Showing 3001 words to 6000 words out of 26574 words

Chapter 2 - YAR BAIWA Complete book by maman Usee .pdf

02 Jun 2025

2038

CE yakoma da ita gobe sai ta fara zuwa kuma da uniform suka sake
fadamai dokokin makaranta yayi musu godiya ya ja Rukayya suka tafi a mai makon subi hanyar
gida sai taga sunbi wata hanyar mexatayi in ba kallo ba ido ya samu abinci dai dai wata yar
plaza taga Daddy yayi parking yace ta jirasa batasan meyaje yiba bai jimaba sosai taga
yadawo da Iedoji biyu a hannusa ya. bude set din baya daba kowa yasa su a ciki sa,ilin da
yadawo yatada mota suka nufi hanyar gida,

Mummy suka tarar harta kammala komai na gyaran gida da Inda sukaci abinci sannu da aiki
mommy yara ga kaya nasiyowa Rukayya da yadin uniform saiki bada dinki ayimata iri biyu iri.
Nasu Sajeeda Dan gobe zata fara zuwa sauran kayan sa wane nixan fita sai nadawo aff ana
manta kinsandai makarantar Boko suna jarabawa ne sai nadawo Hutu zan kaita zadai aci gaba
da koya musu extra lesson kamin da dawo hutun Dan naga ba wani Hutu mai yawa bane
murmushi tayi hadi da yimasa godiya da fatan alkhairi,
Rukayya kuma tana zaune ta kurawa TV Ido ko kyabtawa batayi mummy ta dafata tace muje
kitayani gyaran daki sai mu Dora girkin rana Dan su sajeeda sai 4:pm zasu dawo ta fice yayinda
Rukayya ta rufa mata. Baya tana nuna mata abubuwa da yakamata ta kula dasu wan nan
kenan,
A cikin yan kwanaki n da tayi a gida. Bata fuskantar komai sai farin ciki ga soyayya da yan
uwanta ke nuna mata suna debe mata kewa sosai sun shaku da sajeeda inka gansu gwanin
sha,awa komai tare sukeyi Dan ko a Islamiya tare suke komai sajeeda itace take koya wa
Rukayya wasu Abubuwan da bata gane ba cikin sa,a kuwa da am fada ta rike shikenan
malamansu har mamakin irin Baiwar da Allah yayiwa Rukayya suke gashidai bawani dadewa
tayi ba amma inka ganta saika rantse ta shekera a cikin islamiyar gida kuma ga lesson ana
musu badama tana kawo wuta sosai Daddy yasan bayada haufin inya kaita skull za,a sakata aji
daya da Sajeeda dayake ita jss 2 take, Tun tanajin kunyar saka wando da Riga harta saba Dan
kuwa yanxu Rukayya ta goge dama can ita kai waye ne da ita batada matsala in basuda lesson
itada Sajeeda suke taya mummy aikace aikacen gida dayake anyi Holiday.

Maman ussee😘 Ina Alfahari da Ku my fans

� 'YAR BAIWAH �7⃣
Maman Ussee

Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa gwanin sha,awah har holiday ya kusa karewa yau ya
kasance Sunday kowa da kowa na falon gidan anata firar duniya gwanin dadi fuskar kowa cike
da annashuwa da anuri Abdallah ne yace Daddy gobe Holiday zai kare kuma kasan kamuna
alkawarin zaka mana shopping yau ko Fadil ya amsa eah little bro Mummy tace harda ni kenan
za'aje shopping din Daddy yace OK to Ku shirya sai muje tare kunji yes Daddy suka mike Dan
shiryawa Rukayya an zama yan gida yanxu kowannen su yafito cikin shiri Rukayya da Sajeeda
jalabiyace a jikinsu dark blue sukayi rolling abin yayi kyau fadil da Abdallah kuwa Riga da
wandone suka sa mummy itama Doguwar rigace ta shadda taji kwado kai familyn fa sun birgeni
haka suka fito suka shiga mota Mummy dasu Sajeeda a Baya fadil da Abdallah a gaba asu
zarce ko inaba sai a Zabira shopping mall nan kowa yayi ta zabar abinda yakeso Rukayya dai
kasa daukar komai tayi Dan ita kunya takeji Sajeeda CE kedaukar komai Biyu inta dauka saita
daukar wa Ruky bayan sun karene sukaje wurin bill akayi bill Daddy yabiya suka sake fitowa
kowa sai kallon su yake nusamman Ruky da Sajeeda kamar yan biyu ba karya Allah yayi
Halitta Dan ko Sajeeda ba bayaba a fagen kyau, Daddy bai zarce dasu ko,ina ba sai Daddy's
smart anan sukaje suka ci abinci suka zaga gari sosai kamin nan suka dawo gida.

Gab da magrib suka dawo zubewa sukayi a fallo kowa ya gaji Dan yau sunsha yawo sun more
sosai gsky bayan su hutane Daddy yaja su Fadil da zuwa masallaci Mummy kuma ta wuce
zuwa dakinta yayinda da umurci su Sajeeda dasuje su yi sallah suma kuma su shigar da kayan
ciki haka suka kwashi kayan zuwa Inda yakamata su adanasu. Bayan sun idar da Sallar Isha
suka fito bayan aka ci gaba da hira can Daddy Yakira sunan Rukayya, Rukayyatu ki shiryafa
gobe zaki soma zuwa skull insha Allah saboda haka saiki shirya kinji murmushin jin dadi tayi
yayinda da ta CE nagode Daddy Allah yakara girma bakomai ai kidage dai kinji ko to 'ya ' yan
Daddy aje ayi bacci saboda a tashi da wuriko kunji yes Daddy af na manta Ga uniform din Ruky
can a bed dina Sajeeda jeki kidauko mata gobe sai a shirya da wur wuri kinji tau Daddy bakida
wata matsala Rukayya. Nariga nayiwa principal magana interview kawai za a maki su zasu baki
komai da komai saboda haka kidage kawai inkiyi kokari za a sakaki class daya da 'yar uwarki
Sajeeda tam ta amsa suka fice dakin su kowa yayi addu'a ya kwanta yayinda 'YAR BAIWAH
take farin ciki sosai mafarkin ta yakusa yazama gaskiya.

Maman Ussee


� 'YAR BAIWAH � 8⃣
Maman Ussee

Monday morning tun 6 suketa shirye shiryen zuwa skull Sajeeda CE ke nunawa Rukayya yanda
zatasa kayan skull din ,kai gsky fa kinyi kyau tawan kinga yanda skull uniform din nan suka
karbeki ta kashe mata idon daya Ruky ta kaimata duka ta goce suka fito falor sunata dariya

yayinda su Fadil ma su. Shirya tsaf Daddy kawai suke jira bai wani jima ba ya fito sanye da
kayan shi dagani shima aiki zaije daya aje yaran, ba bata lokaci Mummy tai musu addu' a suka
fice dukkansu suna daga mata hannu,

Bayan sun shiga mota Daddy ya tuka zuwa skull din dake dai dai Bafarawa east, garin yacika
sosai da mutane kasan cewar yau Monday masu zuwa skull na fita yayinda masu zuwa aiki ke
kama ga bansu da zuwa aiki kai tsaye daddy cikin makarantar ya danna motarsa wato KEY
SCIENCE ACADEMY, bawani bata lokaci Sajeeda dasu Fadil suka nufi assembly yayinda
Daddy ya nufi principal office da Rukayya bayan yagabatar da ita a fadamai rules din makaranta
ya amince kamin nan aka bashi takarda yasa hannu yayi godiya sosai ya wuce yayinda PC ta
kira senior master domin a iyiwa Ruky inter view da Name dinta aka fara ta amsa Rukayyat
Sa'eed bayan nan kuma sai aka cigaba da yimata sauran questions tana amsawa yanda
yakamata, mintuna kalelan aka bata class yayinda aka kira, class master dinsu ya rubuta name
dinta a Register kuma aka umurce shi daya kaita ya gaba tar da ita wa yan class as a new
student kai tsaye , Jss 2 blocks ya nufa da Rukayya kamar dai yanda Daddy ya. Bukata cikin
sa,a kuwa ajinsu Sajeeda ne bayan shigarsu, student suka mike tsaye,
Good morning sir, morning how r u today, we are All fine sir, OK sit down,
Anan yagabatarda ita yayi kiran register kuma ya umurci class rep data bata set shikenan yafita
Dan yagama aikinsa,
Fitarsa keda wuya Sajeeda ta doka uban tsalle ta rungume Rukayya tana murna sosai, Hi kinga
Allah ya amshi addu,a na ko so yanxu muna class daya if u did not understand anything just ask
me � murmushi kawai Ruky tayi hadi da samun set bayan nasu Sajeeda yayinda su Muhibba
yan sit dinsu Sajeeda suke tambayar ta dama tasantane eah yar uwatace she's my sister daga
nan kuma aka cigaba da gaggaisa irin na new students da old kundai gane😜 uncle me English
ne ya shigo da yake ba musulmi bane ya gabatar da lesson dinsa ya kuma basu pappers dinsu
na fist term bayan ya kare sai mai science yashigo shima yagabartar da nasa lesson din kamin
nan aka buga aje break fast Sajeeda da Rukayya tare suka fito zuwa dinning area anan ne
Sajeeda ta ringa nunawa Ruky abubuwa da dama wadanda bata saniba da kuma Inda ake
komai da komai haka suka kasance har time dinda aka koma class ba laifi Rukayya ta dage
sosai sai sun hada Kansu ita da yar uwarta ba abinda basayi tare har lokacin barin skull din
yayi suka shiga skull bus Dan dama ita ke mayardasu gida saidai da safe Daddy ya kawosu su
Fadil da Abdallah bangarensu daban kasancewar su a primary suke sunada masu bus din duk
da skull din dayace amma kuma Nursery daban primary daban ss da jss ne kawai a hade
Sajeeda da Ruky suka shiga tare aka yita sauke wadanda ke kusa yayi da aka zo unguwarsu
suma suka sauka sunayiwa sauran yan mates dinsu bye bye sai mun hadu gobe inji su Hibba
sajeeda ta amsa da to,
Bayan su shiga gida suka tar rar dasu Fadil da Abdallah har sun dawo kasancewar su 12:30
ake tayar dasu sukuma sai 1:30 suke tashi Daddy. Baidawoba haka suka cire uniform dinsu
suka sake wanka kamin nan suka saka uniform dinsu na Islamiya da time yakusa yi.

A RABA FA?

Tun bayan tafiyat 'Yar Baiwah Baaba kullun cikin cewa take harda Dan zazzabin ta na kewar

jikar tata kullun ta lisafe da ko kwana nawa yar baiwa tayi a birni kullun tunanin ta yanxu a wane
hali jikarta take sai dai zuciyarta tana hayamata duk Inda yar baiwa take to addu,ar da take
mata yana tare da ita da A kullun baaba sai taiwa Rukayya addu,a kuma batason taji lbrn
komai indai ba firar mutuniyar ta bane hakan CE ta kasance ko a wuri mahaifinta sai dai yana
da jarumta baya nunawa dankar ya karyawa baaba zuciya haka suka kasance gidan shuru
shuru har na tsawon sati biyu tun basu saba ba har yazama jiki suka saba kowa yadan fara
sakin jikinsa aka dawo yanda ake da saidai kuma in an tuna ayi kewa sabo kenan.

Maman ussee😘

� 'YAR BAIWAH �9⃣
Maman Ussee
Ruky da Sajeeda zaune a dakinsu sunata fira sai dariya kakeji wow gsky nazata inaje skull din
nan zan fuskanci Matsala, ashe ba haka nan bane, kai dadina dake tawajena tsoro gareki,
ninasan ba abinda zai faru kawai dai kedince akwai tsoro. Kinga tashi kar muyi latti kinsan halin
mutumin naki mai tajwid akwai disgi ni kuma na tsani mutun mai disgi hakafa ranar safa CE
kawai bansaba ya hanani shiga ajin Ruky tace OK kinsan dai gobe akwai Hadda ko saboda
haka yau. Ba, bacci Dan kar muje bamuyiba kinga gbe akwai skull cox Hutu yakare yanxu da
dare zamu rika yin Hadda dinmu,

Bayan sun kammala ne suka fito sanye da uni din Islamiyarsu sama sama suka ci abinci Dan
karsuyi latti ayi musu duka sauri sukeyi Rukayya rike da hannun Fadil yayin da Sajeeda take
rike da hannun Abdallah Dan a kafa suke zuwa Islamiya tun bayan ranarda Daddy yakaisu,
Sunci sa,a suna shiga ana tare yan latti kai tsaye ajinsu suka nufa. Bayan sun aje su Abdallah a
nasu ajin.
Ai kuwa basu tsiraba Dan koda suka je mai tajwid yariga yashiga hkr suka fara basa dakyar
suka ci sa,a yabarsu suka shiga bayan shanyasun da yayi a waje haka yakaraci darasin sa
yabar ajin.
Basu suka tashi ba sai misalin 6:pm aka tayar dasu kowace daliba ta kama hanyar zuwa
gidansu, Ruky da Sajeeda tare da yan kannesu suma suna dai daga cikin masu zuwa gida
kasancewar magrib ta kusa da isarsu gida kowane ya nufi dakinsa Dan bayarda farali suna idar
da Sallah falo suka xo , a nan suka tararda mummy itama ta fito yaran Daddy sannuku har
kunyi sallar ne eah OK to Allah ya karba ya bada lada suka amsa a tare ameen mummy, yadai
Ruky hope ba matsala a skull ko karki damu da sannu zaki sabane fatana kawai Allah
yataimaka yabada sa,a kuma a dage kunji eah suka sake amsawa, haka sukata fira jefi jefi
kiran sallar Isha ne ya tayardasu bayan sun kammalane suka fito domin cin abincin dare,
Anan suka tarar da Daddynsu Dan rabon da suganshi tun safe daya ajesu a skull gaida shi
suka fara kamin nan kowa ya zauna a set dinsa mummy tayi serve din kowa akaci akasha aka
koshi sai kowaya kama gabansa yayinda Ruky da sajeeda suka fara tilawar Haddan su dakuma
assignment dinsu bayan su kammala sukayi addu,a suka kwana sai. bacci.
Kashe gari haka ta kasance tun wuri suka kimtsa suka fito inka gansu kanar wasu twins gwanin
sha,awa yau ma Daddy ne yakaisu skull daga nan ya wuce GT Bank da acan yake aiki bayan

an kare Assembly kai tsaye kowace daliba ajinsu ta nufa Dan daukar darasi Sajeeda da Ruky a
tare suke tafiya har class dinsu kowace ta zauna a set din ta kamin class master yaxo yakira
register daga nan kuma
Malami mai lesson ya shigo ya fara gabatar musu da lesson.

Maman Ussee😘

Naga sakonku nagode sosai da kulawa nasoyana Allah yabar zumunci.

� YA RBiAWAH � 1⃣0⃣
Maman Ussee

Time din break yayi Sajeeda da Ruky suka fito waje class sunayin break yayinda sauran student
ke lamarin gabansa, Ruky nikuwa Sajeeda kinsan abinda yake bani mamaki a,a saikin fada wan
nan malamin nan na daxu mai disga mutane din nan kinga yanda yabar ummy nata zuba surutu
ya kyaleta amma na tabbatar da wani member din class ne daya sha zagi yau kuma na ga sai
wani shige mata yake kodan yaga tafi kowa girmane a class din, hey are u jealous 😀 Ruky
takai mata duka wane irin jealous kuma ni ina ruwana dashi kawai dai naga hakan baidaceba
ne shiyasa na gaya miki OK to kawo takalminki na ajiye miki kije ki gaya musu ustaziya
Rukayyatu 'YAR baiwa í ½í¸ dalla Banason rainin hankali daga kawai na fada miki Abu shikenan
sai ki wani canja min magana 😀😀😀 dariya sajeeda tayi hardasu kyalkyatawa kamar zata
fado kasa aiko Ruky ta ji haushi ta kwashi kayanta fuu ta fice daga wurin hava ke kuwa sorry
mana tsayani muje tare INA ko saurarenta bataiba ta fice class abinta sai daga baya ta saiko
suka shirya kamin adawo break.

Sannu sannu.bata hana zuwa sai dai a Dade ba,a kai ba yau su Ruky zasu zana end of second
term examination, a cikin skull kuwa bawanda baisan Sajeeda Abubakar &Rukayya Sa,eed ba
komai nasu atare sukeyi duk Inda kagansu tarene ba abinda yake rabasu ko a gida ma hakan
ne gasu da ilmi uwa uba kyau gasudai ba wani girmane dasu ba Dan daka gansu zaka yarinta
karara a tare dasu sai dai sunada ladabi ga girmama na gaba dasu a class inkaji suna surutu to
lallai Abu mai mahimmanci suke tattaunawa. Baruwansu da wasu frnds sudai barsu da karatu
Dan kullun abinda Daddynsu yake jaddada musu kenan kosunyi fada to yanxun nan zakaga
sun shirya al,amarinsu yana mutukar.birge jama,a ko unguwarsu bamai cewa sun tsokaneshi
Dan su karatun ne kawai yasha musu kai alhmdllh cikin sa,a suka fara Rubuta exams dinsu har
suka karashe akayi holiday,

Murna gurin Rukayya ba,a magana Dan dama ta matsu ayi Hutu Dan taje Raba dama Daddy
yace da anyi Hutu zasuje tare suyi one week sai sudawo sabida islamiyarsu dayake sunyi nisa
sosai, bayan sun dawo gida da kwana biyar suka daga sai Raba gabaki dayansu harsu Fadil
da Abdallah ai kuwa kuxo kuga murna wurin Baaba kamarme taga yan jikokinta musamman ma
Yar baiwa taga yanda tayi Haske ta goge hardasu kiba gwanin sha,awa kai lale marhabin da
yan sokoto cewar Malan sa,idu nan nan kawai yake da 'ya'yan nasa yanajin wani farin ciki a
ransa yarsa CE ta dawo haka tubarkallah masha Allah, bayan an nutsa kowa yaci ya koshi aka

fara sabuwar fira yayinda suka gode sosai da namijin kokarin da Daddy yayi musu godiya suka
ka rayi da fatan alkhairi, satinsu daya a Raba suka juyo yar baiwa kawai suka bari koshima
badan sunsoba saidan rokon da Baaba tayine shi,isa suka barota ta kara sati sai Daddy yazo
ya dauketa sukoma, bayan kwana biyu Baaba na zaune itada Rukayya suna tadi take
tambayarta bawata matsala daiko eah bakomai lfy lau wllhi bakiga yanda ake bani kulawa ba
sosai da sosai to madalla ai hakan akeso Allah dai yasaka musu da alkhairi Rukayya ta amsa
da ameen amin shiyasa nake sonki Baabata dankin iya addu,a 😀 dariya Baaba tayi tace ja,ira
har yanxu dai sakarcin naki nanan Ruky tace to in ban maki ba wanikeda shi Wanda yafiki ai
kekadaice dagake. Bakari � tabdi wai yar baiwah yaushene kika iya surutu haka lallai zaman
birni ya saka ki iya magana 😳ai baaba Dan baki zauna da Sajeeda bane haka take kamar
parrot indai surutune uhum menene fara kuma me Ruky zatayi in banda dariya aikuwa Baaba
takaimata duka ta goce tsaya kiji parrot akecewa inaga sai naje sake skull dinmu kin kara
wayewa ja,ira kekam dai Allah ya shiryeki ta CE ameen tana murmushi.
Maman Ussee😘

�YAR BAIWAH �1⃣1⃣
Maman Ussee😘

Satin Rukayya biyu daddy yazo yadauketa suka koma sokoto cike da kewar iyayenta
musamman ma Baaba dasuka shaku sosai,
Haka Rayuwa taci gaba da kasancewa yau farin ciki gobe akasin haka dama ita rayuwa haka ta
gada , amma a wurin Rukayya abin ba,a cewa komai Dan kullun cikin farin ciki take yayinda duk
tayi sallah saita Roki Allah yasa kama daddy da aljannah hakama mummy dakuma iyayenta.
Haka suka karaci holiday dinsu har ya kare duk Wanda yasan Rukayya ada idan yaganta a
yanxu bazai ganetaba inhar ba farin sani yayi mata ba Hutu kwanciyar hankali haiba kwarjini
duk sun baibayeta batada wala matsala a skull ma hakan ne Dan so dayawa tasha samun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login