Showing 12001 words to 15000 words out of 23840 words
Chapter 5 - A WANI COMPANY PART COMPLETE BY MEERAT OMAR.pdf
abun
da ya ce kin shirun tayi ta cigaba da kukanta ƙara janta yayi ta ko faɗa jikinsa wani irin faɗuwar
gaba ce ta ziyarce sa sai yaji Kamar ya taɓa shork da sauri ya rabata da jikinsa ya na komawa
ya zauna "kije office ɗin ƙasa zan nemaki anjima" tana sha shekar kuka ta fita wata irin dariya
p.a ta tintsire da ita a lokacin da tazo wucewa ita dai bata kobi ta kanta ba ta fita abunta
Suhailat ganin hawaye akan fuskarta ya sa ta miƙe da sauri tana rukota "menene ya faru
Ayrah?" hawaye ne ya kara zubowa "ki yi shiru Please ki faÉ—amin kinga kin tayarmin da hankali"
bata labarin abun da ya faru tayi shuru Suhailat tayi tana nazarin abun kafin tayi murmushi
kawai ta bar magana "to kiyi shiru kinji ina ga wani abune a wajan" goge mata hawaye dake
fuskartata tayi ta na cewa "yauwa ko kefa nifa sai nagama kamar idan kina kuka kinfi kyau
wollah" murmushi kawai tayi tana boye kanta akan cinyarta.
P.a miƙewa tayi da sauri ta nufi office ɗin Abdul ta na shiga ta tuntsire da wata muguwar dariya
shima dariya yayi "albishirinki?"ta ce" goro" ya bata amsa "part one dai munyi nasara saura two"
ya ce" a haba dai?" Ta ce" ai dama na faÉ—a wallahi Sai yarinya ta gane kuranta naso ma ace bai
gane menene a kujera ba kasan nan gaba menene shirinmu?" girgiza mata kai tayi alamar a'a
matsawa tayi ta raÉ—a masa a kune "gaskiya wannan shawara taki ta matukar yi tabbas ranar
muna da shan kallo a Company nan" ta ce" sosai ma kai dai kawai a zuba eyes kaga yadda zan
juya rayuwar yarinyar".
Mikewa yayi ya fita office ɗin h.o.d na Company ya shiga da sauri ya miƙa ya na gaidasa
amsawa yayi cikin sakin fuska dan duk cikin ma'aikata gidan babu wadda ya yarda da shi kamar
h.o.d zama yayi ya na masa magana lokacin "É—azu kafin na shigo Company an kashe Camera
dake office É—ina menene dalilin haka?" "sorry sir É—azu p.a ke faÉ—amin wai na bada umarni a
kasheta saboda za'a yi wani gyara ne a office É—in naka wannan dalilin yasa na kashe" ya ce" ita
p.a ɗin ce ta faɗamaka haka?" "eh sir" murmushi yayi yana cije laɓansa na ƙasa "sir ko haka da
matsala ne" ya ce" a'a babu wani matsala" ya faɗa ya na miƙewa yana fita ya koma office ɗinsa
zaune ya ganta tana danna waya a zafafe ya ƙarasa in da take ya ɗauke ta da mari wani irin
taurari ta shiga gani suna giftawa ta fuskarta "sha-sha-sha mara tunani duk ranar da kika sake
maka manci haka kin ji na faÉ—ami Wllh a bakin aikinki" zaro idanu tayi waje sai tajima gaba É—aya
zafin mari ya kauce idan ta bar aiki tasan rayuwarta ta shiga wani hali.
Miƙewa Ayrah tayi suka fita daga office ɗin "Aunty Suhailat amma dai kin daɗe kina aiki anan
ko?" "eh gsky na daÉ—e sosai Ayrah tun kafin zuwan wannan Mdee É—in" "Alokacin wani Mdee ne
azalumi. Kina so na baki labarinsa? gyaÉ—a kai tayi alamar eh "Okay Bari mu dawo daga sallah
zan baki labarin" ta faÉ—a dai-dai lokacin da suka isa masallaci.
Bayan sun idar da Sallah zama suka yi cikin lambu dake gefan gun
"Ada idan kikazo neman aiki tofa Mdee ɗin baya taɓa yarda ya ɗauke ki aiki Sai ya lalata ki.
Idan baki yarda da haka ba toh sai dai salary naki ya zama zaku raba wannan dalilin yasa yan
mata dayawa a lokacin suka shiga wata rayuwa wasu daka haka kuma suka koma karuwanci.
Zaro idanu tayi tana kallonta "Amma toh Aunty Suhailat ke ya kika yi?" murmushi tayi "Alokacin
da na zo neman aiki Mdee ya nuna min haka babu yadda zanyi saboda ina matuƙar bukatar aiki
dan dashi zan taimaki iyayena dole ina ji ina gani yake raba salary na biyu ya ban rabi duk wata
hantara idan ya tashi yimin yake haka ya mai dani p.a É—insa dan kawai ya cimma burinsa, da
yake Allah shine mai kare bawansa sai Ubangiji ya tona masa asiri aka koresa duka daga wajan
aikin
"Shiyasa zakiga wasu mata idan zasuje aikin Company suyita rawa kai wallahi ya wanci
Company ma aikata su ko kaÉ—an babu Allah a ransu amma fa bana ce mike duka ba" "A'a wasu
dan kin san a ko ina akwai nagari akwai na banza" "Haka ne Aunty Suhailat Allah ya sa mu
dace" "Ameen ya rabbi" "Sannan ki dunga kula ba kowane zaina miki murmushi ba ki zaci sanki
yake a'a wani yana da manufa a kanki ki yi a hankali sister ki san da suwa zakiyi mu'amala"
Sun daɗe agun suna tattaunawa kafin su meƙe su koma ciki "Kije office ɗin Mdee ko zai buƙaci
wani abun, kiga lokacin tashi yayi" gyaÉ—a mata kai tayi ta na nufar left ta hau
Tana isa ta gansa zaune a ya na danna lapton É—insa da'alama kuma wani abun yake, zama tayi
kan kujera sai da ya gama sannan ya É—ago ya kalleta "Yau bazan samu damar kai ki gida ba
saboda ina da wani aiki so zansa drive ya Kai ki" "Toh shikenan nagode Sosai" "Ita kuma
godiyar ta mece?" sunkuyar da kanta tayi batare da ta basa amsaba murmushi yayi ya cigaba
da abun da yake
Fitowa tayi zuwa haraba Company drive na ganinta ya buÉ—e mata mota ta shiga, suna isa ta
sauka tayi cikin gida, ta na shiga ta kwanta akan kujera "Wash Allah Mama wollah yau na gaji
da yawa" "Ke kuma aikin me kika yi da kika gajin?" "Ni fa ba aiki na yi ba kawai gajiya na yi"
"Raguwa ni nataɓa gani angaji ba tare da anyi aiki ba" "Allah Mama ana gajiya" ita dai Mama
murmushi ta yi ta cigaba da abun da ta ke dan tasan idan ta biye Ayrah to bazata taɓa bari ta ba
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya í ¾í´—í ½í´¥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
# SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account
Arewabook@hauwauomar05
Page_10_11
Washegari tun wuri Ayrah ta shirya tana jiran Suhail ganin lokacin sai tafiya yake ya sa ta tashi
da sauri tanawa Mama bye bye. Tana fita bakin titi ta tsaida me napeep shiga tayi tana faÉ—a
masa inda zataje. Suna isa ta fito tana bashi kuÉ—insa ta nufi bakin get É—in security da ke gun ta
gaida tana shiga ciki, sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta ƙarasa left ta hau
Tana isa office ɗin Mdee taji ƙofar a kulle nufar inda p.a take tai tana tambayarta Mdee baizo ba
har zata mata masifa ta tuna magungun Mdee sai kawai tayi murmushi tana É—aga mata gira
"Yes Mdee ya je wani guri sai zuwa anjima zai ƙaraso nan so idan kinga bazaki iya jiraba sai ki
koma gida sai ya dawo"
Bata ce mata komai ba ta juya tai tafiyarta abunta ƙasa ta sauka Suhailat ta gani da'alama
kuma itama zuwanta kenan da sauri ta ƙaraso "Ayrah yau ke kaɗai kika zone? naga Kamar
Mdee bai shigoba" "Eh Aunty Suhailat good morning" "Morning dear fatan kinzo lafiya?" "Lafiya
qlau ta bata amsa yau kinga wani taro za'a yi a Company so karfe biyu kowa zaije gida sai
bayan nan za'a dawo kamar 4:00 idan an tashi ki biyo ni muje wani waje dan shiryawa kinji" "a'a
Aunty Suhailat zanje gida kawai sai na faÉ—awa Mam.. Kasa karasa maganar tayi ganin Mdee
tsaye yana kallonsu da'alama kuma ya daÉ—e a wajan
Nufo su yayi ya na isowa wajan ya kalli Ayrah sai kuma naga ya cenza hanya yayi gaba abunsa
murmushi Suhailat tayi "Maza kije ki kaima Mdee coffee kin ji" "toh tace tana bin bayansa suna
isa office ɗin p.a ta gaidasa ƙasa-ƙasa ya amsa ya na nufar na sa office ɗin. Ya na shiga ta turo
ƙofa ta shiga
Tunda ta shiga taga ko É—agowa ya kalleta baiba, nufar wajan coffee tayi ta haÉ—a masa aje masa
a kan table É—in tayi wata tsawa ya daka mata wadda tasa gaba É—aya hanjin cikin ta É—aurewa "Ke
wace kalar sha-sha-sha ce? kinji nace miki ina bukata ne?" ya faÉ—a a tsawace jikinta ne ya fara
wani irin rawa dan-danan hawaye ya shiga zuba akan fuskarta so take ta bashi haƙuri amma
bata da karfin haka tsaki yayi ya zauna akan kuje yana dafe kansa da hannu biyu "Ya salam" ya
furta a hankali ya na rufe idanunsa shin me yake shirin aikatawa ne ohh ya Allah
Da gudu ta fita daga office É—in p.a dake zaune takaleta tana mamaki dalilin da yasa ta fito tana
da gudu tana kuka. Ƙasa ta sauka tashiga office ɗin Aunty Suhailat tana shiga ta rungumeta
tana wani irin kuka numfashi tane ya fara sarƙewa dalama kuma ciwonta ke ƙoƙarin tashi
Suhailat hankali ta ne ya yi mugun tashi da sauri ta kwanta da ita ta fita waje a guje ko left batai
tunani hawa ba ta shiga haura bene da bibiyu gaba ɗaya ta shiga damuwa buɗe ƙofar tayi ta
shiga tana haki p.a tsayawa tayi tana kallon ta ko bin ta kanta bataiba ta shiga cikin office É—in
Mdee ganin Suhailat a wannan yanayi yasa yayi saurin meƙewa yana kallonta nuna masa ƙofa
kawai take ta kasa magana "Menene ya faru ki nutsi ki faÉ—amin" "Sir Ayrah" "Ayrah sir" tun kafin
ta karasa ya fita da sauri ya na sauka ya faÉ—a cikin office É—in p.a na biye da shi samunta yayi
kwance idanunta a rufe da sauri ya ƙarasa ya na taɓata. Ɗaukarta yayi zuwa pearking lot tun
daga nesa yake ƙwalawa drive kira da sauri ya taso ya zo ya buɗe masa motar shiga yayi yana
ruƙe da ita suka nufi asibiti Company
suna isa asubiti da sauri Dr ya sa aka shiga da ita É—aki gaba É—aya Suhail ya rasa nutsuwarsa ji
yayi hawaye na bin kunchisa da sauri ya saka hannu ya na gogewa ya san koma me ya faru
shine sula shi yaja da baimata tsawa ba da hakan bazai faruba
Mama da ke zaune tan kaÉ—e gari dan bata so Ayarh ta dawo bata gama girkin ba tasan hali ji
tayi gabanta yayi wani irin faɗiwa a hankali ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunan Allah laila hailla
anta subuhanaka inni kuntu mina zalumin shi take ambata a zuciyarta
Sai da suka ɗauki kusan 20m kafin su fito daga room ɗin. Da sauri ya miƙe ya na ƙarasawa dan
jin me yake faruwa dafa kafaÉ—arsa Dr yayi kafin ya ce "Muje office sir" babu musu ya bisa suka
shiga office É—in nasa zama yayi akan kujera yana nuna masa shima kujera babu musu ya
zauna, cire farin glass É—in dake fuskarsa yayi ya na duban Suhail "Bakomai ne ya haifarma da
wannan shiga yanayi da ba tashiga É—inmuwa ne kasan a wasu lokuta mutum idan bai saba da
abuba toh aduk lokacin da abun ya faru da shi ya na shiga gigici da É—imuwa kuma ita yarinya
ce qarama, dole ne sai an dunga kiyaye wasu abubuwa sir "Insha Allah za'a na kiyayewa,
yanzu zan iya ganinta?" "why not yanzu haka tana É—akin hutu zaka iya zuwa, zuwa anjima idan
ta tashi zaku iya tafiya" godiya ya masa ya miƙe ya fita
A cikin company kuwa kowa ya ya fito a office É—insa sun tsa-tsaya sai mai da magana ake ita
dai Suhailat tana gefe ta haÉ—a hannuwa ta biyu a fuska babu abun da ke zuba daga idanunta
sai hawaye, gashi babu damar ta bi su Mdee hospital É—in. Yana shiga cikin É—akin ya tarar da ita
kwance tana bacci karasawa yayi gaban gadon ya zauna ya na kallonta "Am sorry Ayrah ni ne
naja miki kiyi haƙuri bazan ƙaraba kinji", ya faɗa Kamar ta na jinsa hannuta ya ruke cikin nasa
kiran dad ɗinsa ne ya shigo cikin waya da sauri ya ɗaga a ɗaya ɓangaren kuma dad ya masa
"Hallo son kana lafiya" "Lafiya qlau dad" "Masha Allah karka manta da taron yau fa ka san taren
na da matuƙar muhimmanci ko?" shiru yayi dan shi gaba ɗaya ma ya manta da wata maganar
taro 'Ko baka jinane?" "Ina jinka dad insha Allah bazan manta ba" "Toh Allah yasa muma munan
muna shiri"
Yana katse kiran ya kira h.o.d cikin Company "Ku shirya komai da za'a bukata na taro, karku
damu sai na zo no kuyi komai yadda ya kamata" "Okay sir Insha Allah za'a yi hakan" katse
wayar yayi ya na duban Ayrah da ta ke bacci abunta 2hours later
A hankali ta ke buÉ—e idanunta ganin Kamar mutum a zaune a inda ta ke yasa ta saurin karasa
buÉ—e idanunta murmushi ya sakar mata dauke kanta tayi daga kallon nasa "Sannu ya jikin"
banza tayi masa tana tuna abun da ya faru wani sabon kuka ta fara "ya ilahi ki yi shiru Please ki
daina kuka nan dan Allah" "Ni ka kaini wajan Mamana bana son zama anan" "Naji zan kai ki
amma sai kin yi shiru" mai makon ma tayi shiru sai ta cigaba da kukanta tashi yayi har ya kai
bakin ƙofa ya ce "Taso muje ai da sauri ta duro akan bed ɗin ta bisa a baya dr suka gani na
ƙoƙarin shigowa murmushi yayi "Sir kace har kun fito" "Eh" ya bashi amsa a taƙaice su na isa
haraba hospital É—in drive ya ta so da sauri "Ka koma Company ni zan kaita gida" "Okay sir" ya
faÉ—a yana buÉ—e masa motar zagayawa yayi ya buÉ—ewa Ayarh ta shiga da gudu ya ja motar
dai-dai wani ɗan ƙaramin stor ya tsaya ya siya mata abun da zata iya ci tare da kayan tea
Dawowa yayi cikin motar yaja suka tafi, suna isa ƙofar gidan da sauri ta buɗe zata fita ruƙe
mata hannu yayi yana girgiza mata kai kwaɓe fuska tayi zatai kuka "Shiit ni bacewa na yi kimin
kuka ba," ya faɗa ya na miƙe mata leda "Idan kin shiga gida ki gaida min da Mama sananan ki
bari sai kinji sauƙi kya dawo aikin kin ji? Allah ya baki lpy kuma kiyi haƙuri nasan nine naja miki"
"Babu komai nagode" ta faÉ—a ta na fita daga motar kwanta da kansa yayi a jikin kujera ya na
murmushi shi kaÉ—ai ya san abun da yake ji akan yarinya ganin har ta daÉ—e da shiga gida ya sa
ya ja motarsa yayi gaba
Kai tsaye gida ya nufa dan baijin zai iya komawa Company a wannan yanayi ya na isa ya nufi
falon ya nasa
Tana shiga Mama ta ta so tana tambayarta lafiya fashewa tayi da kuka tana rungumeta, ruƙeta
tayi suka nufi cikin É—akin suna shiga ta kwanta akan tabarma "Wai Ayrah menene ya faru?" "Kai
nane fa ya ke ciwo" ta faɗa a shagwaɓɓe "Amma ke kam wai yaushe zaki daina kukan ciwon
kai ni Allah na zata ma ko wani abune ya faru tashi toh ki ci abunci kisha magani" "A'a Mama ni
na ƙoshi ta" faɗa tana miƙa mata ledar da Mdee ya bata "Ita kuma wannan ledar menene a
ciki?" "Mdee ne ya siyamin kuma ma ya ce na gaidaki" "Toh Ina amsawa mungode sosai da
É—auwai niyar da ya ke" ita dai Ayrah bata sa ke cewa komai ba ta rufe idanunta
Da da dare suna zaune Ayrah ta dubi Mama "Wai Mama mu Shikenan haka zamu cigaba da
rayuwa mu kaÉ—ai?" shiru Mama tayi bata ce komai tabbas itama a koda yaushe tana wannan
tunani shin idan rayuwa ta ciga da tafiya haka watara na fa zata mutum alokaci sai dai yar'tata
ta yi itama rayuwa ita kaÉ—ai, ganin hawaye na zuba akan fuskarta ya sa ai Ayarh saurin nufo in
da ta ke "Dan Allah Mama kiyi haƙuri idan magana ta bata miki daɗi ba" murmushi kawai tayi
tana rungumeta adaran dai haka suka kwana cikin tunani rayuwarsu
Washegari da wuri ya tashi ya shirya yana fitowa security ya buÉ—e masa motar ya shi, su na isa
ya shiga office, Suhailat da dama zuwansa ta ke jira, ta tashi da sauri ta nufi office É—insa kanta
aƙasa ta shiga da salama amsawa yayi ya ɗago ya na kallonta "Good morning sir" "Morning
how are you" "fine" "Dama sir tambayarka zanyi ya jikin Ayrah" "Jikinta da sauƙi tana gida, sai
bayan ta ƙara samu sauƙi zata dawo aiki" ya faɗa yana danna lapton ɗin dake gabansa "Okay
Allah ya bata lafiya" "Ameen ya rabbi" godiya ta masa tana fita daga office É—in
Tana fita p.a ta tare ta "Am me Mdee ya ce akan yarinya, har yanzu tana asibiti" wani kallo
Suhailat ta mata tana wucewa abunta "Mtss kada Allah ya sa ki faÉ—a yar raini hankali, daga
gani yarinya shikenan kunbi ku liƙe mata Allah shiƙara wallahi ni na so ma ace ta mutu muga
Æ™arshen iskanci" [8/13, 4:06 PM] Masoyiya í ¾í´—í ½í´¥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
A WANI COMPANY
BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
fallow my account
Arewabook@hauwauomar05
Page_12_13
Yau kusan kwanan Ayrah uku agida bata zuwa aiki. Gaba É—aya baya jin daÉ—in aikin ji yake
Kamar akwai wani abu da yayi giɓi cikin aikin na sa. A