Showing 18001 words to 21000 words out of 26574 words

Chapter 7 - YAR BAIWA Complete book by maman Usee .pdf

02 Jun 2025

1735

take sha,awar ganisaba a yanxu Dan
tasan ba shiri sukeyi ba itadashi amma meyasa nake muradin faninsa oho tabaiwa kanta amsa
kawai mantawa zanyi dashi Dan ba abinda ke tsakanin ni dashi haka kurun tunanina yarasa
Wanda zai tunano sai wanda na tsana bayan anyi musu Hutu bada dadewa ba Daddy ya shirya
musu tafiya Raba itada Sajeeda Dan acan zasuyi hutunsu hakan yayiwa Rukayya dadi ba
kadanba koba komai zataga mamanta da Baaba dakuma Abbanta kasa boye murnarta tayi har
Ranarda suka daga dayake su biyu kadai Zasu Daddy sarkin tsaraba a kullun baya gajiya da
lalurori haka ya shirya musu tsaraba mai tarin yawa yatafi dasu domin yakaisu gida murna gurin
Baaba kamar me taga jikarta ta kara girma gwanin sha,awa nan nan kawai tayi da ita Daddy
kuwa yasha Addu,a kamar me Dan kuwa malan Sa,idu harda kwala yayi gurin iya Daddy godiya
bakomai ai yiwa Kaine Rukayya tamkar 'yace a gareni nadauketa tamkar Sajeeda basuda wani
banbanci a gurina Salame kam saboda kunya kasa magana tayi saidai murmushi bataso ta
zake da yawa saboda Rukayya yar farice a gurin ta ,kwanan Daddy daya ya juya zuwa sokoto
Dan aikinsa yakuma gaya musu ranarda zaidawo daukar su ba laifi yasha Tsaraba shima irin
tasu ta mutanen k'auye shike da mutunta juna aka Rabu ana murna da farin ciki saidai duk da
Zamansu a can din bai hanata tunanisaba har mamakin kanta takeyi lol Ruky an kamu da son
uncle F Sajeeda takanyi mata kirafi akan yawan tunane tunane but sai kawai tace mata
bafa tunani komai nakeyiba kawai dai INA kewar mummy da Daddy ne haka zata kyaleta but
itama kanta tasan akwai abinda yake damun sister dinta batason fada ne kawai kuma zata
kyaleta inayi tsami saji cewar Sajeeda

Umar kam tun ranarda yakoma gida yahadu da baccin rai yayi alkawarin barin kasar kozai
samu sawaba ga jiya sai shirye _shiryen aure sukeyi Alhaji Basheer kawai take jira aje asaka
rana a biyawa diyan ta sadakinsu Dan kam harta hada lefe nagani na fada duk ta zauce ji takeyi
kamar ma ace gobene saurin auren Dan kuwa Hajiyarsu Salma asiri taketa banka musu itada
danta ganin ko anyi ma Umar baya tasiri shiyasa suka maida kambun yakinsu zuwa ga
Hajiyarsa ba laifi a gurin su Dan kwalliya ta biya kudin, sabulu hakonsu na gamda cinma Ruwa.
Shikan Faruuq BISA yayi ta zuwa umara Dan acewarsa gara yakaiwa Allah kukansa kozai rage
zafin ra dadin da zuciyarsa ke masa bada dadewaba ta fito bai fadawa kowaba sai randa zashi
yayi musu sallama ya fice yayansa ya ajiyesa airport jirginsu yadaga sai kasa mai tsarki haka ya
wanzu ba dare ba rana yana Addu,ar samun Rukayya Allah yasa ita alkhairi CE agaresa
Alhmdllh addu,arsa ta karbu Dan kuwa yanxu Rukayya batada wani aiki saina tunanin sa
kwata2 wan nan hutun a Raba bata wani yi enjoying dinsaba.


Maman Ussee


� 'YAR BAIWAH � 5⃣7⃣


~Maman~ ~Usseey~

★ Masha Allah Abu yayi kyau Domin An Daura aure Lami lafiya komai yatafi yanda yadace
Yayinda Yan Daurin Aure suka nufo Hanyar Dawowa Sokoto Dan Can Ne Bidirin Yake Dayake
Daurin Auren. Ne kawai Malam Sa'eed yace azo Gida ayi sauran komai Yabarwa Baban
Amarya wato Shugaban Biki Daddy� Wanda Yayi Alfahari da Hakan,, da Baban Rukayya
yamasa.

" A bangaren Amarya kuwa tun Safe aketa shagalin Biki Amarya wanka ,, kawai take Dauka
na mutunci Ba karya kam Sosai tayi kyau misalin . Karfe Hudu aka Fara walima Wanda Akayi
Nasiha mai Ratsa jiki game da zaman Aure da yanda Hakkin miji yake akan matarsa. sosai Abin
ya ratsa Jama,a Sai gab da magrib Aka yi Addu,a Allah yabawa Amarya zaman lafeeya da
Samun zuri,a Dayyaba ,,Aka watse tun Kare walima Rukayya da Sajeeda keta Kukan Rabuwa
Duk Wanda yagansu sai sun Basa tausayi Saida . mummy Ta nuna Baccin Ranta kamin Suka
Hakura Dan Dolene su Rabu dama Sabo akewa kuka.


★ Uwargida kam tun da FAROUQ yayi Fushi ya tafi taketa jin Badadi a Ranta,, Haka
yaturo mata Sakon cewa Zai turo Ta Dauki abinda Takeso Yau zasu Tare a Sabon Gidansa
Komai ya zuba mata aciki kawai Dai ta tattare abinda takeso Dan By 3:pm Zai turo adauketa ,,
Tana kare karanta massege din Ta Fara tattara yan komatsan ta Zuciyarta sai Zafi take mata .
Haka Yan uwanta da Danginta suka Zauna tare da Ita bamai Bata shawaran Kirki Duk zuga. Ta
kawai Akeyi Wanda Hakan kara Ingiza Zuciyarta kawai yakeyi . Maman ta batazo ba Acewarta
sai An gama Biki Zata Zo da Sabon Tuggu Dan Tasamu labarin cewa Salma Nada Juna biyu
yanxu sun samu Gidin zama . A gidan Umar Farouq . (ohhh kuji min Mata 'yarta fa ke Auren
Farouq din Amma ita Dukiyarsa,, CE kawai A Ranta Allah kashiryar Damu kasa mufi K'arfin
Zukatan mu Ameen) Haka suka wuni Har Gurin 3 din kamin Yaturo aka Dauki Salma da Sauran
K'awayenta Da yan Uwanta yan Kore masu Rakiya .
★ Ba,a Zarce dasu Ko,ina ba Sai Gidan Farouq Dake Unguwar Guiwa lowcost ,,, Gidane
Babba nagani Nafada An kawata gidan Ba karya indan Nace Zan Iya Fayyace muku Yanda
tsarin Gidan yake Yazama ,, Waist of Time . Lol . part Biyu ne A gidan sai Garden da Kuma
Dan karamin swimming pool ,, da Filn Wasan Ball kusan Irin Ukku Basket Bolly da Kuma Hand
Ball. Sai shuke shuke da kuma parking Space . Wanda yake da isowarka ,, Gidan Mutuwar
Zaune Salma tayi ta sake Baki tanata Kallon kayyatuwar ,, gidan A Ranta take cewa Ohh All
This is myn Wata ,, Zuciya kuma take cewa Ku biyu fah mtseww..... Taja Tsaki Wallahi dai
Kishiya batayiba Acid CE Hava ,muna Zaune kalau a Hadani da ,, yar bakin Ciki zaki Ganene
inkin Shigo Gidan Wata kawartace tadan bugetah tace .
” ke Ki fito Mana kin wani hakince a Cikin mota ni na matsu naga ,, ya cikin gidan yake Dan
gaskiya Salma ur lucky kinga yanda gidan ya Hadu kuwa Sakowa tayi ta Nufi Dayan part din
taga A Rubuta kamar Haka “ This Belongs' to RUKAYYAH!!! A Ranta Tace ,,, Ohh Farouq Dan
Rainin Hankali ne jifa Ko gidan ban saniba gashi ,, Duk Nama Rasa INA ne Nawa part din Mai
gadine ya iso Gun da Take ya ,, Rusuna yace Hajiya ,, Ga makulin Part dinki gaya can Karba
tayi bayabo ba Fallasa ta nufi Dayan Part Din sauran Jama,artah suka Rufa mata Baya ,,Ta

bude ta Shiga “Ni ma dai Sauri nakeyi na Shiga na ganewa Idona Menene Acikin Gidan Dan
gaskiya Ba karya fah ,, Wow„ na Furta A Hankali. Dan A gaskiya ,, Ba,a cewa komai wani
Makeken Falone. Na Hango D'auke da Wasu Kayyatattun Kujeru komai Na Falon Black ne da
White ,, Kai harma pent din Jikin Bango ,,, Dan Kara min koridor nagani Wanda Zai sadaka da
Store da kuma Kitchen daga ka zagaya kuma Ga Dinning nan sai kuma wata yar Hanya ,,
Wanda Zata sadaka da can Cikin gidan Dayan bangaren kuma Dakuna ne kusan ,, Guda Hudu
a Jere sai Daya kuma A ,, Gefen Wadan nan da Alama Guest Room ne wato D'akin Bak'i . Sai
kuma Wata Hanya Daga gefe Can na nufa ,, Wani Katon Falon nagani A gurin ,, Shikuma an
masa Kwaliyar Pink komai pink da White color Fantastic na Fada ,, Tare da Zuba Idanuwa na
Dan nabasu Abincinsu Shikuma Kofa Biyu ne nagani da Alama Dakin Mai Gidan ne Wata
Hanya nabi naga kuma ta sadani da Dinning anan Nan ,, Ne Nafahimci Falon Maigidane Dana
Salma Sai aka Sanya Kitchen a Tsakiyarsu dakuma Dinning Area ,, dawowa nayi nashiga
Kifarda Naga su Salma sun Bude sun Shiga ,,,Zaune nayi Dana Hango wasu Mayyun Leader
sit, Kut� mai kud'i ya More Wan nan Dukiya haka da aka zuba a Gidan nan Kuryan Room din
wani Gadone Hadararre mai Rumfa!
★ Suna Tafe ina binsu a Baya ,, Kowane Room sanda muka Shiga ba karya gaskiya Dakin ,
mai gidane kawai banmu shigaba Dan a kulle yake Falon suka Dawo nima nasamu Gurin zama
,,, sai Kallonsu nikeyi yayinda my Usseey. Yaga Ana shan Juice kala2 yaje yadauko Daya
yafara sha banma lura ba sai Ganin shi nayi yanata zukar lemu ,,, Zare Ido nayi nace Kai
Rufa mana Asiri da shegen kwadayi gobe ma Bazan taho tare dakaiba Dan kar ka k'ara
Kwasamin lol.

★ Yan Daurin Aure sun ,iso lafeeya yayinda Ango da Abokansa basu Zarce ko,Inaba sai
sabon Gidan FAROUQ . Dan anan zasuyi liyafarsu . yana isowa Kota kan Salma baibiba kawai
Wuce ta yayi ya Shiga Dakin sa,, kawayenta sai tsokanar sa sukeyi suna Ango kasha Kamshi
Murmushi kawai yamusu ya fice abinsa Salma ,,ta bisa a Baya yana Shiga itama ta Shigo
Zatayi Magana yadakatar da ita da Hannu Durkushewa tayi ,,tafara mai kuka Abinda Bayaso
kenan Dole ya Rarrasheta ,, Harsuka shirya kunsandai Mata da Miji sai Allah ,, Haka ta Daure
suka Gaggaisa da fans Dinsa yayinda aka Bata kyata kala2 Kawayenta ke karba suna godiya,,
yayinda Bakin Farouq yaki Rufuwa Har Gab da magrib kamin suka watse Dan suje akai Ango
gurin Wankisa .

★ Shirye2 aka farayi na zuwa wajen Wanke Amarya ,, Wanda ba,a Bata lokaciba ,,, Aka
kaita bayan an karene Aka dawo da ita gurin mummy kuzo kuga. Kuka anxo Rokon gafara
Haka mummy ma sanda tayi kwallah saboda sabo ,, kakar Amarya sai Baaba sai tsokanar
Rukayyah take . haka taje Gurin Daddy dakyar ta Rabu dashi Dan Saida yamata wayo ta
Hakura haka suka nufi ,,Gidansu FAROUQ aka damka Amanar Rukayyah a Hannun Hajiyarsa
sosai tayaba takuma karba ta sanya Alkhairi Kamin aka wuce da ita Zuwa Gidanta Wato Gidan
Ango FAROUQ .

" Salma najin tsayuwar motar kawo Amarya Hankalinta ya matukar tashi ,,Jitakeyi wani. Abu
na taso mata kamar Zata mutu . haka ta Daure ta Gimtse har aka Shigo da Rukayyah Lullebe
da Mayafi ,, Aka Damkata Hannun Uwargida Sarautar mata Dakyar Salma tayi control din kanta

Dan,, jinsu kawai takeyi haka suka karaci Surutunsu ,, suka Ja Rukayyah Zuwa part dinta
Wanda komai Dayane Dana Salma saidai ita Kalar na Rukayyah Pupplene da White ba laifi
Daddy yakashe mata Kunya Dan itama an zuba mata dukiya wane Diyar wani Shahararren mai
Kudi ,, Rukayyah Bata taba Tunanin Zata kasance Haka A Rayuwarta. Ba wan nan wata
BAIWAH ce daga Allah Da Addu,ah a Bakinta tashiga har kuryan Dakin ta suka ajeta Saman
Bed. Yayinda kowa yaba tsarin gidanta yakeyi wasu kuma Cewa sukeyi Rukayyatu tayi dace
mudai Fatanmu Allah yabada Zaman . lafeeya da Zuri,ah Mai Albarka.


~Maman~ ~Usseey~


“Special Thanks to you my Beloved oneces ,,Bazan taba mantawa dakuba Nagode Sosai da
Kwarin Guiwarku a gareni ”

★ Maman Khairy Allah ya Raya mana Ummul-khair.
★ Ummu -Alkhairi B. B
★Bintu Tijjani Zaifada
★ And my Lovely Aunt Sister Zainab Mai Kano Allah yakawo yan Biyu Ameen.
Thanks much more Luv u all my Fans Lodi-Lodi.


� 'YAR BAIWAH �5⃣8⃣

~Maman~ ~Usseey~

★ Gidan Amarya ya Rage daga Sajeeda sai Afra da Afnan da wasu Fans Dinsu mutun Biyu
ne su Biyar kenan. Yayinda Rukayyah ke lullub'e a Mayafi Zuciyarta sai duka takeyi ,, Wai yau
itace a gidan Aure gidan Umar Farouq abu kamar Almara .
"Sajeeda tace wai yaushe ne Zasu kawo wan nan Angon ne 10:30 fah Afra tace kin San sai
anmasa Huduba kuma kinga Sai sun tsaya Dan Kinga dakwai masu so Su yi masa Naseeha
Dan Rike macce Biyu sai jarumi Sajeeda tayi Dariya tace Tab kenan . Yayanku Jarumi ne ko
Afnan tace sosaima ,, kinga zai nunawa Sistern ki Jarumta irin tasa Aisha tace kai kudaina
Tsoratata mana kufa zolayace daku Safeena tace No way Ai dolema ya Hakura saboda Sabon
Shiga CE Sajeeda tace Ohhh kukan Allah yashiryaku kunga kamar naji Tsayuwar mota may be
gasu nan sunzo Suka kara feshe ko,ina da Turare kamin suka sami Gu suka zauna Rukayya
Hawayene kawai ke zuba a Idan nuwanta Dan yanxu ne yakara tsinkewa lol.

★ Bayan an kare wankin Ango Gidansu aka nufa Dan Ayi masa,, Hudu ba sosai Alhaji
Basheer ya Masa Nasiha mai Shiga jiki yayi Adalci a Tsakanin su karya nuna musu banbanci
Kuma ya Rike su Amana,, Ya tsaya tsakani da Allah karya fifita wata akan wata ya kwatanta
Adalci . Haka aka kaisa gurin Hajiyarsa Itama dai Fadan tamasa na a Rike Aman da Adalci ,,
daga nan aka Daukeshi zuwa gidansa Abokansa sai tsokanar sa sukeyi ,, Shikuma sai Dariya

kawai yakeyi yana Wani jin Dadi har suka iso Part din Salma suka nufa dashi ,, Suna Zaune
itada Kawayenta daketa zugata da Sallama suka ,, Shigo aka tsaya Akayi jawabin na Salma ta
zauna lfy da yar uwarta Kuma Farouq ya kwatanta Adalci ,, Akayi Addu,a Kamin aka Baiwa
Salma Kayanta na tande tande ,, Ba yabo ba fallasa tayi masa saida Safe shima ya mata ya
lura sosai Bata cikin Kwanciyar Hankali,, amma bayanda ya iya haka Suka Ja Farouq zuwa
part din Gimbiya Amarya .

★ Da Sallama suka Shiga yayinda wani Daddad'an kamshi mai sanyaya zuciya ya doki
Hancinsu da Sanyi mai Dadi ya Ratsa su har Kuryan Daki inda Rukayyah take suka kai Farouq
sai Daukan su Photo akeyi gwanin kyau Haka aka yi Barkwanci da Haka dai suka karasa
komai suka D'auki Su Sajeeda Domin kaisu gida ya Rage daga FAROUQ sai RUKAYYAH .
What a wonderful Day Shurune ya Ratsa Nadan wani Lokaci Yayinda Farouq yayi gyaran
murya yamatso kusa Da Rukayyah ya Bude mayafinya tare dacewa . Amincin Allah ya Tabbata
gareki yake ma,abuciyar Kyau. Girgiza mata Kai yayi Dan Ganin Hawaye ,, a Fuskarta Hannu
ya sanya yashiga goge mata Fuskarta yayinda ya umurceta data tashi ta Dauro Alwala su
nunawa Allah Farin Cikin su Da Zuwan Wan nan Ranar mai Albarka.
" Ba musu tashiga toilet tayi Alwala shima yashiga yayi yajasu jam,in Sallah Raka,a Biyu
sukayi kamin ya matso kusa da ita ya Dora . Hannunsa akanta yashiga yi mata Addu,ah da
kuma Fatan Samun Zuri,a Tagari . kamin ya je ya Dauko Plate da cup ya dauko Leda Wata
gasaasar kaza yazuba a plate din ya Dauko fresh milk ya zuba dakyar ya lallab'a ta ta ci kadan
bada yawa ba kamin tayi brush Shikuma ya fita anan ne Rukayyah ta samu ta zauna a saman
bed duk sai taji wani iri saboda Bata saba ba . farouq kam Dakinsa dake part din Rukayya
yanufa yashiga Toilet ya washa Ruwa kamin yafito ya feshe Jikinsa Da Turare Yana katewa ya
nufi Room D'in Rukayyah Zaune ya tarar da ita Yace a,a wai Ke Zama ma kikayi ,sunkuyar da
kanta tayi kasa ya matso kusa da ita yace kinga kidai kije ki cire wan nan kayan ko na cire miki
su da kaina Rasa mezatace masa tayi sai murza yan yatsun ta takeyi matso wa yayi kusa da ita
ya ,, Fara Rike mata Hannu wani Shock ne taji yajata Dakyar ya lallabata tayarda tacire kayanta
ya Dauko mata wata Sleeping Dress .Purple colour. Had'ararriya ta Hadufa ba karya gaskiya
yaja Hannunta suka fara zagayawa sanda yanuna mata komai dakomai hard Room dinsa saida
yakaita ita dai Takasa sakewa Bayan yakare nuna mata komai ya dawo da ita zuwa Room Dinta
Upp din. Wuta yayi yakara A,c suka kwanta Yajawota ya Rungumeta can cikin Jikinsa Jikinta ne
yafara Rawa Dayaga Haka sai ya Rada mata a kunne just be Free ba Abinda zan. Maki duk da
Haka Bata Sake ba Haka yashiga wasa da ita son Ransa Sanda yakusa Wuce gona da iri
Rukayya ta Fara masa kuka badan yasoba ya barta A haka sukayi Bacci Wanda zankira da An
daiyi maganin Ace Ba,ayi ba Dan Ba Wanda yayi Baccin kirki acikinsu Sai guraren Asuba ya
barta yatashi Dan zuwa masallaci ita kuma ta Shiga Toilet wanka tafara yi kamin tayi Sallah ta
zauna tafara karatun Al-Qur,ani Mai Girma har gari ya waye.

★Tun ficewarsu Farouq Salma takasa Zaune takasa tsaye da kyar ta iya control din kanta
ledarma ko Kallon ta batayiba fuu tashige Room Dinta kawayentane sukaci kazar Banda kukah
ba abinda Salma keyi ba irin Zugarda Zuciyarta batayi mata ba O my God yanxu Farouq dina
na can tare da wata ko wane karatun yake koya mata oho Ashe haka mata sukeji idan An masu
Kishiya da gaskene Ashe Ba,a Bacci haka ta wanxu cikin Tunani Matar tasiri Har Garin Allah ya

waye yanda taga Rana haka taga dare . Shigowar Farouq ne ya sanyata ta fara Baccin karya
kamar gaske tayar da ita yayi yace taje ,, tayi Sallah Lokaci yayi kamin yashafa cikinta yabata
kiss ya wuce mtsewww taja Tsaki Aikin Banxa Bayan ka gama Lalacewa da wata shine zakazo
kamin Dadin baki( Hattara mata wallahi muji Tsoron Allah yakamata musan irin abinda zamu
gayawa mazajenmu saboda mumuke Neman Aljannah a gunsu Allah yasa mudace Ameen.)
Haka ta Daure taje tayi Alwala tayi Sallah ta Shiga wanka bayan ta idar da Sallah tafito tashirya
cikin wata Atamfah Dinkin mai kyau tana ta wani cika da batsewa kamar wadda Akayi wa laifin
Wani Abin.

" Bayan ya dawo daga masallaci part din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login