Showing 105001 words to 108000 words out of 126208 words

Chapter 36 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

Advertisement

rai nason taso masa yana danneshi,ta yaya zai barta
ta koma aiki?,aikin da tun ranar daya ganta cikinsa bai sake samun nutsuwa ba sai daya
tabbatar ta daina zuwa ta sanadin aurenshi,randa yaga nuradden din cikin office dinta da qyar
ya samu ya saisaita kansa,ji ya dinga yi kaman hawan jininsa zai tashi,sannu sannu ya dinga
ambaton sunan Allah har ya samu zafin da yakeji ya sauka,yunwar da yakeji ta dawo masa
sabuwa fil,bashi da mafita illa slipper dinshi daya zira ya sauka zuwa qasan.

Karon farko da zauna kan dining din,ya jawo warmers din ya soma budewa daya bayan
daya,take qamshi ya cika wajen wanda ya qara qaimin yunwar tasa,tun kafin ya soma ci a ido
abincin yayi masa,sanda ya soma ci kuwa saiya samu kansa da lumshe idanunsa,dadin girkinta
ya ninka fiye da wanda ya sani a baya,a nutse yaci abincin,ya kuma yi qoshin daya manta
rabonshi da yayi irinsa,baibat abincinba sai daya diba wani yayi guzuri ya haura sama dashi.



Bayan ta idar da sallar asuba bata koma ba ta soma gyara dakinta,sannan ta fito falo,ga
zatonta zata dauki fulasan abincin kamar yadda ta saba kowanne lokaci amma saita tarar anci
fiye da rabin abincin,harara kwanukan abincin tayi kaman su suka mata laifi
"Dan rainin hankali,nina kwana ina baqinciki,shi kuma ashe zuwa yayi ya cika cikinsa,bacin
raina dadi ma kenan yake masa,bai taba cin abincina ba sai yau daya fuskanci a bacin rai nake
kenan,aikuwa bazan yadda ba nima" da wannan tunanin ta gama komai na gidan,ta kuma
shirya abincin safe ta jera yadda ta saba sannan ta shiga wanka.
Tara saura ta gama komai,ta shirya tsaf cikin laffaya data nade jikinta fes da ita,qafarta
sanye take da takalmi me tsinin dunduniya,ba qaramin kyau tayi ba,kana kallonta kasan
sabuwar amarya ce.

Tana tsaue bakin dining tana break don ko zama batasonyi bare ta makara taji takun takalmi

da alama ana saukowa ne daga sama,tasan shine don haka taqi daga kanta bare ta
dubeshi,daga saman step din ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,tana nufin fita kenan zatayi
da gaske?,a ina shahida ta sauyo hali ta koyi musu da kafiya?,bari ya zuba ido yaga iya gudun
ruwanta,dole ya nuna mata shine mijin itace matar,zata ga qarfin qwanji yau kuwa idan batayi
wasa ba.

Bai qara taku daya ba yana tsaye yana kallonta harta gama,ta ciro paper daga jakarta tayi
rubutu ta ninke ta aje anan sannan ta tattara jakarta ta zuge ta riqe a hannunta ta soma takawa
don ficewa.?*Alqawarin Allah*
39


"Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba
haka taci gaba da takawa.

A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace
meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata
ya bata umarni kai tsaye
"Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama
"Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?"
"Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma
na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata
shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun
nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat
jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma
qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai
bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby
"Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so"
abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba
hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata
saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace
wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata
yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci
"Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso
yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba
tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin
hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa "Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa
kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari
da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa
maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba
qafarta.

Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata
yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa
gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya
gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya
abinshi yayi shigewarsa wankansa.

Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi
ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin
zugi na ratsata.

Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka
da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin
yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya
sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta
lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da
sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya
tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun
azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma
gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata
irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa
masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da
Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace
mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai
saboda mugunta.

Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a
baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo
yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta
maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye.
Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma
fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta.

Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa
ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden
data ji din ba kadan bane.

A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a
kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a
qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin
zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a
hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata
da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara

"Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya
yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi
nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen
yake mata,gami da sauke numfashi "Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba"
"Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai
fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan
tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace
"Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala"
"Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya
sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?.

Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana
kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya.

Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da wata roba
dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso saitin qafar ya aje
robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere ya dora robar akai,bai kalleta
ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa
sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna
mata wurin,tun tana jin ciwo harya soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai
daga kai ya dubeta ba,lokaci lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko
sau daya taci sa'a basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya
fice dasu.

Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura qofar da
zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman dakin nasa,a bakin
qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa karo yana dawowa tana shirin
sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba yace "Ina zaki haka?"
"Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce
"Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na fuskanci
baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi
"Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage
"Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?"
"Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya soma
quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin rabeshi,qyaleta yayi
harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya cikin qirjinsa ya mata wani
kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro
tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana
kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba
bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin
gami da cewa

"Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda
yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata
alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a
bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta.
Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan jakar,ya
rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi
"Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi niyya yi
"Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi
"Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan kaso,bakinka
rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana tsaye cak yana kallonta
saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta
"Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata vata taba
zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a kunnesa,hakanan taji
kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta wani sashe daban
"Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar jakar aka sake
kira
"Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne daga
kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan aikinta
bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa
"Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya yanke
wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya soma lanqwasashi
"Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya watsashi cikin dan
qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta
"Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da aure ba?,ko
baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da amfani dashi ba" ya
qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran
"Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema
rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar ba?,me na
tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata shine kake
aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko yace wani abu
ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi ba,batasan me yake ji cikin
zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana da ikon maida bara bana daya dawo da
ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata
amfani da zahiri ne ba tare data binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai
gami da fidda qaramin murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai
tunzurata ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a
haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama dashi
"Donke baki damu da rayuwata ba saime?,akwai dubbai da suka damu da ita,don na taimakeki
ma na rabi rayuwar taki shine kike wani zaqalqalewa kina zaton ke watace a wajena?" Ido da
baki duka ta saka tana son tantance me yake cewa,daidai lokacin da qararrwar dake nuna
akwai baqi can falon qasa ta soma kadawa,saiya miqe kawai yana tabe mata baki ya fice ya
sauka qasa.

Daada ce ita da mubina da khadija,su sukayi waya dazu kan zasu rakota,tun bikin daada
bata koma ba umma tace saitayi sati uku,sai yanzu ta soma shirin komawa,zuwanshi gidan
wajen daada hira babu adadi,ta fuskanci abubuwa da dama game da zamansu ba tare daya
gaya mata ba,da batayi niyyar zuwa gidan ba sam,amma taga ya kamata ta danyi gyara ko
yaya ne kafin ta wuce karta tafi tabar baya da qura,don tasan umman shahidan koda wasa ba
zata taba taka gidan shahida a yanzu ba,donko hira ake bata sanya baki,yaji qishin qishin din
zata zo din yau dalili kenan dayasa ya tsare shahidan a sama don kar daada ta ramfo
komai,don hausawa sunce babba babba ne,abinda zai gano ko kahau bishiyar rimi ba zaka
hangoshi ba.

Shi ya tarbesu daada tahau baza ido
"Ina ita waccar ja'irar,kaine kake tarar baqin ita kuma tana me?" Murmushi ya saki
"A'ah a'ah,kawai yaune na karbata,tana sama batajin dadi ne,ta samu targade a qafarta"
"To ce mata ta sauko,don tayi targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta nade?,oh
ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye"
"Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin tsokana,da
ido ta bishi baki sake
"Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan yace
"Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin zuciyarta tanajin
sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika da fata da addu'ar Allah yasa
itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta watsa musu qasa a ido,mubina yasa
ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri
muqulli don zuwa ya sama musu abinci
"Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo"
"Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in fito ya
maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya fita,tace saidai yahau
sama ya sauko mata da shahida
"Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba"
"Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki nahau,tunda goya
mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba daadan tahau saman,inda
mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo.

Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin zuwan
daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa anwar magana ya
barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,bawani
sauyi data gani tattare da shahidan na mace me aure,saita tabe baki,zata fara magana
shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson fashewa da kuka
"Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya ganni,sannan
kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login