Showing 9001 words to 12000 words out of 22578 words
Chapter 4 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf
gurin, da
sauri su Abba sukayi Kansa suna salati, goggo Kuwa kuka tasaka wai za a kashe mata jika, ita
kadai sai surfa uwar masifa take..
Uncle faruq ne yayi saurin dagoshi suka hada ido ,yasa hannu ya bubbuga bayansa tare da
buda idon sa yace "Abdul kana lafiya ? Mai yasame ka ?" Wasu zafafan hawayene masu dumi
ke zubowa daga cikin idon sa, yama kasa cewa komai sai kallonsu kawai da yake da ido.
A gigice salwa ta karaso gabansa ta durkusa ,tayi zaman sallah hawaye na bin kuncinta,Tana
girgizawa Abdul Kai, "ya Abdul Dan Allah katashi kada ka mutu wallahi Yaya ba laifina bane
laifin kaddarar muce ,bansan komai ba, Allah shi yabarwa Kansa sani, ubangijinmu baya bacci
nasan ayanzu haka Yana ganin halin da muke ciki Dan Allah katashi" "uhm Abdul yayi
murmushin takaici yace "meyasa haka Mai yasa salwa? Mai nayi muke Daman kinason yaya
suhail,meyasa Zaki cutar da zuciyata a lokacin da aka daura aurenku da yaya, nadamu daga
baya Kuma sai na sawa zuciyata dangana, Dana fahimci yaya bakya gabansa hakanne ya Bani
kwarin gywa akanki, shine yanzu zakije soyayya tajaki har ku kwanta da yaya, yanzu gaki
gashinan ancika miki burinki soyayyar bangare Daya bazata taba yuwuwa ba,dole sai da
bangare biyu kanwata" hannu yasa ya goge hawaye ,"yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi ni
dakaina nayarda yaya suhail baya Sona sabi da shi ba tsarana bane kada kamin mummunan
zato wallahi ba laifina bane ka tsaya na Maka bayani" banza Abdul yayi mata hadi da mikewa
daga jikin uncle faruq ya taka zuwa dakin goggo,gaba daya mutanen gurin binshi sukayi da
kallo,i takuwa mufida cewa tayi" oh jibeshi Dan Allah wai akan mace a kan mace zai kashe
Kansa, mudai Allah ya kawo mana sauki da ran gwami.
A fusace suhail ya bar gurin ransa namasa zafi yanajin mamey na kiransa yayi mata banza, shi
Kuwa Abba karasawa yayi ya tsuguna tare da dago salwa ya goge mata hawaye yace "kiyi
hakuri ummiterh Maza kibi mijinki Allah ya yimiki albarka" Babu musu jiki a sanyaye ta soma
tafiya har ta fita daga falon jikinta Babu kwari.
Suma mutanen gurin duk watsewa sukayi kowa ya koma part dinsu, Ihsan ce kurum ta shiga
dakin goggo Dan taga halin da Dan uwanta yake ciki.
Tana shiga ta sameshi a kwance idanunsa a lumshe, ya tada Kai da kafar goggo, gefan
gadon ta samu ta zauna, hadi da kamo hannun sa ,murya a sanyaye tace
" Ya Abdul!"
A hankula Abdul ya bude idonsa ya saukesu a kan kanwar sa Ihsan , murmushin karfin hali ya
sakar mata Sannan yace
"Naam Ihsan"
"Ya Abdul kayi hakuri Dan Allah kada ka sawa kanka damuwa wallahi na kasa samun nutsuwa
tun lokacin da Naga ka fadi, Dan Allah Yaya ka kwantar da hankalinka, tun da kaga haka tafaru
to ka kaddara salwa ba matarka bace, yaya da wannan tunanin da kake gwara ka tashi ka
dauro alwala kayi sallah ka roki ubangijin da ya dasa Maka soyayyar salwa a zuciyar ka akan ya
kawo mana mafita " Ihsan ta karasa maganar tana dan rausayar da Kai.
Kafin Abdul ya bude baki yayi mata magana, sukaji an turo kofa, wace, Ameera ce idanunta
sun cicciko da hawaye ,bakin ta har rawa yake wajan karasowa tace"ya Abdul! Dan Allah kada
ka kashe min kanka wallahi ni ina sonka Kuma inason rayuwarka , please kada kayiwa
rayuwata illa idan katafi kabarni bansan Inda zan saka rayuwa ta ba, ina sonka ka yaya" adda
Ameera ta sake fashewa dakuka idanunta na zubda hawaye.
Shi Abdul mai makon ma yaji ta bashi tausayi sai Kuma wani sabon haushinta dayaji ya ziyar
Cesa ,wata uwar tsawa ya daka mata yace "shiruu ..... Ni nace miki mutuwa zanyi da zakizo
kina karamin ciwan Kai, meyasa baki da hankali ne Ameera ,kinzo kin sani agaba kina kuka
kamar Wanda mamey ta mutu, nace bana son ki bana kaunarki kifita' daga rayuwata kinkiji" ya
karasa maganar yana huci kamar wani zaki.
"Yaya Allah ina sonka Dan Allah kadaina cewa baka Sona bana jin dadi, rayuwata takace yaya
kadaure ka bani zuciyar ka, wanan shine kadai samun masalaha a gidannan domin mamey
tace Indai baka aureni ba ya huzaifa bazai taba auren Ihsan ba"
Uhm Abdul yayi wani murmushi mai ciwo sanan yace "idan huzaifa bai auri Ihsan ba zata
mutune? Ko mazan duniya sun Kare ne ,Indai sabida 'yar uwata Tana son yayanki za ayimin
sarka da haka, to kucire Rai da aurena domin zuciyata ta mutum dayace Kuma na mallakamata
ita, fitar min daga daki tun kafin na miki Dan banzan duka a gidannan"
Ihsan dake gefe Kuwa Tana Jin abin da Ameera take cewa ,kuka tasaki ta ja kafafuwanta da
ker tabar dakin, bata tsaya a ko ina ba sai a dakin su,bakin gado ta je ta zauna, tare da kallon
ko ina na dakin, duk sai taji Babu dadi ,sabi da Babu salwa ,Daman salwa ce mai rarrashin TA
to itama yanzu abar rarrashi ce, Kuma an rabata da ita, yun kurawa tayi ta kwanta ,hadi da
lumshe idonta tace "lamarin gidannan sai a hankula yanzu ita mamey abin da tace kenan kawai
sabi da Abdul bai so Ameera ba, shine Nima zata rabani da farinciki na, bayan ni ba soyayyar
bangare Daya nake ba, Yana Sona ina sonshi,haka dai Ihsan ta cigaba da tunane tunane har
bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.
°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Tun da salwa TA karasa sashen Big bro taji dakin a rufe' hatta falon nasa gaba daya ya kullesu,
cikin bakinciki da takaici ta samu daidai mattatakalar dake lanbun gidan TA zauna, tagumi ta
rafka Tama rasa mai yake mata dadi, cikin bakinciki da zafin abin da suhail yayi mata yasa ta
fashe dakuka tana cewa "yaya why ? Mai yasa baka Sona kasakeni mana wan da yake Sona
ya aureni " Tana kuka tana surutai ga sauro Yana TA faman cizonta,
Tanan gurin a zaune aka fara wata iska mai karfi da walkiya, lokaci guda hancinta ya toshe ta
Soma alamun mura, yayyafi aka somayi can Kuma ruwa mai karfin gaske ya soma sakkowa
kamar da bakin kwrya,har ta mike zata tashi sai Kuma TA koma TA zauna ruwan ya cigaba da
dukantanta Tana kuka tana ranar sanyi ,domin ita atunannin ta wannan shine mafita ga
rayuwarta gwara ta mutu ta huta inyaso tabi abbanta da ummanta.
*SALWA*
*©HAFSAT UMAR DANGORO*
Chapter 5
Shi Kuwa gogan naku yanacan kan bed a lullube sai dai ya kasa bacci shi kadai yake ta
faman juyi a kan bed din, musamman yadda yaji an soma zuwa sai yayi tunanin ai ya rufe' kofa
to ina salwa TA shiga, mike wa yayi da sauri kirjinsa na dukan Tara_tara har ya fito daga part
din, a gigice ya shiga duba ko ina na part din amma bai ganta ba, runtse ido yayi ya bude hadi
da cewa "ya salam wai maiyasa nake hakane?" Furzar da iska yayi tare da juyawa a fusace zai
bar gurin, juyawar da zaiyi ya hangota zaune a lanbun gidan a kwance sai karkarwa take Tana
wani irin nishi kamar ranta zai fita, zaro ido suhail yayi hadi da cewa
"Innalillahi wa inna ilaihirraju un" ya fada tare da kwasowa a guje ,Yana gudu Shima ruwa na
dukan sa har ya karaso in da take, da sauri ya durkusa a kasa tare da tallafo kanta yace "tashi
ummiterh ki tashi ,meyasa Zaki zauna ruwa ya dakeki babee? Kuka salwa ta saki hadi da sake
rungumo shi tace "yaya ! Yaya sanyi ,sanyi nakeji , cak ya sake tallafota hadi da dannata
kirjinsa kamar zai SATA acikin kirjin nasa, kuka tacigaba dayi Tana cewa "yaya Shin Dan Allah
dagaske Daman baka Sona, kake azaftar Dani haka" shiru yayi mata batare da yace komai ba,
ya dagota gaba daya zuwa kirjinsa tayadda Yana iya jiyo sautin fitar numfashin ta itama tanajin
nasa.
Tafiya ya somayi har ya Isa falon sa, Kai tsaye akan kujerar ya ajiyeta, Ganin yadda take rawar
sanyine yasa ya kama hijabin dake jikinta ya cire, a take yaji wani abu ya fizgeshi Jin ganin
yadda rigar ta manne a jikinta, sakamakon ruwan da ya daketa, runtse ido yayi tare da budesu
a kan kekkewar fuskarta yayi ,sai da yakai kusan minti 5 Yana kallonta Yakasa dauke idonsa a
kanta can Kuma sai ya mike , bedroom ya shiga ya dakko rigarsa fara jallabiya ya Mika mata,
Kar ba tayi, ta tsaya tana kallonsa ko zai tashi ,ina bai masan Tana yiba, wata uwar harara ta
watsa masa Sannan tace" Yaya ka tashi zan canza rigar" banza yayi mata baice komai ba
Kuma bai tashi ba, saima kara gyra zama da yayi ,ya cigaba da Danna waya,
Sun kuyar da kanta tayi tare da rabawa ta gefansa ta huce bathroom ,shikuwa gogon namu
bin bayanta yayi da kallo hadi da yin kwafa yace "saina gyra maki zama wato na tashi ko, bazan
tashi din ba sai dai karki cire uban mai zan gani a jikin naki" ya karasa maganar hadi da yin
tsaki.
Salwa tana shiga bathroom ta rasa mai zatayi sabi da takaici, sai kawai ta shiga cikin
kwamin wankan ta fashe da kuka, tare da takurewa guri Daya, sai da salwa tayi mai isarta
Sannan tayi wanka ,ta zura jallabiyar ,sai gata tayi zulun_zulum aciki Inda kasan a nannadeta
haka tayi mata yawa, diban kayan da ta cire tayi ta ratayesu Sannan ta kara tsayawa a cikin
bathroom din ta kurawa kofa ido Tana ta tunani,ko tunanin mai take oho
Shiru_shiru suhail Yana falo Yana jiran fitowarta Amma sai yaji shiru, Nan take yashiga zagaye
falon Yana tunanin ko dai yarinyar Nan ta mutune, kasa jure hakan yayi ya koma bedroom ya
dakko zanin gado karami mai Dan kauri, ya fito, bathroom run din ya nufa, can Kuma sai ya
tsaya a bakin ban dakin Yana tunanin, kamar ya shiga kamar Kar ya shiga ,Kar yaje yagano
abin da yafi karfinsa,wata zuciyar Kuma tace "to saime idan kashiga ai matarkace tasunna, ya
halatta kaga komai, kafada big bro ya dage hadi da tabe baki ya tura kofar, a razane salwa TA
dago suka hada ido ,cike da mamaki yake kallonta, itama kallon nasa take cikin takaici, can
Kuma sai ta fashe da kuka mai karfi ,har da kwanciya a bathroom din Tana kuka, haushi da
takaicine ya tsaya a zuciyar suhail,bai San Lokacin da ya daka mata tsawa yace "yimin shiruu....
Uban mai nayi miki kalla yadda kika batamin riga daga baki ki saka shine har kika kwanta acikin
bathroom haka, baki da hankali to wallahi sai kin wanke min, tashi Maza" ya daka mata tsawa,
ai da sauri salwa ta mike Tana zazzare ido har da 'yar kwalliyar ta a ido , baki ta tabe tace
"tsakani da Allah Yaya baka kyauta min ba yanzu da ace bakaya a jikina fa, shine zaka wani
shigo Kai tsaye" "wai ke wane ya koyamiki wannan 'yar iskar shagwabar duk anbi an bata ki,
kafin a aura miki ni ba a ce miki kinzama mallakina ba, to ma wai ,mai zan gani a jikinnan naki
kamar kaza aba kamar na hureta" ya karasa maganar hadi da janyo tawul ya ajiye a gefe
Sannan ya kamo salwa, suka tsaya face da juna, hannun sa ya Kai kan wuyan ta ya shiga balle
maballin rigar Sannan ya saka hannu ya daga rigar cak ya cireta, wata uwar kara salwa ta daka
hada fadawa kirjinsa tayi mutuwar tsaye, abin da bata sani ba tun tuni suhail ya runtse idonsa
Dan Shima bayason wani abun yashiga tsakanin su, Amma sai Kai fadawa jikinsa da tai ta
rungume shi yayi sanadiyyar dauke war numfashinsa na Dan lokaci ,can Kuma ya Yi kokarin
saita Kansa, da sauri ya dauki tawuldin ya lulluba mata, ya fice, sake zama salwa TA karayi a
gurin zaman dirshan tace "na shiga uku Daman yaya 'dan iskane?" Runtse ido ta sakeyi
Sannan ta saki wata ajiyar zuciya ta mike, ta daki jallabiyar ta SATA a ruwa ta wanke, Sannan ta
sakeyin wanka ta daura wani tawul din ta fice.
Lokacin da ta fita bata sameshi a faloba hakan yasa tayi tunanin Yana bedroom ya kwanta,
Dan haka itama ta nemi guri a falon ta kwanta sanyin AC na sake dukanta ahaka bacci ya
dauketa badan tanajin dadin yin baccin ba.
Shiru_shuru suhail ya na kwance Amma baiga salwa tashigo ba, abin ya bashi mamaki ,da
yayi tunanin ko ya kwanta yayi baccin sa, Amma sai ya kasa sabi da tunanin halin da take ciki,
tsaki yayi ya duro daga kan bed din ,ya kunna kawai ,daga shi sai gajeran wando, fitowa yayi
falon ya na nemanta hatta bathroom sai da ya duba bai ganta ba, abin ba karamin bashi
mamaki yayi ba, a hankula ya furta "to ina yarinyar Nan ta shiga?" Juyawar da zaiyi ya hangota
kwance a kan 3 star sai baccin ta take Tana sauke ajiyar zuciya, tsayawa yayi cak a gurin ya
tsuramata ido Yana kallonta zuciyarsa a chunkushe, tsaki yayi ya karasa kusa da ita ya zauna,
yayi tagumi Yana tunani, "Anya Anya kuwa gaskiya da sake ,ni bazan iya zama da yarinyar Nan
ba ,haba Abba ya zakai min haka" shi kadai dai ya cigaba da durutansa Yana kallonta,can
Kuma yaji bacci mai nauyi ya soma kamashi,babu shiri Big bro ya mike ya saka hannu ya
dauketa chak kamar 'yar baby, bai ajiyeta a ko ina ba sai kan bed, bargo ya janyo ya rufa mata
Sannan Shima ya kwanta a bayanta bacci mai nauyi yayi awan gaba da su.
...............
A bangaren Abdul Kuwa yadda yaga dare haka yaga safi,domin kwana yayi Yana tunani
yasaka wancan ya warware wannan, abin duniya ya hadu duk yayi masa yawa, ciwan son
salwa Yana son ya sashi a masifa, shi kadai sai surutai yake Yana cewa "yanzu shikkenan
narasa salwa har abada' bansan yazanyi ba, ni inan kamar zan mutu sukuma sunacan Babu
abin da ya damesu,mebima soyayyarsu kawai suke Sha, Anya zan iya cire soyayyar ummiterh
a zuciyata ,wai meyasa hakane ,meyasa zuciyata zata na rayamin wani abu akan Dan ,uwana
Kai Anya kuwa, to kodai na kashe big bro in yaso sai ni na aureta, Kai gaskiya bazan iya kashe
shi ba yaya suhail ba ko wanine yace Yana son salwa bazan iya kasheshi ba, balle Kuma d'an
,uwana kash na nemi wata mafitar dai" haka dai Abdul yayi ta sake sakensa Yana surutai a
haka har gari ya waye ko runtsawa bai ba, Banda bacci marawo dayiyi awan gaba dashi.
*SALWA*
*©HAFSAT UMAR DANGORO*
Chapter 6
========IN THE MORNING========
Da sassafe su adda zubaida da dasauran 'yan matan gidan suka zo lambu suka zauna tsabar
gulma da munafirci , sakamakon wanna lanbun a bakin kofar part din big bro yake,
Shiru_ shiru suna zaune a part din goggo ko zasuga shigowar su salwa ,Amma ina sai sukaji
shiru hakan yasa suka dawo lambu domin su kashe kwarkwatar idonsu, sai dai zuwansu bai
karamisu komai ba sai haushi da takaici, mufida ce ta kalli zarah tace "iyee wai uban mai sukayi
haryanzu shiru basu fito ba, ni fa nayi tunanin zanga shegiya a harabar Nan a yashe Amma
Kuma naji shiru" dariya Ameera tayi tace "ai dole kuji shiru jiya sun kwana basuyi bacci ba ,idan
ma Zaku daina jira kudai na ni kunga tafiya ta" ta mike tare da yin hanyar part dinsu,harara
zubaida ta watsa mata tace "to uban mai suke Harda zasu kwana basuyi bacci ba? Kinsan dai
Babu abin da zaici da wanan kwailar" dariya zarah tayi tace "au Amma dai itama macece ko,mai
zasuyi idan Banda soyayya, Nima bazan iya jiran wanan takaicin ba, itama ta mike tayi wayi
cikin gidansu, kuka zubai da ta saka hadi dacewa "wallahi ni Daman nasan ni kadai nakeson
yaya suhail tsakani da Allah gashinan duk baku damu ba akan abin da akayi Mana', wallahi
saidai idan yarinyar Nan bazata fito ba Amma saina koya mata hankali..... Haka dai zubaida
tacigaba da masifarta tabar gurin..
Tun da salwa TA tashi ta juya ta ganta a kan bed kusa da suhail,hankalin ta ya tashi, runtse
ido tayi ta bude tare da saka hannu ta goge idonta domin ta faeka idan ma mafarki take, aikuwa
tana budewa still dai akan gadon ta ganta, tagumi ta rafka tare da kurawa fuskar big bro ido,
azuciyarta Kuma tace "ni dai nasan da kafata ban shigo dakin Nan ba afalo nazauna har bacci
ya daukeni, to Amma abin tambayar shine waye ya kawoni dakinnan ,ko dai yayana, sake kura
masa ido tayi tagsnshi baccin sa kawai yake Babu abin da ya sameshi hankalinsa kwance,
hakan yasa ranta ya baci ,wato ma ita tana zaune tanajin yunwa shikuma Yana kwance ya saki
baki Yana bacci ,to kenan ya zanyi na tasheshi ne?" Tayi tambayar a