Showing 87001 words to 90000 words out of 107121 words
Chapter 30 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
muku da alkhairi,ina jin dadi.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
170-175
By
AsmaBaffa.
Tashinsu Ummi ta shiga da niyyar yi amma sai ta saki baki tana kalonsu kowanne daure da
dankwali,toilet din Mama ta shiga ta ebo ruwa kadan ta watsa musu da sauri suka bude ido,sai
yanzu suka tuno a gidan Baffa suke fa
Ku je kuyi sallah fetsararru ku shiga sashen Umma Rahina ku gaisheta tana fadin haka tayi
waje,Omar kallon hannunsa da kafafunsa yayi yasan aikin Iklas ne ,murmushi ya watsa mata
sai ki kwance ni yarinya, hannun daya daura ya kwance,wai yaushe ma kika daureni ban sani
ba,murmushin dake kara mata kyau saki masa kana ta bacci ta fada tana kwance masa sannan
itama ta kwance nata kafar,
Sallah sukayi sannan suka nufi sashen Haj Rahina,dukkansu yan matan Umma suna
palonta har Sadiya da Aisha sunzo gaida Ummansu,Iklas sai da ta kara cin Uban kwalliya me
kyau,ta kashe dauri tare da kara fesa turaruka,hannunsu sakale da juna sukayi Sallama palon
Umma,yuuuuuuu suka zuba musu Ido,Najja ce ta maka uban tsaki tare da Hararar Iklas da
Omar,
Suma kannensu su biyu su Amina harara suke kawai aikowa da Iklas,Sadiya da Aisha sun
Lula tunanin duniya,a ladafce suka gaishe da Umma ta amsa kadaram kadaham,ba yabo ba
fallasa,duk sauran kannen Sadiya iya Omar suka gaisar,Iklas tana kallonsu bata kulasu ba
itama,
Kallon Amina Iklas tayi tace yan mata an girma sai aure,haka kika kara girma,kallonta ta
mayar kan Sadiya da ta yamushe a gefe daya,tace a'a Ashe kina nan ya kk,ga Maman yan
biyu ma,gaskia Aisha kinyi saurin samun ciki,daga kaiki sai ciki.duk wannan maganar da Iklas
ke musu Amina karama ta girmi Iklas bare su Sadiya,
Gaba daya su Sadiya ganin yanda Iklas ta kara komawa,ta mirje ta kara yar kiba,ga kyau
komai yaji duk sai suka raina kansu,musamman irin tsadajjiyar atamfar dake Jikin Iklas,sai
kallon Takalmanta sukeyi,
Komai na jikin Iklas unique ne,abin sai ya birge Sadiya da Aisha da suke jin jiki a dakin
miji,shi yasa rainin hankalin ma da Iklas tayi musu basu damu ba Sam,sai su Najja yan mata da
Amina su suka dauki zafi,ganin sun girmi Iklas amma tana raina musu hankali dan kawai tana
auren yayansu,Haj Rahina kuwa sake sake takeyi Aranta gaba daya jikinta ya mutu taga lallai
baza ta iya samun Nasara ba,amma zata nemi shawarar kawarta Haj binta.ko da wani taimako
da zatayi mata. Umma sai mamakin rashin kunyar Iklas takeyi a ranta tace yarinyar nan jaraba ce naga
Alama tafi karfinmu.
Umma ce tayiwa Najja Signa da Ido kan ta rama abinda Iklas tayi musu,a masifance cike da
rashin tarbiya Najja tace Ya Omar kayiwa matarka kashedin fada mana magana anyhow,duk
cikinmu ba sa'anta,dan kina matarsa bazaisa ki samu damar raina mu ba,banza a banza yar
matsiyata daga zuwa cin arziki an mallake mutum da tsafi,
Aisha ce ta bige bakin Najja dalla rufe mana baki,Iklas tace nafi karfin na tsaya ja inja
dake,ta karkace dauri taci gaba baki isa ki kirani yarinya ba,saboda na fiki sanin duniya,yarinya
baki San komai ba tunda baki aure ba,Sadiya ce cike da sanyin jiki tace pls a bar zancen ya isa
haka kiyi hakuri Iklas ki kyalesu yara ne basu inda duniya tasa gaba ba.daga har Iklas sunyi
mamakin Sadiya da Aisha,sun canja kamanni da hali.
Umma harara ta Dallawa Sadiya,Omar mikewa yayi tare da Jan hannun Iklas ransa
bace,Najja ce ta biyosu a baya ta sha gaban Iklas tare da narka wata ashar uban me kika sani a
aure, ke karamar yar iska ce,
Kallonta Iklas tayi ta dan saki murmushi yarinya kenan,Najja ce ta kara karfin muryarta mene
abunda kika sani Wanda ni ban sani ba,me zaki nuna min?
Iklas a nutse take fadanta silent killer ce,nasan tsayinta nasan kaurinta what of u?oh nasan
zaki sani tunda ke taki ba Sadaki kika sani dole kinga da banbanc.....shut up a tsawace Omar
ya furta,banza yar Tasha me tallan kwai da Apple cewar Najja,maganar ta konawa Iklas rai,wato
Omar ya gama bazawa a danginsa ita tayi talla,ga zahiri kowa idan ya tashi yi Mata gori da yar
matsiyata yar talla suke Mata, Sahar ma ta fada mata,a ina sukaji har ta saida Apple da Egg
tabbas Omar ne zai fada,wani bakin ciki ne ya lullube Iklas,
Bata San sanda ta cakumo Najja ba,Omar ya fara tafiya ya zata Iklas na bayanshi sai yaga
wayam, hangosu yayi rukume da juna suna dambe, dama ga Najja garin jiki ne da ita
narkekiyace ga tsayi ga kiba,Iklas kamar biri ta dafalfale Najja,Najja ce ta dage ta ciji Iklas a
hannun da ta shaketa, fatar hannun Iklas ta dauke sai jini,Iklas ma bata bari an shata a banza
ba,Najja ta gartsawa cizo a kunne sai jini Shar ta Kunnen Sadiya,
Samu tayi iya karfinta ta lankwasa yatsan Najja na tsakiya ji kake rukus, da sauri Najja ta
durkushe kasa tana wayyo ta ballamin yatsana wayyo Umma na shiga Uku,
Omar da sauri ya karaso wajen bai wani tsaya bata lokaci ba ya fyallawa Iklas wani
lafiyayyen mari,cik Iklas ta tsaya dafe da kunci,Najja na ganin haka tayi luf ta daina kuka sai
dariar mugunta ma da takewa Iklas a boye,gwalo tadinga yiwa Iklas,Omar kuwa Najja ya kama
ya Mikar ta tsaye,yana antaya mata zagi banza shashasha jaka,dabba wuce ki bani waje kafin
na kwadeki,Baku da aiki sai jaye jayen fada da gulma,wlh idan Iklas tazo gidan nan kika kara
tararta da fada sai na karyaki haka Omar yayiwa Najja tas,
Ido suka hada da Iklas wacce har yanzu tsaye take kamar gunki,suna kallon juna Iklas ma
tayiwa Najja gwalo ta rama itama harda itama dariyar duk abinda Najja tayi Mata sai da ta
rama,Kafin Omar ya juyo Iklas ta Nutsu bai San me sukeyi ba,
saida Najja tayi nisa ta juyo tacewa Iklas Apple and egg ta shige gida.Omar yayi Dana sanin
Marin wifey dinsa da yayi yaga tabbas Najja yar iskace itama,ashe tuggu ta hadawa Iklas dinsa
gashi ya jangwalo tsiya,taya zai lallasheta duk da yasan itama wifey din tasa tsokanar tsiya
gareta.
Matsawa yayi wajenta fuskarsa ba rahma yace muje ke kuma ai yana magana Iklas ta rushe
masa da kuka ji kake Tim ta fadi kasa tana ta birgima da shure shure,wayyo wayyo wayyo zasu
kasheni dangi sunyi min taron dangi,dama ba sona yakeyi ba,yafi son danginsa dani,an
zalinceni,zai kasheni,miji me dukan mata aka aura min dama, ni gwara na koma titi talla
na,baya tausayina wayyo Allah na tun ina yar mitsilata an fara yi min tabo ajiki akan dangin miji.
Tsakaninta da Allah Iklas ke shure shurenta,Mama da Ummi sunji kamar hayaniya da gudu
sukayo waje, su Umma ma dasu Sadiya duk sun fito,Iklas suka gani tana shure shure Omar na
tsaye gefe guda yana tintsira dariya danshi dariya abin nata ya bashi.
Ummi ce fara magana ke meye haka lfy?kunamace ta harbeki, Umaru mene haka?da Sauri
Iklas ta kalli Omar still kuka takeyi,ido Omar ya mintsina mata wai ta rufa masa Asiri.
Tana sheshekarta tace ba...ba...cinnaka bane ya cijeni,kuma Honey ya kwace min
wayata,mene kuma honey inji Ummi, wani farin ciki ne ya lullube Omar shikam abin kunyane
ace ya mari Iklas da hannunsa,
Kowanne cikinsu tsaki yaja Mama tace naga ranar da zakuyi hankali, Ita Sadiya birgeta
sukayi ita yanzu ta isa tayiwa Alhaji Balarabe haka.ai ranar sai dai gawarta,gata tana aiki tana
daukan salary amma jin dadi da zaman lafiya ya gagareta,duk sun tashi a banza.
Kowannensu part dinsu suka wuce,Suna shiga Mama ta kallesu Babana fada min gaskia me
ya faru ban yarda daku ba,ganin Basu Umma Rahina Iklas tace Mama Najja ce fa ta zageni
tace min yar tallar Apple and egg shine mukayi fada amma saboda Ya Omar yafi kaunar
danginsa ya mareni a gabanta kalli inda ta cijeni Mama, su biyu suka rufarmin wai su ga yan
uwa,Mama wai mutum ya daga hannu ya doki matarsa ta sunna ai ya fadi ba nauyi,
Omar mukus yayi yace Mama..... rufemin baki shashasha sosai Mama taji haushin
Omar,fushi sosai tayi da Omar,Ummi kuwa tasan dole Iklas Nada laifi a zancen nan amma
Mama taki yarda,duk suna zaune Palo kowanne tsit kakeji in banda Mama da ta dage tana yiwa
Omar fada, ka samu mace me sonka haka ka fara shirme akan Wanda basu da makiyi kamarka
etc Iklas sai taji bata son fadan da Mama kewa Omar, sai taji ya bata tausayi gashi Mama na
fushi dashi,Ummi sai Hararar Iklas takeyi, Omar ne yayi magana Mama kiyi hakuri haka mana,ai
duk ita ta jawo baki San tsokanarta ba,duka Mama ta danawa Omar a bayansa, me makon aji
Omar yayi kara Iklas ce ta gantsare ta saki kara,tare da cuno dan bakinta gaba Mama dan Allah
Ku kyaleshi haka nifa kawai fada miki nayi ba dan ayi masa fada ba,sai dukansa kikeyi kiyi
hakuri ki kyaleshi dan Allah mama kinji,Iklas harda marairaicewa,a hankali ta tayiwa Omar
magana mu tashi mu tafi gidanmu kawai.hangame baki Mama tayi tana salati,Ummi kuwa daria
tayi gwara da tayi miki kika gani,na fada miki yaran nan idan kina shiga fadansu kunya zakiji ba
yan goyo bane.
Mama tace ga zahiri na gani to wlh Ku tashi Ku tafi tun wuri, tunda sukazo suke samu
magana kamar yaran goye cewar Ummi. Da sauri Omar ya mike,Iklas ta dauki Jakarta da gyale
Omar ne yace kuyi hakuri Mama....Ku je Allah raka taki gona marasa kunya. Iklas sumi Sumi
tabi bayan Omar wai ita kunya.
Sahar ihu takeyi tana kuka da Neman taimako tare da susar gabanta tana kiran Mummy,
da Gudu mamanta ta fito tare da Daddy sukayi kanta a gigice,dan danan Mummy ta fara kuka
ganin abinda Sahar keyi.
Sunkutarta Daddy yayi ya sata a mota sai asibiti, sunje an basu gado tare da yiwa Sahar
Allurar bacci, amma a banza sai da akayi mata Mayan allurar bacci har 3 sannan aka samu
bacci ya dauketa.
Tubeta likitoci sukayi wasu tsutsotsi farare birda birda cankam a cikin al'aurar Sahar kuka
kawai iyayenta keyi, su Kansu likitocin basu taba ganin cuta irin ta Sahar ba.kowa saida ya
tausaya mata domin da Allurar baccin ta saketa zataci gaba da ihu da Susa tana birgima, ba irin
kudin da Daddyn Sahar bai kashe ba,magani sukeyi both na asibiti Dana gargajiya, amma abin
ba sauki, Daddy ya gaji ya maidata Canada can ma ba sauki.
Tun a hanya Omar ya tsaya ya siya musu gasassun kaji da kayan makulashe tunda suka
taho Omar bai kalli Iklas ba itama haka kowanne da tunanin dan uwansa ya masa laifi.kowanne
buri yakeyi aje gida ayi wacce za ayi.
Iklas daya room din taje tayi wanka tayi Sallah tana jira ayi isha tana ta azkar dinta, Omar
kuwa yana masallaci sai da yayi isha ya dawo, Iklas kuwa wata kwalliyar ta tsantara ta hade
cikin wando 3qtr fari da T-shirt ja,ta daure gashinta da Jan ribbom jelar gashin na lilo jambaki
ma ja. Da Sallama Omar ya shigo fuska ba rahma,amsa masa tayi ciki ciki kafarta daya kan tana
kallon wani American film a mbc 2,zama Omar yayi a wata kujerar wacce ke facing din tata,sai
wani mayen kallo yake binta dashi na so da kauna tare da tsantsan sha'awa. Tasan yana
kallonta amma taki kallon inda Omar yake bare ma yasa rai zata kulashi gashi so yake su hada
ido amma taki yasan shima yayi laifi kuma mata sai da siyasa ake iya saitasu,dole sai da
dabara musamman irin su Gomnati da sukeji da tashen kuruciya.
Tasan Omar ita yake kallo tana sani ta dinga murguda Baki tana fari,sai murguda bakin
takeyi taki dainawa, dariya ke Neman kwacewa Omar, suratul Fil ta karanta ta koma ayatul
kursiyyu Omar ya ganeta waishi mayene shine take karatu kar ya cinyeta,
Baice mata komai ba,ta wani Dora hannu saman dukiyar fulaninta ta kara dagosu Sama ta
gyarasu ta kama rera tsohuwar wakar Hausa ta kwalele,ta dauki wayarta tana latsawa ba tare
da ta kalli inda Omar yake ba taci gaba da wakarta wata kalar a hankali tace ka gani ka gani
kwalelenka. Gani tayi Har yau Omar kallonta yakeyi mikewa tayi tare da yin wata mika wacce ta
rikita Omar, tafiya tayi cike da yanga da karairaya ta je room ta jawo ledar naman da Omar ya
siya.
Omar shigowa yayi ya fisge ledar kajin tare da turata baya, a hankali yayi mata amma sai da
ta fadi dama a zaune take, Omar kuma a tsugune,kuka ta farayi masa dama Omar hanyar yi
mata magana yake nema,zuwa yayi da niyyar lallashinta,ai kuwa Dane bayan omar tayi saida
suka tintsire kasa ta shake wuyan Omar bada karfi ba ita a dole shakeshi tayi wai yaji zafi,
chakulkuli ya fara yi mata tana hawaye tana daria,tsayawa yayi yana kallon dariyarta me
matukar kyau da birgewa,tsawaya tayi da dariar itama sai kuma ta fara sheshekar kuka
kwanciya tayi flat a kansa kamar ta hau katifa,ta rungumeshi kam kam taci gaba da rera
kukanta bilhakki tana cewa ka.....ka....ka...mare...ni... Ni.... A...a....gabanta....am so sorry to ya
isa indai akan mari kike ta wannan fushin tashi ki rama abinki,ba tare da ta dago ko daina kukan
ba tace ai....ai...dan...ka...San...ba...bazan....iya.... Ramawa...bane....murmushi yayi kece wifey
ba kya jin magana,yan uwana ne fa,ko ba komai suci darajata,dama....dama...haka zaka....ce
mana...tunda....ni....ba...yar....uwarka....bace....lika....maka.... Ni...akayi....shine....ka... Min.....
Wayo....ka....gama... Shanye... Min.... Zumata....yanzu....ka....tsaneni...yau Omar yaga ta kansa
da Iklas taki shuru,taki tashi daga jikinsa kuma.ci gaba tayi amma..ni..a gabanka tace min...me
Apple and egg....to baby am sorry tashi muyi magana haba yan matana, ninefa honey ki.
Asmabaffa
Tnx alot readersⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
175-180
By
AsmaBaffa
Ci gaba da lallashinta yayi yanzu fa kika fansoni wajen Mama har dukana tayi kanki kinga
kinji tausayina, a kaina kika kekashe idonki gaban Mama ki hanata yi min fada ko?
Ni...ni... Ba tausayinka naji....ba....kawai...dan kar amana daria ne aji sirrinmu....murmushi
Omar keyi tare da shafa bayanta yace a'a gaskia kin kara birgeni ba duk mace ce zata rufawa
mijinta asiri haka ba kamar yanda kika min,na gode Allah miki Albarka,dadi Iklas taji tayi abun
kirki wai ana yabonta.
To tashi kiji wata magana,mikewa tayi ta zauna ta tankwashe kafafu kamar me zaman
tahiya.
Goge mata hawayen Omar yayi yana kinga duk kin bata min kwalliyar,hannayenta ya riko
gaba daya fuskarsa ba alamar wasa,Wifey in tambayeki? Kai ta daga ae,kina sona kuwa
anya?kai ta daga wai ae,magana zakiyi mun,mugun Sonka ma nice number 1 cewar Iklas,Omar
ne ya nisa to dole kiso yan uwana,bai dace kina biyesu kuna fada ba,bayan kin San baki da
gaskia,yes sun miki laifi kema amma ke kika fara tsokanarsu,ko ba komai duk sun girmeki fa
last burn dinta ce kawai bata girmeki ba.
Kina so ace na auri marar tarbiya da hankali,a'a amma ai dai kasan ni bana tsokanar mutum
sai da dalili,kuma ai ma kai na tarewa fada tunda ba sonka sukeyi,to na gode sosai kin kyauta
da kika tare min kinji,Allah tsundumaki a Aljanna,tana zuburo Baki tace Ameen,Omar yaci gaba
bana son tsokana da jaye jayen rigima kin San fada dasu baya mutuwa fa,to ni tsoronsu nakeji
ai ni in fada ma banki mu kwana muna yi ba,kasan sunana kuwa sanda ina jss case buyer ce
ni,cewar Iklas
Siyen fada nakeyi a schl na tarewa mutum a bani kudi,nayi business na fada,to ai naga ke
ba karfi gareki ba kuma matsoraciyace tsokana kawai kika iya,dariya Iklas tayi tace lallai na
waje baiga gari ba,baka San muguntata bane in na dinga hadawa mutum gadar zare sai ya
raina kansa kaga dai yanda na tsillewa Sahar mazaunai ko? to ba komai nayi ba yanzu kawai a
nutsatsiyata ka aureni ka godewa Allah da har kai zan hada a marin nan da kamin,yanzun ma
kawai dan kai mijina ne kuma kaci sa'a ina sonka .
yanda take tawa Omar kuri sai tsoron tsiya.naji case buyer cewar omar yanzu dai Allah kinji na
rantse na kuma ji ko a labari kinyi kokawa da wata musamman yan uwana zaneki zanyi ba mari
ba,
Bakwa son Zaman lfy,yan uwana daban ke matata daban,karama dake sai rigima,idan karfi
kikeji,duk sanda kika ji kina jin karfi kizo ki nuna minshi on bed,kuma dole ki so yan uwana idan
basu sona case dinmu daban kema namu dake daban ne, na gama magana.kekebewa tayi
zatayi kuka hannunta ya saki je kiyi kukanki ba a jikina