Showing 93001 words to 96000 words out of 107121 words

Chapter 32 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

7341


dakin Omar,suhaila ta gani da suleim zazu tafi schl,Anty ina kwana suka gasheta sukayi gaba
da gudu,ita kuma ta fada room din Omar a kan bed ta hangoshi yana ta baccinsa cike da
nutsuwa,komawa tayi ta sa key a kofar saboda tsaro.

Tana dawowa ta haura saman bed din tare da rungumeshi kam tana shakar kamshinsa tare
da manna masa kiss a goshi,a hankali ya bude idonsa masu matukar kyau,ganin Gomnati a
jikinsa ba karamin farin ciki yayi ba.

Ba tare da bata lokaci ba shima ya Kara manneta a kirjinsa wifey I miss u da kyar nayi
bacci jiya,baki zo ba har jiranki nayi,miss u more honey nayi niyyar zuwa bacci ya sace ni,cikinta
ya Shiga shafawa ya gudan jini na lafiya yake?haushi Iklas taji yace gudan jininsa wato ya
kwace mata mijinta, Shinema gudan jinin naka,ni wlh shi yasa banso haihuwar nan ba,yanzu sai ka dinga
daukansa ni kana shareni,dariya Omar yayi me kishi da danta haka akeyin Maman babyn?ta
tsani danta? Kece fa zuciyata gaba daya,cike da shagwaba tace to ai jini yafi zuciya
muhimmanci shine zaka ce masa gudan jininka ni a bani zuciya,saboda ka samu da,fari tayi da
ido Wanda ya susuta Omar lokaci guda tare da cewa dadin abin ai kafin ayi dan ni aka
samu,kuma ai da nane.

Dariya Omar yayi kinsan me kike cewa kuwa wifey? Wannan shine ba kano ba birni,ba
cinya ba kafar baya, shi yasa tunda ke danki ne kinga shi gudan jinina,ke kuma zuciyata kinga
ai kun kwaceni du ke da baby,ni dai Allah ban yarda ba cewar Iklas ,ok to a bashi zuciyar ke
gudan jini ko?kafada ta make abinda nafi so zuciyarka shine zaka ce a bashi ita,dariya Omar
keyi yace to na bashi liver ta,da Sauri tace tab bai isa ba bazan yarda ba,Kasan kuwa
muhimmancin liver da zakace a bashi ita yama fini kenan sosai fa ina laifin ka bashi yar
madaciyar jikin hantar taka tunda shi yaro ne,ko ka bashi timbi ko hanji,

Fashewa da dariyar shiriritar Iklas yayi tare da kara kankameta sosai abin dariyar Gomnati da
yawa yake, tafin hannunta ya mannawa kiss yana bin hannun da kiss ya gangaro wuyanta nan
ya fara lasar wuyanta cike da salon kwarewa tattare da nutsuwa a hankali ya dinga sarrafata
tunaninta ya gushe nan fa suka dinga baje harka,bayan sun nutsu wanka sukayi cike da
nishadi,Omar na ta zuba mata albarka, Iklas dinsa dabance,tana shagwaba shi sai abinda yake
so,gashi tana fahimtar matsalarsa ko bata so sai ta faranta masa,yanda yake bata wahala bata
taba nuna gazawarta,
Burinta taga Omar kullum hankalinsa kwance,gaban kowa tana nuna rashin kunyarta dan ta
faranta masa.

Har kaya ita ta sawa Omar tare da shiryashi suka fito fes fes dasu,Ummi bataga Iklas ba
tunda taga haka to lallai Omar yana gidan,Iklas ta birge Ummi da take kula da mijinta,
Suna hirarsu kasa kasa murmushi dauke a fuskar Iklas suka shiga wajen Ummi suka
gaisheta Ummi tana in kaga Zara kaga wata,suna ta murmushi suka je wajen Mama, tana

ganinsu haka taji dadi a ranta amma sai ta tamke fuska ta fara yiwa Omar fada Dama nasan
baka jin magana Babana saida ka kwana a gidan nan sabo da mun dauko matarka, ka kiyayeni
fa,jikinta ya fada haba Mama nifa gwara ki hakura ki kyaleni dan Allah,Iklas ce tayi magana cike
da marairaicewa Mama kiyi hakuri ki kyaleshi.ai na kyaleshi Iklas ya zanyi da shi ya fiye
rikici,that's my Mum cewar Omar.

Kuje ga breakfast can a dining,Mama ta kara da cewa Iklas yan uwanki na kasar Libya jiya
sunyi mana waya ni da Ummi,nayi magana dasu cikin harshen turanci duk da ba wani iya
turancin nan nayi ba sosai dama Abdallah ke koya min,sunce zasuzo ganinku nan da 3days sai
Ku kirasu kuji komai,number tana wayar Ummi,sosai Iklas take Murna ko ba komai yan uwansu
zasu zo dangin mijinta su gansu asan suma suna da gata.

Omar ne ya kira yan uwan Iklas a wayarsa suka tabbatar masa nan da 2days gasu nan ganin
yaransu,ai kuwa Saturday na zuwa aka tura driver ya daukosu maza su biyu mata biyu,dayar
macen Babba ce sosai ta manyanta,dayar kuma budurwa ce yar gidan best Frnd din Baban
Iklas me suna KHAIRAT. zankadediya itama,part guda Baffa yace a ware musu shima yana nan zuwa next day zaiga
yan uwan matar dansa, Iklas ta rasa inda zata sa kanta sabo da murna,su Sadiya ma sunzo
sun gaishesu,bangaren Hajiya Rahina ma an rakasu sun gaisa,ba tare da ta nuna musu wani
dan hali ba,su Sultan,Raj,yan uwa da abokan arziki duk sun zo sun gaishesu,haka frnds din
Iklas suma,Maman saleem,saleem da matarsa duk sun je.
Su Kansu mutan libiya sunji dadi sosai,

Khairat tunda Allah yasa tazo gidan tayi tozali da Omar mijin Gomnati taji duk duniya ba
Wanda take so da muradi sai shi,dan haka ta like masa ta manne masa,shi kuma ganin yan
uwar abin kaunarsa ce Gomnati Iklas sai yake kulata yana karramata,itama Iklas data ga haka
bata damu ba tayi tunanin kawai saboda mijinta ne shi yasa take matukar ji da ya Omar,Wanda
ita Khairat balarabiyar kasar libiya Sam ba haka bane a ranta tsabar son Omar ne yayi mata
yawa,Wanda tana jin baza ta iya rayuwa ba sai da shi,dole sai dai itama ya aureta tunda
musulunci ya bada damar auren mata har hudu,
Shi yasa take Neman hanyar da Omar zai fada tarkon sonta, ita tasan Iklas din Omar ta fita
kyau amma dole ne ta sameshi ya aureta.

Shi yasa khairat Sam bata zama a bangaren da Baffa ya basu kullum tana wajen Iklas
saboda taga Omar kullum yana manne da matarsa,shi yasa take nacewa kusa da Iklas,Khairat
taga Iklas yarinya ce shi yasa take so tayi mata wayo ta kwace mijin,dan burinta ta dauke Omar
su koma kasarsu da zama,Khairat shekarunta 28 dan haka ta girmewa Iklas wacce kwanan nan
ta cika 17yrs kwata kwata.

Shi fa Omar Khairat ta fara damunsa tana shiga rayuwarsa shi da Iklas, ba dama su kebe
waje daya sai tazo ta takura musu,dan dai kawai dangin Gomnati ne da tuni yaci uwarta an
wuce wajen,
Amma dannewa kawai yakeyi yana biye mata ganin Iklas bata Nuna damuwarta ba,

Idan sauran bakin sunce time yayi ya kamata su koma kasarsu fafur Khairat ke hanasu wai
a bari suga yar uwarsu ta sauka lafiya wato Iklas,Ummi da Mama sun gano take taken Khairat.
Omar yaje gidan Sadiya da Aisha ba tare da ya Sanar da kowa ba,ya musu Sulhu sosai da
nasiha sosai sun samu yanci mazan nasu sun fara canjawa inda suma su Sadiya suka kara
jajircewa wajen kula da miji,har makaranta ta koyon girki da dabarun zaman aure suka shiga.
Har sauran kannansu sun biya musu sun shiga kuma suna ta kula da tarbiyar sauran kannensu
tare da yiwa Ummansu Nasiha kuma ta dauka.
Har wajen Baffa suka je gaba dayansu har Umma Rahina suka bashi hakuri kan abubuwan
da suka shuka.

Haka Maman Omar ma sun bata hakuri Aisha ta haifi yarta mace me suna Mufida, Sadiya
kuwa anayin Hutu tazo ta dauki Suleim da Suhaila Suna gidanta suna jin dadinsu dan Alhaji
balarabe kashe musu kudi yakeyi yana shagwaba su.

Mijin Aisha ma Nasihar iyaye data Omar sun jawo ya nutsu ya canja hali,sai kiba da kyau
da su Sadiya suka karayi. Kullum sai sun Sawa Omar albarka, har Baffa da Umma Rahina suka
fadawa abinda Omar yayi musu,haka Mama har Godiya suka Mata.

Iklas ta shiga damuwa akan Khairat tana shigewa mijinta tayi hakuri tayi kawaici ta gaji
haka.musamman da taga Omar na biye mata,shima Omar Haushin Iklas yakeji yaga kamar ta
daina sonsa bata kishinsa,tana ganin yanda Khairat ke manne masa amma bata nuna
komai,shi kuma kara yake mata kawai,baya ga haka da tuni ya kwadawa Khairat maruka yanda
take zama tana goga masa kafardarta a tasa, tana taba jikinsa ko ta rike hannunsa in tana
masa magana.ga shi kullum shigar banza takeyi a gidan ko kunyar su Baffa bata ji.
Kamar kullum yau Omar da Iklas suna zaune a palon Mama sun baje suna cin abinci
Khairat ta fito taci kwalliya ta matse cikin Riga yar fingila da wando sai kamshi takeyi, wajen
Omar ta nufa tare da zama kusa dashi tana gugan jikinsa, ran Gomnati yayi mummunan baci

Kishi ya tashi dama ta gaji da halin Khairat,Iklas wani azababben kishine ke azalzalarta
kwakwalwarta ta dau zafi, zuciyarta tafasa kawai takeyi,Omar ya ga halin da Iklas ta shiga
amma yace me yasa tun farko bata dakatar da abinba.
Iklas tana so taga Omar ya matsa amma taga cin abincinsa ma kawai yakeyi. Iklas a ranta
tace kut inama ina da lafiya da billahillazi sai nayiwa matar nan abinda ko a mafarki baza tayi
sha'awar zuwa Nigeria ba,amma zanyi maganinta, maganin shege sai dan banza.
Gani tayi Khairat ta zuba lemo a glass cup za ta kai bakin Omar,cikin Zafin Nama Iklas tasa
hannu ta fisge cup din tare da watsawa Khairat lemon a fuska, ta mike tsaye tare da nunata da
yatsa a tsawace tace get out before I scatter your skull into peaces, dama ga su da tsoro Da
Sauri Khairat ta fice,Omar zaiyi magana Iklas ta daga masa hannu ya Isheka ya Ishe.....bata
karasa ba mararta ta mirde,ta kulle tare da zamgewa da cakudewa. Rawa jikinta ya fara Kar kar
kar....... Gumi ne kawai yake keto mata,wani azababben ciwo taji Wanda ko a labari,,films,da
mafarki bata taba sani ba,mararta ta dafe ta daddage iya karfinta cikin siriyar Muryarta ta
tsandara Ihun daya fito dasu Mama da Ummi daga kitchen a guje.

Sulalewa kasa tayi tana kuka wayyo Allah na Ku taimaka min,a kaini asibiti na mutu
acan,tuni Omar yana kanta shima hawaye yazo masa yana tunanin idan ya rasa Iklas tasa ta
kare.

Iklas ta rike Omar kam yana kiyi addua pls yanzu za a tafi asibiti,tana kuka ta fara La'ila
ha illalla la'ilaha ilallah taana rerawa ita kadai yanda zakuru sukeyi kawai kirjinne da bata
duka,tuni su Ummi sunyi waje kiran driver,Mama na hada kayan haihuwa,
Suna cikin mota tana cinyar Omar kwance su Mama a gefe,Ummi tace dan Allah Iklas ki
rufemana baki haka akanki aka fara haihuwa,Omar shafawa Gomnati marar yakeyi yana lallashi
tare da tofa mata addua.

Ciwon ne ya lafa mata suna mota driver na tsala gudu, mikewa zaune Iklas tayi tana goge
gumi tana wash naji salama,suna shiga asibitin ciwon ya dawo yafi na da,cije baki Iklas tayi
tana Bala'i.....Bala'i....gashi......nan.....Omar sai hawaye yakeyi yanda Iklas ta haukace gaba
daya gashin kanta kamar daga bakin kura ya fito,yanzu bata ma San me take cewa ba,kuka
takeyi tana nishi tana Ku miko min danwake na kwandala,abani ko dan malelene,haka aka
turata a gadon asibiti har dakin da aka kwantar da ita,patients da malaman asibitin kowa
dariya sukeyi da tausayin Iklas yanda take fadan abu barkatai.

Ummi ce ta kalleta tace yar bantan Uba taji wahala, Mama tace sannu yanzu Likita zaizo,
Iklas ta Kalli Mama ta fara tooooooo.......yayi sauri yazo yamin Allura ta kwandala. Shi kansa
Omar ta bashi dariya dannewa yayi.

Ummi ce tsuguna a jikin gadon ai kuwa Iklas Neman abin rikewa takeyi ta tugewa Ummi
dan kwali ta jefar,da Sauri Ummi ta matsa ta dauki abinta tana daurawa tace harda ciremin
dankwali?Iklas tana cijewa tace idan....dan kwalin na kwandala ne to a bani......lallai.... Nace a
bani. Nurses da likitoci sunzo sunce Kaine mijinta? Da sauri Iklas tace yana ina bakin mugu
azzalimi,ta fashe da wani irin kuka me karya zuciya.Omar hankalinsa ya kara tashi gashi kusa
da Iklas hannunta cikin nasa amma take nemansa bata ganeba.




AsmaBaffa

Ku kwashe min da tafi readers.


Tnx all nayi delay ban cika alkawari ba, amin afwa nima ko ta kwandala ce.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

190-195



By
AsmaBaffa





Ciwon daya taso ne gadan gadan yasa Iklas ta daina kuka sai muzurai da cijewa kawai
kuka ya gagara,likitoci sun bazu a kan Iklas yayinda Gomnati ke sambatu karfinta ya kusa
karewa a hankali tace doctor kayi min Allurar guba tunda dai haihuwar nan baza ta zo ba,Omar
ya rude addua kawai yake tofa mata, Iklas tace Ku fadawa mijina ya yafemin bazan warke ba,irin wannan ciwon nasan sai dai na
tafiya lahira,Omar ne ya rungumeta yana hawaye am sorry wifey insha'allah zaki tashi,kan
Omar ta shafa tace kamar Omar dina,nine matata Honey dinki ne,kayiwa Mama biyayya
sosai,idan baka bita ba dole kaci wutar jahannama,domin bakusan Haihuwa ba. Sakinsa tayi,likita yace ya basu waje ga wani sabon ciwon daya taso mata,Ummi tace kiyi fa
a Hankali Iklas Maza suna jinki, da karfi tace Maza? Maza basu San Haihuwa ba....wayyo Maza
basu San Haihuwa ba.
Likita ne yace su Ummi su fita duka zasuyi Aiki,Omar yace bazai yuwu namiji ya duba masa
mata ba,dole suka kawo mace da mata nurses,harda shahararriyar nurse din nan
Subby,Maman waleeda ma anyi mata Transfer Hospital din ita ce ta karbi haihuwa da
gaggawa,Subby ta Daura drip,Hajiya Jamila,Jamila Sule duk a asibitin suke aiki sai kaiwa da
kawowa sukeyi wurin Iklas,

Tun safe ake abu daya Har yamma Iklas bata haihu ba,bakar azaba take sha kawai,Subby
tayi gumi sosai,Iklas kuwa da taji shuru sai tace kuji na fada muku bazan Haihu ba kawai kuyi
min Allurar guba,Omar ya rasa Inda zai sa kansa,Sallah sai da yayi rafkannuwa da yawa,
Babbar likita King ita ta zo ta kawo wasu dabaru cikin Ikon Allah 5pm kan yaro ya danno
kai,Iklass ido yayi jajir yayo waje,ansata nishi ana fush,babu bakin magana ya mutu murus,nishi
ake ta sata suna taimakawa,Rabin Rabin jikin Baby yayo waje aka taimaka ya fito du da komai
a hannun Subby, Zukeken Namiji ta santalo me kama da Ubansa,lafiyayye katon gaske, yaro na fitowa Iklas
ta sume, sai da tayi 5mnt ta farfado,nan akayi mata Allurai kala kala,nan danan nurses suka
gyara yaro tsab,sannan aka fara yiwa Iklas aikin fito da jinin cikinta tas,tare da gyarata ta Huta
sosai sannan Ummi ta shigo ta taimaka mata a bayi tayi wanka sosai ta gasa mata ko ina nan
ma Gomnati harda kukan ruwan zafi,kafin su fito room din sai kamshine ke tashi,abinka da
private hospital me tsadar gaske kai ka rantse Hotel ne,baza kace a asibiti kake ba,Iklas ita
kadai ce a room din ba a hada mutane room daya,kowa da nasa.

An canja bedsheet ma sabo,tana fitowa suka fada toilet ma'aikata suka gyara
shima,kamshin dadi ne kawai ke ratsa ko ina,
Iklas ta hana a fadawa Omar ta haihu wai sai ta shirya,a cikin jakar kayan haihuwa harda
body lotion da su turare,da man gashi da handdrier,wata nurse da tazo domin sauran sun
tafi,tace lallai haihuwar fari ce wannan shiri haka.

Aikuwa Iklas ta busar da gashinta da hand drier ta tajeshi tsab ta shafeshi da man gashi me
kamshi,da turaren gashi ma aka shafa,tea ta sha me kaurin gaske,sannan taci kaji da sakwara
miyar egusi,Omar kuwa tuni Subby ta fada masa ta Haihu lfy amma ance ya jira za a kirashi,ai
kudi ya zaro wanda bai san yawansu ba ya bawa Subby yar Albishir,sauran nurses ma kawai
kudi yake ta fella musu,

har yau shuru,har yayi Sallar isha yana jira,Iklas zama tayi ta shafa body lotion dinta me arnen
kamshi,
Ta sa Wani Sabon dinkin doguwar rigar material black and milk yayi mugun mata kyau,sama
ya dame kasa ya bude,Gomnati fa ta gaji amma haka ta dage tana kwance ta shafa powder
ta,ta sa red jambaki,kamar ba ita ta haihu ba,
Dagwas da ita tana kwance Ummi ta mika mata turaruka ta shafa wasu ta fesa
wasu,kamshi takeyi na fitar hankali,jariri kuwa tuni Mama ta goge masa jiki da zaitun bayan ya
dan dade akayi masa wanka tas dashi aka shafa masa lotion irin na jarirai masu matukar tsada
da kamshi Omar ne ya siyosu tun cikin Iklas na 7mnths,kaya masu kauri da pampers aka sa
masa suma kayan sai da Mama ta shafa musu turare kafin a sa masa

Yaro gwanin sha'awa,sai da komai ya zama normal sannan a hankali Iklas tace Ummi a
kira min ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login