Showing 6001 words to 9000 words out of 26574 words

Chapter 3 - YAR BAIWA Complete book by maman Usee .pdf

02 Jun 2025

1736


kyaututuka da dama awajen malamai kai harma da students akan baiwar da Allah yayi mata
ilmi. Ba,a magana Dan ko quiz za,ayi to Ruky da sajeeda na ciki haka ma divert ko inter schools
compotions za,ayi to dolene asaka yar baiwa ga tada da speach mai dadinji dakuma saurare
takowane fanni gata ilmin addini Dan kuwa saura kadan ta Haddace alkur,ani mai girma,
Sajeeda namatukar son Rukayya kamar yan uwanta na jini haka take jin ta kamar uwa daya
uba daya suke ba,abinda Rukayya zata CE tanaso Sajeeda. Batace tana sonsa ba koda kuwa.
Baimata ba a duniya inhar kanason kaga. Baccin ran Sajeeda toka taba Yar baiwa haka ma ko
a wurin Rukayya batason ko kadan taga yar uwarta cikin damuwa kuma sajeeda bata taba jin
haushi ko kyashin Rukayya tafita ilmi ba duk da dai itama tanada nata iya gwargwardo wadan
da basu sansuba cewa ma suke yanbiyu ne kasan cewar tun bayan dawowar, Ruky a gidansu
Sajeeda Daddy bai taba ban-ban ta musu kayaba kai harta takalmi da sarka iri daya ake saya
musu hakan yayiwa mummy dadi sosai yanda Daddy yadauki Ruky kamar sajeeda baya taba
nuna wani banbanci duk abinda zai iya yiwa sajeeda to tabbas zai yiwa Rukayyama, duk da
yasha samun yan korafe korafe a gurin Abokanansa dakuma wasu amma indai ya fahimci ba
maganar arzikice takawo kaba, tun daga ranar kun raba hanya dashi bayason sa 👀 ido Dan
yasan duk abinda yayiwa Rukayya Dan Allah yayi kuma yanada tabbacin zaisamu ladansa a
gurin Allah .

Haka abin yake ko a wurin mummy indai kawayenta suka fara kushe Rukayya nan da nan zata
watse mutun komai dangartakar ta dashi kuwa ita a ganinta ko ba ita, ta haifi yar baiwa ba ai
Abbanta ciki daya suka fito dashi kuma duk abinda zai cutar da Rukayya bata sonsa Dan tasan
duk abinda tayi Dan zumuncine kuma Dan Allah da fatan samun lada a gun Allah. ( Anya a wan
nan zamanin zaka iya samun Dan uwanka maisonka da kaunarka saboda Allah kuwa zumuncin
yanxu sai a hankali kowa nasa kawai yasani Ya Allah kabamu ikon so da kuma kauna ga yan
uwanmu, Ameen ya Ra bbi).
Rukayyace zaune a falo tana koyawa su Abdallah home work dinsu Sajeeda kuma na gefe tana
Dan duba wani English litreture mummy kuma ta fita da yake yau ba Islamiya kowa na abinda
yasa a gaba sallamar Daddyce ta sa kowannensu dago kansa sama Dan amsa sallama Sannu
da dawowa Daddy, yauwa yaran Daddy sannunku da gida umman taku har yanxu bata dawo.
Bane wan nan zuwa biki haka har yamma tayi gashi inaso muje gidan wani amininah da muka
Dade bamu haduba baya kasar jiya yadawo muje muyimai. Barka da dawowa ko bakwaso �
sukayi ga aki dayansu Daddy muje basai munjira mummy. Ba kawai cewar Sajeeda yes Daddy
kinji Abdallah , no gsky daddy ajira sai mummy tazo inyaso sai mubarshi sai anjima da dare
muje Daz my gal shiyasa nake sonki dan kinada hankali ba kamar wadan nan ba Sajeeda ta
turo. Baki fadil kuma gwalo yayi mata ta kaimasa doka ya goce ya boye bayan Sister Ruky plzz
my sist kice karta dake ni to meye namin gwalo ai nima watarana Daddy zai yabeni bakaman
kai ba ko little bro cewa da Abdallah eah hakane Sist kyalesu shida sister Ruky, muma
watarana rana sai mun musu gwalo dat my bro oya give me five suka tafa ita dai Ruky
murmushi kawai tayi itama tace da fadil leave them kaji sweet.bro dina itama sajeeda ta kwai
kwayeta kaji sweet bro dina Ruky ta jefa mata pillown kujera ta gudu ita da Abdallah zuwa
daki hmmmm Sajeeda da Ruky kenan everlasting friend

Maman Ussee😘

I love you All my fans 💋

� YAR BAIWAH �1⃣2⃣
Maman Ussee😘

Misalin karfe 8:30 mummy da 'ya'yata suka shirya cikin shiga ta alfarma kowansu yaci gayu,
Daddy ne ya leko ohh wai haryanxu baku kammala bane koyaya? Nop we r ready kai kadai
kawai muje jira OK let go.
Gida ne na alfarma Wanda ya amsa sunansa gida, ba karya naira tasha kuka a gidan Dan an
zuba dukiya a duk fadin Sama road ba gidan da yakai kayatuwar gidan kai tsaye Daddy cikin
gidan ya nufa yayinda mai gadi ya wangale get suka shiga,
Wow Aljannar duniya lallai gskyr hausawa ne dasuka CE na zaune baiga gariba habar gidan
tamkar a kasar turai duk da dai darene amma tamkar rana saboda hasken lantarki, gefe daya
motocine a gibge, an jera su Reras a car pack, sai kuma a center akayi wani Dan round aka
shuka flowers ruwa nata bulbulowa kamar korama hasken fitillu ya haske ko,ina ba, cewa komai
dayan gefen kuma wurin hutawa ne da kujeru sai rumfa tsayawa na fada muku gayatuwar gdn
bannar lokacine, iya haduwa gidan ya hadu sosai kai tsaye car pack Daddy, ya nufa yayi

packing, kamin nan suka fito zuwa cikin gidan,
Wornder shall never end kunga Fallon gidan kuwa😳 wasu kayatattu. Royal chair's, na hango
kai sun hadufa ba karya masu kudi suna sha,aninsu. Gefe guda Dining area ne dauke da wani
katon dining table tsarin falon komai red an white ne kai hartama da paint din falorn red ne da
white kai nasha kallo fa saura kadan nadan saki layi nadai yi sauri na saita kaina Dan karsu
dagoni😜,
Daddyne yafara zaunawa tare dasu Abdallah kasan cewar shi ba bako. Bane a gidan in yazo
kai tsaye yake shiga ba wani dar dar, mummy kuma tare da Ruky da Sajeeda,
Wata matace tashigo da ganinta mai aikin gidance sannuku da zuwa Bari na kira Hajiyar tana
sama bawani bata lokaci aka fara cika musu gabansu da cima kala_kala, yayinda kuma Daddy
ya daga waya ya sanarda abokinsa isowarsu Dan yasan halin matar gidan inta itane saidai su
kwana anan baxata sakko. Ba , Bayan min tuna kadan sai ga shinan ya sakkon mutun mai
baiba da kamala ga kwarjini, da murmushi sa ya tarbi abokin nasa ya rungumeshi aka fara
gaisuwar yaushe rabo,
Alhaji Basheer kenan Amini kuma uban gida a wurin daddy mutun ne mai son mutane kowa
nasane yanada daraja Dan Adam baya wulakanta talaka duk Wanda yaxo gunsa zai tarbeshi
kamar nasa ga taimako sabanin uwargidansa Hajya kubra macce mai fada ga nuna isa batason
talaka ya rabi mijinta Dan ma Alh Basheer na tsaye ne kuma yana takwarata da Allah kadai
yasan tsiyar da zata tsula. 'Ya'Yansu shidda Abubakar Umar Usman da Aliyu sai kuma twins
Afra&Afnan bayansu bata sake haihuwa. Ba, Abubakar shine babban dansu sai Umar ke
bimasa duk da bawata tazarace tsakaninsu ba Usman da Aliyu ma bawani nisa a tsakaninsu,
bayan ta haifi Aliyu tadan jima bata sake haihuwa ba har an cire rai sai Allah yabata cikin afra
da afnan Alh Basheer yayi murna kwarai da gske kasancewar bashida yara mata duk maza ne
adalinlin hakane su Afra suka taso cikin gata sosai ba iyaye bakuma ga yayunsu ba .

Bamai takura musu sai abinda sukaso sukeyi tun suna yara abindai ba,a cewa komai idan
kanaso kaga fadan Hajya to taba mata yan biyunta ba abinda sukeso a duniyar nan Wanda
Hajiyarsu bata musu(Jan kunne👂Hatara iyaye mata mukula sosai da sangarta 'yayanmu
dominsu amanace awanjemu ki👉 sani Allah zai tambayeki game da tarbiyar da kika. Baiwa
'yayanki dolene mu tsawatar musu Dan ance kaso naka duniya ta kishi inkaki naka duniya ta
soshi haka zancen yake Allah yasa mugane Ameen)
Alhaji Basheer rikaken Dan kasuwane kuma shahararren mai kudi Wanda ketashen kudi a wan
nan zamani duk da dai ba sa,an daddy. Bane kusan Allah mai hadin zumunta. Wata rana ne
Alhaji. Basheer yaje Bank dinda daddy ke aiki domin ya cire wasu kudade nashi sai aka samu
akasi bai samu yanda yakeso ba kuma gashi tafiya zai yi yarasa mafita shine daddy ya
taimakesa yasamu kudin iya adadin abinda yakeso to tun daga ranar yazama duk indai kudi
yakeso a bank dinsu Daddy to Daddyn kawai zai nema hartakai ma daddy da kansa ya sha
kawoma Alhaji Basheer kudi har gida wan ne yasa sukayi sabo har Alhaji Basheer yakan Dan
saka daddy wani abu Wanda yake na sirri kuma ayimasa yanda yakeso batare da ansha
wahalaba wan nanne dangantakar Daddy dakuma Alhaji Basheer ,
Bayan sun gaggaisa Ruky da Sajeedama suka gaida shi cikin girmamawa, sosai yaran suka
bashi sha,awa ya yaba da hankalinsu sosai har yake tambayarsu ajinsu nawa da skull dinda
suke suka bashi amsa kai tsaye ya CE gaskya kunada kokari so keep it up duk Kansu dariya

sukayi sukace Insha Allah , Jim kadan sai ga Hajya Kubra manta manta anfito ana wani tako
daya bayan daya kamar,batason taka kasa tana wani nuna is a ,daga saman stairs falon ta nufa
gurin da su Daddy ke zaune anata labaran duniya shida Alh su mummy kuwa hankalinsu nakan
palasma TV dake jikin bango suna kallon news. Au Alhaji wai baki mukayine,murmushin taikaici yayi, yana mai jinjina hali irin na matarsa , Eah
kawai yace mata yaci gaba da abinda ke gabansa .
Sannuku kawai tace dasu takoma warta dama ko sakowarda da tayi taga Alhaji ya matsa mata
da kirane shine ta sakko taga meyene gaidata su Sajeeda suka shiga yi a dakile ta amsa tayi
ficewarta Alhaji baiji dadin abinda tayi ba ammato ya ya iya.
Wuraren 10:30pm suka yima Alhaji Basheer sallama ya dauki kudi yabasu sukaki karba aikuwa
yayi juyin duniya sukaki saida yanuna bacin ransa kamin nan, daddy ya umurcesu dasu karba
kishi Sajeeda CE ta amsa Ruky kam ki tayi saboda kunya.
Muje zuwa

Maman Ussee😘
Kuyi hkri aiki ne yamin yawa shiyasa but insha Allah gobe zanyi mai yawa nagode sosai
masoyanah�

� YAR BAIWAH �1⃣3⃣

Maman Ussee

Da isarsu gida kowa, yanufi dakinsa Dan kwantawa, a huta yaukam ba, zancen fira , Ruky da
Sajeeda wanka kawai sukayi sai alwala kowacce ta nemi shifida, sai. Bacci

Kashe gari tun safe suka tashi bayan sun kammala ayunkan gida kai, tsaye dakin mummy suka,
nufa bayan sun gaidata da. Ne ,
Suka nufi dakin daddyn su, shima sukayi gaidashi, kamin nan sukaje suka ci gaba da sauran
yan aikace aikacen gida Dan mummy bata barinsu girki saidai ta nuna musu amma har yau
bata sake musu girki ba acewarta su yarana har,
Yanxu baza ta sake musu komai ba, sai nan gaba iya kacinsu shara sai wanke wanke , da
sauran Dan abinda , baza,a rasa ba.
Time din break nayi kowa ya halara mummy tayi saving din kowa, aka fara cin abinci , bayan an
kammala ne Daddy ya ke tambayar su daya bayan daya koda matsala ne Dan,
Dama haka yakeyiwa kowa. Daga nan duk mai bukatar wani abu saiya fada kowa yace ,
Bakomai Daddy ya wuce zuwa Bank. Dan yau ba skull ana hutun good Friday ne yaran yau
basa zuwa skull , Bayan sun kamala aikinsu sai suka tambayi mummynsu sunaso, ne suje dubo
wata yar class dinsu datake, nan unguwarsu . mum tace dasu karsu Dade suyi sauri su dawo ,
tau suka amsa kamin nan suka dauki hijabs dinsu,
Suka ficce daga gidan , gidansu Hafsat suka nufa nan ne bayan layinsu da sallamar su suka
shiga cikin gidan, bayan sun gaida umman Hafsat sai suka shiga dakin Hafsat din, bayan yan
gaishe gaishe , suka fara fira irin nasu na yan makaranta, Basu suka dawo ba sai bayan an
taso daga salar jumma,a dayake yau Friday ne , kai tsaye gida suka nufa koda sukaje mummy

tayi baki bayan sun gaida sar da bakin mummy dakin su suka shiga suka sayi sallah bayan sun
kammala, suka fito suka Debi abincinsu suka koma dakin su, sunata wasa da dariya batare da
wata damuwaba yan biyun mummy kenan!!!

Maman Ussee😘
Note
Dan Allah kuyi hkr wllhi kwana biyu bana jin dadin ne amma yanxu naji sauki zanci gaba dayi
muku insha Allah nagode sosai da kulawarku💯


� YAR BAIWAH�1⃣4⃣

Maman Ussee

Safiyar Talata tun safe suka tashi suka fara shirye 2 na zuwa skull, bayan sun kammala da
komai da komai Daddynsu yadaukesu yakaisu bayan ya ajiyesu sai ya ficce zuwa wurin, aikinsa
Su Abdallah da Fadil ma nasu bangaren suka nufa, yayinda Sajeeda da Rukayya, suma suka
wuce, zuwa assembly, ground, After ankare Assembly duk student's suka ficce, zuwa classes dinsu Dan daukar darasi, bayan
Class master din su Ruky yashigo ya kira register, sai aka fara gabatar musu da lesson din
nasu .
Kwanci tashi baya hana zuwa yau har su Sajeeda da Rukayya sun rubuta JSCE lafiya lau
murna gurin Daddy da Mummy kamar me, Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa har
lokacin da exams dinsu ya fito Daddy yayi musu alkawarin zai canja musu skull dan ya yaba da
kokarin yaran yayinda Alhaji Basheer shima yayi alkawarin zai bada nasa contribution, din idan
zasuje gaba Dan shima yaran suna birgesa, more especially
Tarbiyarsu ga girmama nagaba dasu,
Kamin karshe Hutu Daddy yakai Rukayya da Sajeeda Raba domin suyi hutunsu acan , sunsha
Hutu kam Dan saida sukayi kusan wata Daya acan ba karamin Dadi hakan yayima Baaba Dan
tana matukar son Rukayya , bayan sun dawo, Hutu kuma sai suka dukkufa zuwa Islamiya Dan
dama sauran kadan su sauke kuma Daddy yayi musu alkawarin sai sun sauka zai kaisu SS one
Dan dama hakan sukeso badan ma sunje Hutu a Raba ba da yanxu sun sauke hakan sukeyi
kullun akaci sa,a kuwa Rukayyace ta fara sauka bayan Sati daya Sajeeda ma tasauke Murna
da Daddy yayi. Bata misaltuwa kullun saiyayiwa yaran sa addu,a Allah yakara musu basira
Alhmdllh Addu,arsa ta karbu Dan kuwa ga sakamakon hakan yagani.
A tare daddy ya hada musu walimar sauka a gida bayan an gabatar musu da wata walimar a
makaranta, ba laifi kam an taru bayan an gabatarda yan naseehohi akayi musu addu,a sai yan
kayan rabo da akayi bayan an rufe taro da addu,a kowa ya watse,
Daddy ne zaune da yaran sa anata wasa da dariya uhuum Abban yara wai mexai hana ka
kokarta ka kai su Iman ne naga can ana karatu sosai ko cewar mummy Daddy ya nisa eah haka
ne amma kudin ne , sunyi yawa kuma nafiso nakaisu Inda zasuci gaba da Hadda Dan ,dama
nayi shawara zan kaisu, Sultan Abubakar Maccido Islamic college, koya kika gani ,ai Ruky da
Sajeeda najin haka su fara murna yeee Thanks much Daddy we love u Daddy Allah yakara budi

sukaje suka Rungume Daddyn nasu suna murna ,daga nan kuma aka ci gaba da hirar duniya
kamin time din sallar magrib yayi , Dad yaja su Fadil zuwa masallaci yayinda su Sajeeda da
Rukukayya suka shiga cikin dakin su domin gabatar da Sallar magri b.
Bayan kwana biyu Daddy yadaukeso sai new skull dinsu dayake akwai masu yin day a ciki
akwai kuma masu yin boarding Daddy baya da Ra,ayin barinsu suyi boarding, Day yasaka su
bayan ya yayi musu registration, da duk wani abubuwa da yakamata sanda akayi musu
interview, aka basu classes saidai ba,a ajesu a class daya ba kamar yanda sukeso , badan
ransu yaso ba,haka suka hakura Dan bayanda zasuyi, haka suka zauna a new skull din taso
dayake akwai Dan banbanci kadan Dan yanxu sai 4:pm suke tashi dan, skull din hade take da
Islamiya Ruky da Sajeeda baruwansu dashiga harkan da banasu ba hakan cema tasa basuyi
wasu sabbin kawayewa ba Dan acewarsu kowa ya tsaya matsayin sa Inda Allah ya ajesa ,
kwana biyu sukayi suna a cikin makaranta akan BAIWAR Ilmin da Allah yayi musu abin sai
Wanda yagani Teachers suka fara sonsu duk Inda kaji cikin skull zance Sajeeda da Ruky akeyi
Abin yafara bawa wasu student's din haushi Dan yanxu da wuya ayi wani skull conpotiong ba
dasu ba gasu da kyau kamar diyan laraba da yawa ss3 student, sun sha musu gargardi akan
wasu malaman, abin har mmki yake baiwa su Ruky Dan su a tsarin su ba soyayya a halin
yanxu Dan Daddy baya barinsu ko da wasa balantana ma a skull dayake dokar makaranta CE .

Maman Ussee😘


� YAR BAIWAH � 1⃣5⃣

Maman Ussee😘

Sajeeda da Rukayya yaran kirki, wadanda bazaka taba cewa sun tsokaneka ba , zaune suke a
harabar, area class, sun duba wani book, dukadai ne zaune a gurin sai wadan da. Baza,a rasa
ba, Sajeeda ta kalli Rukayya, yadai Sist naga ki wani iri neyake faruwane. Murmushin karfin Hali
kawai yar baiwa tayi, Mekigani ne hln ba komai, nikuma dadina dake shegen zurfin ciki yanxu akwai abinda yake
damunki a duniyar nan dabaza ki iya fada mun shi ba, koda yake ,may be kinada ,
Wata wadda ya dace kiyi sharing din fillings dinki da ita wadda ta wuce ne, nakula dake tun jiya
bakya jin dadi but saboda, karfin hali irin naki nayi ta tambayar ki amma kin ki, fada ,
Namiki alwarin yau idan har baki gaya min. Ba to damunje gida nikuma sai na gayawa ,mummy
ita ai dolenki, ne ki fada mata 😳 zaro ido Rukayya tayi hadi dacewa hava Sist kin kasa
fahinmta ta. Kawai ne nagaya miki am OK ,
Kawai dai na tuna da Raba ne shiyasa hmmm Rukayya yaushe kika koyi karya nidai nasan wllhi
dakwai wani abin da kike boyewa kuma zan gyaleki. Baxan sake tambayar ki. Ba amma nima
wata rana ko kin gani cikin damuwa to karki kuskura kice wai zaki tambayeni meke damuna,
Dan ba fada miki zanyi ba ta tashi fuu da dauki sauran tarkacenta ta kara gaba, dafe kanta
Rukayya tayi Dan batasan ya zatayi da fushin Sajeeda ba ,
Tana matukar son 'yar uwarta.
To amma tayaya zata iya fada mata wan nan abun ai sirrin ta ne. Bedace sai Sajeeda taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login