Showing 45001 words to 48000 words out of 107121 words
Chapter 16 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
Kallo ya kare mata ke bakya damuwa wai hada jiki da mazan wasu?haushi ya kara turnuke
Iklas bata San sanda ta kwanyawa Omar mintsini a cinya ba har cije baki takeyi dan
mugunta,shakota Omar yayi ai kuwa Iklas dole me karfi yau baza ta kyaleshi ba,said suka fara
kokawa tukuru suka kaure, shi Omar a hankali yakeyi da tsokana amma Iklas ita da gaske
takeyi sai nishi takeyi wlh bazan dinga kyaleka ba na gaji ina ma Abu kana zagina.
Sosai Omar ke shan dariar Iklas ita dole fada takeyi,Iklas da kanta ta gajiyar da kanta kawai
ta fashe da kuka nan take Hankalin Omar ya tashi baya son ganin kukan Iklas,
Bai San sanda ya rungume Iklas ba yana jijjiga ta tare da shafa bayanta,lakwas tayi tana
goge idonta,cikin rada ya tambayeta kin gaji ne?kai ta daga masa wai eh,bacci ko?nan ma cike
da shagwaba ta daga masa eh.to shine abin kuka kalli yanda kika farfasamin jiki da dukanki
dama haka kike da karfi harda naushina fa kikayi ko dai kin taba zama a China ba a sani ba.
Fashewa da daria Iklas tayi da ta tuno haukar da tayi tana ta kokawa da Omar bayan ita ta
wahalar da kanta,hannunta ya kama suka wuce Room dinsa cike da shauki,Iklas tasha mamaki
ganin har an gyara ko ina neat yana kamshi,suna shiga Omar ya dauketa kamar baby ya
daurata bisa bed maza kema yi baccin tunda naga adawa kike dani kina min bakin ciki nayi
bacci ke bakiyi ba,akan Mama ta dorani kan cinyarki kike bakin ciki.murmushi tayi abinta ta juya
masa baya sai bacci.
Shi kuwa a.c ya rage mata ya lullubeta da hadadden bargonsa ya shige toilet domin yin
wanka gashi yau so yake Iklas ta rakashi masallacin juma'a sallah,ya Dade bai je ba.
Sai 1 Iklas ta farka Arba tayi da kyakyawar fuskar yana zaune kasan bed hannunsa kan
cikin Iklas kansa bisa bed yana ta bacci shima.minti kadan ya bude idonsa ya dorasu ana Iklas
wacce ta shagala wajen karewa halittarsa kallo.
Kunya taji ta mike tayi hanyar fita daga room din,pls ki shirya za muje masallaci yau.OK tace
tare da komawa dakin Ummi.
Ummi sosai ta kara yiwa Iklas nasiha tare da nuna mata muhimmancin miji.shiryawa Iklas
tayi cikin wata rantsatsiyar doguwar Riga baka me adon Golden,cikin akwati set 4 da Mama ta
bata kafin a hada mata lefe.
Yana gyalen tayi a kanta,ta sa takalmi Golden da da jaka Golden masu tsadar gaske,kamar
balarabiya haka ta fito.walwali kawai takeyi.
Ummi ta yiwa sallama ta wuce dakin Mama da fara'a Mama ta tareta ina zuwa haka?Mama
ya Omar zan raka masallaci zaiyi sallar juma'a.
A dawo lfy a kula sosai kinji.to Mama insha'allah cewar Iklas.
Har room din Omar ta kara komawa sai taku dai dai takeyi,a jikin mudubi ta ganshi da gani
kasan karfin hali kawai yakeyi,wata mashahuriyar danyar shadda ya sa ita ba fara ba ba kuma
milk ba,yayi matukar kyau dan dagwas dashi,sumar nan taci kudi luf luf da ita,turaruka masu
tsada ya fesa sannan ya kwashi wayoyinsa,Iklas an saki baki ana kallon zasu makara kawai
hannunta ya rike suka fito cike da taku me birgewa.
Yaran Umma suna tsakar gidan sai gulma akeyi.wucesu sukayi Omar wata gangamemiyar
mota fara Sol ya nufa driver ya ba key ya tukasu suna Kane bayan mota, har masallacin da
Omar ke zuwa.
Bai fito daga mota ba sai da aka tayar sannan ya saki Iklas yaje yabi sahu,ana idarwa ya
dawo cikin mota wajen ta,driver ya jasu ya fada Masa wani park yace can zasu je.shima wajen
shakatawar manya ne,da Iklas dinsa ya fito.nama ya siya musu da abubuwan ciye ciye anan
suka zauna cikin lafiyayyen wajen inda aka tanada saboda masu zama suci a wurin.
Kafarsa ya dauka daya tare da zare takalminsa ya dorata kan kafar Iklas gaba dayansu
wani yanayi zazzafa suka tsinci Kansu ciki tare da son kasancewa da juna.cike da farin ciki a
zukatansu suka dinga baje girki a cikinsu.
Sun mike zasu tafi sai ga Sultan da Raj suma tafawa sukayi suka fara yiwa Omar cakaki
Jan Iklas yayi suka fara tafiya,kafin su karasa mota,dan saurayin da ya taba bige Iklas ya
karaso wurinsu har wani kishi yake shifa bai yarda ba Iklas yake so.
Haba baby Iklas rannan naje gidanku akace kun bar unguwar ina ta nemanki,nasha
wahala wlh ko sunana fa Baku sani ba,pls ki bani numberki kinji.ya kalli Omar Wanda ya gama
hasala.sannu malam, baby wannan yayanki ne?naga kuna kama dashi.Iklas murmushi tayi ta
fara magana,
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
85-90
By
Asmabaffa
KUJI DADINKU READERS.
Sannu ya gida? Yayana ne mana,mun manta an rabu ko sunanka bamu tambaya
ba,washe baki yayi Suna na IBRAHIM ZAKARI ana ce min IBZZY BOY.daria ta kusa kwacewa
Iklas yanda yace Ibzzy boy har da daga hannu kamar masu wakar raps.shi a dole nigger.
Omar yaso yayi maganinsa amma ganin kwata kwata ibzzy irin banzayen mazan nan ne
sai ya shareshi,Iklas harda jin haushin Omar baya kishinta dan bai San matarsa bace ita.
Waya ta dauko da niyyar karbar number Ibzzy sabi da taji haushin Omar ba ko kishinta,fisge
wayar Omar yayi tare da sa yatsa daya a dan chakurkurin kirjin Ibzzy ya tunkudashi baya sai da
Ibzzy ya kusa faduwa,da masifa Ibzzy ya tasowa Omar dole sai ya ci mutuncin Omar, daukeshi
da wani zazzafan mari Omar yayi Wanda yasa Ibzzy dafe kumatu ba shiri,kafin ya dago Omar
har ya finciki hannun Iklas kamar tsinke kawai janta yakeyi har mota ya jefata,driver kuwa yaja a
kabar Ibzzy da kumatu kumbure,a fili ya furta kai wlh saina ci uwar guy nan sai naga ubansa
dan babarsa.
Gida suka koma a compound suka ci karo da Abdallah zai fita da Sauri yazo wajen Iklas
wacce ke kukan masifar da Omar ya zazzaga mata kan Ibzzy.da sauri Abdallah ya kai hannu da
niyar sharewa Iklas hawaye Omar ya bige hannunsa,bai gane ba ya kara yunkurowa zai rukota
Omar ya shiga tsakani da Sauri ya tsaya a tsakiya,
Ya kare Abdallah kar ya taba Iklas,gocewa Abdallah yayi ya zame ya nufi Iklas anty wa
ya Saki kuka kara kai hannu yayi,Omar ya jawo rigarsa baya kiiiiiiii ya dawo dashi baya,
Abdallah sarkin naci kara komawa yayi shima Omar cikin zafin nama ya cakuma Abdallah ya
turashi baya yana zan mareka wlh,to yaya kuka fa take, cike da masifa Omar yace ina ruwanka
ko huruminka ne ban son shishigi...wuce kasan inda dare ya maka.sum sum Abdallah yayi gaba
abinsa yana kallon Iklas,an hanashi lallashinta.
Janta Omar yayi suka wuce wajen Mama... kallon Iklas tayi taga alamar tayi kuka,lfy Iklas
me ya sameki?tana shesheka cike da shagwaba tace ba ya Omar bane dan kawai wani ya
sanni munyi magana shine ya dinga min bala'i harda murdemin kunne wai zai cire min kunne,
dadi Mama taji ganin Omar zai fara son Iklas fa,hmm nace Mama batasan zaman da sukeyi da
Iklas ba su kashe su rufe.
Lallashinta Mama tayi tare da balbale Omar da fada,Omar kuwa kememe yaki karbar laifinsa
Mama muna tafiyafa ta kama magana da wani dan ta raina min hankali ni ina sauri zasu tsaya
bata min lokaci idan zancen takeso yazo gidan mana zasu shiga rayuwata harda cewa wai ni
yayanta ne..to ba hanani karbar number sa kayi ba,kinji ko Mama dan karyane fa wai zata karbi
number sa, to koma ki karbo mana yanzu tunda baki da hankali
Sai da ka bari muka dawo da ka barni mana tun acan cewar Iklas,gajia Mama tayi da cacan
bakinsu tace dan Allah Ku je part dinsa kuyi can ni kun cika min kunne na rasa me gaskia
cikinku.
Da sauri Omar yace ni Karta zo min room,tabe baki Iklas tayi to me zanci da room din naka ko
kace Nazo bazanzo ba tun yaushe na daina kulaka ma,ae naji cewa Oga Sir, yazo zai wuce
amma saida ya matso jikin Iklas ya take mata yatsa daya.ihu ta fasa Mama tace maganinki
kenan Babana muguntar tsiya gareshi in kika bashi haushi,ki dinga kyaleshi kishinki yakeyi fa
ke baki gane ba.
Karki yarda ki fada masa ke matarsa ce kinji ko,kai ta daga,idan ya warke kuma zaki koma
schl sosai taji dadi wai zata koma schl,wayyo aikin gomnatinta.
Umma Rahina ce tasa yarta Naja aikin kan tasan yanda za ayi ta shige jikin Iklas sosai har
ta jawo musu ita ta dinga shiga part dinsu,kuma ta gargadi su Sadiya su daina nuna mata tsana
a fili,ta hakane zasu samu nasara..Sadiya tafi kowa tsanar Omar kawai jiran lokaci take ta
kaddamar masa ba tare da kowa ya gane ba.
Ibzzy Boy ya cika da haushin Omar marinsa da yayi,kuma bazai daina son Iklas ba dole
ya nemi gidan da suka koma yaje can,domin so yake ko ma ta halin kaka shi dai ya auri
Iklas.wasu manyan kawensa mata da suke masa kawalcin mata JALILA WANKAN TSINKE da
FATI GOCEWA ya kira ya shaida musu komai wankan tsinke tace haba Ibzzy kar ka ba damu
mana kai da kake kullum matane frnds dinka amma ka kasa da wannan kucakar,
Fati gocewa tace ka bari kawai zamu je wajen LAWISA ICEN KABARI harda LADI PIJO wlh
sai mun shawo kan wannan yarinyar ba gaggawa a nutse zamu wayar da ita dole ka aureta ita
din banza dan uwarta ko da ubanta take kwana wace ita ta kara narko wasu manyan zagi.nan
suka taru Ibzzy sai barin kudi yake musu.
Saleem ya kira wayar Ummi ta bashi address din gidan su Omar zai kawo musu ziyara
sannan zai ga Iklas dinsa.sai dadi yake ji.har ya matsu Sunday tazo.
Sahar taji labarin Omar yayi budurwa nan ta fara bala'i wlh bai isa ba yana warkewa zan
koma gidansa dole na tara dukiya nayi tafiyata,ko wacece bata isa ta rabi Omar ba,kuma ko ya
aureta sai na koreta kuma sai ya saketa wlh,kai zan iya hallakata nan Sahar take ta bala'i a
Office.wannan alkawarin sahar kenan itama.
Iklas ce tazo sanye da yar wata Riga da kadan ta wuce gwiwa me dogon hannu ce red
kanta ba dankwali sai gashi yarab,tunowa tayi bata bawa Omar magani ba tunda sukayi fada ga
dare yayi.da tayi fushi dashi amma yanzu ta hakura zata je room dinsa duk da yace karta kara
zuwa masa. A hankali da sallama ta shiga dakin nishin Omar kawai ta jiyo,kan sofa ta ganshi kwance
amma dai tunda aka fara maganin suna ganin sauki,da dane da tuni Omar ya Dade da suma,
Karasawa tayi ta dakko maganin wajensa taje ta zauna gefensa kadan ta dago kansa sai
sannu take masa yau da yake baya cikin hayyacinsa ba gardama yasha maganin,
Addua ta dinga tofa masa tana sannu kaji ya Omar tare da kara harde yatsunsu waje daya.
A hankali ya dawo normal yau Iklas tsokanarsa taso yi dan haka zamewa tayi ta kwanta
cinyarsa,haushi ya kama Omar yarinya ba kamun kai,ta gama lalacewa a dalilin talla.
A ransa kuwa ji yake kamar su zauna haka har abada, zuciyarsa ta gayamasa kai bafa
muharramakar ba ce kaji tsoron Allah don yana ganinku,ai da sauri Omar ya daga cinyarsa ya
hantsilo kan Iklas ya mikar da kafarsa,
Magagin baccin karya tayi ta wani taho luuuu ta fada jikinsa,zameta yayi daga
jikinsa,hannunta daya ta dauka ta wani jefa luuuu kan cinyar Omar,wata zuciya ce tazowa Omar
ya dauki hannun Iklas yayi wancakali dashi tare da mikewa ya shige toilet.
Iklas kuwa daria taitayi amma kuma sai taji dadin hakan ta rasa me takeji haka tare da ita
kuma bata ji a wani namiji sai Omar kadai.musamman da ta fada jikinsa sai taji wani ni'ima ta
shigeta kamar ta karayi,tunani tayi tace ai kuwa tunda naji dadi saina dinga daneshi wlh,
Wata zuciyaar tace zai rainaki,can kuma a fili tace to mene ma wai tunda mijinane sai na
dinga masa wayo.
Ai a islamiyya dama malam yace mana idan mace ta taba mijinta ladane,a radio har wanka
akace idan kunyi sunna ce.
Tab bazan iya wanka gaban Sir ba,murmushi tayi tace kai wlh a wandonsa watarana ina
hango sandar girmansa tayi katoto da yawa zureriya bazan iya kallonta ba.shuru Iklas tayi ta
fara tunani ai kuwa sau da dama nasha tabota by mistake uhmmm maza wlh yan iskane.
Ya Omar Sam bai taba nunawa ko a fuska yaji wani abuba.Allah shiryeka Sir da gani nasan
maita zaiyi.ita Kadai take zancenta har Omar ya fito daga wanka.
Daure da towel yana tsane jikinsa kamshin sabulun wankansa ya cika mata hanci.tunda
Omar ya fito Iklas ta kura masa ido wuri daya take ta kallo a jikinsa,kawai joystick din Omar take
karewa kallo ta cikin towel a dole sai ta gano adadin girmanta.
Omar yana kallonta shi kam ya sallamawa Iklas ya kyaleta abin nata yafi karfinsa amma
akwai time zaiyi maganin marar kunya.
Hakawai yaji Iklas ta tuntsire da daria a fili tace yau mun shiga uku mu mata.tsaki Omar yaja
tare da maka mata harara.janye idonta tayi ta nutsu ta koma kallon kyan diri da skin na
Omar,ciwonsa ya fara tashi yajiyo Iklas sama sama tace Allah me baiwa.
Da Sauri ya dakko kayan baccinsa har zaisa yaji an karbe kayan a hannusa yasan Iklas
ce,bako damuwa ta fara shafa masa man zaitun na magani.
Mugun sha'awarta ce ta kara taso masa, ga shigar da tayi ta mata kyau ta janye
hankalinsa. Har ta gama jikinsa har rawa yake sandar girma ta harba, Iklas kuwa ta samu abin
daria sai kare wa joystick kallo takeyi tana murmushi hakan ma a boye takeyi kar ya
kamata,Iklas ita kawai abar maza daria take bata,don akwai sanda ta leko daga gidansu taga
wani Arne na fitsari a tsaye sai da ta tsaya ta kalle masa sandar girma tsab tana daria.
Har yan ball idan taga zasu wuce sabo da wandonsu ana ganinta suma saita sa musu ido
tayi ta sheka daria.
Mikewa tayi da niyyar tafiya ji tayi Omar ya jawota tare da dorata saman bed dinsa,ya hau
bed din shima cike da sha'awarta,ido ta zaro tana ina ina.....wlh....uhm...uhm tana yarfe hannu
Omar Wanda ya mata rumfa tana tsakiyarsa,..nifa....ba...fa...daria nayiwa abakarba...kawai
kawata na tuno. Kayi hakuri ni indai a gabanka ne nama daina daria gaba daya.ba tare da Omar ya furta
komaiba ya fara kokarin cire mata kaya, kuka ta fara da yace abinda kikewa dariar ai zan baki.
Sosai ta saki kuka na rantse da Allah bazan karaba I promise u,ni ban taba gani ba dan
Allah ka yafemin,daria ta ba Omar sai da yayi murmushi sannan ya sauketa kasa.
Tambayarta yayi kinyi wanka da sauri tace yes.bed chair ya nuna mata to maza kwanta
can,a'a dakin Ummi zanje ni, OK to bari na baki abin da sauri ta koma ta kwanta inda yace.
Hakikanin gaskia Omar baisan me Iklas kewa daria ba,ita ta fallasa kanta da ta kama rantse
rantse dama kuma yayi zargin hakan saboda yaga inda idonta ke kallo.
Wasu rantsatsun kayan baccin maza yasa rigar kalar singlet wandon Short ne guntu farare
kal,turare ya fesa kala wurin 4.sannan ya kwanta tare da adduoi.
Iklas tuni bacci ya dauketa.yau ikon Allah Omar baiyi ciwo ba har suka tashi lfy,sai mugun
mafarkin da yake yawan yi.
Iklas da murna ta fadawa Ummi,kowa yaji dadi.yau kuma Sunday yau saleem zai zo wajen
su Iklas. Omar na dakin Mama Iklas ta rude sai shige da fice takeyi a kitchen,Duk abinda takeyi
Omar na lura da ita,ya gama Dana mata tarkonsa.
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR