Showing 21001 words to 23840 words out of 23840 words

Chapter 8 - A WANI COMPANY PART COMPLETE BY MEERAT OMAR.pdf

05 Jun 2025

749

"Ameen Mamana" ta faɗa ta na sumbatarta a kumatu
tsaye ta ganshi a jikin motar da alama kuma dama ita ya ke jira tuntuni, tunda ta fito ya ke binta
da kallo wani irin kallo ya kemata Wanda bai taɓa ma ta shiba dube-dube ta fara yi a jikinta dan
ganin ko wani abune da sauri ya kawar da kansa ya na shiga cikin motar shiga itama tabyi yaja
su ka tafi su na isa ya fito ya yi ciki ko left yau bai hauba ya nufi stap..

Shiga ya yi cikin office ɗin, dafe kansa ya yi ya na furza da wani wahalala numfashi shi kaɗai ya
san abun da ke damunsa tabbas yau ce rana da ya kamata ya aiwatar da abunda zuciyarsa
keson ya aiwatar ɗin. Da Salama ta shiga cikin office ɗin ɗaga kai ya yi ya kalle ta, nufar gurin
haɗa Coffee ta yi da sauri ya dakatar da ita "Kije kawai bana bukata" ba ta damu ba ta nufi
hanyar fita daga office ɗin ƙasa ta sauka wajan Aunty Suhailat ƙarasawa ta yi fuskarta ɗauke
da murmushi


"Ke Jiddah Jiddah ki tashi fa na ce" turo baki ta yi gaba tana jin haushin tashin da'a kamata wai
Ammi sai ina bacci ki ta tashina" banza Ammi ta mata ta nufi kofa tai fucewarta

a hankali ya ke sakowa daga bene Ammi ce ta tsaya ta na kallonsa murmushi ya yi lokacin da
ya ƙaraso guri "Ammi kallon fa?" "Ai dole na kalle ka son yau na ga abun da ban taɓa gani ba,
kai ne wai yau ka sa ka manya kaya? kuma ba karamin kyau su ka maka ba" dariya ya yi sosai
wadda ta kara masa kyau Ammi dai kice sokike ki ce bana sa wa" "Da toh sawar ka ke ne"
murmushi kawai ya yi "Anya babana ba wajan wa ta zaka ba?" haɗe rai ya yi kamar bai taɓa
dariya ba dan in da abun da ya tsana a rayuwarsa toh bai wuce amasa maganar mata ba shi ya
yi soyayya ma ya ce ya yi me shifa gaskiya har yau baiga wace ta isa ya sota ba, ganin ya haɗe
rai kamar baya dariya ya sa Ammi cewa "Allah dai ya shiryaka Babana wai ni kam kai kullum
idan aka maka zance budurwa sai ka sauya fuska shikenan sai kayi ta zama ba kai aure ba, kai
kasani yanzu ka yi duba da Sa'a nin ka duk sunyi aure wasuma har ya'ya gare su" "Ammi su su
kaga zasu iya wahala" ya faɗa ya na wucewa murmushi kawai Ammi ta yi tai gaba abunta dan
yau ne Abieey zai dawo Nigeria

Momy ce zaune a cikin bedroom ɗinta ta na waya sheƙewa ta yi da wata dariya "Ke dai bari
kawai kawata ai komai na shirya shi yanda ya kamata yoh Allah na tuba taya zanyi sanya da
wannan aiki idan kika ga ban aiwatar ba toh kice ni zainab an buneni ne a rami kinga a lokacin
ai babu abunda zan iya" ta faɗa tana ƙara sakin shu'umin murmushi Yusra da ke tsaye a bakin
ƙofar ɗakin duk taji abun da mahaifiyartata ta faɗa hawaye taji na zuba a fuskarta shin yaushe
ne Momy za ta gane ta dai na irin wannan abubuwan? da sauri ta bar bakin ƙofar gudun karta
fito ta ganta..

Cikin murna Fahad ya fito ya na murmushi ganin abokin na sa dan baitaɓa tunani da gaske
zaizo gidan na saba kama hannusa ya yi su ka shiga cikin parlon zaunar da shi ya yi akan
kujera ya nufi cikin bedroom ɗin ya na kiran Samha fitowa ta yi da fara'a "Badai har babban
baƙon namu yazo ba?" "wallahi kin ga ko ya karaso' murmushi ta yi tana fita a ɗakin drinks ta
ɗako da sincks ta nufi kan centar table ɗin ta ajiye ma sa "Ina yini brother" murmushi ya yi ya na
kallonta "Lafiya qlau Samha ya gida" "Alhamdulillah yau dai Allah yayi munganka a gidan mu"
"Ai kuwa dai" ya faɗa a taƙaice zuba ma sa juice ɗin ta yi ta na miƙe ma sa godiya ya ma ta ya
na karɓa

Suhailat ce ta dubeta "Kinga Ayrah bari naje office ɗin H.o.d na kaimasa wannan file kinji, yanzu
zan dawo" "Toh aunty Suhailat sai kin dawo" fita ta yi ta barta a office ɗin haɗe hannuta biyu ta
yi akan kuncita tun ɗazu babu abinda ta ke tunawa sai Mamata ko wane hali ta ke ciki yanzu


lumshe idanunsa ya yi ya na jin wani irin ya na yi a jikinsa gaba daya jijiyoyin kansa sun tashi,
p.a ce ta turo kofar tashigo sai da ta ambaci sunansa sau uku bai ɗago ya kalleta ba hakan ya
sa ta ajiye file ɗin da ke hannuta ta yi ta fita ta na tunani ko menene ya faru da Mdee zama ta yi
akan kujera da ta kasance mallakinta
Shin kodai taje ta faɗawa Mdee tana son zuwa gida Saboda Mamata bata da lafiya? a'a gasky
bazata iya ba tashi ta yi ta fita dan zuwa cikin lambu da ke Company, tana zuwa ta zauna kan
fararen kujerin da ke gun lumshe idanunta ta yi ta na jin wani irin ya na yi shiba damuwa ba shi
ba farin ciki ba "Ya Allah ka sa Mama ta na cikin ƙoshin lafiya" ta furta hawaye na bin gefan
fuskarta "Ameen" taji an ambata a bayanta da sauri ta buɗe idanunta wanda su ke kawo ruwa
Oga Abdul ta gani tsaye ya haɗe hannusa biyu akan ƙirji murmushi ya sakar Ma ta ya na zama
akan kujera da ke gefanta fine girl ya faɗa ya na murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa
kawar da kanta ta yi da sauri kuma ta miƙe ta nufi hanya fizgota ya yi ta faɗa jikinsa, ƙoƙarin
kwacewa ta ke amma ina gaba ɗaya ya ruke ta cizo ta gartsa masa da sauri ya saketa ya na
dafe gun da gudu ta fita a wajan ta na haki dafe ƙirjinta ta yi ta na ambata sunan Allah

Office ɗin Suhailat ta shiga ganin har lokacin bata dawo ba ya sa ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi
zama tayi akan kujera shin wananan wane kalar bala'i ne

Motoci ne yan uban su guda biyar ke shigowa cikin katafaran gidan da wani irin gudu Jiddah da
ke tsaye a jikin window da gudu ta sako zuwa ƙasa a hankali ya sako ƙafarsa zuwa waje

kyakyawan dattijo farine tass kana ganinsa zaka san cewa shine mahaifin Abrad saboda ya na
yin Kamar su dai dai da kwayar idanunsu iri ɗaya ce rungumesa ta yi ta na murna "Oyoyo
Abieeyna" "Oyoyo Mama" Abieey ya faɗa shima ya na rungumeta Yusra ce ta nufo gurin itama
da buɗe hannusa ya yi ta faɗa jikinsa a hankali ya saki ajiyar zuciya ya na jin wani irin kewa da
kaunar ya'ya na sa Momy ce ta fito ita da Suhaima itama rungumesa ta yi Murmushi Momy ta
sa ki "urwelcome Sir"
Murmushi ya ma ta ya na kallon Ammi da ke fitowa daga part ɗinta wani irin sanyi yaji na
ratsasa lumshe idanunsa ya yi da sauri ta ƙaraso ta faɗa jikinsa, a tare kuma su ka saki ajiyar
zuciya mai ƙarfi haushine ya ya turnike Momy da sauri ta wuce abunta, Bunta Suhaima ta yi ita
ko Yusra taɓe baki tayi alamar ko a jikinta waige-waige Abieey ya fara yi tuntsirewa Jiddah ta yi
da dariya dan ta san mai yake nema juyawa ya yi ya kalleta "Mamana lafiya daiko"? "Abieey na
san fa wa ka ke nema toh sai dai kayi haƙuri dan ya Abrad dai bayanan tun ɗazu ya shirya ya
tafi zance" ta faɗa ta na karayin dariyata mai kyau da sauri kuma ya juya ya kalli Ammi ya na
son jin da gaske ne abunda Jiddah ta faɗa taɓe baki Ammi ta yi "Kadai san yarinya nan da
shirma kawai dai bai san zaka dawo bane yau shiyasa ya fita kuma kaine kace kar'a sanar ma
sa zaka masa bazata" baice komai ba ya kama hannuta su ka nufi ciki bunsu su Jiddah su ka yi
a baya Yusra ce ta ce
"Wai ke yarinya nan yaushe zakiyi hankali ki daina shirma?" turo baki ta yi gaba "Duk randa kika
daina nima zan daina" Mtss Yusra taja tsaki dan gaba ɗaya Jiddah shirmanta ya ma ta yawa
suna isa parlon ya haura sama dan hutawa bunsa Ammi ta yi "Nifa Ammi nasan yanzu kin daina
kulamu saboda Abieey ya dawo ko" murmushi kawai ta yi tai gaba abunta dan ta san halin
yaranan

Suhailat ce ta shiga office ɗin ta zauna "Kin jini shiru ko siste" ɗaga ma ta kai ta yi alamar eh
"Wallahi muntsaya wani aiki ne shiyasa ni kaina duk na gaji, ta so muje muyi sallah" babu musu
ta miƙe tabi bayanta su na isa masjid ɗin su ka ɗaura alwala shiga su ka yi ciki, bayan sun
idar Ayrah ɗa ga hannu tayi sama ta na rokan Allah akan ya bawa mahaifiyata lafiya ganin tana
hawaye ta na addu'a ya suna fitowa Suhailat ta tambayeta lafiya ta ke kuka? rungumeta ta yi ta
cigaba da kukan "Please Ayarh kiyi shiru ki faɗamin karki sani nima cikin damuwa" "Aunty
Suhailat Mamana Mamana" "Menene ya faru da ita" "Bata da lafiya jiya da na je gida ko buɗe
idanunta ba ta yi" "Ya salam shine kuma kikazo aiki yau Ayrah why' "Itace ta ce na zo yau
saboda jikin na ta da sauƙi" "Okay toh kiyi shiru kinji kar mutane su ga kina kuka Insha Allah
Allah zai bata lafiya" goge ma ta hawayen da ke fuskartata ta yi "Smile" ta faɗa duk dan ta sa ta
cikin farin ciki murmushi ta yi _Yawwa Hajiyata ko ke fa kinga yadda ki ka yi kyau? da dariya
nan kamar wa ta Ashwariya �" "Kai Aunty Suhailat ni ina na isa na zama Ashwariya" "Allah
har kin fita Ayrah ki godewa Allah ke ɗin mai kyau ce"

"Kinga zomu shiga ciki" binta ta yi su ka nufi ciki office ɗin




Insha Allah anjima page 20 zai sauka wanda ya kasance page na karshe a free page shin me

kike jira yar uwa har yanzu baki payment ba kin san dacewa yanzu nema wasan zai fara ohh ya
rabbi Allah sarki Ayarh ko zataci jarabawoyin da suke bibiyarta sai dai muce Allah ya bata ikon
cinsu Ayrah baiwar Allah

*Littafi*
*A wani Company*
*₦300 babu tsada idan kinyi shirin biya*
*9165855674 hauwau umar Abdullahi opay*
*Zaki turo evidence ta wannan Number*
*09165855674 *
*Jinjinata agareku masoya na ina matukar ƙaunarku.❤️ Sosai kamar yadda kuke ƙaunata
*MUCH LOVE LOVER'S*


*_~MEEYRAT CE~✍️_*
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya : https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ



*A WANI COMPANY *


*HAUWA'U OMAR*
Cute Meerat.


*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*.


# SQUAD 2024.

Page_20

*Last free page*





Juyi yake cikin haɗɗaɗen office ɗin mai kamada fadar shugaban ƙasa idanunsa a rufe suke dan
mutum na iya zaton cewa bacci yake a hankali ya furzar da nunfashi lokacin da yake buɗe
idanun nasa wowwwww!! Masha Allah Mdee Suhail kenan cikakken matashi mai ji da kansa
tattausan hannunsa ya sanya ya janyo telephone pole ɗin dake gefensa wasu ƴan nambobi ya

danna sannan ya kai kunne cikin wata irin kasalalliyar murya mai nuna buƙatuwa akan wani
abun ya furta "Ayrah!" Abinda ya iya furtawa kenan sannan ya ajiye wayar, P.A ɗin ta fahimci
abinda yake nufi hakan yasa ta mike dan kiran wacce ya ambata ɗin.



Wani irin kallo ta bisu dashi kamar na nuna ƙasƙanci sannan ta taɓe baki kamar ba zatayi
magana ba sai kuma ta ce" keee!... dukkanninsu suka fuskanceta dan basu san da wacce take
a cikinsu ba, haushine ya turniƙeta hakan yasa cikin fushi ta ce"kee ba dake nake magana ba
Ayrah?" kallonta Ayrah tayi da lulu eyes ɗinta bata ce komai ba dan yawan magana ba ɗabi'arta
ba ce "Mdee na kiranki Malama" ta fice daga office ɗin a fusace. Numfasawa Ayrah tayi sannan
ta miƙe jiki babu kwari tayi waje.


Turo ƙofar ta yi a hankali ta shiga gaba ɗaya bata jin wani ƙwari a jikinta ganin idanusa a rufe ya
sa ta karasa ta zauna akan kujera murmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anarsa sai da ya
kai kusan five minute a haka kafin ya buɗe idanunsa da su ka yi wani irin ja tsoro ne ya kama
ganin yanayin idanunsa ya sauya launi, miƙewa ya yi bai ce ma ta komai ba ya nufi bakin ƙofar
ganin yasawa ƙofar luck yasa tsoro ya kamata dan hakan bai taɓa faruwa ba juyowa ya yi ya
na kallonta ya ɗau tsawan lokaci ya na tsaye kafin ya cije laɓansa wani irin abu ya ke ji wanda
bazai iya misaltawa ba shifa yau yaci alwashin cimma burinsa kuma tabbas zai bi zaɓin
zuciyarsa.


"Sir!! Sir!!"

Murmushi ya yi lokacin da yake sake tunkarota har sannan kuma bata fasa kiran sunansa ba
idanunta sun kaɗa sunyi jaa zallar tashin hankali ya wanzu akan fuskarta inna'lil lahi wa ina
ilayhi raji'uun wace irin mummunar ƙaddara ce ke neman tarwatsa rayuwarta me yake shirin
faruwa ne??, Jin da tayi ta gagara yin baya ya tabbatar mata da cewa tazo ƙarshen bangone
yayinda Suhail ke gabanta so close wanda har suna iya jin numfashin juna. Zufar da tagama
wanketa take ƙoƙarin gogewa amma abun ya faskara bakinta sai rawa yake da alama akwai
abinda takeson furtawa amma harshenta yayi mata nauyi hannayen Mdee da taji yana yawo
akan fuskarta shine abinda ya ƙara tayar da hankalinta me Mdee ke ƙoƙarin aikatawa ne?,
Daman ƙaddarar data kawota Companyn kenan?, wane wanda zai ceceta cikin wannan
mummunan lokaci ya Rabb Ayrah ta furta cikin ranta, iskar da yake hura mata ita ce ta dawo da
ita daga duniyar tunanin data shiga ashe da gaske ba mafarki take ba! Da gaske *A WANI
COMPANY* ne haka ta faru?, da gaske ita Ayrah ke cikin wannan mawuyacin halin?, Me zatayi
wanda zata kuɓutar da kanta daga wannan masifar? Tamkar a mafarki haka zuciyarta ta ayyana
mata wani abu wanda lokaci ɗaya ya yi tasiri cikin ranta har ta ɗauki hakan matsayin hanyar da
zata kuɓutar da ita hakan yasa ta kalli gefenta hankali tashe glass cup ɗin da ke kan table ɗin ta
janyo nufar wuyanta ya yi ya na shin-shina lumshe do yayi saboda wani ƙanshi turare da yaji
wani zafin nama taji ya zo mata da sauri ta ɗaga kofi ta sauke ma sa aka da sauri ya ɗago ya

na kallonta da runani idanunsa kafin ya yanke jiki ya faɗi agun dafe ƙirji ta yi tana zare idanu
"Nashiga uku ni Ayrah me na aikata haka" da sauri kuma ta buɗe kofar ta fita da gudu ta wuce
p.a ta sauka zuwa ƙasa ganin ta fito da gudu ya sa p.a ta shiga cikin office ɗin ihu ta saki ta na
kuka "Nashiga uku ta kashe shi fita ta yi zuwa ƙasa ta na ƙwalawa security ku tareta karku bari
ta fita ta kashe Mdee Inna lilahi" abun da ke fita a bakinta kenan lokacin kuma tuni Ayrah ta
daɗe da fita gaba ɗaya daga Company dan gudu karma a ganta ta get ɗin baya tabi...




Wani irin azababben gudu ya keyi dalilin kiran da aka yi masa tuƙin kawai yake amma a zahiri
tunaninsa baya wajen sosai kwakwalwarsa ta shagaltu da tunanunnuka wanda suka yi masa
ƙawanya cikin ransa,kyakkyawar bugawar da zuciyarsa ta yi ya sanya ya ja wani uban burki ji
kake ƙiiiiiiiiiiiiii! a matuƙar tsorace da kuma tsananin tashin hankali yake kallon gabansa
gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak meya aikata ne haka?, something fishy!.


*_Kowacce ƙaddara tanada mafarinta kamar yanda ƙaddarar Ayrah ta kasance ƙarƙashin WANI
COMPANY wanda yake da mabanbantan mutane masu mabanbantan halayya da kuma ɗabi'a


Alhmdllh wannan page shine karshan free page hajiya ta ki zo ayi tafiyar da ke dan ni nasan
bazaki dana sani karanta Novel ɗina ba...


Shin ina Ayrah ta tafi? Mdee na raye ko ya mutu? dama Mdee ya na da wa ta manufa kenan
akan Ayrah?


Idan kinyi shirin biya.
9165855674 hauwau umar Abdullahi opay
Sai ki turomin evidence ta wannan Number
09165855674

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login