Showing 15001 words to 18000 words out of 22578 words
Chapter 6 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf
sila ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri haba sai kace Abdul shine
autan maza" "Dalla malama dakata min ke uban Maine bakiba akan yaya suhail duk haukana
na kaiku, malama tashi ku fitar min daga daki" Ameera ta fada idanunta na zubda hawaye. Sum
sum su zubai da suka mike domin yau dinnan Ameera ta basu tsoro .
Acan bangaren su zaman Kuwa ,gaba dayansu suna zaune a falon bilal , kowanne ya zabga
tagumi da tunanin da yake, Umar ne ya soma magana yace "ni Kuwa Anya big bro Kansa Daya
Kuwa? Haba jibi fa yadda ya tozarta yarinyar Nan agaban su ameera ,Daman ya akaciki balle
yanzu, gaskiya abin da yaya suhail yayi bai kyau taba ko kadan " "uhm ya Umar kenan ni kasan
mai Bama Taron dayasa akayi ne ya tsayamin araiba yadda su Abba suke cewa yaje yayi
tunani akan haka Yana wani cijewa shi adole baya sonta kamar Wanda akayi masa dole, to shi
an fada masa rasa mijin aure tayi Naga dukkanmu Sonta muke shine zaina wulakanta ta,
wallahi ina jiye masa ranar nadama" cewar Khalid,shikuwa bilal cewa yayi ...
"Uhm ku wai mai kuke tunani game da big bro? Nufinku wai baya son ummiterh?" ",eh mana
yaya baya sonta haka muke tunani" "lallai har yanzu ku yarane, big bro Yana son salwa domin
shi Kuwa yakeyiwa salwa soyayyar da mu Bama Yi mata, ina da tabbacin Big bro bai taba
soyayya bane shiyasa har yanzu bai San mainene soba,shi Kansa bai San yanason ummiterh
ba, ya tabka babban kuskure da yasaki salwa, wannan abin da yayi sai ya hanasa rayuwa mai
dadi ,Kuma lokacin da zai sauke girman Kansa da takama, salwa ta masa nisa batajin kira,
babban abin da zai bashi matsala a Nan gaba shine uncle LAMI'DO ,Dan Abba kaifi dayane
baya yafiya Kuma baya magana biyu, gashi yayi rantauwa bazai mayar da auren ba, Inda zaku
San big bro Yana son salwa, lokacin da ta fadi kukalli yanayinsa duk ya fita a hayyacinka, to
wannan ma somin tabine" cewar ya bilal ,shiru sukayi dukkan su suna nazarin maganar bilal,
can Kuma sai zaman yace tabbas yaya suhail ya debowa Kansa abin da yafi karfinsa, yanzu
GA irinta Nan Abba ya damkawa Abdul salwa , uhm Allah ya kyauta kawai.
í ½í²‹ *SALWA* í ½í²‹
*©HAFSAT UMAR DANGORO*
Chapter 9
Tom ana saka salwa a mota abbane da Kansa ya shiga gidan gaba, ya Soma tuki sai Amma
da uncle faruq dake zaune a baya shikuma uncle Kabir Yana zaune a gefen Abba, suka nufi
asbiti, sai da sukayi tafiya mai nisa Sannan, suka Isa babban asbitin dake cikin garin TARABA,
sunayin parking, nurse suka fito da sauri dauke da gadon mara lafiya, salwa aka fito da ita aka
sanyata agadon, Sannan suka shiga da ita, Kai tsaye emergency room aka shiga da salwa,
sukuwa su Abba suna tsaye a harabar dakin, sai kaiwa da komawa sukeyi,gaba ki Daya
hankalinsu a tashe.
Daya daga cikin doctor din asbitin ne ya fito daga cikin dakin, da sauri su Abba suka karasa
gareshi hadi da cewa "doctor! Doctor!! Ya jikin nata ,ta farka?" Sukayi tambayar cikin tashin
hankali,
Murmushi doctor yayi yace " am uhm Karku damu Babu abin da ya sameta, kunyi BABBAR
dabara da kuka kawota ta asbiti da wuri,yanzu dai kawai tsorata tayi GA damuwa da take ciki,
inason ka biyoni zan Maka bayani" doctor yayi maganar Yana kallon Abba.
Bin bayansa Abba yayi har suka Isa zuwa office din doctor, bayan sun shiga zama doctor yayi
sannan Shima Abba ya zauna, sai da suka dauki kusan minti 2 sanan doctor yaja dogon
numfashi ya kalli Abba yace " am yallabai,ka kwantar da hankalinka ba wani abune ya faru da
yarinyar ku ba, kawai dai furgicine dakuma damuwa da Tayi mata yawa ,inason Dan Allah ku
kula da duk wani al,amarinta so a halin yanzu depression din bai yawa ba ,idan ma akwai wani
abu da kuke mata bata so ,yakamata ku daina tun kafin damuwa tayi mata yawa har yazo ta
kamu da ciwan zuciya, idan da dama kuyi kokarin kirkirar mata farinciki tayadda zata na
mantawa da abin da ke damunta" shiru Abba yayi daga bisani Kuma yace" nagode sosai doctor
in Sha Allah Zamu kiyaye akan haka, yanzu ina son ganinta zan iya?" "Ah ai Babu komai Zaku
iya tafiyama zuwa anjima idan ta Dan huta, yanzu kushiga sai ku ganta kafin anjima sai ku
huce" okay Abba ya fada sannan yayi doctor godiya har da yimasa kyautar kudade masu yawa,
sosai doctor Shima yayiwa Abba godiya ,daganan Kuma Abba ya fita zuwa gurin su uncle Kabir.
Yana zuwa yayi musu bayanin da doctor yayi masa akan salwa, sosai suka shiga damuwa
dajin haka Amma sai uncle faruq yace " yanzu yaya abin da Yakamata muyi shine mukoma
gida muzauna akan wanan lamarin domin musamu mafita akai ,Dan Indai har munasan
ummiterh ta bar damuwa akan suhail dolene mu ni Santa su d'akuna" girgiza Kai Abba yayi
alamar gamsuwa da shawar da uncle faruq ya kawo, "yanzu dai mushiga muga yanayin jikin
mata" cewar Amma.
Shiga sukayi dakin bakinsu dauke da sallama, salwa na kwance a kan gadon idanta a lumshe
kamar mai bacci, Amma ce ta soma Isa bakin gadon ta zauna hadi da kamo hannun ta tace
"sannu salwa" a hankula salwa tashiga bude idonta a kansu Tana kallonsu Daya bayan daya
kamar yau ta soma ganin su, Amma ta kalla kamar zatayi kuka tace "Amma ina yayana? Baizo
ba ko, shin dagaske yaya baya Sona ya sakeni?"
Shiru Amma tayi tare da sun kuyar da kanta domin Tama rasa abin da zatacewa salwa, ganin
haka yasa Abba saurin karasowa kusa dasu yace "sannu mamana, ya jikin naki?" "Uhm uhm
dasauki Abba, Abba ina yayana yake nasan Yana tausayina bazai rabu Dani ba ko?" Gaba
kidaya mutanen dake gurin ta basu tausayi ,wani murmushi Abba yayi mai cin Rai ,zuciyarsa na
suya kamar zata fashe sabida bakincikin abin da suhail yayi, can Kuma ya tattaro gabaki Daya
karfin halinsa ya dafa goshinta hadi da shafo kanta zuwa bayan gashinta Inda ya kwanta a
gadon bayanta, Sannan ya tausasa murya yace "mamana !! "
"Naam Abba"
"Kiyi hakuri kinji ,kimaida komai ba komai ba Indai maganar yayankine karki damu Zamu sake
zama Dani da sauran 'iyayenki akan maganarku ,yanzu baki da lafiya abu Daya nakeso shine ki
kwantar da hankalinki kinji, banason Naga kina sakawa kanki damuwa yanzu Zamu huce gida,
daga yanzu banason na sake ganinki ko a part din Ihsan ko gurin goggo bana son ki je, iya
kacinki dakin Amma, kafin musan matakin da muka dauka akai, yanzu Maza ki tashi mutafi"
Salwa kam tsuruu ytayi Tana kallon Abba domin dukkan abin da yake fada kallon sa kawai take
gabaki Daya hankalinta yatafi can duniyar tunanin suhail,komai ya daina mata dadi batasan
lokacin da tunanin zuci yafito filiba tace "yanzu yaya wani ka saka?" Bakinciki ne ya tokare
zuciyar Abba wato bamashi take sauraraba , tunanin ta kawai tatafiyi akan Big bro,magana ya
soma mata yace "mamana Anya kuwa kinason farincikina?"
"Uhm uhm ab Abba inaso mana" ta bashi amsa a takaice .
"To Indai kina son farincikin na daga yau Babu ke Babu Suhail ko tunaninsa ban amince kiyi ba
,umarnine ba shawara ba, haba so kike ki kashe kanki, ko sokike ubangiji ya kamamu akan
haka, mun kasa ruke amanar da d'an uwanmu ya bar mana, in to ba haka nake ba, banabin
San raina, muddum mutum yayi ba daidai ba yazama dole na nuna masa kuskurensa , suhail
danane Kuma kema 'yatace ,Dan haka bazan bi San Rai na maida ke dakin suhail ba, yaci
gaba da wahalar dake ba Dani za a Yi wannan aikin ba, Amma temaka mata ki kamota mutafi
gida" yayi maganar Yana nufar kofar fita ,suma sauran su uncle faruq binsa sukayi abbaya har
zuwa parking space.
°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Tom acan bangaren suhail Kuwa part dinsa ya koma ,abin danuya ya ishesa ya masa zabi,
gaba daya duniyar sai yaji kamar garwashi Dan zafi, zagaye dakinsa ya shiga Yi ,Yana tunani
kwalla fall ta cika idonsa, gajiya yayi da zagaye dakin, Dan haka ya samu kujera ya zauna, dai
dai gurin da salwa ta takure ya kurawa ido Yana kallo, sosai ya shiga tunano abin da ya faru,
musamman lokacin data furgita gumi nazuba daga fuskarta, tsaki yayi ya buga hannunsa a
kujerar har sai da yayi kara, mikewa ya sakeyin yayi, ya cire kayansa hadi da daura tawul ya
nufi bathroom Dan yayi wanka, Yana bude kofar bathroom din abin da ya faru tsakaninsa da
salwa shiga dawo masa, lokacin da take cewa, "yanzu yaya da nacire kayafa kawai ka tashi ka
turo kofar" dakuma lokacin da ta kwanta a kasan gurin tana ta burgima ,tsaki yaja kawai ya fice
daga bathroom din ya fasa wankan, Kai tsaye dakin sa ya shiga ya kwanta, borgo ya janyo ya
lulluba, Dan sanyi sanyi yakeji, Dan haka ya rufe' idonsa ya soma bacci, sai dai kash baccin ma
ya gagaresa ,juyi yashiga Yi a kan gadon ko zai samu bacci ya daukesa Amma ina Abubuwan
sai karuwa suke damuwa ta masa yawa, tashi yayi zaune ya kurawa hannunsa ido hadi da
botsa dan karamin bakin sa yace "oh my God,meyasa na haikata haka, yanzu kenan awane hali
kanwata take ciki?" Yayi tambayar wa Kansa daidai lokacin da yake tuno salwa tana kuka Tana
cewa "yaya mai yasa zaka rabu Dani mai nayi maka, wallahi ina sonka Dan Allah Yaya kada Kai
haka" runtse ido yasakeyi ya furzar da iska daga bakinsa yace "to ni wai mai yasa nake haka,
kai karya ne taya zance natsani salwa Bayan ita rayuwa tace, kash bazan iya bacci ba, dolene
sai na ganta tukunna , to ai basu dawo ba ,Amma dai bari naje .
Mikewa big bro yayi ya nufi part din su Amma, motar da yaga sun shigane yaganta a parking
space,shai dar sun dawo kenan, fuskarsa dauke da murmushi ya karasa dakin Ihsan hadi da
tura kofa, bakinsa dauke da sallama ya shiga, amsawa Ihsan tayi mamaki cike fall a fuskarta
,tadaya bangaren Kuma Tana fishi dashi akan sakin salwa dayayi.
Karasawa yayi gefan kujerar dakin ya zauna, kallonsa Ihsan tayi tace "yaya barka da dare
,lafiya na ganka a wannan Daren" "uhm uhm Ihsan su Amma sun dawo?" "Eh sun dawo yaya
tun dazu ma" "okay, shiru yayi Yana tunanin abin da zai fada mata domin ya San halin da salwa
take ciki batare da ta Gane so yake yaji halin da take cikiba, can Kuma sai yace " Amma dai
lafiya ko ya naganki ke kadai ba Kyjin tsorone?"
"Ehy yaya tun dazu sun dawo Kuma lafiya kalau, sai dai Amma tace ummiterh bazata dawo
dakinnan da zama ba, mebima barin gidannan za ayi da ita"
"Wa.. wh.. what mai to akai ta ina kenan, ban fahimta ba?"
Suhail ya fada a gigice har Saida Ihsan ta tsorata da lamarin sa, ido ta zaro tace
í ½í²‹ *SALWA* í ½í²‹
*©HAFSAT UMAR DANGORO*
Chapter 10
"Yaya lafiya Naga ka gigice to Kai Maine ruwanka Dan an dauke salwa daga gidannan, ai Kai
Daman haka kakeso tun da Daman ka tsaneta"
Jikin suhail ne yayi sanyi Yana rasa abin da zaice ,kawai ya mike ya fita ko sallama bai mata
ba, ita Kuwa tabi bayansa da kallo, Tana son karantar abin da ke damunsa, har ya bar dakin.
Yana fita jikin bangon dakin su Ihsan ya tsaya hadi da dafe Kansa, gaba kidaya yarasa mai
zaiyi so yake yaga salwa Amma Babu hali, gashi dare yayi, wata dabara ya tuna ,can Kuma sai
yayi Dan murmushi,ya huce bangaren su Amma, sai da yaje daidai bakin kofar ya tsaya, yayi
shiru Yana babbuga kofar a hankula Dan sun ruga da sun rufe',cikin bacci Amma taji ana bugun
Kofa, mikewa tayi zaune Tana goge idanunta alamar mai Jin bacci, karf ta hada ido da. Salwa
,wadda ta zabga tagumi Tana tunani ,ta kurawa gurin Daya ido, cike da mamaki Amma ta sa
hannu ta taba salwa hadi dacewa "lafiya ?' a furgice salwa TA dago fuskarnan tata dauke da
damuwa, can Kuma sai ta kakaro murmushi tace "uhm uhm Amma baki bacci ba?" "Ai ke zan
tambaya tunanin me kikeyi har yanzu bakiyi bacci ba ,banace ki rage damuwa ba bakyajin
magana wallahi" salwa ce ta jiyo bugun kofar da sauri takatse Amma dacewa "Amma kinga ana
buga kofa bari naje na bude " tamike zumbur sabi da Kar Amma tacigaba da yimata fada,
karasawa tayi bakin kofar ta bude, Nan take idanuwanta sukayi arba da abin kaunar tata Wanda
tafi kowa so a rayuwarta, zuciyarta ta dafe sakamakon bugawa da taji tanayi da sauri da sauri,
idanuwanta suka kara kanka cewa bakinta yashiga rawa, jitake kamar ta rusa kuka tafada
jikinsa sabida farincikin ganinsa ,Amma Kuma da ta tuno da irin wulakancin da yayi mata sai taji
kamar ta shararamasa mari ,batare da tace masa komai ba ta juya hadi da mai da kofar ta rufe
ta dawo, kan bed din ta koma ta kwanta ,tanajin Amma nace mata "waye?" Batai magana ba sai
da ta tabbatar kukan da take ya ragu muryarta ta Dan saitu tukunna tace "Amma Babu kowa
kawai nice naji kamar buga kofar ake " "murmushi kawai Amma tayi ta kwanta hadi da girgiza
Kai alamar bata yadda da abin da salwa tace ba ,kawai dai ta jine Dan karta kara mata wani
damuwar, salwa kam kara kudundunewa tayi har fuskarta ta nannade bargon ta zura a cikin
bakinta Dan Kar Amma tajiyo sautin kukanta, sanan ta cigaba da kukanta iya karfinta ,tanayi
Tana tunanin wai suhail ita zaice ya tsana.
Shikuwa suhail kasa matsawa yayi daga jikin kofar sakamakon tozali dayayi da abincin da
yazo nema, a hankula ya sulale a bakin kofar gurin yayi zaman dirshen Yana tunani, jikinsa duk
ya mutu yarasa abin da zaiyi zuciyarsa ta daina masa zafi da radadi, tabbas sai yaji inama ace
ya karbi shawarar uncle faruq dayace yaje yayi tunani ko na kwana dayane, ya zu gashinan iya
kacin kwana Daya yayi da salwa a rayuwarsa ,Yakasa sukuni balle Kuma ace tsawan
rayuwarsa tabarsa tabbas akwai sake, rarrafawa yayi ya sakko daga mattakalar benan ya fice
gaba daya daga part din , part dinsa ya nufa ya zauna a falonsa ,tagumi ya zabga yayi shiru
Yana tunanin mai zaiyi yaji dadi, can Kuma sai ya tuna da abokinsa samir, wayarsa ya janyo
hadi da nemo number samir, domin ita kanta Number sai annemota Dan rabonsa da yayi waya
da samir tun ranar da aka daura masa aure da salwa, ya kirashi yake sanar masa ya dawo gida
gaba kidaya bazai koma ba sabi da Abba yace idan zai koma dolene yatafi da salwa, shikuma
Yana tunanin idan ya tafi da ita ajinsa zai zube, shiyasa ya cewa samir bazai dawo a wanan
lokacin ba, yanzu GA shi ta kwabe masa dolene ya nemi samir.
Bugu biyu samir ya daga hadi da karawa a kunnen sa yace "hi ango ango ango ,ango kasha
kamshi wallahi abokina Babu ruwanka ,wato soyayya ta boyeka kamanta damu yayi" sai da
suhail ya bari samir ya gama surutansa sanan yayi tsaki yace "kaga da Allah malan ya isheni
haka, ka shirya jibi zan dawo U.S akwai magana mai mahimmanci danake so muyi" "to abokina
Amma dai da amarya zaka taho ko, ina aunty tamu bata mugaisa mana " bakin cikine ya tokare
zuciyar suhail baisan San da yayi tsaki ya katse wayar hadi da hulli da ita yace "shashasha
kawai" daga haka Kuma ya sakko kasa daga kan kujerar domin shi zaman kujerar ma yanzu ya
addabesa ,in takaice muku karshe dai big bro anan bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi.
In the morning í ¼í¼…
12:45
Tun da gari ya waye Amma take TA faman rashin salwa akan ta tashi taci abinci Amma kamar
Yana magana da gawa ,salwa baccinta kawai takeyi sakamakon jiya da daddare bata samu
bacciba ,kara dukan bayanta tayi tace "ummiterh, ummiterh tashi mana" motsi salwa ta
danyi,hakanne yasa hankalin Amma ya Dan kwanta Dan farko tayi tunanin Babu Rai ajiiinta,
Mika salwa tayi Sannan tadan bude ido suka hada ido da Amma kana tace "Amma ina kwana?"
Harara Amma ta wata mata tace "kinsan karfe' nawa yanzu Kuwa, tun dazu nake faman tashinki
kinki ki farka yau ko sallar asba baki tashiba ,Anya ummiterh,keda sallah bata huceki kecema
mai tashin wasu, gaba daya sabi da namiji kintada hankalinki kallifa duk yadda kika zama daga
jiya zuwa yau haba salwa, dan Allah ki kwantar da hankalinki akwai lokaci in sha Allah Nan
gaba sai kince dama baki tada hankalinki ba, dasannu Zaki rama Indai namijine, suhail danane
Kuma nasan halinsa nasan abin da zai iya da abin da bazai iyaba, Nan gaba dole zaiyi danasa
akan abin da yayi miki kitashi kiyi sallah sai kici abinci ,abbanku Yana son ganinki" shiru Amma
Tayi tan akallon