Showing 105001 words to 107121 words out of 107121 words

Chapter 36 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

Advertisement

23 Mar 2025

7370

ciki,haka ake ciki ba cuta r laulayi?ni rawa ma nake son
yi,remote ta dauk tare da danna kida,
Omar ne ya karbi remote ya canja waka tare da karo vol na speaker yace oya tashi kimin
wannan rawar, to ai slow music ne sai dai in ka mike tsaya saboda wannan rawar kalarta kenan
ya dace ace da namiji,

Kawai kimin na gani pls cewar Omar nanfa Iklas har bending down takeyi a slow,omar ya
tuna tana da ciki kar ya zube,ya kashe kidan du,Gomnati zo kiji wata magana?tana zuwa ya
dauketa yayi ciki da Ita suka Lula wata duniyar ta ma'aurata.

Omar ya kara mannewa Iklas saboda cikin ya kara sa mata wani sweet din daban,Iklas ta
kammala degree dinta,yayinda take zuwa office din Omar yawanci tare sukeyin aikin,aikin Hajji
da Umrah sunje da yawa,yau Omar yana Office Iklas ta hade cikin wani unique material kamar
yan mata,ta shirya girkinta a dan wani basket me tsananin kyau,prince yana wurin Baba
Karime,driver ne ya kaita Office din Omar,tana zuwa building din mutane sai gaisuwa ake
kaiwa,yayin da Omar yace sunanta Gomnati,kowa da Gomnati yasan Iklas,ya fito mutane
yaransa suna take masa baya zaije Sallah,ya hango motar Iklas an kawota,da Sauri ya sallami
mutanen ya karasa wajen motar cike da takama,dakansa ya bude mata ta fito,hugging dinta
yayi,wata siririyar sukaji tayi musu sallama,juyawa sukayi dan ganin ko wacce,wata yar budurwa
ce zata kai 25yrs sai mayen kallo takewa Omar tare da cewa sunana xahra Eabraheem,ina aiki
a company ka,pls ko zan iya ganinka,
Wani matsiyacin kallon Omar yayi mata tare da Kallon Gomnatinsa sannan yace ki tambayi
my heart idan ta yarda fine,Iklas wacce ta gama kumbura sabo da kishi matsawa tayi jikin Omar
har dagen kafa takeyi wai dole sai ta kareshi Xahra na kalle mata miji,Da masifa Iklas tace u r
fired from ths company as from 2day kar na kara ganinki,
Allah sarki Xahra ta jawowa kanta kuka ta farayi tana ba da hakuri,Omar yace my peace a
barta pls,ba tare da Iklas ta kalleashi ba tace baka da wannan damar yaro,dariya Omar yayi
yanda Iklas ke kuri da nuna takama kamar company ta
Yace kalli mutane yanda suke bina suna biyayya ke kuwa yar cukula dake sai ki tamin
tsiwa,baki ta turo cike da shagwaba ni a haka kake zuwar min? zigidir kake zuwa duk wani tabo
dake jikinka na sani,su kuwa fa sai ka dau wanka,
Hanci ya lakuce mata tare da mika mata key din Office bari nayi Sallah kar na rasa jam'i,kiss
ya manna mata a goshi sannan ya wuce,

Xahra ce ta karaso wajen Iklas tana rokonta akan a yafe mata,karki damu amma dole na

canja miki Company,gaba Iklas tayi da basket dinta na food tace wa Xahra follow me,
A kujerar Omar ta Office ta zauna tana juyaya da ita nan take tayiwa Xahra transfer zuwa
company da Sadiya ke kula dashi,sai godiya take.
Tunda Iklas ta zauna take faman shigar da kudi ta computer tana calculation,Omar yana
shigowa ta nuna masa komai sai murna yakeyi Gomnatinsa wise ce,

Iklas yanzu ta mallaki kadarori da dama,sosai take juya kudade itama,Suhaila da Ummi
sai abinda suke so take musu,frnds,da dangin mijinta du tana kyautata musu da arzikinta da
karfinta,har tallafi take kaiwa gidan marayu tare da Dora Omar akan harkar taimakon talakawa
sosai, Gidan Kajin Mama wata rantsatsiyar mota ce ta shigo bayan mintuna Omar ya fito cikin shiga
ta Alfarma kamar wani sarki,budewa Iklas yayi ta fito wow Iklas ta gama zama queen,handbag
dunta na hannun Omar,Prince ma yana gabansu ya hade sosai,Iklas da yaron cikinta Wanda
batasan tana dashi ba, Ma'aikatan sun San Iklas amma basu ganeta ba sun zata bakuwa ce tazo daga kasar
larabawa,yanda suka ga Omar yana hugging dinta yasa suka gano matarsa ce,wani cikinsu
yace daga Kuwait naji ance ya auro matarsa
Sai da Iklas ta sanar dasu cewar Itace Gomnati me siyan Kwai da Apple,sai mamaki sukeyi
suna tayata murna da farin ciki,wai dama Ashe Allah yayi itace matar Ogansu kamar wasa suka
taba haduwa a wajen,har fada sukayi ranar,gashi Ashe har sun haifi Prince,
Iklas Karin Abashi tasa Omar yayi musu,ita kuma ta raba musu kyautar kudi,sannan suka bar
wajen,Ma'aikata sai Albarka suke sa mata sosai,tare da mijinta,ranar sunsha Addua.

Iklas tana gidan Mama Omar ya barta ita da Prince suje su kwana daya,zai je gobe ya
daukosu,Gomnati an baje suna musu dasu Najja da Ummi sunce ciki ne da ita Gomnati tace
lallai kuna bata bakinku,dan kunga na canja jin dadine mijina yana kula dani,ba wani ciki Omar
yace sai nayi 5yrs zan kara haihuwa,gwara ku kyaleta cewar Mama.
Shuru sukayi suka kyaleta,sunyi shirin kwanciya sai ga kiran Omar a wayar Iklas, hello
honey? Kinga ba wani honey Ina compound fito mu tafi gida,kaifa kace na kwana honey, ae na
sani ai na fasa yanzu,amma saida ka bari na fada musu,in ba so kike raina ya baci ba kawai ki
bar musu Prince kizo mu tafi gida ko kuma nazo cikin gidan na daukeki,,
Shagwaba ta fara yanzu dan Allah ka kyauta min?hmm zo muje gida kyayi shagwabar a
can,dit ya kashe wayar,Kinga ki tashi kibi minji kar yazo yana yi mana rashin kunya da tijara a
gidan nan akanki nasan yanzu kwa zama Aljanu cewar Ummi,
Ikkas tana fushi ta dauki Jakarta da kayanta,ta barwa Prince nasa tayiwa Mama Sallama ta
fita,

Shiga motar tayi tana kumburi,Sorry my heart na kasa bacci ne shi yasa cewar Omar,
Gomnati tace muje kawai nasan me kake so,amma baka kyauta min ba ka sani ko?haka kake
min sai ka amincemin naje Unguwa yini ko kwana sai kace ka Fasa ka dawo ka daukeni,ko ka
turo driver ya daukeni,

Baza ki ganeba my liver bana gajiya dake ne,bana iya hakurin rashinki kusa dani, nima ai
bana iya hakurin dakai kawai dai ina daurewane,ke kina iya daurewa ni kam ban iyawa wlh,na
gaji ma Hutu zamu dauka muje london, a'a muje saudiya kaga an kusa aikin hajj cewar Iklas,
duk inda kike so ai nan Zamuje Gomnati ba a ja dake, Dukan wasa tayi masa kadan a kirji,ka gani ko ban son Tsokana,suna shiga gida da kyar
suka iya shiga bedroom kamar zasu cinye juna tun daga compound,sun kwashi sabon Amarci a
ranar.
Abdallah an zama katon saurayi ya gama degree ya dawo,yayinda ya like shi Suhaila zai jira
tayi Candy ya aureta,Itama Suhaila tana son Abdallah sosai.Suleim kuwa tace karatu zatayi me
zurfi kamar Yaya Omar.Najja kuwa ansha bikinta Iklas sune kan gaba,amma Omar ya hanata
sakewa,kullum yana like da abarsa, an kai najja Sokoto,ta auri wani local gvt chairman. Aisha ma ta kara haihuwar lafiyayyen da Namiji,Sadiya kuwa yanzu Allah ya bata ciki wata
2,mijinta kamar ya cinyeta,sauran kannensu su biyu suna part din Mama tana kula dasu.

Iklas taga cikinta yana ta girma,gashi kamar alamar ciki take gani,tabbas su Ummi sunyi
gaskiya,lallai maganar Omar cewar Allah ya nuna musu Ishara gata ana mata allurar planning
gata da ciki yanzu,
Kuka ta sakawa Omar daya dawo,wlh honey ciki ne dani na shiga Uku,
Har asibiti Omar ya kaita aka tabbatar ya wuce 3mnths,Omar da kyar ya kwantar mata da
hankali ta hakura,tasha kuka kuwa,Omar Sam bai nuna yasan tana da ciki ba tun tuni.biyeta ya
dingayi yana lallashi da salon wayonsa harta hakura.

A airport na Abuja Omar da Iklas suna manne da juna wannan tafiyar an bar Prince wurin su
Mama,Jannat matar Saleem da tsohon cikinta zasu tafi egift suka gaisa da Iklas tare da
wucewa wajen nasu screening din.
Omar tun kafin a fara yi musu screening domin zuwa kasa me tsarki,yana wajen Iklas
dinsa,minti 1,2 yazo ko kina bukatar ruwa?juice?snacks etc haka yake tayi ko yazo ya danyi
Hugging dinta yana kissing dinta,a chair ma daya zauna tana kan cinyarsa, yana ta
lallabata,sai shagwaba take masa,tun mutane basa kallonsu har suke kallonsu suna sha'awarsu
kamar wasu turawa ana zuba love,
Tashi Omar yayi tare da dawowa wajen Gomnati dauke da ruwa Faro ya mika mata,kiss ta
bashi a kumatu,wata tsohuwa ce ta matso kusa dasu ta fara zazzaga musu masifa,wannan
aikin hajjin zakayi kuwa dan nan,wannan baza ka barta kuyi Ibada ba,kabi ka like mata,wani
Iskanci ne wannan kana lasheta da tsotsa kamar tsohon maye,
Kema da laifinki munafuka ke kike bashi hadin kai wannan bazai barki kuyi addini ba,,ka
hana kanka ka hana wani ibada saboda Iskanci ya ratsaka, tsaki tsohuwa taja tare da komawa
cikin mutane tana ci gaba,Maman Khayree ce tace dan Allah Iya ki kyalesu haka,irinkune kuke
jawowa yara na muku rashin kunya,yo bazan fadi gaskiya ba fisibilillah yaran nan har karar
tsotsa kakeji kamar suna shan alawa,mu bamu San wannan ba,ohh ni Delu karshen duniya
yazo sai ta fashe da kuka,kaji fa tsohuwa da karfin hali.
A jirgi ma Delu ta sawa su Omar Ido,idan Omar ya rungumo Iklas ko yayi wani abun sai Delu
tayi masa dakuwa wato ambola,dariya take bawa su Omar ma

Iklas ana Madina,ita kadaice yau ta koma hotel dinsu bayan ta dawo daga masallaci tayi
Sallar Isha.
Darul salam Hotel ta shiga har Room dinsu ita da Omar sai yatsina takeyi ta gaji,tana shiga
Room dinsu Omar yana kwance yana hutawa da alama bai Dade da dawowa ba shima,Hi dear
kawai tace tare da shigewa toilet,wanka da Brush tayi ta fito tayi shirin Bacci,shima Omar hakan
yayi,tana zaune tana zuba kamshi tare da cin Apple,zuwa yayi ya zauns kusa da ita tare da
rungumota jikinsa yace wifey najiki so silent,mene kara narke masa tayi tace wash na gaji
massage nake so,
Kwantar da ita yayi on bed flat ya Fara mata tausa me dadi,yaga ta fara masa bacci sai ya
koma yi mata cakulkuli,nan ta fara dariya sosai,ba shiri ya tsaya tare da cewa me nake gani a
hakorinki kamar Gold teeth guda daya a hakoran sama gefen right side?dariya Iklas tayi tare da
cewa my King Hajiyayye kenan, na koma Hajiyayye nima,yau naje hospital aka samin,haba inta
zuwa Sadiyya ko hakori daya babu,ya ka gani my King yayi ma kyau,idan baiyi ba baka so na
cire,

Omar Wanda ya tsaya ya kasa motsi saboda yanda hakorin makkan yayiwa Iklas mugun
kyau,da Sauri yace no ina so kinga yanda yayi miki kyau kuwa wifey,I love it. Bakinta ya fara
tsotsa kamar sweet,nan Iklas ta fara sarrafa Oganta Omar,kafin kace me sun zauce akan
juna,nishin sweet tare da furtawa juna sweet words masu wuyar fassara da nauyin dauka ga me
karamin kai.sunna suke daffakawa ba kama hannu kamar su hadiye Kansu.



ALHAMDULILLAH

da Allah ya bani dama da ikon Kammala wannan littafi nawa,ina fata ya fadakar ya nishadantar
tare da fatan kunji dadinsa masu karatu.

Masu comments akan wannan littafin Ma'aikaciyar Gomnati,masu bibiyarsa kullum,da masu
tambayarsa idan ba ayi posting ci gaba ba,duk kowa ma da kowa naga sakonku,bani da bakin
Godiya Tsakanina daku sai Addua,naji dadi, nayi matukar farin ciki ba adadi.naso na sa Sunan
duk wasu masu comment a Novel din nan domin karramaku readers amma ba time.gaba
dayanku NA GODE NA GODE KWARAI
Allah ya biya muku bukatunku. Love u all.really miss u.kamar kar na daina typing wannan
Novel wlh amma ba dama.Allah sarki Iklas da Omar dina.


Littafina me zuwa bayan sallah idan Allah ya kaimu da Rai da Lafiya shine:

✳CIRANIN AMANA✳

Ina fatan yafi MA'AIKACIYAR GOMNATI komai da komai Insha'Allah.

Allah sadamu da Alkhairinsa, Allah sa muyi azumi lafiya mu gama Lafiya.Allah ya Bamu lafiya
me dorewa,ya Gafarta mana zunubanmu, ya Bamu Nisan kwana me amfani,ya samu a
Aljanna,ya tseratar damu daga wuta,ya azurtamu da arziki me amfani duniya da Lahira.


GODIYA DUBU DUBU MALALA GASHIN TINKIYA MUTANENA.



AsmaBaffa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login