Showing 63001 words to 66000 words out of 107121 words
Chapter 22 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
kawoka fitar min a daki,ke kuma kin tsaya min a kai wuce ki bani waje.a bed
dinsu ta zauna ta fara cin abinci ta ragewa Ummi nata.
Omar fa shi ya hadu bazai cewa Iklas yana sonta ba direct kawai zata gani in action, idan
tafiya tai tafiya,ya tabbatar ta gane sai kawai a zarce da I love u. Fadar wance sonki nake,ko ina
sonki da farkon farawa to kauyancine kajifa Omar. Iklas lallai in hakane jira ya ganki.
Asmabaffa tana jinjina ga masoya novel din nan a duk inda suke. Allah ya saka muku da
Alkairi.â“‚â“‚â“‚
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
â“‚â“‚â“‚
130-135
By
Asmabaffa
Misalin 10am kowa ya gama shirin daurin aure maza da mata cikin kwalliya suke kowa
yana ji da kansa,
Iklas tasan Ya Omar farar shadda zai sa tunda sanda ta kai masa breakfast yana shiri,yasha
kyau tsayawa fadar kyan Omar bata baki ne
Iklas ma wanka tayi ta shirya cikin farar shaddarta kwal,sai kyalli takeyi taci dauri da
dankwalin shaddar,Ummi ce tace haba Iklas kefa matar aure ce karki manta ki dauki
mayafi,fafur Iklas taki yarda ita ba fita zatayi ba baza ta sa mayafi ba,
Part din su amare ta wuce,basu mata komai ba sabo da gargadin Umma,kallon yan mata
taje yi,itama ana binta da kallo tasha shadda me tsada,wasu cewa sukeyi ko yar Gonna ce,
Sadiya amarya Iklas tasa ta fara linke mata kayan da ta sa,kafin daurin aure,ai kuwa ba
musu Iklas ta shirya mata komai,Aisha ma sai da ta aiketa wajen Umma Rahina ta kai mata
wasu plates,
Tana tsakiyar yan mata ana hira da ita tana tofa albarkacin bakinta cikin manyan mata,
Sadiya ce tayi magana pls Iklas a fesa roomfreshner a waccen part din an daura aure
yanzu angwaye zasu zo mana.
Nan ma da sauri Iklas taje tayi yanda tace,ta dawo kamar yanda yan mata ke kara goga
powder da gyara kwalliya haka Iklas tayi amfani da kayan kwalliyar Sadiya tayi kwalliya,
Duk mutanen wajen kallon Iklas sukeyi duk Inda ta juya,tayi kyau ga iyayin tsiya gareta
kamar babba,shi yasa suke kara mamakinta.musamman in tana tsara zance da kawo shawarar
dabarun zaman aure,
Aisha ce tace Iklas jeki ki bude palon gasunan sun zo,sosai suke mamakin Iklas dama haka
take da saukin kai da ladabi,Iklas kuwa komawa tayi ta bude,ta fito zata dawo ta hango Omar
da Sultan sai Raj da sauran frnds din Omar da yawa,
Ido suka hada,da ido ya mata alama ta koma ciki,wajen su sadiya ta koma,bayan Omar ya
raka frnds nasa sunyiwa mutan gida Allah sanya alkhairi rakasu yayi suka tafi,
Iklas ya kara gani this time around da gyale fari jikinta maza damkam angwaye biyu ko
wanne da abokansa sun zo,komawa tayi da nufin shiga palon da angwaye suke,ji tayi an fisgota
sai da ta fada jikinsa,kamshin turarensa ne ya sa ta gane Omar ne,har part din Mama ya jata,
Warning ya mata kar ya kara ganinta a waje,hakura tayi ta koma cikin dakin Ummi tayi
kwanciyarta ta dinga bacci abinta.
Sai da su Sadiya suka kwashe kusan 1wk suna biki,ana gama shagali aka kai ko wacce
hadadden gidanta,aka barsu daga su sai halinsu.
Koda Babar saleem tayiwa Ummi maganar saleem yana son Iklas hakuri Ummi ta basu ta
sheda musu anyiwa Iklas miji,har auren Iklas ta fada mata, saleem ya shiga damuwa sosai jin
labarin Ashe an Dade ma da yiwa Iklas aure, amma daga karshe ya fawwalawa Allah.
Baffa ne ya kira Omar ya bashi Umarnin lallai ya maida Sahar dakinta,sabo da baban
Sahar yana ta bashi hakuri saboda Sahar ta dami Daddynta da naci,su kuma suna son
yarsu,farin cikinta suke so,shi yasa Sahar ta lalace da yawa, Omar kamar zai mutu har zazzabi
yayi,yace wlh bazai je gidansu ba sai dai a fada mata ta koma,Sahar murna tayi tace ko dan
naci uban yarinyar nan bari na koma,tattara kayanta tayi ta koma gidan Omar,gani tayi komai na
gidan an canja new kamar ma ba gidan ba,tasha mamaki a ranta tace Ashe dai ya damu dani.
Iklas kuka takeyi kullum an maida Sahar ta zama kishiyarta,shike nan zasu dinga kwana da
Omar.
Ummi da Mama ke lallashinta amma kullum bata da sukuni danma tana zuwa schl da
damuwarta sai tafi haka,
Tunda Sahar ta koma Omar bai koma gidanba ko sau daya,har ta kwashe 2wks amma mijin
nata shuru,Mama ta sa Omar a gaba kullum fada takeyi ya koma gidansa kar ya shiga hakkin
Sahar amma yaki,ko ta koreshi wani gidan yake komawa cikin jerin gidajensa.
Satin Sahar 3 da tarewa Baffa ya umarci mama kan ta kira Iklas Ummi da Omar,kafin ta
kirasu sai ga yan uwan Baffa Da aka daura auren Omar da Iklas sukayi sheda da kuma Wanda
sukayi wakilcin iyaye du sun hallara a falon Baffa
Omar baya gida yana Office sai a waya aka kirashi,minti kadan Omar ya Iso,Iklas sanye da
hijab anyi lukui a gaban Baffa,Haj Rahina ma an kirata,Sahar tazo don tunaninta tunda taji Baffa
ya nemeta to kudi zai bata,Sultan da Raj an cika harda sauran yaran gidan.
Duk kowa yana wajen,Omar sai mamaki yakeyi ko lfy,
Taro aka bude da addua,sannan Baffa ya fara magana,nasan wasunku basu San me yasa
na taraku ba wasu kuma sun sani musamman yan uwana da Mama,Ummi,Iklas, sai Sultan da
Raji,ga limamin masallacin da akayi a idonsa shima shaida ne cewar a masallacinsa muka
daurawa Iklas aure ita da Dana Wanda kowa ya sani wato Omar,
Omar bamu sanar maka ba sakamakon kana hali na cuta,mukace a bari sai ka warke,nan
wajen Baffa ya bada labarin kimai,shedu ma suka tabbatar da hakan,har pics da video Sultan
da Raj suka nunawa kowa.
Omar ne ya fara gani ya rasa ma me yakeji a ransa ga dadin Iklas ta zama mallakinsa
sannan ga haushin anki fada masa da wuri an ja masa rai,an barshi da damuwa.
Yana so ya danyi koda romancing Iklas ne amma ya dinga tunanin babu kyau,an barshi a
duhu maza sun tsaya masa da matarsa sunyi hira,tayi rawa a gaban maza, sai yanzu yaji ya
kara jin haushin saleem da yayi hira da matarsa,Ibzzy ma haka tab wannan duk laifin Iklas
ne,sai yanzu ya tuno yanda Iklas ba ruwanta take taba jikinsa anyhow Ashe tasan komai ita ba
rashin kunya ce tayi mata yawa ba,
Tunani ya shiga yanda zai sawa Iklas sonsa a ranta sannan asha love,tunowa yayi yanda
Iklas ta dinga raina masa hankali,a ransa yace dole na rama.Iklas kuwa dake gaban Baffa kanta
ta cusa tsakanin cinyoyinta ta dunkule wai kunya,
Sultan sai daria sukewa Omar kasa kasa.yaran Mama harda Suhaila sai jin dadi sukeyi,Haj
Rahina ce ta mike tsaye akan wannan aka bata mana lokaci,dan sunyi aure sai me,fasikan
banza fuuuu ta ja su najja suka bar dakin cike da takaici,nan take tayiwa Aisha da Sadia waya
ta shaida musu komai.Haj binta ma ta bugo waya suna ta gulmarsu ta kulla tsiyarsu idan Iklas
ta tare.
Sahar kuwa wani wawan tsaki taja hade da shewa tace ta shigo gidan indai miji ne Mara
amfani holoko to gashi nan,kizo kiji dadi mugani.ficewa tayi ta shiga motarta ta bata wuta.
Baffa kuwa kai ya girgiza yace Allah shiryeku sauran mutane sukace ameen,nan taro ya
tashi saura Mama,Ummi ,Baffa sai Iklas da Omar ba bata lokaci Baffa yayi musu Nasiha
sosai,haka Mama da Ummi ma sunyi tasu Nasihar,an yanke nan da 3days za a kaiwa Omar
matarsa,godiya Omar yayi wa Ummi da iyayensa da suka bashi Iklas amma fuskarsa a
daure.an kasa gane yanayinsa.
Iklas dadi taji kamar me zasu tafi gidansu ita da Omar dinta,shike nan itama tayi gida,sai
kaji ana cewa mun tafi gidan Iklas, ga Omar Allah dole ne ta dinga baccinta a jikinsa me kamshi
laushi da santsi,inyi girkina,inyiwa Ya Omar abinci,muyi wasanmu etc
A ranta take zancenta ta
A hankali ta dago da kanta Omar ma a lokacin ya dago caraf suka hada ido,gani tayi fuskar
Omar ba alamar Rahma,gabanta ne ya yanke ya fadi wato ma dole akayi masa baya
sonta,Inusa me wanki ta tuno zancensa sai kuma taga kamar Omar baiyi farin ciki ba it means
ma karya ne baya sonta,
Lallai dole na fara addua da Sallar dare zata fara Allah sawa mijinta Omar sonta ya basu
zaman lfy,yasa ta zame masa Alkhairi shima ya zamar mata alkhairi.
Sallamarsu Baffa yayi tare da sanar musu gobe jirgin karfe 6 na safe zai bi ya koma kasar
Russia wajen aikinsa,addua sukayi masa sosai kowa ya tafi aka bar Baffah da Mama.
Iklas na bayan Ummi,Omar na binsu a baya hijab din Iklas ya dan ja juyowa tayi amma har
yau gani tayi fuskarsa a daure,jawota yayi kiiii kamar zai doketa,ihu Iklas tayi wayyyo.....ta
tsorata ta dauka dukanta zaiyi,da sauri Ummi ta juyo ai da sauri Omar ya saki hijab din Iklas,
Ummi ta riga ta ganshi,kara juyawa Ummi tayi taci gaba da tafiya,Omar ya kara fusgo
hannun Iklas,da gudu Iklas ta kwace ta sha gaban Ummi,ke wai wacce shashasha ce,cewar
Ummi,waigowa Iklas tayi tana kallon Omar tace wlh Ummi wani abu zai min,Allah ki masa
magana zaneni zaiyi.
Ke rufe min baki marar wayo wuce muje ciki,an kusa kaiki gidansa ai kuje Ku cinye juna
ma,karki sake ko a waya ki kirani komai raunin da yaji miki,Iklas bata gane maganar Ummi ba,ta
zata zancen duka da tace shi Ummi take nufi za a ji mata ciwo.
Sun shiga room Iklas zata rufe kofa Omar ya mata irin abu da kafa ya buga kafar a kasa
kamar zai kwasa da gudu ya damkota,ai kuwa ta saki kofar ta fada dakin da gudu.
Daria Omar yayi ya wuce part dinsa,misalin karfe 1 na dare,Omar ya kasa bacci,sai yanzu
ma yake tsananin son jin dumin jikin Iklas, fitowa yayi yaci Sa'a kofar su Iklas ya ganta a bude
yanda Iklas ta barta dazu.
Lallabawa yayi ya leka dakin,Iklas da Ummi kwance gado daya suna ta baccinsu,karfin hali
Omar yayi ya matsa kusa da Iklas,a hankali ya kama tashinta ta hanyar Sosa mata kunne,
Firgigit ta bude idonta,alama yayi mata da tayi shuru,saboda Kar ta tonawa Kansu asiri tayi
luf tana kallon Omar,tasan idan Ummi ta gansu fadan har Ita.
a hankali yayi rada ki taso muje dakina,kafada ta noke tana masa nuni da Ummi, kara rada
mata yayi ni zakiji tsoro,nine mijinki,itama rada masa tayi ummi zata kamamu.
Tsaki yaja a hankali ki taso kawai malama na fada miki,ni lokacin da kike zuwa kina taba min
jiki hanaki nayi?lokacin ma fa ban San ke matata bace amma na kyaleki,murmushi Iklas
tayi,harara Omar ya watsa mata,ki taso ki biyani jikina da kika dinga taba min,mijinki ne ni Allah
ya konaki kinki bin umarnina kinji dai nasihar Ummi ko, Tsorata Iklas tayi kar Allah ya konata fa,Omar ya kara da kizo ko na kwanta anan Ummi ta
kamamu.
Da sauri Iklas tace a'a dan Allah zanzo muje ni,kar ka jawo min masifar Ummi dan laifina zata
gani,muje kawai,mikewa tayi a hankali kamar barayi sadaf sadaf suka fara tafiya,Ummi kuwa
dake bacci motsi taji kusa da ita ta farka, mikewar da Iklas tayi shine ya tashi Ummi da ga bacci,
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Iklas yanzu iya shegen da kika dauka kenan,nasan Umaru
bazai aikata ba ke kika kirashj a waya,dawo ki kwanta ko wlh na saba miki,mu zaku mayar yan
Iska, tuni Omar ya bawa Ummi hakuri yace Ummi cewa tayi nazo na dauketa tafi son dakina.
Salati Ummi ta kara saki jeka Umaru Allah maka Albarka ai nasan halinta,ficewa Omar yayi
da sauri cike da kunya.wlh Ummi bani nace yazo ba cewa yayi.....rufe min baki Ummi ta kai
mata duka dan ubanki kwanta ki rufe min baki,Iklas kija mutunci ki ina fada miki namiji ba dan
goyo bane.
Rushewa da kuka Iklas tayi wiwi take kuka haushi takeji Omar ya kala mata sharri ya zame
kansa gashi ya barta Ummi tana jin haushinta,shi kuwa ya wanke kansa tas wurin Ummi.
Gajia tayi da kukan ta shige toilet tayi Alwala ta fara nafila da adduarta Allah sawa Omar
sonta,ya sota ita kadai a duniya,Allah bata ikon yi masa biyayya yasa su zamewa junansu
Alkhairi.
Tana idarwa harda karantawa Omar suratul Yaseen Allah sa masa sonta,ita gani takeyi Omar
baya sonta shi yasa yanzu yasa Ummi tayi mata fada.da yana sonta ai bazai zame Kansa ya
kyaleta ba.
A ranta tace Allah kaimu gobe lfy Allah sai na rama zai San nice Gomnati.
Washe gari Iklas da fushi ta tashi cike da shirin ramuwa kan Omar shima sai tasa an masa
fada yaji kunya.
Pls kuyi hakuri da wannan bazan iya forcing kaina nayi muku 2 pages ba,typing akwai wahala
ga shi akwai schl ba time,Ku danci wannan tuwon Ku kora da ruwa kuyi bacci.
Tnx alot readers ..
Asmabaffa[4/10, 9:20 PM] El-hajjí ½í²¥: â“‚â“‚â“‚
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
â“‚â“‚â“‚
135-140
By
Asmabaffa
Jira kawai Iklas takeyi taga ta inda Omar zai bullo amma shuru,Mama ce ta fito cikin
shiri,tashi maza dauko mayafi zamu fita,ba shiri Iklas ta fito dauke da mayafi,driver ne ya kai su
Iklas wurin wani saloon,Mama ta biya kudin komai yanda za a tsantsare Iklas,
Komai da ya dace iyaye suyiwa yarsu Baffa da Mama sunyiwa Iklas kayanta babu banbanci
da na su sadiya sai dai color daban,na Iklas Dark brown ne komai,haka kayan kitchen Mama
tayiwa Iklas Wanda ya take nasu sadiya,kayan gyara Dana kamshi babu abinda ba a siya mata
ba wadatacce,kayan yaji da sauransu du an shirya mata part dinta,
Allah ya taimaki frnds din Iklas da wasu dangin Mama har aka gama shirya kayan Sahar
bata nan,kayan sawar Iklas du an kai gidanta an shirya mata lefe kuwa Baffa ya bada kudi
Mama ta hada mata akwati 8 ba abinda babu masu tsadar gaske da kyau domin English wears
kaf da wasu tarkace a Russia Mama ta hado su murna Iklas keyi za a sha wanka,Omar kuwa
gagarumar walima ya hadawa frnds dinsa maza a wani katafaren waje,ranar kai Iklas ranar za
ayi walima.
Omar kafin ayi jeren Iklas har ma'aikata yasa suka kara yin adon golden jikin ginin Wanda
yafi na da iri iri,ko ina sai ka rantse adon zinari akaiwa ginin wajen Iklas, komai dark brown da
Golden ne,har labile idon gari.tsayawa fada muku yanda part din Iklas ya hadu iya haduwa
karshe ya zarta tunanin me tunani,sai na gama novel din nan kaf ban gama ba, Iklas koda suka dawo ma Omar na busy bata Ganshi ba,Iklas manya tsabar gyara duk inda
ta zauna kamshinta sai yayi kusan 1wk bai bar wajen ba,ko gidan mutane taje to sai tabar musu
tsarabar kamshinta.
Washe gari dangin su Mama mutum biyar sunzo raka amarya gobe,haka dangin Baffa,ga
frnds din Iklas zuga guda,Rana ta Uku ranar kai amarya,da wuri Iklas taje wurin Saloon da
lalle,masu mata lallen mutum uku ne ,sai mai gyara gashi,Karfe 4pm Iklas driver ya dawo da
ita,kunga Iklas kuwa yanda ta koma?tab zankadaziyya kenan,dama gata fara kwal,ga lalle yayi
kyau over,
Tana shiga room dinsu mero lallausa tana jiranta,nan itama ta hau nata gyaran,gashi sai
bata abubuwa akeyi ta shanye wannan ta cinye wancen,Lallausa da Mama sun koya Iklas
harkoki sosai na mata da ake amfani dasu,Mama da Ummi sun hada mata wasu da yawa an kai
gidan,store kuwa both na Iklas Dana Sahar an dankareshi da kayan abinci haka kitchen ma.
Karfe biyar su Omar suna can suna Walima,amarya an shiryata tsab