Showing 15001 words to 18000 words out of 23840 words
Chapter 6 - A WANI COMPANY PART COMPLETE BY MEERAT OMAR.pdf
hankali ta mike da ga kwance da ta ke ta
na kallon Mama meƙewa tayi ta shiga toilet dan yin wanka, ta na fitowa ta nufi cikin ɗakin ta
shirya tsaf cikin doguwa riga ta atamfa hajjab ta zura Masha Allah ta yi kyau sosai fitowa tayi ta
na wa Mama bye bye ta fita sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta samu mai napeep É—in da zai kaita
zuwa Company tana isa ta shiga ciki office ɗin Suhailat ta shiga ta na ganinta ta miƙe da sauri
ta rungume ta "Oyoyo sister yau kinzo kenan?" murmushi tayi tana gyaÉ—a mata kai "ya jikin
naki?" "da sauƙi Aunty Suhailat"ta ce" Masha Allah Mdee ya san kinzo ne?" "a'a yanzu na zo ai"
ta ce"Okay maza kije zuwa anjima kya dawo kinji" fita tayi ta nufi office É—in Mdee É—ago kai p.a
tayi ta na kallonta dan ita gaba É—aya ma ta manta da ita wuce wa tayi zuwa ciki yana ganinta ya
ya yi murmushi, Murmushi ita ma tayi tana zama akan kujera ya ce" ya jikin na ki?" "da sauƙi"
ta bashi amsa.
Kasa tashi tayi ta haÉ—a masa coffee dan tana gudu abunda ya faru ranan ya sake faruwa jita yi
ya ce "coffee" jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi wajan haɗa coffee ɗin tana haɗa masa ta zo kan
table ta ajiye zama tayi akan kujera tana wasa da yatsun hannunta sai da ya gama tsaf kafin ya
miƙe kallonsa tayi nufar ɗakin hutunsa yayi ita dai tanan zaune har ya shige kuma bai mata
magana ba ta kai kusan 20munith kafin ya fito cikin cuz brown Masha Allah yayi kyau sosai.
hanyar fita yayi juyowa yayi yana kallonta ganin ba shi take kallo ba yasa ya ce "muje ko"
É—agowa tayi ta na kallonsa dan bata gane inda maganarsa ta dosaba "cewa nayi ki taso muje"
babu musu ta miƙe ta bi bayansa p.a na ganinsa ta miƙe karasawa yayi "bani file ɗinnan" miƙa
masa tayi har yayi gaba tace "am sir ko nazo muje tare ne?" "ban nemaki ba idan da ina da
bukatar hakan da zan faÉ—amiki" shiru tayi bata sake cewa komai ba har suka fita zuwa waje
Shiga yayi cikin motar itama ta shiga suna isa drive ya fito ya na buɗe musu ƙofa tana ganin
inda suka zo ta haÉ—e rai haka kurum a bar mutum shi kaÉ—ai har ya gaji murmushi yayi ya na
juyowa ya kalleta dan ya ji abunda ta ce ganin ya na murmushi ya sa tayi shiru suna isa ya
nuna mata wajan zama karasawa yayi wajan meeting É—in
Mrss Afif ne ya dubesa ya ce" muna bukatar gine mai kyau na zamani mun yi la'akari da kaf
Company babu kamar wannan shiyasa muka kawo kwangila mu nan" haka suka cigaba da
tattaunawa tun tana sa ran zai taho su tafi har ta gaji meƙewa tayi ta fita ganin ta fita ya sa
hankalisa ya dawo kanta ko ina zata sai ya ji ya kagu su tashi daga meeting É—in tana fita kai
tsaye wani lambu mai kyau ta karasa lambu cike ya ke da bishiyoyi daban daban Kamar su
mangoro, gwaiba, dabino banana, da dai sauransu ai ta na ganin bishiyar mangaro ta karasa da
sauri ta na murmushi dan ta na matukar kaunar mangoro wani dutse ta gani agun da sauri ta
karasa ta na jefawa ganin ya ƙi faɗowa gashi ta gaji ya sa ta zauna agun tana haɗe rai Suhail
da fitowarsa kenan ya na nemanta security ne ya ce masa ya ganta ta shiga lambun cen nufar
gun yayi ya na zuwa ya ga ta haɗe hannu biyu a kumatu ta na hawaye da sauri ya ƙasa ya na
tambayarta abunda ya faru nuna masa mangoro tayi kuma har lokacin ta na hawaye murmushi
yayi kawai ya kira wani security bashi umarni yayi akan ya ciro masa mangoro da yawa ya kai
masa mota ai ta na jin haka ta miƙe ta na murmushi jindaɗi "toh taso muje ko" babu musu ta
bisa suka fita a lambu suna shiga cikin motar ta zauna lokaci zuwa lokacin sai ta leƙa ganin har
yanzu security bai tahoba ya sa ta ƙara turo baki "menene kuma toh?" ta ce" bashine har yanzu
bai tahoba" "ke kuma rashin haƙuri" juyar da fusakarta tayi ta na ƙara turo baki murmushi kawai
yayi security na zuwa ya buÉ—e boot ya saka musu zagayowa yayi "sir an saka a boot" okay ya
bashi amsa drive ya ja suka fita kai tsaye gida ya kaita suna isa ya sa aka É—ako mata ledar
mangoro mai uban yawa sai murmushi take kamawa tayi ta na shiga cikin gidan sakin baki
Mama tayi tana kallonta ganinta ruƙe da uwar leda ta ce "ke ko Menene acikin wannan ledar?"
"mangoro ne" ta bata amsa tana murmushi "wato kefa na fahimci ma ba aiki kike ba a Company
wallahi kawai shirma kike" turo baki tayi ta na shiga É—aki da abunta tashi Mama tayi tana bunta
a baya zama tayi akan tabarma ta na buÉ—e ledar "kuma fa walloh Mama ya nuna mangoro" "eh
gashinan ai nagani sai ki bada himma kisha" É—auka tai zata kai baki "amma ai kya wanke ko?"
dafe kai tayi ta na dariya "wollah ni nama manta ana wani wankewa" ta ce" dama ya za'a yi ki
tuna tunda yau ala ya haÉ—aki da mutumnin ki"
Suhailat ganin har yanzu Ayrah bata zoba kuma gashi lokacin ta shi ya kusa ya sa ta miƙe dan
shirin tafiya gida ta na fitowa taga p.a ta sako daga saman "amma yawa Ayrah fa?" kallon sama
da ƙasa tayi mata kafin tace "wacece kuma haka?" shiru Suhailat tayi bata sake cewa komai ba
dan ta fahimci p.a bata da mutunci ko kaÉ—an kama hanya tayi tai wuce warta
"Ayrah!! Ayrah!! ki tashi daga bacci nan kin san fa babu kyau bacci yamma ko tun da kika dawo
kike ta bacci ko abinci baki nema ba" buÉ—e idanunta tayi ta na kallon mahaifiyata
A hankali ya ke sauka daga matata kalar bene sanye ya ke cikin white cuz ya haÉ—e gashinsa
guri É—aya farin ne tass gashinsa ya sauka har gadon bayansa da wani irin sauri security suka
nufosa suna isowa gun gaba É—aya suka rusuna É—ago kai yayi yana kallon su ya salam kyau iya
Kyau kyakyawa ajin ƙarshe sanye yake da farin glass a fuskarsa gefan sa wata mata tace
wadda aƙala zata haura shekaru (45) itama fare tass kamar dai shi sanye take cikin Black
abaya mai duwatsu tayi rolling da belt na abayar hannuta ruƙe ya ke cikin na haka suka jera
suna tafiya gwanin ban sha'awa suna isa bakin motar aka buÉ—e musu suka shiga kai tsaye kata
faran gida dake maitama hills estate ya salam gidane iya gida girman gidan ya zarce misali
gaba É—aya gidan zagaye yake da security ta ko ina mai gadi ne ya buÉ—e get É—in da jerewa
motocin suka yi zuwa cikin gidan tun kafin su gama parking ta fito da gudu ta na ihu duk da
tsakanin cikin gidan da pearking lot da nisa amma hakan bai sata ta howa da gudu ba ta na
murna "Oyoyo Ammina Oyoyo ya Abrad" shine kawai abun da take furtawa ta na gudu
murmushi yayi kawai ya kalli Ammi itama kallon na sa tayi da sauri ta faÉ—a jikin Ammin ta na
murmushi cen kuma hawaye ya fara zuba akan fuskarta "Ammi shine kuka tafi kuka barni ni
kaÉ—ai ko?" "ohh Jiddah toh yanzu kuma menene abun kuka ai gashi mun dawo ko?" gyaÉ—a kai
tayi ta na kallon Abrad jan hanci ta yayi ya na cewa "rigimama Ammi" murmushi tayi ta na turo
baki "nifa fushi na ke da kai" "kaina bisa wuya na idan kikai fushi da ni ina zan kama" ya faÉ—a ya
na yin gaba abunsa dan shi bai cika yawan magana ba wananan É—in ma yayi ta ne kawai wani
haɗaɗan falo ya shiga mai tsanani kyau irin falon nane da ko gidan shugaban ƙasa ba a
samunsa a hankali ya zauna a kan kujera da ke gun ya na lumshe idanunsa wani irin sanyi ne
ke ratsa masa zuci yau dai gashi ya dawo Nigeria duk da badan Ammai taje ta tawo dashi bana
babu abun da zai dawo da shi
Ammi kama hannu Jiddah tayi suka shiga na su apartment É—in sai surutu ta ke kamar redio dan
Jiddah badai magana ba
Ayrah fitowa tayi cikin ƙanan kaya masu kyau da shaƙi kallonta Mama tayi tai murmushi "kin yi
kyau sosai" murmushi tayi ta na zama akan tabarma "wallahi Mama na ƙagu gobe tayi naje aiki
saboda za'a bani salary na" murmushi Mama tayi "waya ga su Ayrah da salary" wata dariya tayi
mai cike da nuna zallar farin ciki ta
Tashi yayi ya haura sama ohh ya rabbi ashe ba komai na gani a ƙasa ba dankareren falone
shima na alfarama bedroom ya shiga dan watsa ruwa
Ɗaure ya fito cikin white towel iya gwiwa hannusa na ruƙe da karami wanda ya ke tsane kansa
da shi
Wani irin taunar cingom take mai bada sauti kallon wata ƙarama yarinya tayi wadda baza ta fi
Sa'ar Jiddah ba "kinji na gaya miki wallahi kika sa ke kikaje wajan mutsiya tan cen ranki sai ya
bacci sakara kawai" "rabi da ita Momy ita yarinya wallahi na fahimci tafi son Ammi" "eh É—in nafi
sonsu kuma ni wallahi duk abinda zakuce sai dai muce haka kuri ni dai wallahi Momy akullum
ba zan daina faÉ—aminki kiji tsoran Allah ba kuma kisan zaki mutu" da sauri Momy ta bige mata
baki "zaki rufemin baki ko kuwa sakarar yarinya sai anyi magana ki farawa mutane wa'azi
angaya miki mu bamu san abunda ya dace ba ne?" tashi tayi ta haura sama tana ƙunƙuni
"Na fahimci yarinya nan sai na shiga dukanta zata dawo hankalin ta" "kema ce Momy tutuni
nagaya miki ki kaita wajan durfus kawai ya rufe miki bakinta wallahi idan ba haka ba duk wani
shirinki sai ta tarwatsa sa yanzu gashi su ya Abrad sun dawo Nigeria kuma da kince ance miki
ba zai taɓa dawowa ba" shiru Momy tayi ba tace komai ba dan itama al'amarin duk ya ɗaure
mata kai
Niko nace Allah kenan babu wani wanda ya isa yayi abunda Allah bai ba hajiyata[8/13, 4:06
PM] Masoyiya í ¾í´—í ½í´¥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
A WANI COMPANY
BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT.
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account.
Arewabook@hauwauomar
Page_16_17
Be ce mata komai ba ya buÉ—e idanunsa "Kin É—auka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai
ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faÉ—a ta na fita dan zuwa
office É—in Suhailat
Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa
ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana
kallonsa ganin da marron É—in cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke
zuwa Company? ta faÉ—a ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi
kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu
musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna
isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh
insha Allah zan faÉ—amata"
Tsaye ya ke ajikin window apartment É—insa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai
kyau haÉ—e gashinsa ya yi ya É—aure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaÉ—i yanayi
ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin
bedroom É—in ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi
wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta
biyo ni zata dakeni ba dan na É—auka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma
ka ke min faÉ—a ko ya Abrad" ta faÉ—a hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah
kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a
É—akin ta na kuka
Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta
"Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faÉ—a" "Da ya miki faÉ—a ke
me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa"
"Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom É—inta dan shiryawa
ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu
ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke
kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa
Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su
ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su
na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa"
Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis
za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun
bashi ciwon kai.
Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta
ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso
gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni
kawai ji nayi ina cikin nishaÉ—i" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin É—akin na su
kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin É—akin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako.
Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama
samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi
sha'awar cinta bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi
"Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daÉ—i sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki
waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci
Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar
jan luck É—in ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buÉ—e ta kasa drive ta ce ya
buÉ—e ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buÉ—e ma ta ko hmm" shiru ya yi
ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buÉ—emin ba" dariya Jiddah ta yi
ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buÉ—e ma ta, da sauri ta shiga ta
na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida
da sauri Yusra ta fita ta yi apartment É—insu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da
gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faÉ—awa kan makeken gadon
ta yi ta na sauke numfashi
Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na
gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su
ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi
hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa
shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta
Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin
mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta
"Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi
da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daÉ—e dan anjima akwai inda zamu" "Thank you
sir" ta faÉ—a tana murmushi
Da sauri ta ke sauka daga kan stap É—in ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama
wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta
"Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faÉ—a cikin