Showing 18001 words to 21000 words out of 22578 words

Chapter 7 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf

salwa ,ita Kuwa salwa cewa tayi "Amma lokaci yariga da ya kuremin narasa
Yaya har abda ,komai zanyi bazan dawo da yaya cikin rayuwata ba, su Abba sunruga da sun
yanke hukunci Kuma kinsan Abba kaifi dayane ,Kuma Nima Koda ace ayanzu za a mai da
aurena da yaya suhail bazan yarda ba komai son da nake masa yazama dole na hakura tun da
mutumin da ya furta ya tsaneka yafi a irga Babu amfanin sake zama dashi domin nasan bazai
taba sonaba har abada', zanyi hakuri na karbi zabin da Allah yasake bani akaro nabiyu ,Indai
Abdul alkairine agareni ni na amince da zabin abbanmu " salwa ta karasa maganar hawaye na
kokarin fitowa daga idonta , shiru Amma tayi tana nazarin maganar salwa, can kuma sai ta
janyota jikinta ta rungumeta tana rarrashin ta,har Saida tayi shiru, sanan ta mike tashiga
bathroom.



💋 *SALWA* 💋

*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 11






Mikewa Amma tayi tsam tashiga kitchen domin ta hadawa salwa abin da zataci, kawai kawai ta
soya mata da kunun gyda , bayan ta Kammala ne tafito, a zaune tasamu salwa kan dadduma ta
idar da salla, karasowa tayi kusa da ita ta zauna sannan ta ajiye mata abincin, murmushi salwa
TA sakar mata tace "sannu da kokari Amma nasaki aiki, aini yakamata na girkamiki" "uhm salwa
kenan to idan ni ban kula dake na ciyar dake abin da zaici ba wazai kula dake, kenan ma baki
daukeni kamar ummanki ba " "uhm uhm Allah Amma ba haka bane kawai dai ... "Kawai dai me?
Yanzu dai kici abincin sai ki tashi kisamemu a babban falo.....





Tom bayan salwa tagama cin duk abin da Amma takawo mata, mikewa tayi hadi da bude loka
,doguwar riga ta dakko baka tasaka, sanan ta yafa mayafinta, Allah sarki kallo Daya zakayi wa
salwa kasan ta fada, sabi da damuwa fuskar Nan tasake zama 'yar kuyat , tafiya ta somayi a
hankula tabar part din Amma,babban falon ta nufa, bakin ta dauke da sallama tashiga anan
tasamu ,Amma Abba uncle faruq uncle Kabir duk a zaune ita kadai suke jira, amsa sallamar
sukayi fuskarsu dauke da murmushi, itama karasawa tayi TA zauna sannan ta dubesu ta
gyshesu amsa sukayi Sannan Abba ya kamo hannunta yace "mamana dawo Nan " komawa
kusa da Abba tayi ta zauna zuciyarta nayimata buga alamar fargaba, uncle faruq ne ya shafa
kanta yace "ummiterh Allah ya yimiki albarka" "Ameen kawai tace tasake maida kanta kasa,
abbane ya sake cewa "mamana kin Yi shiru kin sun kuyar dakai kasa alamun har yanzu akwai
damuwa atattare dake ?" Murmushin karfin hali salwa TA kakaro ta kalli Abba tace "ah am uhm
Abba Babu komai kawai ina tuna abbanane" "murmushi uncle Kabir yayi yace "to ummiterh mai
akayi miki har kike tuno abbanki bayan mu muna raye Kuma kinsan Zamu iya yimiki duk abin da
zaiyi miki,karkiji tsoron komai ki fadi duk abin da kikeso zamuyi mikishi Indai bai saba daga
addinin muba" "hakane uncle ,kawai ina kewar abbanane, sabi da alokacin da yake raye yayana
Yana Sona sai da ya bar duniya Kuma yaya ya tsaneni bayan Babu shi aduniyar, mai yasa Dan
Adam yake a hakane, maiyasa zai karyamin zuciya ? Kwallar dake makale a idonta tasamu
damar sulalowa zuwa kuncinta ,jikinta narawa ta kankame Abba, Shima Abba rungumeta yayi
Yana bubbuga bayanta Yana cewa "kiyi hakuri mamana meyasa har yanzu kika kasa mantawa
da suhail bayan shi ya manta dake, look mamana bai kamata ace muna yawan tuna mutanen

da mukasan zamansu acikin zukatanmu ba alkairi bane, ki kalli Abdul Maine laifinsa tabbas
nasan shi bazai watsa min kasa a ido ba ,Dan Allah mamana ki hakura da suhail ki karbi zabin
da nayi miki" "uhm uhm Abban bawai zabin ne bai min ba wallahi Abba yaya suhail Yana Sona
har yanzu ina ganin soyayata acikin idanunsa ,Dan Allah Abba idan har zancire Rai da soyayyar
yaya suhail to ku daukeni daga gidannan, nafison natafi can wata kasar nayi rayuwa ni Daya,
ina son na manta da yaya abba Dan Allah kuyi min wanan alfarmar in yaso idan nadawo
nasamu nutsuwa sai ayi auren da yaya Abdul"


Shiru Abba yayi ya dan nisa kadan sannan ya kalli salwa yace "shikkenan mama na zaki iya
tashi ki tafi inshallah zamu zauna da sauran iyayen ki muga me zamu yanke akai, kallon Abba
salwa ta danyi kamar tana nazirin wani abu daga bisani Kuma tace"shikkenan Abba"jiki a
sanyaye ta mike taso ma tafiya har ta fita gada fallon.

Bayan fitar salwa su abbane suka bi Bayan ta da kallo cike da tsananin tausayin ta Amma ce
tace"u uhm gaskiya ya kama ta a duba lamarin yarinyar Nan me ze hana a bata Wanda take so
tun da na fahinci cewar suhail mafa yana sonta ,kawai yarintace ke damunsa , idan akayi haka
sainake ganin kamar ba a masu ADALCI ba" "shiiiii ya Isa haka banason maganar banza Indai
MAGANACE Akan suhail banason ta yanzu abu guda nake bukata shine ki kawo shawara akan
yadda zamuyi yamanta da babun suhail acikin rayuwarta" "haba Abba maiyasa zakace haka
wanna hukuncin da aka yiwa suhail yayi tsauri kobabu soyayya inaganin AI akwai zumunci " "ya
ci uwarsa zumuncin,shi ba zumuncin ya take ba" zaro ido uncle faruq yayi cike da mamaki Wai
yau abbane da zagi gaskiya ransa ya baci, zancen uncle faruq ya katse da cewa "ni ina
tunanin kawai akai yarinyar Nan makarantar kwana in yaso sai a hadata da soja yana gadinta
daga cikin sojojin suhail " jijjiga Kai Abba yayi alamar gamsuwa da maganar uncle faruq ,sanan
yace " yanzu kuna ganin wace makaranta yaka mata mukaita ?" " No ai Bamu yakamata mu
yanke wacce za a kaita ba Yakamata muji ra,ayita tazabi Inda takeso mukaita sai tafi samun
kwanciyar hankali "cewar uncle Kabir.


Kallon Amma Abba yayi yace " Tom ina gajin ke yakamata ki tambayeta mebi tafi fada miki
tun da ke macace batajin kunyarki kamar mu Maza" "toh Amma tace Sannan ta mike ta bar
wajan.


Abangaren big bro kuwa akwati Daya ya dauka yazuba iya kayan dayasa zaiyi amfani dasu
idan yaje u,s , mikewa yayi cikin riga dawando farar riga wando Blue mai kyau da sheki, sosai
ya masa kyau ya amshi jikinsa, akwatin sa yaja yafita, Kai tsaye part din Amma ya nufa ,dakinta
ya nufa domin yasan Babu kowa sai ita, da sallama abakin sa ya karasa sanan ya nemi izinin
shiga" salwa Kuwa na zaune a gaban Amma jitake kamar ta tashi tabar gurin da bantason
sukara hada ido, wata zuciyar Kuma tace " a,ah ummiterh ki zauna kada kitashi amma tayi
tunanin wani abu, daukar shawarar zuciyar tata tayi TA zauna hadi da sun kuyar da kanta kasa.

💋 *SALWA* 💋



*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 12


Shigowa suhail yayi tare da durkusawa a gaban Amma ya gaisheta sanan yace "to Amma ni
zan koma" cike darashin fahimta Amma tace "ka koma ina ?" "U.s zan tafi yau dinnan " "u.s
Kuma suhail maiyasa ai lokacin da ka dauka bai Kare ba" "eh Amma sonake na tafi akwai wasu
Abubuwan dana keson karasawa acan " "okay Babu damuwa Allah ya kiyaye hanya ya tsare ka
daga sharrin makiya mahassada kakula kaji" "ameen thumma ameen Amma zamurinka waya
idan nakoma " har da zai tashi ya fita Kuma sai yaga salwa tayi shiru ko gaysuwa Babu , sai da
ya tattaro duk wani kuzarinsa sanan yace "uhm ummiterh kintashi lafiya ?" Shiru salwa tayi
kwallar da take makalewa tashiga gangarowa daga idonta , daker ta iya tattaro kuzarin Daya
rage mata tace "in ina... Ina wuni yaya" "lafiya kalau kawai yace ya mike yace "to Amma ni zan
huce" daga haka ya juya baya ya soma tafiya, da sauri salwa TA dago jajayen idanuwan ta tace
" Amma ki tsayar dashi Dan Allah kada ya tafi ya barni ,uhm uhm yayana Amma kice ya tsaya
Dan Allah, salwa TA mike tare da fadawa kan gado ta fashe da kuka, shikuwa suhail tuni ya
sauka daga mattakalar dakin ,sai da yayi nisa Sannan ya juyo idonsa ya kada yayi jajur kamar
garwashi.


Yana fita daga part a hanya ya hadu da ihsan ta dawo daga school, cike da mamaki ta karaso
kusa dashi ganin yadda ya dakko jaka Yana tafiya, da sauri tace "yaya lafiya ina Kuma zakaje
naganka da akwati" uhm yayi kwafa tare da sakin murmushin karfin hali sabi da karta Gane
yanayin da yake ciki yace "lafiya kalau Ihsan kawai dai zan koma u.s ne " "mai yaya u s Kuma
to mazaka komayi acan ?" "Mai zankoma Yi acan Kuma bayan acan nake aiki ,kinsan aurena
da ummiterh ne ya dawo Dani TARABA ,to Kuma Daman hutun da na dauka yakusa karewa
shiyasa zan koma can kawai " "to ..... Th.. to kenan yaya idan katafi yaushe zaka dawo ?" Tayi
tambayar kamar zatayi kuka, "uhm Babu rana Ihsan" daga haka bai sake cemata uffan ba ya
shige part din goggo, ita Kuwa Ihsan bin bayansa tayi da kallo fuskarnan tata dauke da mamaki
.




Yana shiga falon ya tarar da su Abba zaune suna tattaunawa , karasawa yayi ya gaishesu

suka amsa, Sannan yace "Abba ni zan koma" "okay tom Allah ya tsare " abin da Abba yace
masa kenan saka makon haushin sa da yakeji akan sakin salwa da yayi, Shikuwa suhail baiyi
mamaki ba Dan Abba bai tambayesa dalilin komawar sa ba,ya mike tsaye zai shiga dakin
goggo, uncle faruq yace "lafiya son zaka koma ?" "Uhm Babu komai uncle Kiran ujilane ya
sameni shiyasa " "oh Tom shikkenan Allah ya tsare ya kaika lafiya son" ameen kawai big bro
yace ya huce dakin goggo, a zaune ya sameta tana cin abinci Abdul nayi mata barkwanci domin
shi Abdul ya warke tun da yasamu abar kaunarsa salwa, shiga yayi ya gaisheta Sannan ta
amsa, Abdul ne ya kallesa yace "yaya ina wuni?' " lafiya klau Abdul ya jikin naka?" Yayi
maganar Yana tsaresa da manyan idanunsa masu kama Dana mage, "da sauki yaya AI
nasamu lafiya Amma yaya yanaganka kamar tafiya zakayi?" "Eh zan huce u s ne shine nazo
nayi muku sallama" saurin zaro ido Abdul yayi yace "u.. u.s fa yaya" eh u s zan tafi ai Daman
acan nake dazama bai kamata kayi mamaki Dan zan koma ba" "toh ... Shikkenan yaya Allah ya
dawo dakai lafiya Amma dai zakazo bikina ko?" "Bikinka Kuma, dakai dawa yaushe?" "A,ah
yaya bikina da my salwa mana Nan da shekara uku" tsaki suhail yaja kawai ya mike yace
"goggo ni na huce " bai jira abin da zatace ba kawai ya fita, zuciyarsa nayi masa wani irin tukuki
da zafi.



Azafafe ya fice kamar wani zaki' sukuwa su Abba bin bayansa sukayi da kallo har ya fice,
uncle Kabir Kuwa cike da tausayinsa yake kallon bayansa, hakama uncle faruq don su sunsan
mai suka hango masa Nan gaba.

Yana fita yasaka akwatin a mota, Sannan ya shiga gidan baya aka jashi zuwa airport, sai da
sukayi tafiya mai nisa Sannan suka Isa, airport din ,,tun daga bakin gate sojoji ne burjik suncika
airport din sunyiwa wajen da,ira ,a yadda na kalli yawan su Kai kayi tunanin wani mai fada aji ko
wani babban mutumin suke jira, sai kawai naga sunzo sun lullube motar da suhail yake ciki, tun
kafin ya fito dukkan su kayi layi hadi da kamewa guri guda, Yana sako kafarsa waje dukkansu
suka Sara masa , batare da big bro yace komai ba ya huce gaba, shika bishi a baya, jirgin ya
shiga ya zauna sa,annan suma suka shiga wani jirgin bawan da suhail yake ciki ba, wan da
yake ciki shi kadaine a zaune yayi shiru yarasa abin da yake masa dadi, komai yanzu ya sauya
masa kamar ba shine suhail ba, haka dai Tana ta tunani har jirgin su yadaga zuwa u,s.



A can bangaren salwa Kuwa kuka takeyi akan gadon kamar zata shide ,hankalin Amma duk
ya tashi , tayi rarrashin Tayi rarrashin Amma ina duk abanza kamar kara kunno salwa take,
kuka take Tana cewa "yanzu shikkenan yaya yatashi ,kwarin gywar danake dashi akansa duk ta
kau,yanzu kenan ta tabbata yaya baya Sona mai nayi masa Ashe Daman zai iya tafi ya bar
marainiyar kanwarsa, Amma ki fadamin meyasa yaya ya nunamin soyayyar karya lokacin ina
karama ayanzu Kuma Babu wadda ya tsana sama Dani, laifinanne Dan na sonshi, ko laifinanne
Dan kaddara tasa na aureshi ,Amma narasa yadda zanyi da zuciyata wallahi da ace ina da
damar sarrafa zuciyata akan son da nake yiwa yaya suhail da tuni na cire domin na fahimci

bana da gurbi acikin rayuwarsa, Abdul ke Sona Abdul masoyina nagaskiya , Dan haka dagayau
zan bi umarnin abba na dau damarar yin karatu kodan yadda yaya suhail yake guduna kawai
sabi da a kauye aka haifeni ni ba Wayayyiya bace, Indai wayewa ce kada su damu hatta matan
gidanan sai na basu mamaki sai na nuna musu ni ba sa,ar su bace,

Abdul ne kadai ke Sona agidannan ,Kuma shi yake mini soyayyar gaskiya ,yasoni tun ina 'yar
kauyeta sanan yasoni a yanzu Dana soma sanin waceceni ,zanje karatun na dawo Kuma na
auri Abdul bazanyi butulci akan hakaba Amma "

Shiru Amma tayi tana sauraronta can Kuma ya dago tace "tabbas gaskiyar salwa ya kamata
ace kicire soyayyar wani da namiji a zuciyarka, ki fuskanci alkibula ki gyra komai na rayuwarki
,ina son kibawa kowa mamaki a cikin gidanan ,ki daure ki koma karatu kinji" "in sha allah Amma
zanyi karatu wacce makarantar kuka zubarmin?" "A,ah zabinki akeso a wace kasa kikeson kiyi
karatu ?" Shiru salwa tayi can Kuma sai ta ce " Amma ina son a kaini Dubai " okay shikkenan ai
ta kwana gidan sauki ma tun da can kika zaba, akwai wani abokin abban ku acan ,zamuyi
magana dashi idan Babu damuwa sai ki zauna a gidansa in yaso sai a hadaki da soja ko biyune
suna kula dake ko" murmushi salwa tayi tace "nagode sosai Amma Allah ya kara miki lafiya da
nisan kwana, bantaba ganin wadda take fifita soyayyar 'yar Dan uwan mijinta ba akan soyayyar
'yayanta ,Amma ke din ta musammance a gareni " "tooo yaukuma tanan kika bullo ,bana son
irin wannan kema 'yatace kamar yadda su Ihsan suke a matsayin 'yayana ,yanzu ki share
hawayenki tun da dai Naga kinzama jaruma ,sai kije kiyi wanka ko Kyji dadin jikinki ,ni Kuma
bari naje gurin abbanku na sanar masa ga Inda kikeso a kaiki" daga haka Amma ta mike ta fita.


Tana fita dakin Abba ta huce ,kwance ta sameshi ya lumshe ido Yana tunani ,sallah matayi
sanan ta karasa gefan gadon ta zauna, a hankula ya bude idonsa yace "hajjau" "Naam ranka ya
dade suhail yazo yimuku sallama?" Kai kawai ya daga baice komai ba, Amma ce tasake cewa
"yanzu Abba kana ganin wanna tafiyar dayayi asan ransa yayi ta?" "Koh ! Tun da kikaga yatafi
AI asan ransa ya koma" "a,ah fa Kai baka fuskanci wani abu daga gareshi ba?" "Mena fuskanta
kawai dai na fahimci yazabi komawa ne akan mun takura saiya zauna da mamana" "a,ah Abba
ba haka bane kayi wa abin mummunan kallo, ni ayadda na fahimta son da yakewa ummiterh ne
yasa ya bar gidannan sabi da idan yaganta Yana tunawa dacewa ka mallakawa Abdul abin da
yafi so a rayuwarsa" hannu Abba ya daga mata Sannan yace" ya Isa haka ,idan har akan
wanna maganar ne ya kawoni Zaki iya tafiya" Abba ya hade rai yayi kicin_kicin, " uhm AI abin
bai Kai hakaba daman maganace akan ummiterh game da makarantar da kace tazaba wane
gari yakeso" "okay ina jinki tazabi makarantar ne?" "Eh tace tanason a kaita Dubai idan da
dama, sai a nema mata wajan kwana, ni Kuma sai Naga AI kana da aboki acan shine nace mai
zai hana ta zauna a gidansa har Allah yasa ta Kammala karatun ta" Kai kawai Abba yadaga
alamun gamsuwa da maganar Amma sai da yayi shiru na dan wasu lokuta Sannan yace "okay
babu damuwa insha Allah zuwa gobe zan kirashi namasa magana ,kice mata ta shirya Nan da
sati daya Zamu tafi" amsawa tayi da to sanan ta mike tayi masa sallama ta fita.

💋 *SALWA* 💋



*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 13



Zarace tashigo dakin da gudu har tuntube take gurin bude kofar , a razane zubaida ta mike
hadi da cewa "ke lafiya?" Duk gaba dayansu suka bi Zara da ido, "lafiya ba lafiya ba, yaufa big
bro ya koma u.s " "what? Zubaida da mufida suka mike zumbur, ban fahimta ba wai kina nufin
yanzu yaya baya gidan Nan ,to mai yasa zai tafi AI naga hutun da ya dauka bai Kare ba?"
Dariya zarah ta kwashe Dashi tace "mai zai sa yatafi Kuwa ban da wanan abin da ya faru, ai
nafada muku wallahi Yaya Yana son salwa kawai dai Yana nuna bayayi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login