenan,ana haka har
mutum biyu suka rasu suka rage saura 3,sauran biyu suka koma libiyansu suka bar
abdurrahman a Nigeria,yasha wuya yasha talauci a kauyuka,har ya fara Aron gona yana
noma,da haka yaci gaba har ya fara samun kudi,ya mallaki gonaki, a wani kauye dake cikin roni
nan ya hadu da abu bafulatana wato Babar su iklas,kishiyar babar abu ce ke gallaza mata
kasancewar kafin Baban abu ya rasu sun rabu da babarta,shi yasa ya kwace yarsa abu ya
bawa matarsa riko,
Nan abdurrahman ya fada sonta ya tausaya mata,da haka ya dage saida aka aura masa
abu,bayan aurensu arzikin abdurrahma ya shahara ga kauyen ana masa sharri dan
mafiya,haka abu ta haifi iklas wacce sak babanta ta kwaso,daga nan ya kwashesu suka koma
abuja da zama tare da Babar abu wato hajia asmau,wacce yanzu suke hannunta kenan,suke
kiranta da ummi tun tasowarsu sukaji mamansu da abbansu suna kiranta ummi shi yasa suka
saba suma.har yau suke ce mata ummi,
Abdurrahman sai da ya mallaki gida a abuja ga har noma ta haka ya biya musu aikin hajji
sannan ya ziyarci kasarsa ya nunawa matarsa yan uwansa maza guda biyu da suka rage a
duniya,haka gaj asmai ummi kenan,duk ya hada musu hanyar da ko sabo da halin rayuwa zasu
iya Neman yan uwansa,
Bayan suhaila Nada shekara 7 da haihuwa abu maman su iklas da mijinta abdurrahman
Baban su iklas suna hanyar dawowarsu daga jigawa zuwa abuja suka tafka hatsari inda Allah
yayi musu rasuwa,dukansu,anyi jaje da jimami,yayinda kakarsu ummi ta kira yan uwansa ta
sanar musu,har Nigeria sunzo,kuma sun bawa su iklas nasu gudunmuwar,dan suma ba yan
uwansa na jini bane,dangi ne kawai sama sama shi yasa basu dauki su iklas ba suka koma
kasarsu,
Ummi kakarsu iklas ce taci gaba da kula dasu,tana sana'ar saida kayan miya,irin su
citta,maggi,manja,wake,barkono etc,har abincinsu ya kare,kudin hannunsu ya kare,komai nasu
ya kare kat hattana kudin makarantar su babu,lokacin iklas tana ss1,suhaila na primary 2,da
haka suka yanke shawarar saida gidan da suke ciki,haka suka siyar da gidan Ganin matane
yasa aka cucesu sosai aka siyi gidan arahar banza,
Da haka suka tashi suka koma wajen abuja gidajen dake kusa da garin abuja kafin a karasa
cikin city,anan suka sayi wannan gidan da suke ciki,an musu tsada sosai anan kudin ya kusa
karewa,shi yasa suka ebo wasu kayan na gidansu da suka siyar Wanda zasu iya amfani dasu
suka zuba a gidan da suka siya,
Sun biyawa suhaila kudin makaranta tun daga primary 2 zuwa jss3 gudun kar a sami
matsala,abinci suka jibge komai da suke bukata sai da sukayi dai dai kudinsu,har da jarin kwai
da apple,ita kuma ummi takeyin sana'ar siyar da kayan miyarta a gida,
Islamiyya ma sun biya kudinta na shekaru,iklas ma an canja schl me saukin kudi,ta biya
daga jss2 har zuwa ss3.ga saida apple da egg,tana dawowa daga schl zata wuce tallanta, zuwa
4 su tafi islamiyya,haka suke rayuwa har yanzu sun kwashe 2yrs.
Yanzu komai ya dagule musu,da tallan da iklas ke zuwa da sana'ar kakarsu ummi suke ci
suna sha,da sauran abubuwan rayuwa Wanda ya zama dole.
Iklas bata da burin da ya wuce tayi karatu me zurfi tayi aikin gomnati dan ta tallafawa
kanwarta da ummi,bata da burin da ya wuce tayi aikin goMnati,gashi aikin gomnati na burgeta,