Showing 12001 words to 15000 words out of 22578 words

Chapter 5 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf

zuciyar ta, "to kodai cizan
sa zanyi ne, a,ah na muntsineshi zafi tashi da sauri ,wata zuciyar Kuma tace "ki samu daidai
lips dinsa ki gasa masa cizo zai mike" aikuwa salwa ta jijjiga Kai hadi dayin dariya ta shiga
matsawa kusa dashi, sai da taje dai dai kusa da fuskarsa Sannan ta tsaya hadi da durkusawa
dai dai kan d'an karamin bakinsa Sannan ta dora nata bakin a kan nasa ta cafki lips dinsa na
kasa, ta gantsara masa cizo, A furgice suhail ya bude ido hadi da kurma ihu yace, "wayyo Allah
na Amma!!!!!!!!! .........." A razane salwa TA daga shi, ta koma gefe ta takure guri Daya, tana
zare ido ,itace ta cijeshi Kuma itace dayin kuka, Harda rawar sanyi duk tabi ta burkice sabi da
tsoron abin da zai mata,

Shikuwa Yana gama ihun ya mike tare da karasawa gaban mudubi ya kurawa bakinsa ido
yadda yaga ya kunbura yayi zumburbur ,runtse ido yayi sabi da tsabar takaici Yana tunanin abin
da zaiyiwa wannan yarinyar ya huce , can Kuma sai ya hau kan gadon kan gadon Rai a hade
kamar Daren mutuwa fuskannan, karasawa yayi kusa da ita, hadi da kama hannayeta duk biyun
ya danne a jikin bangon Sannan yace "ni sa ankine, Daman haka kike bakina kikeso ko,
shikikeson Kisha, hawaye ne suka soma zuba daga cikin idon salwa tana kuka tana girgiza
masa Kai alamar ita ba haka take nufiba Amma ina sai ya sake cewa" uhm ni Daman nasani
ragowar 'yan kauye aka auramin wato kenan abin da aka fada game da ke agidannan gaskiya
ne kina bin Maza" gaba daya salwa ta tattaro dukkan kwarin gywarta tace "wallahi Yaya ba haka
nake ba Dan Allah ka saurareni wallahi ni bana bin Maza" tasake fashewa da kuka, "yimin
shiruu... "Ya dakamata tsawa Nan take Tasha jinin jikinta tayi kumm., A,C ce ke har bawa a
dakin Amma ita salwa gumi take tsabar tsorata da lamarin yayana nata, bata Ankara ba, taji ya
hade bakinta da nashi, lokacin guda yashiga tsotsar bakin dakarfi, Yana datsa labbanta da
hakoransa, sai da sukayi kusan minti 10 a haka Yana azaftar da ita Sannan ya daketa, baki
takeson ta bude tayi kuka ko zata samu sallama Amma ina takasa kukan ganin yadda bakin
yake zubar da jini, sosai yadda yaga tanayi ta bashi tausayi Amma sai yaki rarrashinta sabi da
ya koya mata hankali Dan bayason raini, fuuuu ya mike ya nufi falon ya zauna, tagumi ya rafka
Yana tunani soyake ya fita Amma ya kasa sabi da kumburar da bakinsa yayi ,bayason ya fita ayi
zargin wani abun ko ayi masa dariya, tunowa yayi Tanada facemask idan ya rufe fuskar Babu
Wanda zai Gane mai ya faru.







Haka Kuwa akai bayan ya Yi wanka ne ya shirya tsaf ko kallon salwa baiba ya saka fecemask
ya fice, itakuwa salwa bargo ta janyo domin ta kasa tashi zazzabi mai zafi ya lullubeta ita kadai
sai rawar sanyi take abin tausayi,gashi koyaya ta rufe' bakinta zafi takeji, hakadai tai ta kwance
adaki ko motsi daker sabi da zazzabi.

Shi Kuwa gogan namu ya na fita part din Amma ya nufa ,a zaune ya samesu a falon ita da
Abba, suna Shira, baki Abba da Amma suka saki cike da mamaki suna kallon suhail,Amma ce
TA kasa jurewa tace "to yau Kuma fuskarce ba a so mugani kamar wata sabuwar amarya, ni
abin naka kara gaba yake Anya Anya suhail, murmushi Abba yayi yace "ai ba karya kikayi' ba
hajjaju sabon angone mudinma kunyarmu yakeji " shi dai suhail baice komai ba Kuma bai cire
facemask dinba ,sai ma sun kuyar dakai da yayi ,ya tsuguna yace "am Abba barka da safiya
Kun tashi lpy" "eyyee lallai ma yaronan yanzunne safiya?" Amma tayi tambayar hadi da zuba
masa ido, Sosa keya yashiga ya yace" am uhm Abba bari naje na dawo" daga haka ya mike da
sauri ya fice Yana Jin Abba nacewa "Oh jibi yaro wai Shima yayi amarya' duk ya rude" .

Suhail Yana fita ya sauke ajiyar zuciya yanufi part din goggo, Yana tafe a hanyar harabar ya
hadu da ihsan zata huce da sauri yace "ke ina zakije?" Yiyi maganar tare da tamke fuska, Sosa
Kai tashiga Yi tace "yaya ina wuni?" "Lafiya kalau " "Daman zanje gurin aunty salwa ne najita
shiru bata fito ba" "to ina ruwanki da rashin fitowar ta ,banason gulma huce ki koma Inda kika
fito, ko dawasa naji kinshigar min daki saina kakkaryaki a gidannan" yayi gaba ya watsa mata
harara, itakuwa Ihsan sakar baki tayi hadi da bin bayansa da kallo har ya fice, tsayawa ta danyi
a gurin tayi shiru can Kuma sai ta juya ta nufi Dakin ta.

*SALWA*


*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 7





Suhail Yana shiga part din goggo dukkan Yan matan dake zaune a falon suka zubo masa ido
suna kallonsa, shikuwa bai bi takansu ba ya huce dakin goggo ,yanaji suna gaishesa Amma bai
kulasu ba ya huce, zarace ta dawo kusa da mamey ta zauna tace "lallaima gayennan wato ku
bukukai ya gaysheku ba sai kace wan da yaga sa,arsa"kwafa mamey tayi tace kekuwa jiya na
zagi 'yar gold ta ina zai kulani ai bazai gaisheni ba, tun da ubansa na zaga, uhm jibifa Mamey
har da wani sako facemask kamar wani munafiki sai kace bamusan asalin fuskar ba" cewar
mufida, uhm ku kuka damu dakuga fuskarsa kuka sani ko ita salwan ce ta hanashi fitowa a
haka sabida kada a kalar mata fuskar miji" cewar adda Ameera " tsaki zubai da tayi tace uhm
wato fuskar tashi ma damuke kallon muna Jin dadi tasa yarufe ta , wallahi sai mun tashi tsaye,
dan yarinyar nan na fahimci ta gama mallake ziciyar yaya suhail.




Tom suhail na shiga dakin goggo yaji zuciyarsa ta wani buga da karfi jikinsa lokaci guda yayi
sanyi ,a hankula ya shiga Jan kafafuwansa har ya karasa bakin gadon ,kafesa da ido yayi Yana
kallonsa zuciyarsa cike fall da tausayin sa... Gefen gadon yasamu ya zauna kusa dashi, hannun

sa ya kama yaruke gam Sannan yace "Abdul ! Kallonsa Abdul yayi daker yake daganinsa sabi
da junwa GA jiri duk yafita a hayyacinsa, "Naam yaya,ina kwana?" "Abdul mai yake damunka
haka, haba kanina tukunna ma kaci abinci?" Girgiza Kai kawai Abdul yayi batare da yace komai
ba ya mai da idonsa kasa, "uhm Abdul bazaka min magana ba? ni nake Maka magana kake
min shiru?" Still dai Abdul baice wani abunba yayi shiru ,gajiya suhail yayi da zama Dan yaji
shiru goggon bata shigo ba ,Dan haka ya mike tsam ya bar dakin.


Kai tsaye Bai huce part din saba balle yabi takan salwa, mota ya shiga kawai ya fice, sai da
yayi tafiya mai nisa, Sannan ya tsaya gefan titi, ya durkusa Kansa a kan sitiyarin motar,shiru
yayi yama rasa mai yake masa dadi a duniyar, "Kai Anya kuwa" ya fada hadi da saka hannu ya
bude murfin motar ya fito, zagaye gurin yashiga Yi Yana tunani ,yayi Nan yayi can abin duniya
duk ya ishesa, "Anya kuwa d'an uwana yanacan kwance duk sabi Dani? To Amma ni mai zanyi
da wannan yarinyar in saketa mana ,Kai idan Kuma nayi haka banyi adalciba ita batace na
saketa ba saini zan saketa ,bayan nasan Nima bajin dadin zama take Dani ba, to Amma idan
ban saketa ba taya zamanmu zaiyuwu bayan ni bason ta nakeba,? A,ah fa to idan ba Santa
nakeba menake ,meyasa zan dinga kishi a kanta, ? Kai Anya ba kishi bane tausayinta kawai
nake, babban taimakon da zanyiwa ummiterh kawai na sauwake mata kowa ya huta, to Amma
Anya su Abba zasu yarda?" Shiru yayi ya dan jingina da jikin motar ,,Sannan ya koma cikin
motar ,kunna motar yayi kana ya soma tafiya ya dauki hanyar da Zata sadashi da gidansu.
Yana Isa gidan yayi parking ya fito, part dinsa Kai tsaye ya nufa , still dai a kwance yadda ya
barta haka take, karasawa yayi kusa da ita yace "tashi?" Banza Tayi Masa batare da tace komai
ba, tsawa ya da kamata yace "nace ki tashi muyi magana ko?' da sauri salwa ta mike hadi da
sun kuyar da kanta tace "Allah ya baka hakuri yaya ina jinka" "uhm yayi kwafa Yana kallonta
can Kuma sai yace "ummiterh! Lokaci guda salwa taji kirjinta ya buga, jikinta yayi sanyi tarasa
dalilin Jin haka, Amma sai ta daure tace

"Na am yaya!"

"Na fahimci zamana dake bazai taba yuwuwa ba domin ni inason zama da wadda zan iya
soyaya da ita Kuma wadda nake so take Sona, so Amma ke ina kallonki a matsayin kanwata
Kuma yarinya karama bana son raini bazan iya zaman aure da keba ,kiyi hakuri kinji bawai
nakasa cikawa Abba muradinsa ba no kawai dai nafahimci ina cutar dake haka Nima kina cutar
da ni ,ki tashi kisaka hijabinki mutafi, kiyi gaba ganinan zuwa kicewa Amma duk Akira kowa
inason a shaida da wanan abin kinji" hawayene masu zafi suka soma fita daga cikin idon salwa,
bakinta na rawa tace "yaya rabuwa zakai Dani?" Banza yayi mata baice komai ba ,saima cewa
dayayi "kitashi kiyi abin da na sakaki" salwa bata sake cewa wani abin ba ta mike tsaye jiri na
dibanta ta dafa bango ta dakko hijab ,bayan tasaka ne ta soma tafiya jinin duk ya bushe mata a
lips sabi sabi da azabar da yayi mata dazu, a haka ta daddafa bango tasoma tafiya har tafita
daga part din sa.

Tana cikin tafiya a hanya taci Karo da ihsan zata fita, da sauri salwa tace "Ihsan " gamamakin
Ihsan taju Tana kallon salwa, yanayin yadda tagantane hankalinta ya tashi, cike da tausayin ta
takaraso kusa da ita ,hadi da kama hannun ta tace "nashiga uku salwa mai yasami bakinki haka
,ina zakije Kuma?" Tayi maganar Tana kallon salwa, itakuwa salwa hawayen da take boyewa ne
yashiga sakkowa, zuciyarta tashiga bugu lokaci guda, kawai ta fada kirjin Ihsan tasaki kuka mai
ban tausayi, hankalin Ihsan ne yatashi Tama rasa mai zatace ,can Kuma sai tace "salwa wai
Maine yafaru kodai yayane wani abu ya sameshi? To ko sakinki yayi?" Kukan da salwa take ne
ya daina fitowa sai dai kukan zuci ,daga karshe Kuma tace" Ihsan ina zakije?" "Uhm inason zan
fita ne ?" Indai ba abune mai mahimmanci zakije ki ba gwara ki zauna domin yaya yace Yana
bukatar ganin kowa a babban falo" "to falo Kuma mai yafaru lafiya kuwa Anya?" Uhm uhm
nashiga uku Ihsan wallahi ni kaina bansani ba ,mebi lokacin mutuwa tane yazo bansani ba,Allah
nagaji da rayuwar wanan duniyar natsani kaina" "kiyi hakuri kinji ummiterh komai yayi zafi
maganin sa Allah yanzu ina zakije to ansanarwa da kowa?" "A,ah yanzu yace naje na sanarwa
da mutanen gidannan harsu uncle" "okay kije Maza kizauna a falon ni bari na kirasu. Daga haka
Ihsan ta bar wurin, Tama salwa TA karasa sashen goggo.




Kai tsaye bangaren mahaifanta ta nufa ,ta sanarwa da su Amma, gaba daya hankalinsu ya
tashi hatta Abba Saida yaji gabansa ya fadi daganan ya yanke shawarar ya kira sauran 'yan
uwansa a waya idan ma basa kusa duk su dawo gida, haka Kuwa akai kowa aka sanar masa
gaba dayansu duk suka cika da mamakin Maine dalilin hada taronnan,hatta Abdul sai da aka
tasoshi ya lallaba ya fito ya zauna, su Kuwa Daman iyayen gulma su ameera sun dade da dura
a falon Dan dama kwanciyace kawai take rabasu da zaman falonnan, kowafa na gidan ya
hallara mutum daya ake jira Big bro, salwa Kuwa na gefen Amma ta dukunkune a jikinta sai
tunani take tana faman kukan zuci.



Yanzu kam big bro bai saka facemask dinba sabi da bakin nasa ya sabe, fuskan Nan tasa a
hade kamar daran mutuwa, duk da hade ran dayayi kyen fuskarsa bai fasa bayyana ba, domin
shi suhail ko mai zaiyi sai kinga yayi muki kyau, musamman ma Yana dariya dimple dinsa na
lotsawa, zama yayi a gabansu Sannan ya gaishesu, amsawa sukayi Sannan suka zuba masa
ido suna kallonsa, kasa cewa komai yayi Dan haka ya sinnar da kansa kasa baice uffan ba,
abbane ya kalleshi yace ...


"To ubbanmu gamu mun hadu Kai muke jira"


Dagowa yayi hadi da Sosa Kai Yana kallonsu Daya bayan Daya can Kuma sai yace "am
uhm Daman Abba uhm ina son na sauwakewa ummiterh ne" daram gaban mutanen dake gurin

ya fadi musamman Amma da Abba da sauran su uncle, zaro ido isana tayi tace "saki?" Ita
Kuwa salwa zumbur ta mike hadi da kuramasa ido Tana kallonsa,


Uncle faruq ne yayi kokari ya tattaro duka karfin halin da yake dashi a lokacin yace" saki fa
BABANA mai yafaru idan Rai ya baci ai hankali bai kamata ya gusheba... Saurin dagawa uncle
hannu yayi yace " ya Isa haka kubarshi yafadi abin da yakeso ayanzu ni kan na tabbat ban Isa
da suhail ba cigaba damaganar ka "
Shiru yayi Ihsan kuwa ta dawo gabansa hadi da kama hannun sa tace "Dan Allah Yaya kada
Kai haka wallahi salwa Tana sonka, kamanta da amanar da uncle ya baka maiyasame Kane
yayana,kada kyen dakake da shi da jiji dakai yasa ka manta da wacece salwa a wajenka....



*SALWA*


*©HAFSAT UMAR DANGORO*


Chapter 8




Tsawa ya daka mata yace yimin shiruu... A kan mai bana son auren nan natsani yarinyar Nan
bazan iya zaman aure da ummiterh ba" "a,ah yaya kada Kai abin da zaka zo kana Dana sani?"
No Ihsan akan wanna zanyi Dana sani? To Indai hakane Allah ya tsine wa danasanin " juyawa
yayi ya kalle ta tare da Mika mata takarda yace " karbi"..... Dumm gaban salwa ya yanke ya fadi,
zuciyarta tashiga bugu lokaci guda hannunta na rawa ta Mika hannu zata amsa idanunta na
zubar da hawaye ,saurin dakatar dashi uncle Kabir yayi yace "dakata suhail anya kana cikin
hayyacinka Kuwa ,salwa zaka saka ? Suhail kayi tunani akan haka kada ka aikata abin da
zakazo kana danasani akai " " no Abba nagaji da aurenan bazan iya zama da yarinyar Nan ba
tamin kankanta nafi karfin nayi RAYUWAR aure da ita ... Tasss yaji saukar Mari a fuskarsa
abbane ,abin da tun da yake ba a taba masa ba ,yau sai gashi akan ummiterh an mareshi AI
yazama dolema ya rabu da ita ko itace autar mata, saurin rike hannun Abba uncle faruq yayi
yace "kayi hakuri yaya please ku barshi badai ummiterh ce baya Soba ,ni da hannuna zan
amshi takardar sakin da yayi mata, Amma yasani Bama magana biyu zan kara bashi zabi akan
haka yaje yayi tunani zuwa Nan da gobe... " Ai uncle bai rufe baki ba yaji Amma tace " Babu
wata dama daza a sake bashi, ku rabu dashi Indai wannan auren ne an rabu, Kuma kamar
yadda ya rabu da salwa ya rabu da ita har abada' Babu kome"

Abbane ya karbe da cewa "suhail danane Kuma Wanda na Haifa da cikina ,ada nayi tunanin
duk abin da mukeso ko bayaso zai hakura ya amshi abin hannu bibbuyu, Ashe ba haka bane"
kallon suhail yayi yace "bani takardar ai ba ummiterh ya kamata ka bawa ba tun da ba ita ta
daurawa kanta aure ba mune ,Dan haka mu iyayenta muzaka bawa" suhail Kuwa gaba daya
jikinsa rawa yake hankalinsa inyayi dubu ya tashi bai taba sanin haka saki yake daciwo ba sai
yau, shiyayi tunanin abin kamar wasan yarane jiyake kamar ya fasa ya mai da takardar Amma
ina bakin alkalami yariga ya bushe, jiki Babu kwari ya mikawa abbansa takardar sakin salwa,
Sannan Abba yace "ku shaida daga yau Babu Suhail Babu salwa har abada' Kuma narantse da
Allah ko da suhail zai mutu bazan maida salwa gidansa ba ko bayan Babu raina ban amince
salwa TA koma gidan suhail ba, Kuma ku shaida na saka ranar auren Abdul da salwa Nan da
shekara 3 kafin Sannan salwa ta Kammala karatunta" kuka salwa ta saki hadi da dukawa a
gaban suhail tana kuka kamar ranta zai fita tace "yaya yaya!! Yaya mai nayi maka zakayimin
wannan babban hukunci ,yaya ina sonka meyasa kakeson kasheni lokacina baiba ,wayyo Allah
na Amma zan mutu.....

Salwa ta sulale a gurin ko motsi batayi, cikin tashin hankali suhail yashiga jijjigata hankalinsa a
tashe hannayensa ya zura zai tallafota ya dagata Abba ya daka masa tsawa yace "dakata
suhail... Ayanzu salwa ba matarka bace Babu Kai Babu ita !" "Kallon Abba yayi kamar zaiyi
kuka yace "Abba ummiterh zata mutu " to saime ina ruwanka da mutuwarta ,da wayaja hakan
tafaru ,Kai Abdul Maza futomin da mota, ke Kuma Ihsan khaleesat ku kama salwa ku fitomin da
ita, Kai Kuma suhail ko a harabar asbitin na ganka ban yafe maka ba" Abba ya fita a fusace,
suma su zubaida mikewa sukayi sukabar gurin domin yau sunga gulma Babu SA,a acikinta
Ameera Kuwa Inda kasan zatayi hauka.

Aguje tanufi part dinsu ta fashe dakuka tare da fadawa kan bed, sukuwa ragowar 'yan uwanta
biyo bayanta sukayi har dakin suna bata hakuri, musamman zubaida da yanzu hankalinta ya
kwanta suhail ya saki salwa ,kallon Ameera tayi ta dafata tace "Dan Allah Ameera kiyi hakuri
komai kikaga yafaru akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login