Showing 6001 words to 9000 words out of 22578 words

Chapter 3 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf

Allah yaya kayi hakuri, wallahi
bansan zaka fito ba, Dan Allah Yaya kada ka mareni, wallahi bani bace nazo Allah yaya Amma
ce tace na kawo Maka abin ci ,Kuma Nima sai da nayi tunanin bazan zoba sai tace AI Kai
miji..... "Shuruuuuuuuu......... Nace, shasha Sha uban waye mijin naki ni.... Ya sake hade rai
yace "wallahi idan bakiyi wasa ba saina kakkaryaki a gidannan ni sa,Anki ne? Waya baki IZININ
zuwa part Dina, ban ce miki ko ido karki sake bari muhada ba, wato ke uwar taurin Kai hadda
shigomin daki Are you monkey?" Kukan da salwa take ne yasake fitowa fili sabi da tsabar Jin
zafin magan ganun da yake fada mata, wai yau itace ake ciwa mutunci haka, Kuma wai yayanta
wan da yake mutuwar nuna mata soyayya ada shine ayanzu ya dauki tsanar duniya ya Dora
mata, Wayyo ni salwa maraici bai ba nasan da ace abbana yana Nan Babu mai kawoni Nan har
aci mutuncina, tsawa yasake daka mata ganin yadda tayi masa shiru batace komai ba ,wato ta
ma maida shi mahaukaci, "keeeh..... " Da sauri salwa TA dago suka hada ido, wani irin
yarrrrrrrr.. taji jikinta ya soma bari kamar ganga, gaba ki Daya TA 'kame guri Daya lokacin da
tayi to zali da kwayar idonsa, sumar zaune tayi ta tsaya cak a haka, ai Kuwa batai aune ba taji
wani saukar gigitaccen Mari a kuncinta ji kake tasssss tasssss, Allah sarki baiwar Allah gigice
war da tayi ne yasa takasa Gane inane gabas inane yamma, gaba daya idanunta duhu take
gani sabi da tsantsar azaba batasan lokacin da ta cakumo rigarsa ba ta rungume shi, tare da
kan kameshi sosai a jikinta, numfashin ta nawani irin fita, zuciyarta kuwa sai bugu take kamar
ganga.

Saurin janyo ta yayi daga jikinsa hadi da cewa" ya Salam... Shi Kansa ta tsoratashi ganin
yadda ta gigice kamar wadda taga wani bakin aljani, shiru ya danyi Yana kallon yadda take

motsi cikin furgici a kirjinsa, sai lokacin ya tuna cewa fa shi sojane Kuma shi Kansa yasan ko
namiji ya mara ba karamin Jin jiki zai ba, balle Kuma salwa da tun da yake asanin sa 'yar
gatace gaba da baya Babu wan da yataba marinta, cike da tausayin ta ya sa hannu tare da
tallafo bayanta Yana shafa fuskarta dai dai gurin da ya mareta, A hankula yake Kai bakinsa
saman kuncinta Yana Dan hurawa gurin iska ko zataji sassaucin marin, itakuwa salwa ajiyar
zuciya ta shiga saukewa hawaye masu zafi nabin kuncinta, shi Kansa suhail din jiyayi kamar
yasaka kuka, ganin irin zalicin da yayiwa kanwar tasa, lokaci guda ya shiga tunano irin soyayyar
da abban salwa ya nuna masa, gaba kidaya sai yaji jikinsa duk ya mutu.

Lokaci guda ya tsinci kansa da son bata hakuri Amma girman Kai da takama ya hana shi, sai
aikin bin ta da kallo.


Cikin mintina kalilan bacci ya dauke salwa sabi da tsabar wahala, har baccin dole tayi,
shikuwa big bro a hankula ya saka hannun sa gaba daya ya dagata cak kamar wata 'yar baby
yayi bedroom da ita, bai ajiye ta a ko inaba sai kan katafaren gadonsa na alfarma, sai dai so
yake ya janyeta daga jikinsa Amma yakasa sabi da ta kanka mesa gaba daya, shikuma
bayason ya tasheta balle tasake masa wani kukan, Dan haka ya hakura ya kwanta Shima a kan
bed din tare da yin rubda ciki, salwa Kuwa har yanzu hannunta na makale a jikinsa.



60:30 pm __________________
Shiru_Shiru salwa bata dawo ba ,Dan haka Ihsan ta mike ta nufi gurin Amma a zaune ta
sameta, ta idar da sallar magriba, Tana addu,a ,sai da ta bari ta idar tukunna tace "Amma ina
salwa taje tun dazu da kikace na kirata har yanzu bata dawo ba" mamaki ne ya kama Amma Jin
wannan magana daga bakin Ihsan,cikin rashin fahimtar mai take nufi Amma tace "ban Gane ba
? Zan kwdanta ta na cinye ne, ina tun dazu ta dawo " "tadawo Kuma Amma daga ina kenan?"
"A,ah dazu na aiketa wajen suhail tun rana takai masa abinci ,Kuma Tana zuwa ko minti 5 batai
ba na bata abincin ta Kai masa, Kuma kice haryanzu bata koma ba to ina taje kanan?" "A,ah
wallahi Amma bata dawo ba ,Amma bari na je gurin ya Abdul ko Tana can" shiru Amma tayi
tana tunani can Kuma bayan futar Ihsan itama ta mike, part din big bro ta nufa kartaje 'yar
mutane ta bata, Tana zuwa taga kofar a bude, da kwanukan abincin ta soma tozali Inda ya bare
a haka suka tafi suka barshi, falon ta cigaba da bi da kallo, har zata juya saikuma, ta mike tanufi
bedroom.

Durum tayi ta tsaya tana kollon ikon Allah hadi da mamaki da Kuma damuwa kwance akan
fuskar ta, a hankula ta furta "lallaima yaronan" kwafa tayi kawai ta fita.


Tana fita suka cikaro da ihsan abakin kofa zata shigo, kallonta Ihsan tayi tace "Amma ina
Ihsan din kinganta? Naje ban sameta a gurin ya Abdul ba" "Kar ki damu ina son yanzu kije ki
fadawa kowa na gidannan akwai taro anjima a part din goggo" "toh... Amma mai ya faru haka,

ina salwa?" "Ba tambayata nace kiyi ba ina son yanzu kije kiyi abin da na saka ki" Babu musu
Ihsan ta fita zuciyarta cike fal da tunani.


Itama Amma sama ta haye tare da mikewa wata kofa wadda ni kaina ban San waye a cikin ba
Kuma bansan mai zatayi ba, tana zuwa ta tura kofar tare da yin sallama, daga ciki aka amsa da
"wa alaikumussalam" cikin muryar dattako, karasawa tayi Inda yake ,Yana zaune a bakin gado
kekkewan dattijon mai kyau ga ilimi da kuma haiba, zama tayi tare da sakar masa murmushi
tace " barka da dare *ABU SUHAIL* " murmushi ya mai da mata tare da cewa "Barka dai
*AMMAN SUHAIL* ya naganki kamar kina cikin farinciki kodai wani abune yafaru ?" "Uhm abu
suhail ba dole nayi farinciki ba ranka ya dade ai kaima wanna albishir ne mai gwabi yalla bai"
dariya Abba yayi yace "toh ina jinki ranki yadade Maza fadamin" "magana ce akan auren salwa
da suhail da muke ganin kamar bazasu kaunaci junan su su zauna a tare ba, ada munso mu
raba auren tun da munga tsakanin Abdul da salwa sunfi shakuwa, sai a maida auren kan Abdul
, to Kuma yanzu na aiketa ta kaimasa abinci sai naji shiru,nabi bayanta,anan ne na samesu a
kwance manne da juna cikin so da kwauna suna bacci" zaro ido Abba yayi yace "wai Dan Allah
dagaske kike ?" "Dagaske nake ranka shi dade" murmushi Abba yayi ya mike tare da
durkusawa kasa yayi sijjada, a hankula ya furta "Alhamdulillah, yanzu Maza a hadamin zama a
gidannan domin musanar da ranar tarewar su" "ai na aiki Ihsan lokacin da na hawo sama zuwa
bayan Isha,I kowa zai hadu a sashen goggo".


Tom acan bangaren suhail da salwa Kuwa, bacci yayi nisa sun dage sai Jan munshari suke ,
abin ka da ba a sababa sun wani makale junansu kamar wasu masoyan Gaske.



Misalin karfe' 8:00 na dare ,ilahirin familyn LAMI'DO na zaune a sashen goggo, kowanne
acikin su yayi shiru Yana tunanin Maine dalilin da yasa aka hada taron, musamman mazan
gidan su Umar da bilal zaman sauban Khalid huzaifa duk sunyi tsit kowanne kirjinsa na
bugu,Abdul ne ya shigo tare da goggo suma gefe suka samu suka zauna suna jiran shigowar
su Abba.


A can bangaren su suhail kuwa,salwa ce ta mike a furgice ganin yadda ta ganta a kan gadon
big bro Babban abin mamaki da fargabar ma yadda ta ganta a jikinsa a rungume, baki ta kwabe
tare da fashewa da kuka, da hanzari Shima suhail ya mike tare da kafe ta da ido cikin masifa
yace "keeh lafiya?" "Uhm uhm yaya Maine hakan zaka tabani, wayasa ka kawoni dakin ka,
Daman Kai Dan iskane?" Ta fada a shagwaba,shi Kuwa suhail tsabar takaici ma yarasa mai
zaiyiwa yarinyar ya huta da bakuncikin ta, wata uwar harara ya watsa mata yace " to uban mai
zanyi dake, mai zan taba a jikin naki, ki bari kizama mace tukunna sai kiyi ikirarin na tabaki ....
Bai gama maganar ba yaji wayarsa na ruri, da sauri ya Kai hannu ya dakko ta ,abin da yaganine
ya daga masa hankali miss call kusan 30 Kuma Amma, da sauri ya daga kiran ,kafin yace wani

abun yaji muryar Amma tace "idan ka gama bacci ka fito musu da 'yar mutane muna jiranku a
sashen goggo" daga haka ta katse wayar, kirji ya dafa hadi da cewa "innalillahi wa inna
ilaihirraju un kardai Amma TA shigo dakinnan, to Amma mai zamuje Yi a part din goggo?" Tama
salwa zaro ido ta shigayi Jin yadda ya tada hankalinsa Yana salati.

Babu shiri suhail ya mike ya shiga bathroom tare da wanke miyar da ta bata shi, ya sauya
kaya, itama salwa da sauri ta mike kafin ya fito ta fita a guje, bata tsaya a ko ina ba sai a
sashen su.

Suhail Yana fitowa bai ganta ba ,Daman yasan za ayi haka, baice komai ba ya fice, daga part
din ya nufi da shen goggo.


Acan bangaren salwa Kuwa bayan ta shiga dakinsu, Ihsan ce ta kalleta tace "Kee wai ina
kikaje ne aketa nemanki?" "Uhm ke dai bari zan baki labari idan mun dawo daga yaron can"
tabe baki Ihsan tayi tace "uhm salwa kenan muje too" dai dai lokacin da salwa TA saka riga
Sannan ta dakko dogon hijabi ta zura suka fita.


Falon goggo ya cika da mutanen gidan yanzu Babu wadan da ake jira sai Ihsan da salwa ,
gefe guda Kuma Big bro ne zaune a kusa da Amma sai watsa masa harara take, gaba kidaya
suhail yariga da yasha jinin jikinsa, sallamar salwa da ihsan sukaji hakanne yasa kowanne a
cikinsu ya dawo da kallonsa gasu, musamman Abdul da bilal da Umar duk sun bita da ido, ita
Kuma tafiya takeyi duk tabi ta tsargu jikinta a sanyaye take tafiya, karasawa tayi kusa da su
Abba ta durkusa tace " Abba ina wuni?" Amsawa sukayi gaba dayansu cike da murmushi
kowanne a kan fuskarsa sukace "lafiya klau ummiterh , juyawa tayi suma su huzaifa ta gyshesu,
suma amsawa sukayi cikin fara,a hadi da kara yabawa da tarbiyya irinta salwa, sukuwa su
zubai da tsaki suka ja, Ameera tace "sai kace wata mutuniyar arziki ado Le ita sai ance tafi
kowa" Sarai salwa tajira Amma batace mata komai ba.


Abbane yayi gyran murya yace" Kun San kowacce kaddara tana iya sauyawa mai kyau ko
mara kyau ,sanan komai da kuka gani ubangiji Yana iya sauya shi, Kuma ance bayan wuya
akwai dadi". Tom babban dai abin da yasa muka Tara wanan zama shine Abdul salwa da Kuma
suhail, dumm gaban suhail ya fadi haka itama salwa da Abdul kowanne sai zare ido yake Yana
Sosa Kai, abbane ya ciga ba da cewa..

"Ada munyi wani tunani game da Abdul ,yadda mukaga tsakaninsa da salwa akwai so da
kauna, sabanin suhail da yake nuna ko,in kula akanta, mun yanke shawarar Zamu mai da auren
salwa kan Abdul " "what' Abba auren salwa Abdul zaiyi?' to nawa auren da yake kanta fa?" Big
bro ya fada a razane batare da sanin maganar ta fito daga bakin saba.

💋 *SALWA* 💋


*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 4


"Ban ban Gane ba wai mai kuke shirin Yi akan haka wannan abu sam bai kamata ba, Indai har
suhail zai saki salwa to Babu Wanda yafi dacewa da auren ta irin bilal" cewar yaya babba, zaro
ido Umar yayi yace Momy bilal Kuma wallahi Indai bilal ne zai auri salwa sai dai in kowa yarasa
ai gwara a barwa ya zaman " haushi da bakinciki ne ya cunkushewa suhail zuciya bai San
sanda yayi wata iriyar kara ba yace "ya Isa haka, wannan ai hauka kuke, sai ku bari idan na
saketa kwayi fadan akan ta Amma Banda yanzu Abba ka fada musu zan batawa yaro Rai anan
gurin" baki Abba ya saki ganin yadda suhail ya gigice lokaci guda yanayinsa ya sauya kamar zai
daki mutane, Daman abin da Abba yakeson sani kenan Kuma ya Gane cewa maganar da
Amma TA fadamasa gaskiya ne yanzu suhail Yana son salwa..

Zubaida da sauran matan gidan Kuwa bakinciki ne ya ishesu jin yadda suke ta fada akan mace
Daya , afili tace "ban da an raina mana hankali muma ai matane sai kuzauna kuna ta fada akan
wannan yarinyar wadda Babu abin da ta sani sai kauyanci ,ai kin banza anyi asa....

Bata karasa abin da zata ceba taji wani saukar wawan Mari a kuncinta hagu da dama ji kuke
tasss tasss , Abdul ne da Khalid suka tsinketa da mari a lokaci Daya, wani uban ihu ta kurma a
razane ta kwasa a guje ta dawo sai da tayi zagaye uku Tana tsalle Tana kuka Sannan ta kwanta
a kasa tana ihu "wayyo Allah Momy sun kasheni , shikkenan fuskata tacire wayyo Momy kina
ina" da sauri Momy ta taso ta zauna a gabanta Tana cewa "sai na ci abu ta kaza na ubanku
Abdul akan wannan 'yar kauyen yarinyar Zaku illatamin tawa,uban mai tayi muku,ai gaskiya ta
fada sabi da tsantsar asara Kun nacewa yarinya guda Daya kamar Rai ,wallahi bazan lamunci
wannan iskancin ba duk Dan iskan da yasake dakarmin 'ya sainayi shari,a dashi shashashai
kawai" itakuwa zubaida Kare makale Momy tayi tana cewa "Momy dubamin sun ciremin fuska
ko , shikkenan nasan Babu mai aurena" "Yi hakuri zubaida tashi Babu wan da ya cire miki fuska
Tana jikinki kawai zafin marine , ai WALLAHI ko fuskar suka cire miki sai daya acikin su ya
aureki marasa tarbiya kawai" ta karasa maganar hade da watsa musu harara.

Uncle Kabir ne yace "to ya Isa haka kuzo ku samu guri kuzauna muyi abin da ya taramu, bana
son sha shanci" "tab Allah ya sauwake nakara zama anan huce Nan, so kake idan muka kara
zama Yan zu Kuma su kashemin ita Dan wallahi ba a Isa ayi abin magana muki magana ba
ATO" "kehh memuna ni kike fadawa haka ni?...ni Kabir kike fadawa haka, to wallahi kika sake
kika bar gurinnan abakin aurenki "

"Innalillahi wa inna ilaihirraju un Kabiru yanzu a gaban nawa kuke wannan abin ,wai yaushe
zakuyi hankali ku hade kanku,wannan wane irin tashin hankali ne Kun hana yarinya sakat
kamar ba jinin kuba, kinga memuna kina rabamin zuri,a saikin bar gidannan" goggo ta fada hadi
da watsawa Momy harara,
Uncle faruq ne yace " aini duk abin baikai na fada ba, tun farko Abdul da Khalid Baku kyau taba
bai kamata ku Mari zubaida b fada ya kamata kuyi mata Amma ba mariba ,ni banason haka
kudaina,yaya ci gaba da magana"

Abbane ya sake kallonsu yace " uhm a gaskiya abin da ya faru yanzu a gurinnan banji dadi
ba, kafin ku fara magana kamata yayi ku tsaya na dasa aya zai fi , Amma Baku tsaya na sanar
muku dalilin da yasa Za a mai da auren salwa kan Abdul ba kawai Kun soma surutai, bakuji mai
nace ba ada munyi tunanin za a maida auren salwa kan Abdul yanzu Kuma Babu wannan
maganar an fasa, tun da dai mun fahimci suhail Yana sonta Kuma itama Tana sonshi" wani
bakincikine yazo zuciyar suhail ya tsaya Jin yadda Abba yace wai Yana son wannan
yarinyar,take yaji haushi yace "Abba yanzu mai ka yanke akai domin zabinka shine nawa ,ina
son in koma daki kaina yanamin ciwo"

"Okay abin da na yanke game da auren ka shine, tun da yanzu mun fahimci kuna tsananin
bukatar junanku, daganan gurin zaka huce da matarka part dinka domin tarewa" kansane yaji
Yana wani irin juyawa bakinsa nason cewa wani abu sai dai Amma ta katseshi da cewa "karka
ce komai da idona na ganku kuna bacci ,ko ba kubane?" Zaro ido suhail yayi arazane, hadi da
sun kuyar da Kansa kasa, domin Babu yadda ya iya yariga da ya kulle Kansa Kuma Babu mai
fitar dashi sai Allah.


Mamey Kuwa salati tayi tana tafa hannu Tana cewa "innalillahi wa inna ilaihirraju un oh yau
anyi walkiya ta haska, kana ganinta sumi sumi kamar batasan komai ba Ashe 'yar bari kice, ba
a banza ba mazan gidannan suka manne miki ,mebi kin taba basu sun Dan Dana ko, wato
sukuma sunji dadi munafukan banza munafukan hofi, Daman andade ana cewa Abdul Yana
ruke miki hannu Yana rungumarki Ashe dagaske ne haka kike,yau gashi har bacci kike da
suhail a boye, duk da mijinki ne ai ky bari akaiki Shima shahararren Dan iska, sumi sumi dashi
Ashe Shima ... " "Keeeh Jamila dakata, bance ki fassaramin 'ya',yaba danace bacci suke wani
abun nace miki sunayi ,idan ma wani abun sukayi ai mijin tane" Amma tafada Rai a bace.


Abdul ne ya mike zumbur jijiyoyin Kansa har fitowa sukayi tsabar zafi da zuciyarsa take masa,
wani irin jiri yaji Yana shirin kwashesa da sauri ya dafa bangon dakin, numfashin sa ne ya soma
fita da sauri dasauri ,lokaci guda ya soma ganin biji_biji take ya yanke jiki ya fadi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login