Showing 1 words to 3000 words out of 26574 words

Chapter 1 - YAR BAIWA Complete book by maman Usee .pdf

02 Jun 2025

1730

Bismillahi Rahamanir Raheem!!! � 'YAR BAIWAH�
Maman Ussee

Yau yakasance jumma'ah yayinda kowa ke hada hadar zuwa masallaci garin yayi haske gwanin
sha'awa kowa lamarin gabansa kawai yake tafe take tana yan wake wakenta dauke da tulu
akanta zataje debo ruwa rafi kasancewar yau kasuwar garin nasu so take taci kwalliya Dan
zuwa kasuwa Sameera kenan YAr BAiwa ahankali kawarta indo ta lallabo tabayanta tace Keee,
hava indo meye haka nihar kin tsoratani wallahi ohh wadda aka kira da indo tayi 😀 tace
kekuma gaki da tsoro kamar kura ko samira tayi murmushi tace to sai kawai naganki kwatam
toya akayi kawalliya naje gdnku banga ki ba eah wllhi Inna ce ta aikeni sayen omo kinga sauri
ma nakeyi tace karna Dade to sa himma nima kinga danakai wan nan din nakare sai mun hadu
kasuwa ko taimata sallama suka wuce.
Kai tsaye gidansu ta nufa da sallamarta ta aje tulun washh wallahi umma nagaji ke banason
shashanci Dan wan nan diban ruwan ne wai kingaji rafin nisa gareshine daxakice wai kin gaji sa
himma kiyi wanka kinga ankusa tasowa daga masallaci, kije kasuwar ki yo mana sayayya ta
amsa da to tashiga daki ta kwabe kayanta tafito da daurin kirji tashiga bayi tai wanka ta fito tana
Shafa mai da hoda nidai gefe nakoma ina kallon ikon Allah anata cika fiska da kwalli da digo
digo ohhh dariyace ta kusa subucemin nadai gimtse INA kallon Samira an takarkare ana Shafa
Jan 👄 takare takoma fannin sa kaya wasu kaya atamfa ce ba laifi kam a wurin samira da ita a
ganinta yau Zata goge sosai.
Sameera yarinya ce yar kimanin shekara goma sha Biyu farace ba Sol ba irin chocolate colour
din nan Allah yamata baiwar kyau bakinta Dan karami dashi dauke da siraran labba ga hakora
farare Sol kanana Jere gwanin sha'awa tanada idanuwa masu kayatarwa irin na mejin bacci
sexy eyes ba laifi kam batada jiki kuma baxa asakata layin maras kiba ba masha Allah da ita
son kowa kin Wanda yarasa ga tada shaf brain shiyasa ake kiranta da yar Baiwa duk abinda
aka fada mata bata mantawa ga hankali uwa uba hakuri batada kiriniya ga basira sai dai kash
abu dayane samera batadashi iyayenta talakawane ga samira nason boko kamar me intaga
Dan birni cewa take Dan koyamini turaci Allah yayi sameera mai son abu duk abinda tasa kanta
to ta rike kenan kuma da an fada mata so daya ya shiga kanta
Umma na fito bani sakon so nake nadawo da wuri so nake naje wurin Dan birni kinsan yau
yadawo Ohh kekam da naci kike to Allah Bada Sa'a ungo ki sayo min kayan yaji da sukari kinji
tace to innna ta amsa tafito tana tafiyarta a hankali ba abinda ke damunta har takai kasuwa tana
sayayarta saiga garbati shida tawagarsa suka tareta ke yar Baiwa sunanda kowa ke kiranta
dashi kenan. Tin dazu ina jiranki kin shanyani mekike nufi itadai bata ce komai ba ta sadda
kanta kasa tana wasa da yatsunta can sai ga Indo ta isu takallesu ta watsar wai kai wanne irin
bawo nekai ana soyayya dolene kunbi kun takurawa yarinya kun hanata sakat duk Inda taje sai
kunbita kamar wasu mayu. Ke yarinya ki iya bakinki mtseew indo taja karamin tsaki kukan
dai anyi shashashai wllhi ilu na tare da garbati yadaga hannu zai mareta sai iro yace kai
Narabaka gidansu basa yafiya wllhi kumuje tunda uwarta tazo indo taja hannun samira suka
wuce kekam dai kinji haushi su wadan nan banzayen zaki tsaya suna garaki to indo yakikeso
nayi dasu kinsan halin garbati zai iya kullamin sharrin da banjiba bangani to ki tsaya sokonci
har a Rena ki in anmiki tsiwa xakiyi kinuna bakya tsoronsu inba haka. Ba kinatare dajin haushi
to Inda banxoba fa sai yaya kenan sai ya kuwa illa in rokesu mtseew kinji haushi wllhi yar Baiwa

nidai muje kiraka ni nasayowa innata magarya tam muje.
Suna tafe suna tadi abinka da kawaye har sun manta Indo kawar sameerace tun suna yara
sa'an ni. Juna ne gidansu ba wani nisa dagidansu sameera indo akwai tsiwa ga iyayi batada
hkr kuma bata daikar raini shiyasa ake shankunta ko a cikin gari uwa uba tanada yayu masu
shiga mata gidansu duk Wanda ka taba ka tsokalowa kanka basa Barin kota kwana. Sallamu alaikum inna nadawo xanje gidansu Dan birni akoya min boko to yar Baiwa saikin
dawo kardai ki Dade kinji ta amsa da to ta fito da azama zuwa gidansu kabeer duk da tana
shakkun Hajiyarsa Dan ta tsaneta hasalima batason yana zuwa gidan baxata manta ranar da
takirata da mayya kekam kullun sai kin likewa Dana to ahir dinki sameera bata kawo komai
aranta ba ita burinta kawai akoya mata turanci ta iya zata jure duk wani fada na Hajiya
matsawar za'ta samu abinda takeso wan nan kenan.
Tana shiga gidan saida gabanta yafadi tadai danne ta Shiva cikin gidan kai tsaye falon Hajiyar
ta nufa suna zaune ita da 'ya'yanta husnah da yusrah sai kamal kanin Kabeer da Sallamarta
tashiga su yusrah naganinta suka washe baki suna dariya ohh Yar Baiwa sarkin son karatu har
an iso kenan cewar kamal Hajiya Kareema najin an ambaci sunanta ta hade rai kamar bata
taba dariya ba Samira na shigowa ta gaida Hajiyar INA wuni lafiya atakaice San nan taja tsaki
mtseew da dawowar tashi baza'a barsa ya huta ba kuma zaki wani zo kidamesa haba Hajjiya
meye laifinta nine nace tazo ai dalibata ya kk ya kwana biyu hpe dai kinzo dashiri danyau akwai
sababin darussa ta murmusa tace eah uncle to shigo ki zauna kamin naci abinci sai mu fara
Husnah kuma Ku shirya musamman ma ke yusrah naga bakya maida hankalinki sosai sunka
turo baki hva yaya week end nefa yakamata mu huta kai bana son shashanci kutashi maxa
Hajiya kareema hararar samira kawai take itadai ta tsani yarinyar nan nacewa ne da ita to
dolene saita iya turanci itada take ba yar kowa ba tashin kauye ko ubanme iya turancin zai
tsinana mata oho yarinya kamar mayya tabi ta ha nata sakat itada danta inyazo week end said
a dare da rana yana tare da shegiyar yariyarnan sai Yarbaiwa cewar Hajiya acikin zuciyarta.
Itadai sameera ta takure gefe jiran fitowar uncle Kabeer kawai take yazo yafara koya mata
abinda zata karu tabar gidan yana kamalawa tafito da book rike a hannunsa yace to daliba muje
garden ko ta mike su yusrah ma suka biyota suka biyo bayanta suna isa kowa ya zauna a
kujera yafara gabatar musu da lesson yayinda yar Baiwa da yayi tambaya take amsawa itada
batamada lesson book amma yusrah sai a hankali gara ma Husnah tana Dan ja haka da haka
har suka kare kasancewar ba lokaci dayawa 'Yar Baiwa tai godiya takoma ta ma Hajiya sallama
ta wuce zuwa gidansu tana zuwa ta rungume ummanta tana murna take Bata labarin abinda
aka koya mata haka rayuwar samera takansance har karshen sati itadai burinta tasamu ilmi
Dan ta taimaki mahaifanta!!!

2 be continued
Maman ussee

� 'YAR BAIWAH�2⃣

Maman ussee

Rukayya 'ya CE ga malan sa'idu ita kadai Allah ya azutarsu da ita bayan sunsha wahala matuka
kamin su sami haihuwa shekarar su 10 da aure ko batan wata ba'a taba yiba a gidansa
kwatsam sai ga cikin Rukayya ansamu karkuso kuga murna a wurin malan sa'idu ya dauki burin
duniya yasaka akan cikin nan mai dakinsa har mamaki take duk da itama tana burin taga
kwanta a duniya Dan baxata manta ba ko haihuwa akayi idan taje barka ba'a. Bata jariri wai
batasan zafin haihuwa ba Dan haka.Baxa a bata ba tasha kuka amma dayake mijinta na
matukar kaunarta sai ya lallasheta da kalamai masu dadi yana kwantar mata da hankali yana
lurar da ita haihuwa ta Allah ce kuma Allah yana sane dasu karta damar da kanta wata rana
suma Allah zai basu nasu rabon haka ne kam gashi hkrinsu yabasu yau Allah yabaiwa
salamatu ciki haka sukayita renon cikin har Allah ya ingantashi Rayuwa kenan(mai hakuri
mawadaci) malan Sa'idu mutumin garin Raba ne asalin su fatakene sukanje fautaci gari gari
anan ne Allah yaha dasa da salame sunana da ake kiranta kenan jinisu ya hadu sosai Dan ita
yar dagacin garin Damagara ce kuma duk bako a gidansu yake sauka suke basa masauki
anan me Allah ya hadasu har aure ya shiga duk da dagaci. Baisoba a cewar sa bayason ya
baiwa.bako yar sa Dan su danginsu auren dangisukeyi haka salame ta dage sai sa'idu aka
wanke aka kaita garin raba duk da sun raina da arxikin sa'idu haka suka baro yar uwarsu suka
koma damagara haka kuma rayuwarsu takansance itada masoyinta gwanin sha'awa malan
sa'idu marayane su biyu mahaifinsu ya haifa malan sa'idu shine babba sai mai bi masa atine
wadda bayan haihuwar tane mahaifinsu yarasu duk nauyin gida yadawo akan Maman sa'idu
duk da lokacin. Bai wani girma ba sosai atine na karama itama haka dai sukaci gaba da rayuwa
yau da dadi gobe da ciyo har Allah ya tashi kafadarsu Atine kuma tayi aure ta auri Habu Wanda
shi a birni yake zama da akayi aure yadauki matarsa suka koma can da zama sai dai insunxo
ziyara

Haka rayuwa tasance gwanin sha'awa salame da sirikarta bamai jin Kansu har aka wayi gari ta
haifo santaleliyar yarta mai ban sha'awa kowa sai santin 'yar yake kamar kasace ka gudu
daranar suna ta zagayo aka saka mata Rukayya sunan mahaifiyar Maman Sa'idu suna
kirantada 'yar baiwa kasancewar Allah yamata hkr tun tana karama batada hayaniya ko
wanason Rukayya haka ta taso cikin kulawa ga takwararta na sonta bataso taji kukanta ko
wasa ake aka doketa yanxu nan zakaga Baaba ta daura ta yafa wai sai taji mafarin dukan yar
lelenta abinka da yara kowa shakkar taba Yar Baiwa yake Dan kar yajaxama kanshi mita a
wurin Baaba Dan har gidansu mutun takanje idai game da yar Baiwane

Luv u all my fans
Maman ussee




� 'YAR BAIWAH�5⃣
Maman Usman

Haka suka ci gaba da ratsa sabara har suka cinma titi sukaita tafiya tun Rukayya na kallon gari

gari har ta gaji tai Bacci tasake farkawa kuma basu kaiba.

Ai kuwa basu suka isa garin sokoto ba sai misalin karfe 6 na yamma suna isa suka dauki
hanyar arkila federal lowcost adai dai saitin wani gida ma dai daici yayi faking kamin nan ya
umurci Rukayya data fito bayan ta fitone ya bude both ya Ciro mata yar Jakarta ya CE shiga
mana ai nan gdnku ne ta dauki jakar ta shiga cikin gdn shi kuma ya bude get yasaka mortar a
cikin gida San yabi bayan Rukayya.

Da sallamar sa ya shiga cikin gidan yana kwalawa Atine kira maman sajeeda maman sajeeda
kin gammu sai yanxu ko oyoyo Abba cewar Abdallah yaxo da gudunsa mahaifin nasa yadaga
sa sama yana dariya sweet boy ya ina mamanku da Auntynku suna kitchen cewar fadil daya
fito da niyar zuwa masallaci ya gaida Abban nasa yaja hannu Abdallah suka wuce Atine tazo ta
rumgumeshi sannu da zuwa my Dear kunsha Hanya ya INA yar tawa banganta ba au ai na zata
tashigo tin dazufa nace da ita tashigo Dan zanshigo da mota kila ko bata gane kofar bane oho
bari in dubota daga nan na wuce masallaci da an fara kiraye kiraye ko ta amsa da to.

Yar Baiwa kuwa tunda tashiga gidan takasa gane hanya kawai sai kalle kalle take ta Shafa nan
ta taba can tanata mamakin ikon Allah can dai ta tsaya a wurin flawers tanata mamakin wai yau
itace a birni muryar mutane datajine ya fargar da ita sai ta kewayo ta Inda ta biyo daga farko
Rukayya INA kika shigane ko baki gane hanyar bane ta sadda kanta kasa shima murmushi
yayi ya ja hannun ta ya kaita har cikin gidan kamin ya koma zuwa sallar magrib,

Yarta barka da zuwa ya su yaya da Baaba ta amsa suna nan kalau sunce na gaidaku harma da
abu akace na kawo muku tau Rukayya bari yanxu kiyi sallah sai kiyi wanka kici abinci kinji ko
bara na kira sajeeda taje dake dakinta saita nuna maki komai kinji ki saki jikinki kinji nan ma
gidankune munan iyayenkine ki daukini a matsayin ummanki ki dauki Abban Abdallah a
matsayin mahaifinki bakida matsalar komai kinji ta ammasa da to,

Kallon falon ta farayi Wanda aka kawatashi da kujeru masu kyau sai kayan kallon da dining
area sai kuma dayan gefen store da kitchen sai dakin yara dake kusa da store gefe daya kuma
room& falor ne sai dakin me gidan dake kusa da na sajeeda cikin kankani lokaci takarewa gidan
kallo a ranta fadi take aljannar duniya dankari Ashe akwai ire iren wadan nan Abubuwan more
rayuwa haka tab gaskiya maganar hausawane da sukace nazaune baiga gari ba.

Murya Sajeeda CE ta dawo da ita a duniyar tunanin da ta Lula yar uwata zomuje kiyi sallah kinji
ta amsa da to yayinda tabi bayan sajeeda dauke da Jakarta a ka suna shiga dakin wani sanyine
ya doki fuskar Rukayya tare da daddadan kamshin air fresh sajeeda taja hannunata sukashiga
bayi ta muna mata komai kamin nan ta fito ta barta me Rukayya zatayi inba sake baki ba ta fara
tabe tabe ba abinda yafi Jan hankalinta irin gani. Kanta datakeyi a mirror sai murmushi take can
dai sajeeda taji shuru ba labarin fitowar ta gashi ita har ta gama sallah amma Rukayya. Bata
fito. Ba ta kwankwasa kofa yadai Ruky naji ki shuru koda matsalane a San nan ne yadawo
haiyacinta ta tuna nan wai bayan gidane ta kunna tap tayi alwala San nan tafito tana fitowa
sajeeda ta bata sallaya da hijab ita kuma ta fada toilet Dan tahadawa Rukayya ruwan wanka.

Bayan ta kamala sallah ne sai ta karewa dakin kallo ba komai bed ne kawai sai drower sai
dressing mirror ba laifi kam gidan ya tsaro sosai bayan tayi wanka ta fitone sai ta Shafa mai
kawai sajeeda CE tabata. Body spray tashafa Dan sajeeda akwai son kamshi zata girmi
Rukayya kadan Ruky cewar sajeeda kidaukeni a matsayin yar uwarki kuma kawarki nasan
bamu wani saba ba Dan ko munje can Raba ba wani dadewa mukeba su mummy sun muna
bayanin komai bakida wata matsala kiyi sallar isha sai muje muci abinci kinji � murmushi tayi
hadi da yin sallah tana idawar itama sajeeda sallar tafara yi bayan takammala ne suka fita tare
suka fito zuwa wajen cin abinci anan suka tarar da iyayesu har sun fara cin nasu sai Abdallah
ne yace daddy wan nan CE new Sister dinmu ko ai na Santa a Raba take itace Baaba take
cewa yar Baiwa ko aikuwa kowa ya fara dariya kai son ka cika surutu dayawa eah sunanta
Rukayya daga yau sister Ruky kunjiko fadil yes momi suka amsa Abin yabaiwa yar baiwa
sha'awa a ranta tace lallai inbaka mutu ba zakasha kallo haka akaci abinci cike da raha ana
kamalawa sai kuma aka fara labarai anan ne kuma Daddy yafara yiwa Rukayya tambayoyi. Ba
laifi tasan wasu wasu kuma bata amsawa sai kuma fadil da Abdallah suka CE su bacci sukeji
Sajeeda ma taja Ruky sukabar mummy da daddy a falo.

Daddy yanisa gaskiya da ace Baaba bata amince ba da an cuci yariya kinga yanda takeda brain
kuwa Dear Mummy tayi murmushi Allah dai yabamu ikon rike amana ameen ta amsa nimafa
azo asan yanda za'ai dani Dan ah gajiye nake ya kashe mata ido daya ta murmusa da tasan
halin Mijin nata,
A bagaren su Sajeeda kuwa banda tadi ba abinda akeyi sun Dade suna fira kamin nan su kayi
addu'a suka kashe wuta suka kwanta Rukayya kam godiya takeyi ma Allah wai yau itace a. birni
dasunan boko.

Muje zuwa kuna tare da Zeenat Yusuf maman ussee


� 'YAR BAIWA �6⃣

Maman ussee

Tun da asuba mommy tashesu daga bacci Dan su yi sallah bayan sun idar ne kuma suka sake
koma wa bacci kasancewar week end ne ba makaranta,
Basu suka tashiba ba sai kusan 10:am wanka suka farayi kamin nan sajeeda ta ja hannun yar
uwartata domin suje cin abinci Dan tasan yanxu kowa ya tashi dayake al,adar gidan ne atare
ake cin abin suna fito gaida iyayensu sunka farayi kamin. Nan Abdallah da Fadil suka gaidasu
suma mommy CE tace 'yata bawata matsala saiki Rukayya tace ba komai insha Allah daga nan
kuma akayi saving din kowa yafara cin abinci amma banda Rukayya dantakasa cin abinci
itasam bata saba dashi ba tafi son dumamen tuwo ko koko da kosai ko waina amma INA ita in
cin wan nan kwamacalar,
Daddy ne ya kula da ita sai yakira sunanta Ruky ya.bakya cin abinci ne ta sadda kanta kasa

cikin in INA tace a gida koko nakesha ko dumamen tuwo ai ko mexasuyi inba dariya ba Mummy
CE tace ki Dan Dana mana kiji ai da dadi inbaxaki iya shaba to kici doyar mana tadai daure tayi
spoont daya na damar miyar typeyocer din ai kuwa saita hau sha Sajeeda dariya kawai take
kasa kasa ,
Bayan sun kammalane daddy yace dasu su shirya aje islamiya yaushi da kansa zai kaisu Dan
ya mika Rukayya nan danan kowa yahau shiri kowa tafito cikin uniform din Islamiya Daddy
yafito suka fice gabaki daya mommy kawai suka bari agidan,

Abakin get yayi fakin yayinda su Sajeeda suka nufin classes dinsu shi kuma ya nufi office din
malamin makarantar yaga batar da Rukayya a matsayin daliba akayi mata tambayi ba laifi kan
Dan ko a can Raba tana zuwa makarantar allo bayan an kamla aka bashi takarda yasa hannu
yabiya kudi sai suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login