Showing 1 words to 3000 words out of 23360 words
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
This is my first novel.
*A true life story*
*Written by fateeyzah *
Bismillahir rahmanir rahim.
Page0⃣1⃣
Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na.
"wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki
tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba "cewar Alhaji kenan.
Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da
maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na
shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa.
Alhaji ne ya fara magana cikin fushi "Amina ki juya ki koma ciki, in ba so kike fushin wannan
mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki".
Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani
kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye.
Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida hawayena da tunanin mafita.
Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan
gidan,don ina tunanin duk da 'Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk
da wannan karan bansan laifin da nayiba.
Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan
saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin
Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds
Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan.
Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da
naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata
tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba.
More comment,more typing.
Yaya zata kaya tsakanin Bahijja da Yaya Baffa.
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story*
*Written by* *fateeyzah**
Bismillahir rahmanir rahim .
Page0⃣2⃣
....Knocking din main door din nayi ,sai da nayi some seconds tukunna aka bude min
kofar,Murmushi tamin tare da cewa "Bahijjah ce,sannu da zuwa,yaushe a Garin" dukka ta min
wannan tambayar a lokaci daya.
Nima na maida mata da martanin murmushi tare da cewa"Nice Aunty Hanna,yau nazo".
"Karaso ciki mana"cewar Aunty Hanna.
Shiga cikin parlour nayi tare da kulle kofar,nan danan ta cika mini gaba da Snack da
Drinks,tukunna ta zauna muka kuma gaisawa tare da tambayarta ina Yara.
Tace "Sun tafi school.
sannan tace "kici Snacks din mana"
Nace "Aunty Hanna bazan iya cin komai ba,don Allah Yaya nanan"?
Ta amsa min da"Yana nan bari inyi masa magana amma don Allah Bahijjah ki daure ki danci
Snack din ko kadan ne".
Na amsa da "to Aunty"
Tashi tayi ta nufi ciki,ni kuma nasa Hannu na dauki Samosa daya na fara ci,ji nayi kamar ina cin
magani.
Sun dau lokaci Basu fito ba,don har na fara gundura da zaman,sai gashi Sun fito dukkansu
fuska ba yabo ba fallasa,nan da nan nasha jinin jikina,na zamo daga one sitter da nake zaune
na gaisheshi,Ya amsa fuska a hade kamar hadari,sannan na koma na zauna,suma suka zauna
a 2sitter dake facing din inda nake zaune. Gyaran murya Yayi tare da tambaya ta"me ke tafe dake"?
Muryata a sanyaye nace "Yaya nazo ne don Allah ka taimake ka rokan min afuwa a gurin Alhaji
Don naje ya koreni,kuma ni bansan mai nayi mai ba wannan lokacin "na kara she tare da
kokarin maida kwallar dake barazanar saukomin.
Ya tambayeni "Bahijjah kikace baki son mai kikayi ma Alhaji ba"?
Na amsa da gyada kana sama.
Yace" alhaji Yace tunda kika koma Sokoto baki taba kiranshi kin gaishe shiba har maganar
auren nan naki da ya taso,baki kira kin sanar dashi ba sai da Yaya Arsala ya kira shi ya fada
mai,kuma Tace yana ji kuna waya da Ammy,amma shi kin maida shi Makiyinki,yanxu watan ki
nawa da komawar ki Sokoto amma ko so daya baki taba kiranshi ba,yanxu tsakaninki da Allah Bahijjah kin
kyauta?,yanda fa Ammy keda hakki a kanki haka Alhaji shima yana da hakki a kanki".
Kaina a duke nace"Yaya nasan nayi laifi amma wallahi Yaya ko na kirashi baya dauka,so uku
ina kiranshi bai daukaba,shi yasa ni kuma ban kuma kiransa
ba,saboda na dauka bai bukatar gaisuwar tawa".
Kara gyaran murya yayi tare da cewa"look Bahijja ni kwata kwata ban ganin laifinku,na Ammy
nake gani,amma zan sami Alhaji muyi magana,yanxu dai mai ya kawo ki garinnan,ina zaton yau
saura 3weeks bikinki?"ya karashe da tambayata.
Nace"Kaduna zan wuce,in gyara kayan bed dina"
Yace"to da kike maganar gyaran kayan bed
kina da kudi ne?"
"eh,angon ya ban 10k saboda in gyaran kayan"
Anan Aunty Hanna ta saka baki tare da cewa«Honey,ni a ganina da Bahijja tabar maganar
gyaran gadonnan kawai ka canza mata sababbin gado,tunda wancan auren nata shekara
10,kaga sun tsufa da yawa"
Yace"A,ah Sweety kibarta taje ta gyara kayanta,tunda tazo da niyyar gyarawa"sannan ya juyo
gareni tare da cewa"Bahijja kije ki gyara kayanki,zan sami sauran 'yan uwa muyi maganar
gudunmawar da za a hada miki ".ya karashe tare da mikewa yana kallon Aunty Hanna sannan
yace Sweety ni na dita,in zata tafi ki duba drawerta ki bata 2k tayi transport" Bai jira cewarmu ba yasa kai ya fita,sai da mukaji fitar motor dinshi sannan Aunty Hanna ta juyo
tare da cewa"Bahijjah kiyi hakuri da rayuwa wata rana sai labari".
Fateeyzah
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story*
*Written by fateeyzah*
Bismillahir rahmanir rahim
Page0⃣3⃣
Nace "to Aunty nagode,kuma muna nan muna kai kukanmu wurin Allah,Allah ya kawo mana
dauki a wannan rayuwar ta gidanmu,wallahi Aunty Hanna ban damuwa da kaina akan yanda
nake damuwa da mutum biyu wato Ammyna da Aunty Zubaida,kina gani yanxu Aunty Zubaida
abin nata kamar hauka amma duk da haka Alhaji yaki dena fushi da ita,kuma yace idan Baban
Fadila ya maida ita gidanshi,wai bashi ba Baban Fadila".
"aini Bahijja ban ganin laifin Alhaji sai na Ummeey da yaranta Mata,wallahi wadannan ba Allah
a ransu,shi yasa nake fadin ma Honey ya bar yadda da kananan maganganunsu amma
yaki,kiri_kiri sun tsare ko inna acikin gidan suna gidan aurensu amma kunnansu na gidan
Alhaji,duk su suke hada fitina,shiyasa ranar da muka yi da Mamy na wanke ta tsab wai naje
gidan Alhaji ta fara min hayagaga wai in fita daga gidan tunda ba gidan Ubana bane,ni kuwa
nace mata ai tasan nawa gidan Uban yafi nasu,don baza ma a hada gidanmu da nasu ba,wai fa
duk abinda ya kawo fitinar sunce wai Alhaji ya karbi dukiyarshi a wurin Honey saboda wai da
kudin yake Almubazaranci wai yana kashemun".
Nace"ai mu Aunty 'Yan dakinmu duk abinda yake faruwa a gidannan bama sani,kina ganin
Asma'u da take kusa da gidan ma Alhaji ya hana ta zuwa wai sai bayan 3month saboda wai
'yan dakinmu muke hada fitina a gidan,tsakani da Allah ga Mamy nan da kullin tana gidan da ita
da Mijinta da 'Yarta amma su ba a hanasu zuwaba sai mu". Aunty tayi gyaran murya tare da fadin"kedai Bahijja mubar maganar nan Allah ya shiryesu,don
ni ina fada ma Honey abun kunya ne a wurinsu ace kamar gidan Alhaji Nagoggo,ana Samun
wannan matsalar.yanxu wai a ina za ayi bikin tunda Alhaji yace badai gidanshi ba kuma kinga
Dokoto tayi nisa". Nace"Mun yanke shawara zamuyi biki ne a Kano gidan Aunty Aisha tunda kin ga nan zan
zauna".
"Ok,yanxu abunda za ayi in kinje Kaduna kin dawo ki biyo tanan ki karbi bedsheets a matsayin
gudunmawa ta don
nasan ba bari za a yi inje bikin ba".
"shi kenan Aunty na gode,Allah ya kara budi".
Tace "amin,ina zuwa".
Tashi tayi ta Shiga daki,sai da tayi like 3minute tukunna ta fito ta mika min kudi tare da cewa
"Ga 12k nan,2k kudin da Honey yace in baki na transport,10k kuma ki kara a kudin gyaran bed".
Take naji kuka ya tawo min na mike tsaye tare da rungumeta ina kuka tare da mata godiya.
Itama kukan ne yazo mata tare da cewa"Allah ya tona asirin wanda ya raba Bahijja da
Alhaji,yanxu Bahijja akan 12k kike kuka,sai kace wadda aka bata millions".
Nace"Aunty ba komai ya sani kuka ba,sai alamarin Ubangiji dana tuna,wai yau nice na ke
murna akan 12k,abunda lokacin da nake auren Tasi'u nafi karfinsa,sai dai ni in
bada,lallai na yadda duniya juyi juyi wanda ya dauketa da fadi yana tattare da wahala,Allah dai
yasa mu dace".
Tace Amin Bahijjah.
Mikewa nayi tare da saba jakata Nace Aunty ni xan wuce dai na dawo a gaishemin dasu
Baby,ta amsa da za su ji,Rakiya ta yimini har main door tukunna muka kuma sallama ta juya,ni
kuma na fice gidan,Achaba na hau wanda zaikaini Agoro Motor Park don in shiga Motar
Kaduna.
Wacece bahijja?
Pls manage
fateeyzah
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story*
*Written by*
*fateeyzah*
Bismillahir rahmanir rahim
Page0⃣4⃣
Tafiyar one hour ta kaini garin Kaduna,inda Driver ya saukemu a Kawo,nan na samu
Napep din da zata kaini gidan Kakata dake Unguwar dan Bushira,tafiyar 30minutes mukayi,inda
Mai Bapep ya saukeni a kofar Gidan,na biyashi kudinshi na karasa cikin gida.
Babban gida ne,wanda kallo daya zakamai kasan masu gidan suna fama da rashi,gidan cike
yake da 'Yan uwan Ammyna daga Yayyinta zuwa Kannita kuma kowanne da Iyalanshi,akalla
Mutanen gidan zasu kai dari(100),bayan gaishe gaishe tare da taya ni muryar auren da
zanyi,direct dakin Kakata na wuce wacce muke kiranta da Granny,shiga nayi ina mata wasa irin
ta Kaka da Jika,bayan mun gaisa,nayi wanka hade da salla sannan na zauna cin Abincin da
aka kawo min daga dakin Matar Kawu Muhammadu.
Hira muka dasa ni da Granny wadda yawancinta hiran gidanmu ne da halin da Ammyna take
ciki,anan na bata labarin abinda ya faru dana je gida da gidan Yaya Baffa da naje.
Aikuwa nan ta bude baki tayi ta surfa balla'i,saboda Granny irin mutanen nan ne da basu daukar
wargi,sai da ya koma ni nake bata hakuri sannan tayi shiru saboda zaka dauka dani take fadan.
Can kuma kamar an tsikare ta tace"ni wallahi badon Amina ta wuce zaman gida ba da sai na
raba Aurensu da NAGOGGO,tunda kwata kwata naga alamar wannan Matar tashi mai hanci
kamar bututu(lolirin hancin Sophie ta)ta gama Mallake shi,in banda kaddarar Allah da
rabon Haihuwarki data Kanninki da munsani sanda ya taba sakinta bamu bari ta koma ba (kaji
Granny da tonon asiri,irin haka har yanda aka nemi auren Mahaifiyarka sai an fadin
maka)amma kana naka ne Allah na nashi gashinan har tsufa abu yaki daidaita".
Nace"don Allah Granny kibar maimaita maganar nan,wallahi in hadda ce ya isa na haddace
wannan karatun dakike fadamun tun zaman da nayi a gidan nan".na karashe maganar tare da
tashi na shige bedroom dinta,inajinta Taci gaba da sababi.
Gado mai runfa na samu na haye tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,'Ya'yana ne suka fado
min arai ko yanxu ya suke,oho,don nadau Alkawarin bazan kuma zuwa ganinsu ba tunda last
zuwan danayi sai da Tasi'u ya bini da sharri(anya ko Bahijja zaki iya yanke alakarki da ta
Yaranki). Nan danan naji kwakwalwata ta fara tariyo min abubuwan da suka wuce har .....
Manage
Insha Allah next page zamu ji wacece Bahijja?
*Fateeyzah*
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story* .
*Written by fateeyzah*
Bismillahir rahmanir rahim.
Page0⃣5⃣
*FLASH BACK*
Mahaifina da ne ga Alhaji Akilu kudan,wato sarkin kudan na wancen lokacin,mahaifiyarsa
Hajiya Atika wacce suke kira da Goggo ita ce mata ta farko a wurin mai martaba sarkin kudan.
Hajiya Atika 'ya'yanta biyu a gidan wato mahaifyana Alh Ahmad NAGOGGO da yayarsa Hajiya
Hajara wadda nake wurinta a sokoto, a lokacin Mahaifina na da shekara daya Allah ya
kaddara rabuwarsu wanda har yau da basu a duniya babu wanda yasan dalilin rabuwar
aurensu,sannan Alhaji Akilu ya auri matansa biyu wato Dayyiba(Umma,wacce ita kadai ce take
da dai a yanxu), da Amaryarsa Zulai(Mama) wanda suka haifammai 'ya'ya kusan sha shidda,
ba lallai bane in iya lissafo su tunda ba wani zumunci mukeyi dasu ba duk da sun kasance 'yan
uba suke da Babana,duba da irin yadda zumunci ya kasance a yanxu.
Bayan rabuwar kakata Hajiya Atika da Kakana,sai ta dauki Babana wanda suke cema
NAGOGGO (sunan NAGOGGO ya samo asaline da yanda a unguwarsu masu suna Ahmad
suna da yawa, shine ake kiransa da Ahmad din Goggo wanda daga baya suka maida sunan
Nagoggo,Wanda har sunansa Ahmad ya bace Mutane suka koma kiransa Nagoggo),ta
daukeshi ta dawo garin zaria dashi wurin iyayenta tabar Hajiya Hajara a kudan.
Tabama ma Babana tarbiya dai dai gwargwado saboda Hajiya Atika irin mutanan nanne masu
fadin gaskiya,wanda komin girmanka sai ta fadin maka,Mace ce mai tsauri wanda ko cikin
Dangi kowa yana shakkarta,Babana nada shekara biyar a duniya tayi aure anan zaria ta tafi da
Babana gidan Mijinta, kasancewa shi baya haihuwa sai ya zamana ya rike Babana kamar
danshi.anan zaria yayi primary school daga nan bai ci gaba ba,duba da yadda mutanen da suka
dauki karatun boko,daganan ya fara bin kanin Mai Martaba legos,wanda wannan ne
musabbabin arzikinsa.
Matar Mahaifina ta farko ita ce Hajiya Maryam,wadda ya auro daga k
Kano,daka ganta kaga bafulatana, fara ce tas,ita keda manyan yara a gidan,yaranta sha
daya,mata hudu maza shidda,Amina,Hauwa,Akilu(Baffa),Faruq,Atika
(Mamy),Ibrahim,Aminu,Jafar,Auwal,Salma,Ahmad(Abba).Hajiya Maryam Mace ce mai son
kanta,kwata kwata batason wani ya rabesu,bayan ita Alhaji ya auri kusan Mata biyar amma
basu dadewa suke fita saboda ta kasan kasa take azabtar dasu,wadanda suka dade a gidan
sune wadanda suka haifi 'ya'ya
biyu2,Amina wacce ta haifi yara biyu, Fatima da Zubaida,sai Huwaila da ta haifi Halima da
Bello.
Mahaifiyata itace Matar Babana ta shida a jerin Matan da ya aura,ita a Bazawara ya
Aureta,tanada yara biyu a gidan da ta bari,Zainab da Mustapha, Haifaffiyar garin zaria ce,don
daga baya su Granny suka koma cikin garin kaduna.
Mu biyar ne yaranta a wurin Babana,Asma'u itace Babba,wanda bayan haihuwar Asma'u sai da
suka rabu da Babana,ta koma gidan b'Babansu Aunty Zainab,chan ma auren yaki tunkunna ta
dawo gidan Babana,bayan dawowarta ne ta haifeni(ni Bahijja,Aliyu,Abdullahi,Taheer.
Mahaifiya Allah yayota mai hakuri don yanda ake takurata a gidan Babana abun ba a
magana,duk wani cigabanta Alhaji ya dakusheshi,tun muna kanana bama fahimta har muka
girma muka fahimci Mahaifiyar mu itace bora agidan mukuma 'Ya'yan bora.
Pls ur comment is needed.
Fateeyzah
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story*
*Written by fateeyzah*
Wannan page din nakine *MUM IRFAAN*Allah ya baki abunda kike nema DUNIYA da
LAHIRA,Amin.
Bismillahir rahmanir rahim
Page0⃣6⃣
Duk wani hakki namu an take shi a gidannan,don ko Almajirin gidan an fi daukarshi da
daraja fiye damu,a hakan ma ana raga mana ne saboda hajiya kaka(Hajiya Atika ),saboda tana
kokarin nuna ma Alhaji abunda yake yi bai daceba,kasancewa bayan rasuwar mijinta Alhaji ya
gina mata gida nan kusa da gidanmu ta dawo,ya saka mata 'yan haya duk da akwai
jikoki('ya'yan 'yarta hajiyan sokoto).
Su kuwa sauran yaran da iyayensu basu gidan,suma Alhaji ya rarrabasu,Aunty fatima da Bello
ya bama Hajiya kaka,Aunty khadija kuma ya bama Hajiyan sokoto sai Halima da take wurin
mamarta.
Bayan ammy ta haifi aliyu ne ta samu teaching a wata private school,amma daga baya sai da
Alhaji yasan hanyar da yabi ya hana ta teaching din,abunda ya faru shine, ummy ta kawo
kararta wurin Alhaji akan wai tana barin mata yara da yunwa,hakan ya kawo musu rashin
jituwa,har sai da hajiya kaka ta sasantasu tace kowa ta ringa girkinta daban,daga baya kuma
yace wai sai dai ta zaba ko teaching ko aurenta,saboda kullin tana fita ana kalle mai mata,haka
ammy ta hakura tabar teaching ya koma sai dai abinda ya kawo ya bata,don ko sana'a a cikin
gida ya hanata.
A wannan lokacin kuma an aurar da mata uku a gidan mu duk daga dakin ummy,wato Amina(ta
auri babban dan Hajiyan sokoto), Hauwah da mamy, dukkansu duk sun hayayyafa.
A lokacin da nake da shekara sha biyu yayi dai dai da ina j.s.s one a kayi bikin yaya Baffa da
Aunty hanna wacce ta kasance diyar aminin Alhaji,a lokacin ne kuma komai na gidan mu ya
kara tabarbarewa dalilin Alhaji ya dauki dukiyarsa gaba daya ya damka ma yaya Baffa don yaci
gaba da juyawa,a dai dai lokacin kuma Tasi'u ya shigo rayuwar gidanmu,wanda dalilinsa na
tsinci kaina a wanna rayuwar da nake ciki.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Fateeyzah*
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*A true life story*
*Written by fateeyzah*
Bismillahir rahmanir rahim
Page0⃣7⃣&0⃣8⃣