Showing 3001 words to 6000 words out of 22578 words

Chapter 2 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf



Chapter 2

Su Kuwa su zubaida,Abdul Yana barin gurin suka kwashe da dariya tare da cewa "Amma
dai anyi asarah wallahi ,jibeshi Dan Allah yadda yawani bita kamar wani jela" ita Kuwa mufita
kallon Ameera tayi tace "oh Amma dai Ameera kinyi asara yanzu sabi da Abdul din kika zauna
kina kuka kin badani" wallahi idan nice sai na bari bayanan zan lakadawa shegiya duka" cewar
zarah "uhm bazaku Gane ba, gwara nima iya kacin kuka nayi kukuwa fa tsabar asara kuna
faman masifa akan mutum daya kune manyan asarar ru" matseatsatssss Ameera tayi tsaki ta
bar gurin.



A bangaren Abdul Kuwa Yana karasawa part din Amma Kai tsaye dakin Ihsan ya shiga, ko
sallama babu tsabar tashin hankali da Jin tsoron abin da ya faru da salwa lokacin da ta buge,
zaune ya same su Ihsan na cewa "haba salwa mai yake damunki kema sai kace bakisan ciwan
kan ki ba na fada miki ki hakura dazuwa part din goggo kin ki kiji, yanzu GA irin tanan jibi kanki
yadda ya kunbura tsabar mugunta Harda gwara miki Kai sukayi" a hankula salwa ta soma
magana cikin sanyin murya Tana cewa "Ihsan narasa mai nayi ma su adda suka tsaneni bansan
mai yasa ba ko kaddara tace a haka ,nifa bani na nace su Yaya Abdul su soni ba , ubangijin da
ya haliccemu ni da Abdul shi yasan yadda zaiyi damu, naso ace Abba da yatashi Abdul ya
auramin a matsayin mijina ko Babu komai zan rage wani kunci da zafi na maraici ,sai dai kash
Allah ya hadani da Wanda take ganin shi yafi dacewa Dani ,nasan cewa yaya suhail jininane
Amma shi bai San haka ba baya duba dangantaka ta dashi, a kullum zuciyarsa na raya masa
cewa yafi karfina mai zaiyi Dani sabi da ya na ganin ni ban Kai ya zauna Dani a matsayin mata
ba, wallahi Ihsan ko da ace sakina yaya suhail yayi bazan Yi kuka Dan ya sakeni ba ,zanyi kuka
ne akan cewa ya mai Dani karamar bazawara" daga haka salwa ta fashe da kuka, gaba ki Daya
jikin Abdul ne yayi sanyi lokacin da yaji magan ganun salwa, bai taba tunanin salwa Tana da
hankali da manyan taka irin haka ba, salwa yarinya ce karama sosai wadda za a iya cewa
batasan mai take a yanzu ba, shi Kansa yanajin cewa inama a dawo da auren ta Kansa ,da ya
nuna mata gata Wanda har a bada bazan ta tabajin ita marainiya bace sai dai In ko tunawa tayi,
sai dai Allah yariga ya tsara salwa matar big bro ce, Babu yadda ya iya bazai ce zaiyi kishi da
yayansa ba ko Babu komai yasan watarar yaya suhail zai sota.

Batare da Abdul ya furta komai ba ya mike jiki a sanyaye ya bar dakin itakuwa Ihsan bin

bayan sa tayi da kallon tausayawa Dan tasan irin kaunar dake tsakanin salwa da Abdul kwata
kwata da dawowar salwa gidan baifi wata 6 ba Amma jibi yadda sukayi sabo har basa so su
rabu.


Kallon salwa tayi tace " salwa sunanki Yana nufin farinciki da kwanciyar hankali, yakamata
ace kazama mai farinciki a Koda yaushe kizama mai kntar da hankali akan kaddara kiyi
hakuri,kinji ki daure kiyiwa uncle biyayya amatsayinsa na mahaifinki kinga dai uncle baya raye,
Allah ya karbi rayuwarsa ya kamata ace kin Yi kokarin cika masa burinsa ki zauna da yaya
suhail ko Babu dadi ki nasa biyayya iya kacin iyawar ki kada ki Gaza akan haka Kuma Kar ki
kuskura Koda da barin bakine kice big bro ya sakeki, kibari ya sakeki da kansa duk da bana
fatan haka, domin wallahi kinyi dace acikin mata dubu ke Zara ce yaya suhail mata basa
gabansa ,kina dai ganin yadda matan gidan Nan ke bin sa suna sanshi Amma shi ko a jikinsa
bama tasu yake ba, Kuma nasan Babu abin da suke yiwa sai kyaun da Allah yayi masa da
Kuma kudi, duk da kasance war yaya suhail yayanane jinake kamar in boyeshi na dinga
ganinsa kullum, sainaji inama nice nasamu wannan damar da kika samu ,sai dai kash Allah
kenan saiya hadani da shi Amma Kuma a matsayin yaya da kanwa, kije kiyi sallah Naga lokacin
sallar azahar yayi idan kin idar sai kizo muje part din big bro muyi masa sannu da dawowa" zaro
ido waje' salwa tayi tace " wa ni in Zaki ki bar jirana .in kinganni a lahira kaini akai wallahi
bazani ba sai kin dawo". Daga haka salwa ta mike tashiga bathroom.

Bayan ta Yi wanka ta dauro alwala, sosai da tafito Naga kyen yarinyar ya karu sabi da ta
wanke kwalliyar 'yan kauyen, bakin drowa ta matsa tare da bude murfin drowar ta dakko wata
doguwar riga pink mai rashin fari, mai kawai ta shafa Sannan ta saka rigar hadi da fesa turare a
jikin rigar da Kuma hijabin ,daga bisani Kuma ta shin fida daddumar ta tayar da sallah.


Ita Kuwa Ihsan part din big bro ta shiga ,kwance ta sameshi a kan bed ya cire jallabiyar ya
ajiye a gefe, idanun sa a lumshe da alamun dai babacci yake ba sabi da idonsa na San
motsawa Kuma yadda ya ke a kwance kamar tunanin wani abun yake, cikin nutsuwa Ihsan ta
karasa hadi da cewa" yaya barka da wannan lokacin" shiru yayi bai ce mata komai ba Kuma har
lokacin bai bude idonsa ba, sai da ihsan tacire Rai da zai amsa mata sai Kuma taji yace
"yakike? A nutse ya sauke idonsa a kan ta yace "ihsan " "Naam yaya Naga kamar baka jin dadi,
nazo gurinka nayi maka oyoyo Amma sai nagan ka wani iri, yaya da kwarin gywata na taho
Amma kasani naji jikina yayi sanyi mai ke damunka?" "Uhm kanwata kenan Babu komai" daga
haka ya juya ya yadauki wayarsa ya shiga dannawa ,itakuwa Ihsan idanun ta na kan abin da
yakeyi, a yadda ta kula ba abin da yakeyi kawai dai Dan Kar ta sake tambayar sane ya dauki
wayar, jiki a sanyaye ta mike tare da cewa "yaya sai anjima" batare da yace mata komai ba
tafita.

Tana fita ta ci Karo da Amma zata huce, da sauri ta soma kakaro murmushi a fuskarta tace
"Amma ! "Naam Ihsan lafiya kuwa naganki a haka kodai ke da Suhail ne" sun kuyar da Kai
Ihsan tayi zuciyarta na raya mata shin ta fadawa Amma abin da ke faruwa kokuma ta zubawa
abin ido taga iya Inda wasan zai tsaya, bata gama tunanin ba Amma ta sake cewa"Ihsan bakice
ko mai ba?"

"Uhm Daman Daman Amma yaya suhail ne Naga Yana cikin damuwa Kuma..." Kuma mai,
kijini da shashashar yarinyar kin kasa fadamin magana " "uhm Amma na fahimci yaya bayason
auren Nan ayanayin da na fahimce shi ba zai iya sanar da ku bane Amma baya son auren
salwa ina ganin Amma da hakura akai, kuma itama salwa bata son yaya hasalima tsoransa
take, ni a ganina kawai tun da Naga ya Abdul na son ta kawai a mai da auren kan ya Abdul"


"Mai Abdul baki da hankali Ihsan har yanzu ka yarinya ce, shi suhail din ne yace miki baya son
salwa to idan bai so taba wazai so, ko ita salwan ce tace miki bata son shi?"

"A,ah Amma kawai fahimtar haka nayi" "uhm kawai Amma tace Sannan tace "kihuce daki,
Kuma ki daina damuwa akan haka kinji dukkansu suna son junansu fatanmu dai Allah ya hade
kawunan mu baki daya" daga haka Amma ta huce ita Kuma Ihsan ta huce part din su.

A bangaren salwa Kuwa bayan ta idar da sallar ne ta daga hannun ta sama idanuwan ta na
zub da hawaye, murya na rawa ta ke cewa "Allah kagani bani da tsumi Kuma bani da dabara, ni
baiwar kace mai tsananin bukatar kulawa da nuna soyayya a gareni, tun ina cikin mahaifiyata
nasa ba da kaunar da take nunamin, har Allah yasa Nazo duniya, yanzu gashi ta tafi ta barni
,Allah kaga halin maraici da nake ciki ba uwa ba uba ba kaka, Allah Kashi ga lamarina, ban San
dalilin da yasa na kasance a matsayin matar yaya suhail ba bayan nasan baya Sona Kuma
bazai taba son mace Irina ba, domin nasan yafi karfina, Amma a haka ubangiji kayi ikon ka a
kanmu ka mallaka min shi ,sai dai har yanzu ban samu zuciyar sa ba, sai Kuma ka dorawa ka
ninsa soyayyata bayan kasan ni matace a gurin yaya suhail, na kasa Gane me hakan yake nufi
ya Allah kayi gaggawar warware min wannan lamarin, akullum kara Sona da kaunata mazan
gidannan suke duk da bansan irin baiwar da kamin ba, Amma nasan ni macece mai hakuri
,Kuma zanci gaba da hakuri har izuwa lokacin da kaddarata zata sauya" Sha fawa tayi Sannan
ta cigaba da yin kukan ta.

Ihsan Kuwa dake tsaye a bayanta batasan lokacin da hawaye kebin kuncinta ba ,sabi da
tsananin tausayin salwa, jiki Babu kwari Ihsan ta karaso kusa da salwa tare da kama hannunta.

A furgice salwa TA dago San bata San da mutum a bayan ta ba, Tana dagowa suka hada ido
da Ihsan saurin goge hawayen fuskar ta tayi tace "Ihsan lafiya yaushe kika dawo, ina big bro
din?" Salwa ta watsomata tambayoyi lokaci guda.

"Uhm salwa !"
"Naam Ihsan "

"Kinason yaya suhail?"

Drumm gaban salwa ya fadi zuciyarta ta shiga har bawa, cikin rashin sanin mai zata ce mata
tace "ba b ban bangane mai kike nufiba?"

"Uhm salwa kinason yayana ko?"

Kukan salwa ne yasake tsanan ta cikin shashshekar kuka tace "wallahi Ihsan ina son yaya
suhail Amma banason kowa yasan wannan maganar dagani sai ke, tun kafin na soma saka
Yaya a idona na so shi, na soshine tun kan nasan waye shi ya kamannin sa suke, akullum
mahaifina bashi da aiki sai bani labari akan yaya suhail Yana cemin, 'yata kin San mai, yayanki
fa Yana gaysheki Yana Nan yace zai zo ya ganki ,zai kawo miki 'yar tsanar wasa, zai siya miki
alewa yace . "Kullum Abba cikin yimin maganar yaya yake, wannan kaunar da yake nunamin
yasa na soma kaunarsa tun kafin nasan mai Nene so ,tun kan na ganshi nake son shi Ihsan,
wallahi Ihsan Kar kice soyayyar da nake masa ce yasa abbana ya bada wasiyar a aurawa yaya
Ni, ko kadan, abbana bai San ina son yaya suhail ba abu Daya yasani shine Yana son yaga ya
hada zumunci" tsayawa salwa tayi da maganar ta share majina Sannan ta ci gaba da cewa "
ihsan na shiga uku soyayyar yaya suhail itace ajalina nasani, ban taba tunanin soyayyar da
yaya yakemin zata koma kiyayya ba sai bayan an daura auren mu, ban sani ba ko Dan ganin
idon abbana Daman yake Sona oho, idan nace miki jiya na fara saka yaya suhail a idona Zaki
yarda, a jiyane nasan kamannin yaya Kuma ajiyan naji soyayyarsa ta kara nun Kuwa a cikin
zuciyata, ki fadamin mai zanyi akai wazan kaiwa kukana ,bazan takura dole yaya sai ya soni ba
Amma ni nasan ina da wan da ya halicci yaya tun da ina da ubangiji shi kadai yasan dalilin da
yasa rayuwa ta ta kasance a haka"


Shiru Ihsan tayi tsabar mamaki da Kuma tsananin tausayin salwa,tabbas akwai babban aiki a
gaban salwa sanan a kawai yaki, domin iya su adda zubaida kadai aka bar salwa da su sai sun
Kai TA kasa to Amma shi yaya suhail wai wayake sone, meyasa haka eh , ko Dan Yana da kyau
ne, Ihsan ta fadi haka a zuciyar ta a fili Kuma tace " kiyi hakuri salwa kici gaba da addu,a akai
Nima zan tayaki addu a kinji " "in sha Ihsan nagode Amma Dan Allah wannan maganar ta zama
sirri a tsakani na dake" "in Sha Allah bazan fadawa kowa ba".

"Yanzu dai ki je inji Amma " to kawai salwa tace ta mike ta fita, bayanta Ihsan ta bi cike da
tausayawa ,Sannan ita ma ta mike ta dakko wayarta, ta soma dannawa.


.......................

Mamey ce zaune a part dinta ta harde kafa Daya kan Daya hancin Nan nata ya sake tashi
sama sabi da tsabar masifa, ita Daman aba ba kyau ba sai ta sake yin muni ,cikin masifa ta ke
kallon Ameera tace "uban mai kikeso yanzu nayi miki , kinzo kin Sakani a gaba sai kace zan

wadda zan bawa mama, shashasha kawai ace wai 'yar qauye tazo tafiki iya Jan hankalin namiji
,ai wallahi ban taba sanin Ameera ke shashasha bace sai yau ,yanzu salwa Zaki tsaya kinawa
kuka, salwa? Nawa take yarinyar to ina ruwanki da son da Abdul yake mata, ai abanza salwa
dai matar aurece koyaki ko yaso haka zai gaji ya hakura ,tun da Tana ganin suhail bazata zabi
Abdul ba ,Kuma wallahi Shima Abdul din sainaci ubanshi kamar yadda ya kuntata min saina
kuntatawa uwarsa ,itama Ihsan din sai dai ta mutu Indai sai ta auri huzaifa ne, bari huzaifan ya
dawo Naga ta tsiya"


Kuka Ameera take Tana cewa" ni wallahi mamey ba salwace tafi batamin Rai ba ,irin yadda
su adda zubaida suka zauna suna cikin mutunci akan Abdul,wai nakasa samun zuciyarsa su
basuga yadda yarinya karama ta hanasu kwanciyar hankali ba, jibesu fa mamey kusan su hudu
duk akan big bro kowacce son shi take ,ai yasin gwara ni so dubu" .
Uhm "dallacan ni rufemin baki duk ai jirgi dayane ya kwasoku Kun bi kun makalewa 'yayan
mutum daya kamar su kadaine mazaje a duniya, baga sauran 'yan uwanku Nan ba duk gasu
Umar ,bilal, zaman ,sauban Khalid ,huzaifa , Amma duk Kun nacewa Abdul da suhail , idan ban
da asra ma ke zarah,wai Abdul kukeso kuna uwa Daya uba daya sabi da namiji kuna gaba
,wallahi Kun bada mata, su Kuma wadan can asararrun zubaida, mufida,zarah da Kuma
wancan aljanar matar salwa tashi wai duk kansu akan suhail,Allah ya raba bawa da wahala,
tashi ni ki bani guri mara zuciya wadda batayo halin harziki ba".


Ita dai Ameera bata sake cewa komai ba ta mike ta nufi Dakin su.


Tom salwa Tana Isa part din Amma, ta Yi sallama, Amma ce ta amsa mata sallamar Sannan
tace "A,ah salwa karaso mana" salwa ce ta karasa fuskarta dauke da murmushi ta cewa "
Amma ina wuni?" "Lafiya kalau salwa, Daman cewa nayi kizo ki kaiwa suhail abinci tun da Naga
yanzu kina matsayin matarsa bai kamata ace ni ko Ihsan muna Kai masa ba" durummm salwa
taji gabanta ya fadi lokaci guda tanemi duk wani kuzarinta ta rasa jikinta yayi sanyi ,saka makon
tunowa da maganar da ya fada mata cewar kada ta sake bari yasake hada ido da ita, Amma ce
ta fuskanci kamar akwai wani abu ganin haka yasa tace "salwa lafiyarki Kuwa yanaga lokaci
guda duk kin sauya?" "A,ah Amma Babu komai Yana ina abincin " batare da Amma TA ce
komai ba ta mike ta dakko mata abincin a plate ta bata Sannan ta koma ta zauna, ita Kuwa
salwa mikewa tayi ta nufi hanyar fita jiki a sanyaye ,kofar ta janyo tarufe Sannan ta nufi hanyar
da Zara sa data da part din big bro.

Amma Kuwa, zama tayi tai shiru daga bisani Kuma tace "tabbas akwai abin da yake faruwa a
tsakanin yarannan, Amma.. Babu komai nasan yadda zanyi.


Salwa ce tsaye a kofar dakin big bro ta tsaya tayi tsuruu takasa motsawa ita bata shiga ba ita

bata matsa daga jikin kofar ba, gashi ta jingina a jiki ta kalli sama ko mai take tunani oho, suhail
ne tsaye a tsakar falon yasha farar riga da wando baki dogo, sai gashin sa da ya taje yasa
hannu ya nad'esa a bayansa, wani bakin glas ya Dora a idonsa wan da ya kara masa kyau da
kwarjini, yayi kyau sosai ko ina zaije? hannunsa rike da kee, hannu yakai kan kofar tare da
budewa, ai kafin ya an kara salwa TA fadi kasa, shikuwa abincin gaba ki d'aya yayo kan sa
,abin ka da Miya duk ta bata masa farar rigar, hatta juice din sai da ya sheko masa jiki, ran sa in
yayi dubu ya baci, ita Kuwa salwa a tsorace take binsa da ido jikinta narawa sabi da tsoro, gaba
ki Daya tabi ta manne a jikin bangon dakin Tana kallonsa kamar wani mayunwacin Zaki,sai huci
yake, gumine ya soma zubo mata, allah sarki duk da AC dake dakin hakan bai hanata gumiba
tsabar kaduwa da tashin hankali.

*SALWA*


*©HAFSAT UMAR DANGORO*

Chapter 3

Big bro Kuwa abin duniya ya isheshi yama rasa mai zai mata ya huce, hannunsa yasaka ya
janyota gaban sa tare da zama gefen kujera, ya kuramata ido Yana kallonta cike da tsantsar
tsana, idanun ta ta sauke a kasa hadi da hade hannayen ta guda biyu hawaye nabin kuncinta
,sai yanzu ta tattaro duk wani kwarin gywarta tace "Dan girman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login