Showing 21001 words to 24000 words out of 26574 words
Rukayyah ya Nufa ya tarar da ita tana ta karatu
murmushi ya sakar mata kamin ita kuma ta Gaidasa ya Amsa ,, yace Yauwa Sarkin tsoro
murmushi tayi cike da kunya kamin ta gama ta fito tadan gyara wasu abubuwan Dayake ma
komai Normal yake sabo ne kawai dayi Sai Farouq kam Room dinsa ya nufa ya koma Bacci
Rukayya ko rasa abinyi tayi taje kawai ta kunnah T.v tashiga Kallo Abinta.
" misalin 8:30Am Afra tashigo gidan D'auke da Kayan Breakfast nasu Da murna Rukayya ta
tareta tace sai yanxu Afra tace tab koyanxuma sakone,, yakawo ni kinga Ficewata ma zanyi
Dan Banaso Yaya ya Yiman surutu yafara cewa INA masa ,,Sakko tun da safe a gidansa ,,
Murmushi tayi ta karbi kayan ta jera a dinning table Afra Bata wani jima ba tafice tace Zata
dawo zuwa anjima Rukayyah cigaba tayi da kallonta sai gurin 9. farouq ya fito D'auke da
Fara,arsa yasha wankan Boyel milk colour ,, yace yadai my Angel ,, tace lfy Lou Kinci Abinci ne
ta girgiza masa kai yace A,a Ba tun dazu aka Aiko Da Abincin ba tace eah INA Jirankane yace
OK to zo muje muci tare suka ci Abinci saida Farouq ya Tabatar taci ta koshi kamin ya barta Ta
gyara gurin ,, ya umurceta data Dauko mayafinta suje part din Salma ,, Ba musu ta yi yanda
yace yayinda yake Gaba tana biye dashi Baya har suka is a Part din Zaune suka tarar da ita
Da. Sallama suka Shiga Rukayyah ta gaidata Wanda dakyar ta Amsa Farouq ne yanuna mata
guri ta Zauna Shuru ne yadan Gifta kamin FAROUQ yafara magana kamar haka :
★ Salma Kinga ga Rukayyah nan Amanace a gurinah kuma a gurin ki Banason Fada,,
Kuma Ku zauna lfy da juna Ku mutun ta junanku duk kanku INA sonku shiyasa na zauna tare
Daku Rukayyah Ki Baiwa Salma Girman ta karki Rainata kibita Duk abinda takeso indai bamai
wahala bane kimata kinsan Junah biyu gareta sai kinyi Hakuri da ita kinji Tace Insha Allah yace
Good . Allah yayi maku Albarka yabani Ikon yin Adalci a Tsakaninku Rukayyah tace Amin kamin
ya fice ita ma takoma part dinta Dayake Yan Yinin Amarya sun Fara Isowa haka dai Suka
kasance Har Rana tayi.
Maman Usseeyí ½í¸˜
'YAR BAIWAH 5⃣9⃣
~Maman~ ~Usseey~í ½í¸˜
★ Gab da Azhr Su Sajeeda sukazo sosai Rukayyah taji Dadi suka Zauna sukayi ta tadi sai
barkwanci sukeyi gwanin sha,awah sai tsokanar ta sukeyi badai ta kulasu banda murmushi
ba,abinda take musu Haka suka zauna sai Dare Suka gyara mata Part dinta tsaf sai Kanshi
ko,ina yake yi Basuda matsalar Abinci Dan Daga gidan Hajiya Ake kawo musu ,, Koyanxu
Abincin aka kawo su Afra suka Ni Driver Dan Ya ajiyesu gida harda Sajeeda sanda suka ajiyeta
a gida suka wuce Warsu gida.
"Rukayyah wani wanka ta Dauka mai Daukar Hankali ta Zauna a sitting Room tana Kallo
Abinta Dan Yau bakonta yazo Hankalinta a kwance. Batada wata damuwa phone dinta ne yayi
Ring ta Dauka tare da Sallama ,, mummy takirata da wayar Sajeeda tace Yadai 'Yata lafeeya
Lou kike ko tayi murmushi tace lfy mummy ba komai yauwa Dama dan na gaya mikine Ki Duba
Acikin Jakar da Sajeeda ta kawo miki zakiga ,, Wasu ledar guda biyu Dayar turarene na
Humrah a Ciki dayar kuma maganine ki sha da Madara tace tau Insha Allah sun tan taba Hira
daga Bisani Kuma suka katse wayar . ta sauke Ajiyar zuciya kamin ta ci gaba da Kallon ta.
★ Farouq Bai dawo gidan ba sai guraren 9:30pm Da shigowarsa bangaren Salma ya nufa
Baiganta anan fallo ba ya Shiga Dakin ta kwance yarar da ita Hawaye duk ya Bata mata
Fuskarta ,, wurin Gadon ya nufa Ya kira Sunan ta Salma. Bata kallesa ba Tace wai Salma
menene yake damunki Kwanan nan duk Kin wani Rame kin Hana kanki sukuni wai menene Nifa
ban kara Aure Dan na muzguna mikiba Dan Allah ki cire komai Aranki please hava Kamar wani
abu duk kinbi kin Hana kanki sukuni Batadai ce dashi komaiba ya Rugumeta yafara lallashinta ,,
dakyar yasamu ta Hakura shiya bata Abinci da kansa ya bata maganinta tasha Dan yaji Jikinta
yayi Zafi saida yaga tadan Fara Bacci ,, kamin yatashi ya wuce bangaren Rukayyah .
★ Da sallama yashiga wow" Ya Furta a Hankali saboda wani Daddadan kamshi da Sanyaya
zuciya Daya doki Hancinsa Amsa Sallamar sa tayi tare da Gaidasa ya Amsa yace hope dai
Bakiyi Fushiba Dan na makara tace No Bakomai Yace OK Kinci Abinci ta girgiza kai yadan
Bude idonsa yace tomeyasa Kosai tare dani Batadaice komai ba ta saddan kanta ,, Kasa tana
murza yan yatsun ta Matsowa yayi ya Shafa Gefen Fuskarta Yace zan Cire wan nan kunyar
Dan. Naga Alama Zata takurani yanufi Room Dinsa saida ya Rage kayan Jikinsa ya yasanya
Short Nikkah da Yar Singlet ya fito Kallo Daya tamasa Ta sauke kanta Kasa ,, Hannunta ya Ja
suka nufi Dining Dan Cin Abinci Sunayi suna Yar Soyayya Nakuma gefe Inata Kallon Ikon Allah.
" Bayan sun Kammalah kowannensu Dakinsa ya nufa Rukayyah Brush tayi ta watsa Ruwa
ta sanya Nightes masu shegen kyau Jajaye ,, ta Bude Tuearenda Mummy ta Aiko mata tashafe
Jikinta dashi ko,INA Kamin Ta zauna kusa da Bed Dinta tana Kallon pictures din da Sukayi
Dazu itadasu Sajeeda. Farouq ne yashigo Dakin Shima Kayan Jikinsa Ja ne masu Guntun
Hannu Zaunawa yayi kusa Da ita Yace mugani ta basa wayar sukaci gaba Da Kallonsu tare
Wani yayi Dariya wani kuma yace kai Kukam dai Kun iya Daukan photo to bari nayi mana wani
pic din ,, Ya Jata sosai ajikinsa yamasu photo Selpic Kamin ya Dora mata kiss Wanda ya Ba,in
kashe mata Jiki ,, Turning Off din Wutar Dakin yayi yafara Yimata wasan ni Da Zafi Zafi Wanda
Rukayyah ta Kasa Gane Ko tantace a ina take ,, Ganin Zai wuce Gona da iri yasanya ta CE
dashi Bakonta yazo ,, Dakyar ya iya Control din Kansa Amma fah Duk da Haka ,, Tasha Wahala
Dan Dakyar Ta lallabasa ya Hakura ,, Amma yadan samu Relief sosai Rugumeta yayi sukaci
gaba da Bacci Kulle musu kofa nayi Tare dayimusu Fatan tashi Lafeeya.
★ Sajeeda CE kwance a Room D'insu sai juye juye take saboda tasaba komai tare sukeyi
itada Rukayya yaigashi Bata jin motsin kowa Lallai Yaune take jin Rabuwarsu da Rukayyah Dan
Abin duk yataru yamata yawa gara Jiya Dakwai mutane to Yau kowa yayi Tafiyarsa Abin ba
Dadi A Hankali ta Furta tace I miss You Sister. Allah yabaki zaman lafeeya da Kwanciyar
Hankali. Wayarta ta Dauka tashiga whatapp ,,, Dan ta tagewa kanta lokaci da Dare . saida
tafara Jin Bacci ta Ajiye wayar Ta kwanta Sai Safe Daddy ya Buga mata kofa ta Tashi tayi
Sallah tadanyi Karatun Al-,Qur,ani Sai Karfe 8 Tatashi tashi Kitchen Dan Ta Dora Breakfast ,, A
kitchen Mummy ta Tarar da Ita Tace Hoo sannu Yau kinyi Abin kanki Murmushi Sajeeda tayi
tace Mummy an tashi lfy tace Lou Yau kin fito Da wuri tace eah Mummy tace Dan kinsan Ba
maiyine keda kikeda Son jiki Murmushi Sajeeda tayi kamin suka ci Gaba da Hada komai a Tare
Har suka kammala Hada komai Suka jera a Dining ,, Kowa yakoma Dakinsa Sai 10:Am Suka
fito sukaci Abinci kamar yanda Suka Saba Kullun ,, Daddy yace Allah Sarki 'Rukayyahtu ana
can mummy tace Ashe Bamu kadai ke Missing dinta ba yace gaskiya Baku kadai bane ,, Yauwa
Sajeeda Gobe Ki shirya kifara zuwa skull Ki shirya da wurifa Dan nasan Halinki tace Angama
insha Allah yace Good ,, suka ci gaba da cin Abinci bayan sun kare Sajeeda tashiga gyara gurin
mummy kuwa Tashiga kitchen Dan Ta Dora Girkin Rana .
★ Da Asuba Farouq yatashi yayinda ya gyarawa Rukayyah Kwanciyar ta Dan Jiya baibarta
tayi wani Baccin kirkiba wanka yafara yi ya nufi masallaci Dan Gabatar da Sallah sanda yanufi
Part din Salma ya tayar da ita kamar Yanda yayi jiya ,, Bai shigo. Ba sai Da aka kare Sallah
Yadawo Room dinsa yanufa ya kwanta. " Rukayyah kam bata Tashiga sai ,,, Guraren 7:30Am toilet tanufa tafara wanka tayi Brush
kamin tafito tashirya tsaf da ita daganinta kaga Amarya yauma kamar jiya gyara ko,ina tayi ta
fesa Turare tadawo Ta zauna tana Kallo a Sunnah T.v Kwankwasa kofa taji anayi ta tashi ta
Dauko mayafin ta kamin ta bude kofar Driver ne shikadai D'auke da Breakfast yace gashi inji
Hajiya tace a Gaidaki Rukayyah ta karba ,, Tace yauwa kace Angode Nima ina gaidata ta Kulle
kofar ta jera komai a dinning ta ci gaba da Kallon ta Hankali kwance .
~Maman~ ~Usseey~í ½í¸˜
'YAR BAIWAH 6⃣0⃣
Maman Usseeyí ½í¸˜
★ Sai guraren 10:Am Umar Farouq yatashi sai wanka yafara yi Kamin ya shirya tsaf Ya fito
ya tarar fa Rukayyah nata Kallo da murmushinsa ya iso gareta tare da Shafa Fuskarta,,,
Amarya Bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida . tadanyi fari da Ido tace Bama zan kashe kowa
ba Yace to muje muci Abinci Dan Nasan Bakici kina jirana ko kai kawai ta Daga masa yaja
Hannunta suka nufi Dinning area.
" A tare suka ci Abinci Yana ta tsokanarta bayan sun karene yayi ficewarsa ita kuma
tashiga gyara gun dasuka bata Ta wanke Kayanda aka saka musu ,, Abinci a Ciki ta sanyasu
cikin basket Dan dama Haka takeyi idan An kawo Na Rana sai ta Bayarda na Safe hakama idan
an kawo nadare saita Bayarda . kayan Rana Da Safe sai ta Bayarda na Daren Tadawo ta
Zauna ta Rasa Abin yi kawai sai ta kira Abbanta bayan sun gaisa yake Tambaya ta ya Sabon
guri Tace lfy Lou Alhamdullah ,, Haka sukata fira yabaiwa Ummanta harda Baaba ma sanda
suka gaisa Daga nan Ta katse wayar ta kira Daddy shima Tambayarta yayi ya sabon wuri tace
Lfy Lou ya kara yimata Nasiha mai Ratsa zuciya game da Zaman Aure ya Sanya mata Albarka
haka tayi ta kiran Yan Uwa da Abokan Arziki Suka gaisa Harsu Afra saida ta kira Tace su Turo
mata No din Hajiya bayan Ta kammala wayar ne Ta kirata cike da girmama,, Daga dayan
Bangaren aka Amsata sosai Hakan yayiwa Hajiya Dadi ta Tambayeta dafatar Ba Wata matsala
tace Bakomai lafeeya Lou yauwa Haka akeso Allah yayi maku Albarka Rukayyah ta Karba da
Ameen ta Ajiye wayar Ta Dan kishin gida kadan Batasan Sanda Bacci ya kashe ta ba .
★ Farouq ne Zaune a room Din Salma wadda yakasa Gane ma kanta cikin kwanan nan
Yana dai Biyematane Dan Bayaso Yashiga Hakkin Ta Allah yagani Bazai iya jure Rainin Hankali
ba Dakyar yasamu ya lallasata taci Abinci saikace Gareta Aka fara Kishiya duk ta fita
Hayyacinta Bayan taci sosai ya Bata magani Tasha Shida Kansa ya mata wanka yadawo da ita
,, Room dinta Ya kwantar Kamin ya yi Ficewarsa Dan Amsa kiran da Alhajinsa kemasa.
" Haka Rayuwarsu Takasance a Tsawon Satin nan Har Ranarda Ya Raba masu Girki Ya Kara
tarasu Ya Musu Nasiha mai Ratsa jiki Wanda Rukayyah kawai ta Dauka Salma kam Biris tayi
Dan Ita yanxu Kwata2 ta canja daga Sanin da Farouq yamata Salma ce Zata Fara yin Girki
Wanda Farouq ya CE Duk mai yin Girki to A part Dinta Za,aci Abinci Hakan bakaramin Haushi
yayiwa Salma ba Amma ba yanda ta iya Dole ta Hakura Dan tasan Halin FAROUQ Baya canja,,
maganar sa " Shikuma yayi Hakan ne Dan A kara Samun Had'in kai A tsakanin su ,,
" Da Dare Salma ta Rangada Girki Mai Rai da motsi yayinda ta Ci uban make ,,upp kamar
ba itaba ajima Anjima ,,ta Duba agogo haka Ta tsara komai sai wani Kisisina takeyi Farouq
baidawo ba sai misalin 9 Bangaren Salma ya nufa Da murna ta Taresa Shikuma sai wani Biye
mata yakeyi Dan Farouq Mutun ne maison a tarairayesa nan da nan ta Gama dashi Room
dinsa suka Nufa ya Rage kayan Jikinsa . Ganin Abin na Salma bamai karewa bane yasa ya
dakatar da ita yace Dear sorry kinsan yanxu Bamu kadai bane Jeki ki kira kanwarki muci Abinci
Kinga tana Jiranmu badan Taso ba ta Tashi yayinda Shikuma yadawo sitting Room yana jiran
Isowar su.
★ Rukayyah na Zaune A Dakinta Bayan ta karasa Sallah Isha Dan yau tayi Wanka karatun
Al-Qur,ani mai Girma takeyi Da murya mai Dadi a gurin mai Saurare Salma tashiga Noking din
Door Rukayyah bataji ba Dan Dayake karatun ya D'auke mata Hankali Abin ya matukar Tunxura
Salma tace Lallaima wan nan Yarinyar dani take Zance murda kofar tayi tajita a Bude Sa kai ,,
kawai tayi Mutuwar tsaye tayi Dan Yau itace Rana ta Farko data taba shigowa part din
Rukayyah tun Kawota A cikin Zuciyarta tace Tab Wan nan Dukiya da aka zuba mata a gidan
nan kamar wata yar Hamshakin mai Kudi A Hankali ta fara Notice din komai Har kitchen sanda
tashiga bata Tsinkeba saida Tashiga Room din da take jiyo Saurin Kira,a natashi bako Sallama
ta Bude tashiga Zare Ido Tayi dataga Wani Hadararen Royal Bed ,, Da kyar ta Hadiye Yawo
Tare da gyaran Murya Rukayya bata Dago ba saida takai Aya ta dago da Murmushi a Fuskarta
Lah Aunty Salma kece yau Shigo Zauna mana Yake Salma tayi tace No bazama Zanyi Abinci
zaki fito muje muci Rukayyah tace OK ganinan zuwa Barin Room din Salma tayi Tana ta
Magana a cikin Ranta lallai wan nan saina Tashi Tsaye yarinya kamar yar Tsana Hmmm Tabdi ,,
tayi wucewarta zuwa nata part din Nidai Binta nayi Da Ido INA Kallon Ikon Allah í ½í¸€.
" Rukayyah Kara Feshe Jikinta tayi da Turare Aoud mai Dan Karen Kanshi kamin ta Dauki
mayafinta ta Rufe Jikinta tana tafiyarta Hankali kwance Harta Isa Part Din Salma da Sallama
tashiga ,, Part din Fuskarta D'auke da Murmushi Farouq ya Amsa shima murmushin yakeyi
Gaidasa tayi tamin ta samu guri tazauna Batare da Bata lokaci Farouq yace muje muci Abincin
ko Salma sai Hararan Rukayyah take Ganin irin Kallon da Farouq yake mata A Ranta tace
Jarababa yaudai kya kwana ke kadai mayyah kawai( Jama,ah kujimin Salma Da Wani zance oh
oh mata Da kishi ) Rukayyah batamasan tanayiba Samun Kujera tayi yazauna Abinta yayinda
Salma ta fara zubawa kowa Abinci Tanayi tana Jan Hankalin FAROUQ Wanda Gabaki Daya ya
Mutu a gurin Kallon Rukayyah Dakyar yasamu yayi control din Kansa ya kula Salma Bayan sun
Kammala cin Abinci suka Dan Taba Hira Sama2 Rukayyah tayi musu Sallama Zata wuce
Farouq yace Angel kona Rakaki ne Tace no Kayi zaman ka Badamuwa Salma tace wane irin
karakata Halan dazata zo wanine ya Rako ta , no kinsan Yanxu Dare yakara yi kar taji Tsoro
Turo baki Salma tayi Yace lallai nida naje kiranta Dazu wani ne ya Rakani Ganin Zata miyarda
Zancen wani Abu yasa ya Dauko wata Caftar aka Basar da Zancen.
★ Sosai Salma tayi mamakin Ganin Irin yanda Farouq yaketa Rawar jiki Daya ,, kusanceta
Kwata2 Batama yi Tunanin Samun irin Haka daga Garesa ba Baccima Kalilan yayisa Wanda
Hakan ba karamin Dadi yayiwa Salma ba a Ranta tace wayasani koya Canye abinsa kamin a
shigo karyar Banxa Anxo ana mana wani fankama ashema nafita sai Rawar jiki yakeyi akaina
ina Amaryar Haka tata kitsawa Har Bacci ya kwasheta . Rukayyah Baiwar Allah Tun da tadawo
part dinta tarasa Abinda kemata Dadi Saboda a kwanan nan tasaba sosai da FAROUQ
yaugashi Zata kwanta ita Daya wata Zuciyar kecemata yanxu yana can Yana yiwa matarsa irin
yanda yake maki wani Abune taji yataso mata Ganin Tunanin ta zaiyi yawa shaidan zaiyi tasiri
akanta yasa Tace "A,uzubillahi minal shaidanirrajim" Ta Basar da Zancen kwanta wa tayi a beda
dinta sai juye juye takeyi Ganin Rakasa Bacci yasanya ta Dauro Alwalah tashiga yin Nafillah
Sallar dare Dan Neman Samun Zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali Yauwa maccen Kwarai
Diyar Albarka Saliha acikin mata nagaidaki Macce Tagari.
Maman Usseeyí ½í¸˜
'YAR BAIWAH 6⃣1⃣
*Maman* *Usseey*í ½í¸˜
★Washe Tun da Asuba Farouq yatashi Yata yar da Salma Kamin ya Fito ya Nufi Part Din
Rukayyah Dayake yanada keys na kowane part . Bude Kofa yayi Yashiga a Hankali yake jiyo
Sautin Muryan ta Tanata Karatun Cikin Murya mai Dadin Saurare Murmushi Yayi Yace
Alhamdullah a Fili Wani Dadi ne ya Ziyarci Zuciyarsa ,, Saboda Tun Aurensa Da Salma baita ba
Ganin ta Dauko Qur-ani ta Karanta Ba duk da Yana iya Bakin k'okarinsa Wurin Ganin tasamu
Ilmi saidai Yau Yakasance Abu mafi Girma a Rayuwar sa Ana Karatun Qur-ani A gidansa Bayan
shi Sabanin Wakokin da yasabaji A gurin Salma wata Soyayyar Rukayyah CE takara Shiga
Zuciyarsa ,, Sosai da Sosai Da Sallama yashiga Room Dinta Zaune yaganta a Saman Sallaya
Sanda takai Aya kamin ta Dago ta Amsa Sallamarsa Da Murmushi ta Gaidasa ,,Barka da Asuba
ya Amsa Da Yauwa Hope kin tashi Lafeeya ,, Qlau Alhamdullah , yauwa Nixanje Massalaci
dama Dan Natashe kine na manta Matar Tawa Malamace Abin Dariya yabata Tace wane Ni
Daliba Dai yace koma Dai menene Allah ya karba ta Amsa Da Ameen Kamin ya Fito Dan Zuwa
Massalaci ya sallaci Asuba.
★ A bakin Kofa sukaci karo da Salma wadda tayi labe tana Saurarensu Turo baki tayi
Farouq yace Salma Ba Sallah