Showing 57001 words to 60000 words out of 126208 words
Chapter 20 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
wajibul manzil da aka basu kan tajwidi,a
hankali ta dago idanunta ta dubi abbun,daita sunkui da kanta qasa,tana tuna duk wani cin fuska
da anwar yayi mata,tanq tuna kalamanshi akanta daya bayan daya,wani daci na tasowa daga
qirjinta zuwa harshenta,saidai ta dake zuciyarta,batason ko daya ta sake zubda qwalla a
rayuwarta saboda anwar
"Uhmmm..." Abbu ya sake bata dama ganin tayi shuru
"Abbu sun koreni ne"
"Kora kaman yaya?,me kika musu?,wannan wanne irin cin fuska ne?" Anty zubaida ta fada a
hasale,yayin da abbu yayi shuru har sai da anty xubaida takai aya
"Dazu gamayyar malaman makarantarku sun sameni har wajen aikina,sun bani haquri kan
abinda ya faru,na gaya musu banda masaniyar abinda yafarun,sun bayyanamin cewa mai
makarantar ne gaba daya ya sallameki,dukkansu basu da masaniyar ainihn dalilin daya sanya
ya koreki ba,duk da kina daya daga cikin haziqan malaman da suke alfahari dasu,idan don
kamarace bake daya kika makara a ranar ba,amma suna so na baki haquri in sha Allahu zasu
magana dashi master din,kuma sunsan yana da sauqi zai fahimta,to,duka dai sun gama
bayanansu,na kuma ari bakinki naci musu albasa cewa kema ba zaki koma ba,idan baki manta
ba dama kan yarjejeniya na barki koyarwa a makarantar,yanzu kuma abinda muka gina
yarjejeniyar akai ya afku,saboda haka yanxu kinga nayi winning,dole ki karbi duk aikin dana
samo miki kenan" ya qarshe yana murmushi,don bashi da ra'ayin tursasa dan adam ne,amma
dama tun asali ta yaya shahida me matakin karatun irin wannan zata tsaya koyarwa a
primary?,wanne irin maida kai baya ne
"In sha Allahu abbu,nima bani da sha'awar komawar har abada"
"Shikenam faduwa tazo daidai da zama,Allah yasa hakan shine yafi alkhairi"
"Amin abbu na gode" ta furta idanunta har yanzu na kallon qasa,nan ta yimusu saida safe da
zummar zata sha magani ta kwanta.
Sai data raba dare tana gayawa kanta ya kamata ta motsa gaba,ta watsar da komai,ta ciyar
da rayuwarta gaba,ya kamata ta shafe komai kaman yadda take gayawa kanta a 'yan kwanakin
nan,idan bata manta ba,idan kuma zata iya tunawa,anwar din data gani dazu da anwar din data
gani satin daya gabata ba shine anwar din data sani shekaru goma baya ba,lallai ba shakka
bashi bane,ya kamata aga wata shahidan ta daban ba wannan ba
"Yes!" Ta fada tana baiwa kanta qwarin gwiwa da tabbacin zata sauya komai.
Washe gari da qwarin gwiwarta ta fito,hakanan tayi yaqin maida murmushi da fara'arta gaba
daya,koda bata samu duka ba taji a jikinta ta maida kaso hamsin cikin dari,wanka ta soma yi
sa'annan ta fito ta shirya cikin kwalliya madaidaiciya a riga da skert na atamfa don kusan tafi
son atamfa saboda tana son kaya cottoon kasancewarta mutum da batason zafi,feshe jikinta
tayi da turarenta na din din din,ta tsaya gaban mudubi tana kalli kanta,ita kanta tasan tayi
kyau,kwalliyar data jima bata bari ta rabi koda fuskarta ba,murmushi ta sakarwa kanta da kanta
tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai taji gaba daya hankalinta ya karkata ga aikin da abbun
yace zai sama mata,batason ci gaba da zama haka
"I need to make my self busy,so i can forget dat am deeply hurt and broke" ta qarshe maganar
tana juyawa cikin hanzari ta dauki wayarta ta fice daga dakin.
A tunanin anty zubaida zata ganta sukuku ko cikin damuwa saboda maganar jiya amma sai
taga sabanin hakan,itama hakan yayi mata dadi sosai,ranar alhamis ce babu islamiyya,haka ta
sake sosai cikinsu huda sukayita buga games bayan sun gama karatu,ta kira mutanen data jima
bata kirasu ba,ta kira zunnurarta sun jima suna hira,har ita kanta ta dinga tambayarta yau da
alama ranar ta musamman ce.
Koda noradden yazo shima yazo yau a sa'a,ta tanqwara zuciyarta ta fita ta saurareshi ba
tare da wani dogon turanci ba,ba laifi kuma ta dan jima wajensa,don ta dauki mintuna aqalla
ashirin abinda bai taba faruwa ba a tarihin zamantakewarsu,ita kanta yau taji zuciyarta sakayau
kaman ta rage mata nauyi daga cikin nauye nauyen dake takure da ita.*zafafa biyar na
kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi
wannan number*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*ga mai buqatar littafina da zanyi bayan kammala alqawarin Allah,yaje youtube yayi searching
SAUTIN HIKIMA,zaiga SUBSCRIBE da jan rubutu ya dannan zai koma black,yayi screenshoot
ya turo zuwa ga number da zatazo a qasa,zan sakashi group din da yardar Allah SUBSCRIBW
KYAUTA NE BA'A DAUKAN KO SISI*
07038670166
*Alqawarin Allah*
2️⃣0️⃣
Zaune yake shi daya cikin dan qaramkn garden din dake bangare raban na gidan
nashi,wanda yasa aka masa shi sannan aka qawata masa,yakan yawaita zama lokaci zuwa
lokaci musamman a sanda yake buqatar kebewa ko yin wani gagarumin aiki da bai buqatar
surutu ko takura,snye yake da t.shirt mai gajeran hannu gami da trouser light and dark
brown,tray ne dan qarami aje a ganshi da butar shayi hadi da qananun kofuna guda biyu
akai,daya kofin yana hannunsa,idanunsa zube kan laptop din dake kunne gabanshi tana aiki
yana kallon wani aiki daya soma tsarawa,inda yake fidda duk wajajen dake da kura kurai,yayi.
Da wani sashen kuma ranshi ke a bace saboda sanarwar da nafisa ta fitar a fashion tv,baisan
ya akayi ba sai saqonnin taya murna ya tashi dashi fal email dinshi,watsapp dinshi da
twitter,angage din ma da ba'akai ga tabbatar dashi ba.
Qarar bude gate din gidan da mai gadi yayi ya shiga kunnuwansa,sai yayi tsai yana
sauraro,iyakar saninsa yasan dai ya gaya masa kar yabar kowa ya shigo masa gida idan ba
muhsin ba,saboda yana son ya hada hankulanshi waje daya,zuciya da qwaqwalwarsa ta samu
cikakken hutu.
Ba'a wuce minti biyar cikakke da budewar ba ya juyo taku,kamn ya juya saiya basar yaci
gaba da abinda yake,don qamshin turarenta daya rigashi isowa ya gaya mishi ko wacece.
Ta dauki minti biyar tana tsaye a bayanshi,hannayenta harde a qirji tana qare masa kalla,ba
shakka ta jarabtu da son anwar irin soyayyar da bata tsammaceta ba,har kwanan gobe kuma
bata ji a jikinta zahiri da badini ta samu irin soyayyar da take kwadayi daga gareshi,haka ta gaji
ta saki hannayenta tana fidda ajiyar zuciya ta taka har inda yake,gabanshi ta zagayo ta tsaya
tana dubanshi,fuskarta a narke haka ta karyar da wuyanta,sai daya mula don kanshi sannan ya
dago ya mata kallo daya,haka kawai yakeji wasu abubuwa marasa dadi akanta,har yanzu
baisan a wanne aji zai sanya nafisan ba,ta kuma qi ta gane taqi ta fuskanceshi
"Baki iya sallama ba?" Sai tadan sassauta kwabw fuskar da tayi,tana son ta koyi sallama duk
sanda ta iskoshi kaman yadda ta fahimci tsarinsa ne amma takan yawaita mantawa,kuma mima
ta gaya mata dole ta siffantu da duk wani yanayi da tasan yana so yana kuma cikin tsarinsa
"To salamu alaikum" amsa mata yayi duk da har yanzu bai daga kai ya sake dubanta ba
"Ba zakace na xauna ba?" Ta fada cikin shagwaba,ture kofin dake gabansa yayi
"Sai nace ma?,ai ga kujera nan kina gani ko?" Kai ta gyada a hankali taja kujarar dake
fuskantarsa ta zauna.
Hannayenta ta hade waje guda,ta sake sassauta murya
"Dear...don Allah me nayi maka?,me yasa kakeson sanya zuciyata cikin rudani,kasan ya nake ji
duk sanda na kiraka baka daga ba,ko na turo maka saqo baka karanta ko ka turamin reply ba?"
Idanunshi ya daga ya dubeta sai ya sake kautar dasu yaci gaba da abinda yake,tunu qwalla ta
cika mata idanu,ta tsani wannan miskilancin nashi ya motsa,wahala takesha,tana ji a ranta duk
sanda ya soma shariya irin hakan kaman dai ya tuna tsinanniyar yarinyar da yanzu tsanarta ta
ninku a zuciyarta wato shahida,data sani baya ga rabasun da tayi ta nakastata yadda ko da
wasa ma bazai sake kawota cikin zuciyarsa ba,amma data taba masa zancan ya tunata ne
ranar taqa zallar bacin rai,ya gaya mata karta sake mishi wannan zancan don ba huruminta
bane,sannan kuma karta sake masa maganar wata shahida,abinda ma yasaka ranta ya danyi
sanyi kenan,ta cika da fatan Allah yasa tabar ranshi kenan har abada.
"Meye laifina dear..." Ta fada cikin son fashewa da kuka,saiya tattara dukkan abinda yake
gefe guda ya rufe system din sannan ya daga kai yana dubanta duba na kai tsaye,yana fata
Allah ya yaye mata wannan son da take masa,sam ko kadan shi hakan baya masa dadi
"Ni na aikeki kona bada daman ki bada sanarwar engage dinmu rana ita yau?" Kai ta girgiza
tana dubanshi hawaye na sake cika idanunta
"Wannan wacce irin banzar dabi'a ce,mu yahudawa ne nafisa?" Nan ma kai ta gyada saidai
cikin ranta tana jin dadi da sauqin radadin da take ji,ta zaci wani babban laifi ne ta aikata,koya
ganta ne ranan nan da saddam randa sukaje dinner din abokinsu,wanda basu dawo ba sai sha
biyu da rabi na dare,ita a ganinta wannan sam ba laifi ne ba,hasalima saika isa ka qasaita ka
amsa sunanka wani sannan za'a ga wani abu daya shafi event dinku a gidan talabijin din
"Kayi haquri,kuskure ne,bani na biya bama siyama ce tace lallai a saka"
"Siyama....ita tace rana ita yau din kiyi wani bikin engage namu kenan?,ohk tunda haka ne rana
ita yau din ita saita tabbatar da abun kota tursasani" ya qarashe fada yana janyo wayarshi dake
gefe,da sauri ta riqe hannun nashi don tafison a kawo qarshen komai,bata jurewa fushinsa,jinsa
take har zuciyarta,kallonta da yayi ya sanyata saurin janye hannun nata,yasha mata kashedin
tabashi ba sau daya ba ba sau biyu ba
"Don Allah dear don Allah,wallahi na fasa ba za'a yi ba" yana da tausayin mace hakanan mutum
ne shi da tun asali yake tausaya raunin 'ya mace ko wacece
"Kome mutum xaiyi ya kamata ya dinga duba da abinda bai sabawa addini da al'adarsa
ba,sannan ka dinga dogon nazari da tsinkaye a duk lamarinka kafin aiwatar dashi"
"Kayi haquri"
"Ya wuce" ya fada a taqaice
"Yanzu daga ina kike?" Kame kame ta soma yi,don tun dazun suka fito gantali ita dasu
mima,yanzu haka suna cikin mota su suka rakota bashi haquri,ko hajiya bilkisu ma batasan
tazo ba,ganin ta rasa qwaqwqwaran abun fada guda daya ya dakatar da ita
"Is ok...yanzu ki wuce gida"
"To yaushe xakazo?,kwana biyu ma gaba daya ka daina zuwa ko cin abinci,mama nata
complain" ta fada cikin shagwaba
"Zanzo da zarar na samu dama"
"Can i call you anjima?" Ta sake tambaya,idanunsa ya lumshe kana ya bude,don maganar ta
soma isarsa
"Allah ya kaimu anjima" miqewa tayi ta masa sallama cikin salon nuna qauna sannan ta juya ta
fice daga gidan,ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji fitarta,saiya hada kayanshi gaba daya don
zaman gun har ya fita akanshi kuma.
Bacci ya samu yadanyi,qarfe hudu ya tashi,yayi alwala ya fice masallaci,daya dawo ya
shiga wanka ya shirya tsaf cikin dogayen kaya wanda bai fiya sakasu ba,ya dauki wayoyinshi
da maqullin motarsa ya fice,ya yiwa mai gadin sallama ya wuce.
Tafiyar mintuna qalilan ta sadashi da gidan anty usaina,suka gaisa sosai da mai gadin
qofar da yake shiga,saidai qofar ana gyaranta ne saboda gate din yana masa tauri bai buduwa
da sauri,tilas yayi rivers ba don son ranshi ba ya zagaya ta daya layin.
Idanunshi fes yana iya hangen qofar gidan daga qofar gidan anty usainar,a hankali ya dauke
kanshi yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,horn daya yayi aka bude masa don tuni ya
zagayo mai gadin,ya saka motar tashi yayi parking sannan ya kasheta ya fito.
Anty usainan ya tadda da yaran ta zaune cikin valcony din dake gefan matattakala hudun
da zata sadaka da babban falon gidan,assigment sukeyi,dukansu suka hada baki suna masa
sannu da zuwa cikin girmamawa ya amsa,har ta miqe zasu shiga ciki taga yana zare sau
cikinsa "Barni daga nan anty na zauna cikinsu nima,sati biyu kenan bamu hadu ba" da d'aya da d'aya
ya dinga bibiyar karatunsu,yammata masu kimanin shekara sha hudu sha biyar da sha
shida,sai namiji mai shekara sha uku,yaji dadin yadda yadda ya samu karatun nasu na tafiya
daidai,wansa daga qarshe ya sallamesu da kyautar dari biyar biyar suka shige cikin gida suna
murna,wajen ya rage daga shi sai anty usainar.
"ya jikin naka?"anty usainar ta tambayeshi bayan sun gama gaisawa,dubanta yayi
"Waye yace bani da lafiya?"gajeran murmushi ta saki
"kana tunanin zaka iya boyemin ne,tun zuwan da kayi cikin wancan satin nasan baka jin dadi"
"Don dai karkice na musa miki ne...amma da nace lafiyata qalau,kawai stress ne na wajen aiki"
kai ta kada kawai,tasan dama bazai taba yarda ba,baisan tsohon abu bane wannan a
wajenta,ta karanceshi ciki da bai
"Hakane....Allah ya taimaka to"
"Amin" ya amsa yana ciro wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo,nafisa ce,ya karanta ya
maida mata da thanks sannan ya maida wayar idonsa kan anty usainan
"Dama inason muyi wata magana ce da kai"
"Toh anty,Allah yasa ta samu"
"Eh to.....zancan nafisa,munyi magana da ita ta sanarmin kace rana ita yau kakesan suje su
sami alhj abba,amma saga bangarenka banji kace komai ba har yanzu,ya kamata fa anwar ka
maida hankalinka jikinka,da da yanzu ba daya bane,kullum shekaru qara yawa suke akan
mutum,baya ga haka ma ya kamata mu fita kunyar yarinyar nan da iyayenta" shuru yayi yana
saurarenra idanunsa na kallon carfet din da suke kai,har sai data kammala sannan ya dubeta
cikin nutsuwa da jeranta kalamai
"Anty,har yanzu banji nutsuwa da gamsuwar nafisa ta zama mata agareni ba,har yanzu ina
qoqari da tsarawa kaina yadda zan amshetq,bana son ayi abinda daga qarshe zai xama wani
batu na daban,ina matuqar ganin qimar mama da abbanta,ina ganin mubi komai a sannu har
zuwa sanda komai zai dai daita,zuciyata ta amshi abun dari bisa dari yadda ya dace"fuska anty
usaina ta canza,har cikin ranta tana jin anwar din zai aikata ba dai dai bane kawai
"Anwar,idan ka sauya ra'ayi ne kawai ka furta,har xuwa yaushe kakeson yarinyar tayita zaman
jiranka?,tun tana kara har takai ga tana takowa ta sameni da maganar,waishin ma idan bakayi
aure ba yanzu sai yaushe xakayi anwar?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da idanu
"Duka anty ba wannan maganar bace"
"To wacce ce gaya min?"
"Kamar yadda na gaya miki ne a baya,har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa da yadda da
soyayyar kowacce yarinya,da nafisa zata haqura dani da nafi kowa murna,saboda zanso mata
ta auri wanda yake sonta ba wanda takeso ba"
"Maganata ta tabbata kenan,kawai anwar ka fasa auren nafisa kakeson cewa,ka shirya butulci
wa mahaifanta" cikin bacin rai ta qarashe maganar
"Banason ranki ya baci anty,za'ayi duk yadda kikeso,zanje da kaina na samu kawu abdulkarim
na shaida musu,Allah yayi mana jagora" ajiyar zuciya ta sauke sannan tace amin Allah yasa ayi
a sa'a,ko kadan batason iyayen nafisa su kallesu amatsayin butulu marasa cika
alqawari,marasa kuma rama alkhairi da alkhairi,daga wannan magana ya miqe "Har zaka wuce?"
"Eh...ina da aiki da yawa kwana uku ban samu shiga company ba"
"To Allah ya taimaka....amm dama inason gaya maka,cikin satin nan nakeso na shiga katsina
mu gaisa dasu baba furai'ah,ya dace kaima ka ware lokaci kaje ku gaisa,don ba qaramin
jimawa kayi rabonka dasu,tun suna qorafin kayi kudi ka watsar dasu sai aike har sun haqura ma
sun daina" bawai zuwanne wajensu baya sonyi ba,katsinarce baya son shiga,shi duk wani abu
daya jibanci tuna mishi da ita baya qaunarsa
"Zanyi qoqari in sha Allah" tana zaune daga nan har ya isa inda ya aje motarsa tana kallonsa,ya
bude ya shiga ya tayar da ita yabar gidan.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ya bacewa ganinta,ta fada dogon tunani,abinda yake dojewa
dai yake nuna tsantsar qinsa shine ke wahalar dashi,lamarin da yake qaryatawa shike
dawainiya dashi,itakam a duniya kaf bataga matar data dace dashi irin shahida ba,har yau yaqu
furta nata meye sanadi?,meye dalilin rabuwarsu,har cikin zuciyarta tana qaunar yarinyar,ta zabi
gida kusa dasu ne don tana saka ran wataran ta dawo mishi da ita cikin rayuwarshi,tarihin
soyayyarsu,yadda tayi tambari ta kuma yi suna bai kyautu ace ta qare a haka a banza ba,ta
sani cewa ko yaqi ko yaso koya nuna koya boye shahidan wani bangare ce na rayuwarshi,ta
jima tsahon shekaru tana addu'a tare da fatan Allah ya shige mata gaba yasa taci galaba duk
sanda ta tasamma tunkarar lamarin,domin cire qiyayya daga zuciyar da ada take cike da
soyayya ba qanqanin abu bane,saidai a jikinta da xuciyarta duka tana jin lokaci yayi daya dace
ta tashi ta gwada tabuka wani abu,koda zaiyi kuka da ita gaba tana da tabbacin zaya gode
mata,duk da batasan meye yayi silar ruguxa wannan kyakkyawar alaqar da aka ginata cikin
fahimtar juna ba.
Cikin lokaci kadan ta soma jin cewa zuciyarta ta karbi canjin da tazo mata dashi,ba'a dauki
dogon lokaci ba uncle hisham yazo mata da upper ta daukan aiki a companyn *TRIPLE R
GEM* kamfanin dake sarrafa duwatsu masu daraja da tsada zuwa kayan ado da qawa na mata
,irinsu sarqoqi,dan kunnaye,zobuna,abun hannu,munduwa da sauransu,mallakin *RAYYAN* miji
ga *RUMANA DA RAIHANA* (DANGANTAKAR ZUCI).
Sun bata matsayin accountant na wajen gaba daya saboda yarda da amincin uncle hisham
da rayyan yayi yasa ya bashi cigiyar wanda zai riqa masa wannan matsayin,matsayin da aka
bata sai taji yayi mata girma,har taso tace ba zata amsa ba,uncle hisham ya zauna yayi mata
bayani da kyau ya kuma nuna mata Allah ne ya bata,fatanshi kada ta bashi kunya ta kumayi aiki
tuquru,tace in sha Allah.
Duk wani abu da ake baiwa sabon ma'aikaci mai matsayi irin nata sun bata,saidai taqi amsar
gida da mota da suke bayarwa,tace bata da ra'ayinsu,ganin haka sai suka qara mata kudi kan
wanda ya