Showing 12001 words to 15000 words out of 26574 words

Chapter 5 - YAR BAIWA Complete book by maman Usee .pdf

02 Jun 2025

1734

dinta ya

canja, gabaki daya fara,ar ta.
Ta dauke murmushin karfin hali tayi sannan tace bakomai Daddy bayaso ya takura ta duk da ya
fahimci dakwai wani Abu amma bayaso yayi forcing, dinta dole saita fada basar da zancen
akayi aka dauko wani zancen na daban,
Basubar asibitin ba sai guraren 10:30pm ya dauki su Sajeeda da Abdallah da Fadil zuwa gida
yayinda aka bar mummy ta kwana da Rukayya kamin gobe su nemi sallama, Sajeeda ma
ba,ason ranta ta tafi ba Dan dai Daddy yace gobe dakwai zuwa skull kuma bai dace Dan
Rukayya batada lfy Sajeeda taki zuwa makaranta ba dolene ita taje , Bayan sun tafi. Mummy ta dubi yarta tafara yimata nasihohi Dan ta kula da kanta, da abubuwan
da duk suka dace uwa ta fadawa yarta wasu Rukayya saidai ta sunkuyar da kanta kasa Dan
kunya takeji mummy sai dai tayi murmurshi , Dan tasan Insha Allah irin tarbiyar da suka baiwa
yaran su da wuya su fandare inba wani ikon Allah ba kuma tana musu fatan samun kariya da
duk wani sharin mai Sharri,
Kashe gari tun safe Sajeeda ta tashi tashirya cikin uniform dinta, tanata jin wani iri Dan ta Riga
yasa ba da komai a tare sukeyi da yar uwarta Rukayya sabanin yau da ita kadai takeyin komai
sabo kenan turken wawa. Bayan Daddy ya ajiyesu a skull saida yabiya office din principal yayi
report, cewa Rukayya batada lfy sai dai next week zata fara shigo wa insha Allah da yake ranar
laraba ne abin yafaru gashi kuma yau alhamis da yau da gobe baxata shiga ba Dan assabar da
lahadi week end ne sai dai on monday , principal din yace it's OK badamuwa Allah yabata lfy sai
dai on Monday din nan tashigo saboda sun fara texts kar tayi missing Dan nasan yar wajenka
she's very hard working student Daddy yaji dadi sosai ya basa hannu sukayi misabaha kamin
nan ya fice daga skull din, zuwa Hospital Dan ya dubo ya jikin na Rukayyatu.
A asibiti kuwa bayan Doctor ya duba ta da safe. Ba wata matsala sai ya rubuta musu sallama
kuma ya umurci data sha maganin ta abisa ka,ida kuma cikin lokaci, Daddy kawai dama suke
jira yazo su wuce da isuwarsa daukansu kawai yayi bayan yayima Rukayya ya jiki ya kwashesu
sai gida daga nan kuma ya ficewarsa zuwa gurin aikinsa, Faruuq ne yafito daga cikin motarsa kiran Mercedes sanye da Riga da wando na jeans wandon.
Baki Riga kuma fara anyi mata rubuta da bakaken harufa an rubuta it's my Time bai zarce
ko,inaba sai admin block yaje yayi sing kamin nan ya wuce staff office ya dauki abinda zai
dauka ya nufi class dinda yakeda lesson wato A class SS one A ajin su Rukayya a zuciyarsa
muradin ganinta kawai yakeyi Dan tun jiya yakejin faduwar gaba gani yake kamar wani Abu
yafaru da ita bayan sun rabu jiya dashigarsa, bayan student sun gama gaidasa Sit dinda take
zama ya kalla amma ga mmkin sa ba tanan sake ,daga Kansa yayi ya kalli wurin bayaso ya
tambayi yan class dinsu Dan kar suyi suspecting din wani Abu ,haka dai ya daure ya fara lesson
din zuciyarsa sai zafi take baiga Angel dinsa ba, wata dubara CE ta fado masa arai dayake jiya
books din su, yana hannu sa shine yayi amfani da wan nan damar ya aiki class captain Dan taje
staff room ta dauko books din tanan zai San in angel dinsa na nan ko bata nan bayan ta kawo
yafara mark yana kiran suna Dan mai littafi yazo yakarbi kayansa , da haka har yakai ga nata
yakira name dinta Rukayya Sa,eed shuru ba Wanda ya karba ,saida ya maimata har sau 2 .
Kamin nan yan class dinsu ka CE uncle yau batazoba ,what? Yafada adan razane sai dai a
hankali yayi kokarin saita kansa kamin. Nan yace saboda meye batazoba yau muma bamu sani
ba suka. Bashi amsa daga baya sukace akwai dai sister dinta a C class sai in ita za,a tambaya
cewa kawai yayi suje su kirata member dayace cikin yan Class din taje block dinsu Sajeeda

danyin kiranta bayan tazo, uncle Faruuq yakalleta ke INA sister dinki meya hanata zuwa skull
yau , uncle batada lafeeya kuma whorse Dan yanxu haka tana asibiti ,Dam Dam Dam yaji
gabansa ya fara duka acikin ransa cewa yake to meke damun my angle yazama wajibi naje
naganta to amma ta yaya zanje? A wane matsayin? Ganin zai batawa kansa lokacine yasa ya.
Baiwa sajeeda book din Rukayya tare dayi mata fatan samun sauki ya tambayi Sajeeda a wane
asibiti ne aka kaita specialist kawai tabasa amsa ta juya zuwa class dinsu Dan daukar lesson
dinta.

Maman Ussee😘

Naga sakonku my fans INA godiya sosai da kulawarku👊
� YAR BAIWAH �2⃣0⃣
Maman Ussee😘

A gurguje ya kammala duk wani abinda yakeyi yaje yadauki excuse, bai zame a ko,inaba sai a
specialist hospital, room by room yayita shiga amma komai alamarta baiganiba kamar ya daura
hannu aka yayi ihu meyasamu Angel ya akayi bansaniba anya zan iya jure rashin ganinta kodai
naje na tambayi sister dinta gidansu, ohh no baxan iyaba banaso ,ta fahimci wani Abu a halin
yanxu she's still young, batasan meye so ba shikadai yaketa sambatunsa , jiyake zuciyarsa
kamar zata faso kirjinsa ta fito in bai samu Rukayya ba ohh wai meyake faruwa dani ne young
girl tanata wahalad dani abanxa batama San inayiba,
car dinshi ya shiga ya tadata ya bata wuta sosai sai gida haka shima yakejin kansa kamar
bashida lfy har mamakin Kansa yakeyi ,wai yarinyarda bata wuce 15 ba take rudashi ,haka
yaga mata kala2 amma baitabajin wani fillings akansu. Ba sai ita, ita din daice a cikin
zuciyarsa!! A katon Falon gidansu ya zube. Dafe da kansa , ya Dade yana zaune a gurin yanata
tunanin ,yanda zai bullo wa lamarin Dafa shi yaji anyi, a hankali ya dago Kansa yayansa yagani
yadai Umar lafiya kake kuwa naga kayi zurfi inata sallama bakajiba, Haka dai naganshi kwanan
nan bai cika son surutu ba dama shi bai faye magana. Ba amma kwanan, nan abin yayi whorse
cewar Hajiyarsu dago Kansu sukayi a tare suka gaida mahaifiyar tasu , cikin girmamawa, cike
da kulawa ta amsa ,dama idan kaga fara,ar ta to tana tare da ya'yan tane .
Hajiya Kubrah kenan manyan mata Abubakar ya dubi mahaifiyar sa mum wai yaushe ne su
Aleeyu zasu dawo ne sunfa karasa exams dinsu jiyama nayi waya da Usman ba abinda ya
tsayar dasu kawai dai shiriritace irin tasu, Hajiya kubrah ta nisa oho sai sun gama hutawa inga
zaman London yana musu dadine shiyasa, Amma duk ranarda Alhaji yaganosu kashin su
yabushe cewar Abubakar kawai Dan dan sun maida ba a, bakin komai. Ba sun kare exams
shine suke tayiwa Abba karya yana tura musu kudi bayan sunsan sun kare Dan kawai rashin
kishin kai, kai dakata ra,ayinsune saboda haka ka kyalesu sai ranarda sukaga dama su dawo
Kai takura maka akayi dakake karatun, wayene ya matsamaka, baice komaiba dai shi a duniya
yana mamakin hali irin na Hajiyarsu kwata2 bata son a takura wa ya'yanta kawai Dan suna da
gata Allah dai ya kyauta,
To Mum su Afra fa sai yaushe, kaga Malan banason sa,ido towai Ina ruwanka ne kai kake biyan
kudin makarantar ne ko ta aljihunka ake biyan kudin meye naka a ciki ,kabarsu suyi abinda

sukeso lokacinsune, Umar Faruuq da yaga surutun nasu kara chaja masa kai kawai zasuyi fita
yayi daga falon yanufi sashensu Dan Inda sabo yasa ba dajin irin wan nan dramer din ,tsakanin
Hajiya da Abubakar, kawai dai shi Abubakar, din ne da na cewa kullun saiyama Hajiya maganar
dawowar, k'annensa Nigeria amma amsa dayace take bashi ,shibazai iya hkra yasa masu ido
bane, gani yayi idan yabiyewa Hajiya da Abubakar sai sun kara karamishi wani sabon al,amarin
gara yabar musu gurin,
Dakinsa ya nufa kan bed dinsa ya zube zuciyarsa sai bugawa take runtse idonshi yayi yasake
budewa ahankali ya furta I LOVE YOU RUKAYYAH.

Sajeeda kuwa yinin ranar a takure tayi shi badadi tasaba komai tare sukeyi ita da sister dinta
gashi yau komai ita daya takeyi har break ma kasa yinsa tayi a dadafe taga time din tashi daga
skull din yayi koshi , jitake kamar tayi,fira taje gida ta shirya ta tafi asibiti dan ganin Rukayya,
Dan batama San an salami Rukayyar ba, haka takeji kamar ma ta wuce asibitin direct. A yauma skull bus dinsu gani take kamar ba tafiya suke yiba Dan bata ganin saurin tafiyar ,yau
Sajeeda kenan aminiyar Rukayya,
San da mai bus ya ajeyeta da sauri ta fada cikin gidan amma ga mamakinta taga komai tsaf an
gyara ko,ina kamshi tashi kawai takeyi ga kamshin girkin mummynsu, bakowa a falon Room
dinsu ta shiga ,Ga mmkin ta sai ganin Rukayya tayi akan bed tanata barci abinta hankali
kwanace ,wani murmushi Sajeeda tayi najin dadi mai kayartarwa da sauri ta isa , bakin gadon ta
Shafa fuskar Rukayya sister ya jikinki hope kinji sauki Dana Rukayya ba. Bacci takeba jin bude
kofane yasaka ta kulle ido, bude idonta tayi a hankali ta Dora kanta a saman jikinki sajeeda naji
sauki sosai sister I miss u so much me too ,sukayi murmushin jin dadi kamin nan sajeeda ta cire
uniform dinta ta fada bathroom domin yin wanka.

Maman Ussee😘

� 'YAR BAIWAH �2⃣1⃣

Maman Ussee😘

Sajeeda ta fito da ga wanka ta shirya cikin dugowar Riga ta Atamfa simple dinki , dama ita bata
Faye yin make up ba inkaga mai Make, up to Rukayyace,
Sallar La,asar ta farayi kamin nan ta zauna ita da Rukayya tana gaya mata abubuwan da suka
faru yau a skull, ohh kinga har na manta ga book dinki da , aka bani dazu uncle Faruuq
,mtseww Rukayya taja tsaki Sist bar fada min sunansa mugu kawai 😳 cike da mamaki sajeeda
ta kalleta wani abune yayi miki hln ,Rukayyah , sai a sannan ne ta tuno da katobarar da tayi but
bayanda zatayi dolene ta fadama ,sajeeda gaskya koba komai baxata iya yimata Hidden din
komaiba,
Nan ne ta sanar da ita duk abinda yafaru . Sajeeda ta dafata kinga kiyi hkr ba shine sanadin
shigarki damuwa ba dama dai can su Sister Jameela suna jin haushinki kawai ki rabu dasu
Allah yana gani ki rage tsanar da kikayi masa wllhi baki ga yanda yadamu dazu ba danace
bakida lfy har tambayana ma yayi a wane hospital, aka kwantar dake nagayamai kinsan kuma
ba kyau ka tsani Dan uwanka musulmi Rukayya nasanki da saurin yafewa kiyafe masa kimaida

komai ba komai ba zai wuce kinji my Sister,
To kawai ta CE amma ga alama maganar bata shiga cikin rantaba tadai basarne Dan bataso
Sajeeda ta fahimci wani Abu a cikin zuciyarta ko cewa takeyi hava Dan bakisan azabarda
nasha bane shi,isa kikace hakan.
Suna zaune a dakin sun dauko sabuwar fira mummy tashigo dakin ta kalli 'ya'yan nata cike da
sha,awa tana matukar so tagansu cikin farin ciki da annashuwa, yadai yaran Daddy ana tadine,
Rukayya kinsha maganin ki eah tasha mummy yanzun nama ta kare sha ai zan kula da komai
insha Allah yauwa yar albarka Allah yayi muku Albarka a tare suka amsa da Ameen.
Faruuq kam Sam zaman dakin ya gunduresa jiyake inama ace yasan gidansu Angle da yaje
yanxu kozata wulakantashi Amma kuma tayaya shida ba yawo yake cikin garin sosai ba
balantana ma ya iya sanin unguwarsu harta, kai ga sanin gidansu Ohh Allah gani gareka , ka
sassauta min wani kuna yakeji a cikin zuciyarsa haka ya wuni ba walwalla a tare dashi da kyar
yaga marece yayi ya Dan samu yayi wanka yasaka kayan sa Dan yazaga gari ko zai rage zafin
ra dadin da yakeji a cikin ransa Dan ya fahimci zamansa shikadai ba karamin kara, dagula
masa lisafi yakeyiba. Unguwar mabeera ya nufa gidansu wani friend dinsa yana cikin tukin
mota phone dinsa, ya hau ring, kamar karya daga danshi a halin yanxu ba kowane surutu yake
iya saurareba indai bana Angel dinsa bane, baima tsaya duba mai kiran ba receive kawai ya
lasha ya kara wayar a kunne Hello!!! Daga dayan bangaren aka amsa Hello sweety ykk koba,a
fadaba yasan ko wacece Salma kiyi hkr ina driving, ne yanxu zan kiraki anjima.
Baima jira cewar ta ba ya katse wayar tare da jinjina hali irin na Salma kullun. Saita kirasa ta
wani mayance masa ko anaso dolene oho.
Wacece Salma? Salma Kabeer 'yace ga Alhaji kabeeru Mainasara , aminin Alhaji Bashirne
mahaifiyar Salma kawar Hajiya kubara CE ta sosai Dan kusan halin su ne yazo daya, shiyasa
amintar tasu tahadu saidai ita mahaifiyar Salma tsayayyar mace CE duk abinda tasa agaba to
ba shakka saita mallakeshi su hudune a gurin mijin amma saboda kissa da tuggu irin na Hajiya
Suwaiba saida tasaka duk aka kori kishiyoyinta yazama ita kadaice a gurin mijin sai abinda tace
ta saye shi tamayar da Alhaji kabeeru mijin Hajiya.
Su shiddane a gidansu Abdullgafar sai Abdullwahab Da Abdulrahman Sai kuma Salma Da
kanwarta Safeeya Salma cikakkiyar yar bariki CE sosai, ta goge sosai da duniya ta hadu da
Faruq ne a ranarda sukaje gidansu ita da hajiyarta tun daga ranar da yafara ganinshi taji a
duniya batada Wanda takeso sama dashi , duk da tanada nanema duk bata saurarensu tun
sanda ta hadu da faruuq da kanta tayi masa talar kanta, butshi ko kallo ma bata isheshiba, Dan
shi ya tsani macce marar kamun kawai Wanda Salma na ciki kawai dai yana kulatane sanadiyar
Hajiyarsa Dan ya taba yiwa salmar walakanci a gaban Hajiyar ta nuna masa baccin ranta kuma
ta umurceshi da karta kuma ganin ya yima Salma walankanci saboda hakan ne yake Dan kulata
but har yanxu itace take kiransa da kuma yawan zuwa gidansu acewar ta zo gaida Hajiyar ne
kuma ita dama Dan taga Faruuq take zuwa gidan.
Faruuq yaja tsaki dama nasan Salmace wllhi baxan daukaba Dan yau najawo kaina kira kenan
ba adadi kashe ma wayar zanyi Dan na huta dai2 nan yayi packing a kofar gidansu misbahu
abokinsa .wayar ya dauko yakira Misbahun bai wani dadeba ya fito ya shiga motar Faruuq din,
suka fice daga unguwar.

Maman Ussee😘

� 'YAR BAIWAH �2⃣2⃣

Maman Ussee😘

Shigiwar Daddyce ta saka su fitowa domin su gaidasa, ahh lallai Rukayya jiki yayi sauki kina
daishan magani ko eah Daddy inasha sosaima to masha Allah,haka aso after sallar Isha kowa
ya hallara a falo domin cin abincin dare kamar yanda suka saba ,mummy CE tayi saving dinsu,
bayan kowa yaci ya koshi Alhmdllh, suka dawo falo domin yin kallon labarai Wanda kusan ma
ince kullun akidar gdn ne kamin time din bacci yayi, saida kowa yara jin bacci San ,nan da
guda2 yaran kowa yabar falon mummy kawai aka bari da Daddy ko suma dama jiran yaran
kawai sukeyi suma suka kashe duk kayan kallon suka tafi dakunansu domin yin bacci,
Sajeeda ta Riga Rukayya tashi daga bacci dayake tasan dawan garin bata tsaya tayar da itaba
alwala kawai ta fada toilet ta dauro ta bayar da farali ta dauko qur,ani ta fara karatu cikin
muryarta mai dadin saurare Daddy ne ya kwankwasa kofar dakin Amma jin ana karatu ya
tabbatar masa da sun tashi daga bacci shima dawowarsa kenan daga masallaci, kira,ar karatun
sajeeda ne yatayar da Rukayya da yake a bayyane take karatun addu,ar tashi daga bacci ta
fara yi kamin nan tayi mika ta sauko da kafafunta kasa ta nufi bathroom domin yin wanka ta
gyara kanta, fitowarta daga wanka daure da towel a jikinta dayan towel din kuma tana tsantsane
kanta , dago kai Sajeeda tayi manya masu gari antashi daga bacci eah Sist shine baki tayardani
ba to ayi hkr ya jikin naki Rukayya ta kalleta cike da murmushi naji sauki sosai kiyi sauri ki
shirya karki makara Allah yabada ladan karatu.
Shaf sajeeda ta manta da wai yau ana zuwa skull Dan ganin yar uwarta bata shirya ba a
gurguje ta shiga wanka ta fito tafara saka uniform dinta ta dauko sock da sandals dinta yasaka
Rukayyace ta daukar mata skull back har suka fito zuwa dakin mummy suka gaidata kamin nan
sukaje dakin Daddy shima shirin yakeyi Dan ya ajiyesu ya wuce gurin aiki GT Bank, yadai
Rukayyah ya jikin naki Naji saiki sosai Daddy to Allah ya kara sauki suka amsa atare itada
Sajeeda, har cikin mota Rukayya ta rakasu Fadil ne agaba Sajeeda da Abdallah kuma a baya ta
daga musu hannu har suka bar unguwarsu zuwa skull su Abdallah Daddy yafara saukewa
kamin nan ya nufi hanyar skull din su Sajeeda itama ya sauketa direct assembly ground ta nufa
bayan gabatarda jawabai aka sallama student kowa yakama Hanyar zuwa class dinsa.

A bangaren Faruuq kuma kasa bacci yayi da dare har wani. Zazzabi2 yakeji yana rufeshi da
kyar ya iya tashi yasha magani zuciyarsa sai zafi da kunci take masa yakasa controlin din
Kansa ,jiyake kamar zuciyarsa Faso kirjinsa zatayi ta fito in bai samu Rukayya ba ,washe
garima sanda ya makara tashi Abubakar ne yaji shuru baiga fitowarsa ba ya shiga knocking din
door din Umar can cikin bacci yaji ana kwankwasa kofar dakinsa bude idonsa yayi ya kalli
agogon dake manne abangon dakin nasa what? Yadan zaro 😳 Ashe har gari ya wayema shut
yau na rasa jam,i saboda ke my Angel I love you ya furta a gurguje ya fada toilet ya dauro
Alwala ya. Bayar da farali kamin nan ya shiga wanka yana fitowa mai yafara shafawa bayan ya
taje Kansa da cum saida ya shirya tsaf cikin shada brown color yasaka hularsa car key dinsa
yadauka da Jakarsa ya fito a waje suka Hadu da Abubakar suka gaisa, kamin nan yashiga cikin

gida domin ya gaida Hajiyarsa ,Yar mulkin tana zaune a falo da ita. Bacci safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login