Showing 1 words to 3000 words out of 23840 words

Chapter 1 - A WANI COMPANY PART COMPLETE BY MEERAT OMAR.pdf

05 Jun 2025

744

[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ





# SQUAD 2024


A WANI COMPANY

BY

HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT






MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS





Page 2,


Washegari tun wuri ya tashi shiryawa yayi cikin cuz Black masu matuƙar kyau da shaƙi,
hannunsa riƙe da yar ƙaramar back ya fito yana tafiya cikin isa da ƙasaita ya nayin yadda yake
tafiya sai ka É—auka ta zame masa dole ne. security ne suka rufa masa baya motoci uku suka yi
combai jeri suke tafiya har suka isa cikin katafaren Company mai matiƙar kyau da girma suna
isa ya ɓale murfin motar ya fito left ya hau zuwa bene na biyar in da office ɗinsa yake a
hankali ya murda handle ya shiga, wow shikansa office ɗin abun kallone Office ne mai matiƙar
kyau zama yayi ya na cire riga dake saman kayan


Zaune ya ke cikin Office talphone pole dage gefansa ya janyo wasu Numbobi ya danna da
basu shige biyar ba "turomin Suhail" ya faÉ—a ya na aje wayar É—ago kansa yayi Masha Allah
babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai shekaru (60) haka farine tass ya ɗaure gashinsa da
wani ɗan ƙaramin ribom. Nocking aka yi duban ƙofar yayi, da sauri kuma ya miƙe yana

rungumar wanda ya shigo cikin office É—in da kansa ya zaunar da shi shima ya samu waje ya
zauna kallon Suhail yayi wande idansa ke lumshe wannan É—abi'a ce ta Suhail koda yaushe zaka
ga idanunsa a lumshe kamar wanda kejin bacci Suhail a salin kyakyawane kuma É—an gayu irin
dai mutanan nane da ake wa laƙabi da classic aje'butter ya na da pink leps sai ƙwayar
idanunsa da ta kasance brown, gashinsa ya sauka har baya.

Miƙa masa takarda dake hannusa yayi duk da yasan haka bamai yuwa bane dan yana da
tabbacin tun da suhail yace ba inda zasa to bafa zaije ɗin ba murmushi yayi yana karɓar
takarda sai da yagama karantawa tass kafin ya É—aga kai yana kallon datinjon wanda ya
kasance mahaifi agaresa "yanzu dad da gaske sai na tafi wance garin? da ku ka turani kadai
san babu wanda nasani acen kuma ban taɓa zuwa ba why dad mai yasa?" shiru mahaifinasa
yayi yana kallonsa dan ya rasa me zaiyi tasowa yayi daga inda ya ke ya zo dab da É—an nasa
yana dafa kafaɗarsa "kayi haƙuri son wannan tafiyar dole ce kai ya kamata kaje ka cigaba da
kulamana da wancen Company dake nigeria banaso abun da yafaru abaya ya sake faruwa"
"shikenan dad naji na kuma amince zanje mudum hakan zai faranta maka rai" wani irin yalwa
tacen murmushi yayi yana sake rungume sa "Thank y my son Thank you" "Never mind dad" ya
faÉ—a yana fita daga Office É—in shifa harga Allah baya son zuwa ko ina ya amsa ne kawai dan
farin cikin mahaifinsa wanda ya kasance gatansa.




"Ayrah" "Ayrah" shine abun da Mama ke faɗa tana tsaye a jikin ƙofar ɗakin fitowa tayi tana turo
baki ita ala dole an takuramata sanye take cikin atamfa maroon mai adon ganye green "ni zan
fita ba daÉ—ewa zanba kinji" "Tom Mama Allah ya tsaremin ke" tafaÉ—a tana shiga É—akin
murmushi Mama tayi tana fita abunta sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta isa gidan alh hadi
wanda ke nesa da anguwar su tana shiga ta isa part É—in hajiyar, da karamawa ta tarbeta suka
gaisa dan hajiya sarai matace mai matiƙar kirki da karamci abunta ko kaɗan bai rufemata idoba
ta na matuƙar tausayin su Ayrah don yawanci ma anan suke samun abinci da zasuci.

"Dama Maman Ayrah abunda yasa nace a kiraki wani alkhairi naji shine nace zan faÉ—amiki ko
Allah zai sa a dace" murmushi Mama tayi tana duban hajiya sarai "Wollah kinga É—azu ne alh ke
faÉ—amin wai Company da suke aiki ana bukatar ma'aikata nayi matukar jin daÉ—in haka na ce
masa kuma in Allah ya yarda zan kiraki na faÉ—amiki idan mun gama magana sai a samawa
Ayarh ko ya kika gani?" farin ciki mara misaltuwa ne ya rufe Mama tama rasa mai zata ce
murmushi kawai take tabbas wannan abun farin cikine agaresu "Nagode sosai tabbas keÉ—in ta
dabance kuma ke mai son muce nagode sosai" Mama ta faÉ—a tana hawaye "haba Aminatu
menene abun kuka anan shin dan nayiwa Ayrah abu shine sai kin tamin godiya karki manta
Ayrah fa tamkar ya take a wajena " "Hakane hajiya tabbas Ayrah yar'kice"

A hankali ya ke É—agawa mutane da suka rakosa airport É—in hannu har ya yi gaba ya dawo da
gudu yana rungume mahaifin nasa tabbas ya san zaiyi kewa zai yi kewar Daddyn'sa "I really
miss you dad" "Miss you too son ka kula da kanka kaji" ya faÉ—a shima yana share hawayen
dake zubo masa

Austiralia to Nigeria sai dai muce Allah ya sauke ka lafiya Suhail...
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ





# SQUAD 2024


A WANI COMPANY

BY

HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT


MARUBUCIYAR
A'ISHA LABIBA.



AND NOW

A WANI COMPANY.

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS



*"Wannan labarin mallakin mai shine kawai ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ta
kowace sigaba idan kuma hakan ta faru bazan kyale ba"*


*BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
*Duk kan yabo da godiya sun ta* *bata ga Allah Subhanahu wata'ala* *mamalakin sammai da

ƙasai*
*Allah kai daÉ—in tsira a bisa shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama tsira
da aminci su tabata a garesa da Ahalinsa da sahabbansa dama wainda suka bisa a tafarki mai
kyau daga yanzu har izuwa ranar alƙiyama


Ep one.


Yau ta kama Ranar lahadi a yau kuma duk kanin wasu ma'aikata ke hutawa a gidajensu
Hadarine Sosai ya haÉ—o
Garin yayi baƙi wata irin iskace ke kaɗawa mai haɗe da ledoji da ƙura mai baɗe idanun mutane.
Gajimare ta yi wani irin baƙi tsawa ake mai haɗe da walƙiya yanayin yadda garin yayi duhu na
iya tabbatar maka dacewa ruwa na iya sauka a kowane irin lokaci.
tsugune ta ke a jikin bishiya ta kifa kanta a kan gwiwarta duk da wannan hadarin da ya haÉ—o
hakan bai sa taji tsoro ba
wani bawan Allah ne yayo gurin, da sauri ya karasa ya na tambayarta lafiya?
ÆŠago kai ta yi ta kallesa da rinanin idanunta wanda suka yi wani mugun ja daga gani kasan ba
ƙaramin kuka ta yi ba
Woww Masha Allah tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yayi Wannan halita
farace tass gashinta ya kwanta har gadan bayanta gawani saje da ya kwanta a gefe-gefe n
fuskarta tana da ɗan ƙaramin baki sai hancinta dogo mai tsini masha Allah yarinya ta haɗu
matuƙa ta na da tsayi sosai ga wani uban Sharpe da ya fita a jikinta. Tashi ta yi bata ce masa
komai ba ta fara tafiya jijiga kansa kawai yayi yai gaba abinsa ya na tinanin ko me yasa yarinya
kamar wannan tafito tsakiyar layi tana kuka duk da wannan uban hadarin da ya haÉ—o wanda a
koda yaushe ruwa zai iya zuba..
Tafiya take a hankali kasan cewar ita ba ma'abociyar sauri bace wata tsawa da akayi yasa tai
saurin rintse idanunta tana toshe kunnanta sunan Allah ta ke ambata cikin yar ƙaramar
Muryarta wadda idan ba kana kusa ba bazaka taɓa jin abun da ta ke faɗa ba,ta kai kusan 5
minute a haka kafin a hankali ta buɗe idanun na ta kamar mai tsoron wani abu Ruwane ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya yayin da ruwan ke zuba tare da wata tsawa da ke
tashi cigaba da tafiya ta yi a hankali duk da ta'taka abu a ƙafarta hakan baisa ta tsaya ba harta
ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidan nasu dake anguwar lokogoma.
Da sauri ta ƙarasa cikin ɗakin tana haki faɗawa kan wata yar taɓarma tayi dake shimfiɗe a
tsakar É—akin a hankali kuma jikinta ya fara wani irin rawa tana fitar da wani irin wahalala
numfashi
Gaba É—aya ta fita hayyacinta babu abin da take ambata sai Mamah Mamah washh Allah na
mutuwa zanyi shine kaÉ—ai abun dake fita daga bakinta
Fitowarta kenan daga cikin bayin buɗe ɗan yalolon mayafin dake ƙofar tayi gabanta ne yayi
wani mugun faɗuwa dan-danan zufa ta shiga keto'mata duk da ruwan saman da ake ƙarasa
shiga cikin É—akin tayi da sauri jawota tayi jikinta ta rungume wasu zafafa hawaye ne ke fita daga
fusakarta da sauri kuma kamar wadda aka tsikara ta tashi ta nufi cikin ɗakin wata yar ƙaramar
leda ta É—ako ta nufi yar randar dake É—akin ta É—ibo ruwa tsayawa tayi tana nazari shin taya zata

bata magani bayan tin safe ruwa ne kaɗai a cikinsu? hawayene ya ƙara gangaro mata. daga
hanayanta sama tayi gaba É—aya ta kasa furta komai sai hawaye dake ambaliya akan fuskart
Ƙarasowa wajan tayi a hankali ta ɗagota tana bata maganin, Kwantar da ita tayi a saman
cinyarta ta na shafa sumar kanta a haka har bacci ya É—auke su

Washegari.
A hankali take buÉ—e idanunta wanda suka mata wani irin nauyi kwance ta ganta kan cinyar
Mamah da ke zaune ta jingina da bango kenan a haka Mamanta ta kwana tafaÉ—a tana jin wani
irin tausayi mahaifiyartata da sauri ta ƙarasa jikinta ta rungume ta murmushi Maama tayi dama
ta daÉ—e da tashi batason ta yi motsine ta tada yar'tata "yanzu Mama a haka kika kwana?
meyasa baki tasheni ba?" ta faÉ—a idanunta na kawo ruwa "da ban tasheki ba ai gashi yanzu kin
tashiko Maza tashi kije ki É—auro alwala muyi sallah" tashi tayi a hankali dan har yanzu jikinta na
mata wani irin ciwo

Austaraliya

Afusace ya ke maganar wanda kana gani kasan ransa ya ɓaci sosai da sauri kuma kamar
wanda aka tsikara ya miƙe yana gyara zaman cuz din dake jikinsa fita yayi cikin sauri security
dake wajan suka rufa masa baya daga musu hannu yayi dan baya buƙatar kowa yanzu a kusa
da shi wani haÉ—aÉ—an É—aki ya shiga mai tsananin kyau cire rigar dake jikinsa yayi ya kwanta a
kan katafaran royal bed É—in dake shimfiÉ—e a É—akin gaba É—aya kansa ya É—au zafi ya ma rasa me
ya kamata yayi shin idan haka ta kasance menene makomarsa kenan? anya zai yarda ya tafi
wani guri No ya faÉ—a yana girgiza kansa gaba É—aya É—imuwa da tashin hankali sun wanzu akan
fuskarsa
Da sauri ya tashi yana nufar badroom, ya na shiga ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi
dan-danan kuma wata nutsuwa tafara saukar masa, lumshe idanunsa yayi a hankali ya na
sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ



# SQUAD 2024


A WANI COMPANY


BY

HAUWAU OMAR
...CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

fallow my account Arewabooks

Arewabooks@hauwauomar05







Page 4,






"Ayrah" "Ayrah wai me kike har yanzu baki fito ba kin san dai ba tsayawa jiranki za'a yi ba ko"
da sauri ta fito daga ɗakin tana gyara zaman zumbulele hijjab ɗin ta da ya sauka har ƙasa tayi
matiƙar kyau. "Mazaki wuce kije gidan alh hadi yana cen yana jiranki tun ɗazu" da sauri ta kama
hanya ta tafi har tayi gaba ta dawa tana kiss É—in Mamanta akumatu murmushi Mama tayi tana
É—aga mata hannu "Allah ya tsaremin ke dear" "ameen Mamana"

Tafiya take cikin sauri duk da ba wani sauri ta'iya ba tayi tafiya sosai kafin ta karasa gidan tana
shiga taga habib da'alama shima fita zai yi da sauri ya karaso wajanta yana murmushi "a yau
Ayrah ce a gidan na mu?" "eh wllh ya habib kwana biyu" "kin guje muba" ya faÉ—a yana dariya
murmushi tayi tana sun kuyar da kanta ƙasa "ki maza ki shiga ciki dad yanan yana jiranki tin
É—azu" da sauri ta nufi cikin falon tana shiga tagasu zaune kan kujerin falon tsugunawa tayi har
ƙasa tana gaidasu amasawa suka yi da fara'a "sai mu wuce ko kar muyi late dan yanzu Mdee
da aka sauya baya da sauƙi kwata-kwata"

Kama hanya sukayi zuwa wajan parking space shiga cikin motar yayi hajiya da kanta ta
buÉ—ewa Ayarh motar ta shiga..
Suna isa ta tsaya tana karanta sunan Company



* JULIUE BERGER NIGERIA PLC*


Company Juliue Berger Nigeria Plc yana hedikwata a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Company ya kasan ce wani kamfanin gine-gine da ke aiki a fannoni daban-daban na gine-gine,
musamman a fannin gine-ginen tituna,

Akwai kamfanoni da dama a Najeriya da ke da alaka da kamfanoni a kasashen waje, ciki har da
kamfanin Juliue Berger Nigeria Plc. Kamfanin ya kasance yana aiki tare da kamfanoni
daban-daban a duniya, ciki har da na Austiralia, don gudanar da ayyukan gine-gine da kuma
bayar da kayayyaki.

Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su isa left zaro ido tayi tana kallon alh hadi dan ita tun da
uwarta ta haifeta bata taɓa ganin irin wannan abun ba murmushi yayi yana nuna mata gurin
"shiga muje kinji daughter babu abunda zai miki" shiga tayi a tsorace jin sunyi sama ya sa tayi
saurin rintsa idanunta tana ambatar sunan Allah Dai-dai left na biyar suka isa fita yayi tana biye da shi nocking yayi a jikin wani office mai kyan
gaske, asama an rubuta General Mdee Suhail . P.a din dake zaune a Office din farko ce ta
basu umarnin shiga shiga suka yi bakinsu dauke da salama zama alh hadi yayi akan kujera da
sauri p.a ta miƙe tana gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska wani banza kallo ta watsawa
Ayrah duk da bata santa ba amma gani farko taji ta tsani yarinya da sauri Ayrah ta sun kuyar da
kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta

Tashi yayi yana ruke da hannuta suka shiga cikin katafaren office É—in wani mugun sanyine ya
daketa da sauri ta kan-ƙame jikinta suna shiga ya nuna mata wajen zama da kecen nesa
karasawa yayi wajan Suhail da fara'a ya miƙawa masa hannu shima cikin girmamawa ya basa
hannu sukai musabaha dan Suhail duk wulaƙancisa yana matukar girmama manya bayan sun
gaisa ne yake faÉ—a masa ga yarinya da yace zai kawo murmushi yayi yana kallon yarinya wani
irin faÉ—iwar gaba yaji da sauri ya kautar da idanunsa daka kanta .

"Shikenan babu komai ka koma bakin aikinka zan mata inter biyu" godiya ya masa ya nufi ƙofar
dan fita tashi tayi da sauri tabi bayansa "kije wacen kujera ki zauna daughter shine zai miki
inter biyu" "tom Daddy" ta faÉ—a tana bin inda ya gaya mata zama tayi akan kujera har lokacin
kuma bai dago ya kalleta ba sai da ya gama abun da yake kafin cikin wata sanyayiyar muryasa
ya ce ya sunanki

"Fatima Mahir"
ta bashi masa itama a taƙaice


Menene matakin karatunki
Secondary

"It's also an opportunity for job seekers, we are hiring young people here"

Ya faɗa a tsawace sunkuyar da kanta tayi ƙasa dan-danan hawaye ya fara ambaliya a

fusakarta


Miƙa hannu yayi ya karɓi takardun hannu nata yana dubawa murmushi yayi abun ba karamin
mamaki ya bataba ganin yanzu ya gama mata tsawa amma kuma ya koma murmushi "shikenan
zan daukeki aiki amma kin san wane aiki zaki yi?" girgiza kai tayi alamar a'a "coffee" Zaki zama
mai kawomin coffee ko da yaushe kuma ban yarda ki kaiwa wani acikin Company coffee ba in
bani ba kina jina" É—aga kai tayi alamar eh ita dai koma me zai bata ya bata in dai zata samu
kuÉ—in da zata na siya musu abinci kuma Mamanta ta daina wankau wata takarda ya É—auka yayi
rubutu "gashinan zuwa gobe sai kizo dan fara aikinki sanan idan kin fita kicewa p.a É—in dake
zaune a Office na farko ta rakaki wajan alh hadi ki kai masa takarda" É—aga kai tayi tana masa
godiya, da sauri kuma ta fita daga Office É—in


tana fitowa p.a taimata wani irin kallo sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana magana "dama cewa
yayi kirakani wajan wanda mukazo dashi É—azu" wani kallon banza tamata kafin tace "ke bana
son iskanci da ni na shigo dake da zakice narakaki wawuya kawai" ita dai bata ce mata komai
ba kuma bata É—aga kai ta kalleta ba duk abunda suke yana kallonsu jin telephone É—in dake kan
table din nata yayi kara yasa tayi saurin É—agawa hlo sir cikin wata irin murya mai amo ya ke
bata umarni gaba ɗaya ta rikice dan bata taɓa jinsa da irin murya ba "am sorry sir Insha Allah
hakan bazai kara faruwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login