Showing 108001 words to 111000 words out of 126208 words

Chapter 37 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

Advertisement

yace waina gama aiki,daxun
nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina daina amfani dashi" rashin sani yafi
dare duhu,wani kallo daadan ke mata akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace "Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da aure,daga

ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba"
"Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da shahida
"Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama akwai
magana a bakinta
"Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta tsaye,take
qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta rarumeshi,bai taba tunanin
tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace
"Daada ai...."
"Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da wuyanta,idan
tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi sallallahu alaihi wasallam"
ta debo salati tana tafa hannuwa

_afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai ciki*Alqawarin Allah*
40


"Ni habiba naga abinda ya isheni.....rahama?!" Tayi kiranta da sunanta na ainihi,daga ita har
anwar din sai sukayi tsuru tsuru suna kallon daada yadda ta dauki abun,kunya da daurewar kai
duk suka cikasu
"Kinason ki gama lafiya kuwa?,kinsan tsinuwar mala'iku kuwa akanki?,so kike ki shiga wuta da
qafafunki?,to wallahi kishiga taitayinki karki jawowa kanki masifa ki jawo mana,rahama!" Ta
sake kiran nata cikin kambama abun,yadda daadan ke magana da yadda shahida ta soma turo
baki fuska a hade cikin bacin rai saiya so baiwa anwar dariya,shi tuni a nasa shekarun ya
fahimci tayine tana sane donta tsorata shahidan,ta kuma sake kawo gyara a zamansun gaba
daya
"Yanzu daada fisabilillahi waya gaya miki wannan maganar?,shi yace miki haka?ko kuwa ni?"
Daquwa ta watsa mata
"Kinci gidanku,don gyatumarki a tsufana ni akwai abinda za'a boyemin?,to wallahi wallahi tun
muna shaida juna ni dake ki gyara duk abinda na gane da wanda ma ban gane ba,duka kin fini
sani ai basai nayi filla filla ba,kin ganni nan bana daukar sakarci,ba abu bane me wahala na miki
dukan tsiya cikin gidan nan kibar ganin kina da igiya a kanki,girma kuwa ban ganshi ba bare ya
hanani dakarki,aiki kuma ba zakiyishi ba haihata haihata...."
"A'ah daada....ba'ace haihata haihata ba" anwar ya dakatar da daada yana boye dariyarsa
wadda shahidan ta fuskanci hakan,ta sake qulewa sosai,wato ita tako ina bata da nasara,bata
da rinjaye kenan?
"Zatayi aiki idan tanaso....amma ba bisa qarqashin kowa ba sai qarqashina,zatayi aiki a nawa
companyn kuma a office dina" ya qarashe zancan yana duban daada ba tare daya dubi shahida
ba,don yasan kai tsaye cewa zatayi ba zatayi ba,amma ga mamakinsa sai yaji ta amsa da
"Na amince zanyi" ta amsa masa idanunta qyar a kansa,tasan yayine don ya qureta yayi da
manufa,ita kuwa tacu damarar takura masa itama tunda har ya bullo ta wannan hanyar,sai daya
gama karantarta ta qwayar idanunta sannan ya girgixa kai
"Well,hakan yayi,daga yau daga yanzu ma na daukeki aiki,za'a dinga kuma baki salary kamar
na kowanne ma'aikaci dai dai da matsayinka,salary dinki shine salary na farko dayafi na

kowanne ma'aikaci yawa duba da matakin aikin dana baki" kaita juyar tana hadiyar bacin
ranta,cikin ranta ba haka taso ba
"Shikenan ma,shine daidai,kaga kuna tare ko yaushe,tuwona maina,yamafi tsari" daada ta fada
tana ware hannaye,daga haka daadan ta miqe bayan ta sake kwakkwafar shahidan,ba yadda
anwar baiyi ta zauna ba tace sam,daqyar shahida ta iyayi mata a sauka lafiya,ya fita rakata.

Cikin kwanakin hakanan shahidan naji na gani ta zauna saman nashi,saidai kwana uku rak
tayi wanda ta jita kaman akan wuta take,a falo duka tayi xamanta,sai shima ya shareta kawai ya
shiga sabgarsa,randa taji dama dama a qafarta ranar ta sake tarkatawa ta koma dakinta.




A hankali take takowa zuwa bakin dining din donta samu tadan dumama cikinta,bayan ta
gama shirinta tsaf kamar yadda ta saba duk lokacin da zata je office,madaidaiciyar kwalliya tayi
wadda ta qawatar da ita matuqa,ta sake fidda kyawunta,kallo daya xaka mata kasan macace
mai aji tako ina,wannan itace ranar farko da zata soma zuwa office din anwar da sunan
ma'aikaciya.

Shi dinma yana tsaye daura da teburin yana kurbar tea gami da jefa soyayyen chips a
bakinsa,kacokam idanunsa nakan wata takarda dake saman teburin kusa da farantin chips
dinsa,wanda ke dauke da zanen taswirar wani gini da gwamnati ta basu kwangilarsa da xasu
soma yinsa cikin satin.
Takun daya soma ji shi yaja hankalinsa,har yakai kofin bakinsa ya janye ba tare daya kurbi
tea din ba,daga sama zuwa qasa ya qarewa kwalliyar tata kallo cikin taqaitattun daqiqa ya
kauda kanshi yaci gaba da shan tea dinsa.

Qarasowa tayi itama ta fara hada nata ba tare data dubeshi ba tace
"Gd mrng" fuska a tsuke
"Mrng" ya amsa mata a taqaice shima yana juya fasalin takardarsa ba tare daya dubeta ba,wani
abu ke tsunkulin zuciyarsa,shigarta sai yaga ta bayyana ado da yawa,duk da ko ina a jikinta
rufe yakr ruf ba wani abu nata daya bayyana,amma sai yake ganin kamar kallonta za'a yita yi
idan suka je,dana sanin cewa tayi aiki a kamfaninsa ya kamashi,inama ace cewa kawai yayi ba
zatayi aikin ba gaba daya,gashi ya ruga ya furta babu damar ya canza,yin hakan zai nuna
qarantarsa ne kawai.

Sai daya gama tas ya dire cup din yana cewa
"Wannan shigar batayi ba,kije ki canza wata ki sameni a mota,idan kuma kika makara to cikin
albashinki" daga haka ya juya ya soma takawa,ya dauki handkherchief dinsa da muqullin mota
dake aje saman daya daga cikin kujerun falon,ta bishi da kallo galala baki sake harya fice,sai
daya bacewa ganinta sannan ta dauke idanunta tana lumshe ido,takaici nason kamata amma
tana daurewa.

Yana daga xaune cikin motar,ta baqaqen gilasan da batasan yana kallonta ba ya xuba mata
ido,karo na biyu kenan daya sake maidata ta sauya shiga amma shi har yau baiga wani abu na
kyanta daya buya ba,bayyananniyar ajiyar zuciya ya sauke,tunda can yasan cewa haka take
halittarta ce,duk kayan da zata saka suna mata kyau gami da dacewa da ita komai rashin kyau
ko tsadarsa,agogon dake daura a hannunsa ya kalla,dole ya haqura ya qyaleta su tafi
hakanan,zuwa yanxu ya cinye sauran lokacin da suke dashi.

Tana zuwa gidan baya ta shiga,baice mata komai ba yaja motar suka fice daga gidan,suna
dab da ginin kamfanin ya tsaida motar,ba tare daya juyo ya dubeta ba yace
"Dawo gaba" jim tayi sai kuma ta fito don batason ma ta yawaita magana dashi.

Tun daga harabar kamfanin ta karanci yadda suke ganin qima daraja da
mutuncinsa,wannan karon baiyi parking inda kowa yake ba,sai dayaje gaban ginin sosai sannan
ya tsaida motar suka fito,basu shiga ta gaban ginin ba saita bayanshi.

Kallon office din babu abinda ya tuna mata dashi face nata office din,kusan tsari yanayi da
kuma zubinsa kamar nata office din,take kewarsa ta kamata,ta lumshe idanunta sanda take
zaune kan cushion din office din tana jira ya kaita nata ofishin.

Abinda ya bata haushi da mamaki shine bai wuce yadda taga yayi zamansa kan tashi
kujerar ba ya shiga ayyukan daya taras kan teburinsa ba,yayin da take zaune shuru bata wani
aiki.

Ganin sun cinye awanni biyu cur a haka ya sanyata gyara zama sannan ta dubeshi
"Ban gane manufar ajeni cikin office dinka ba,ka mantane aiki nazo yi?" Sai sannan ya daga kai
ya dubeta,saiya maida kan cumputer dinsa yana cewa
"Na fiki sanin ai aiki kikazo yi,gaggawar me kike?,zakiga aikin naki ai" daga haka ba wanda ya
sake tankawa wani,saidai sau uku tana daga kai sai taga kaman kallonta yake,daga kanta yasa
ya kauda nashi kan,saidai har yanxu bata kamashi dumu dumu ba shi yasa bata tabbatarwa da
ranta hakanne ba.
Minti talatin bayan nan yace
"Hadamin coffee,ki bude can ki ciromin cake guda uku" duk yayi maganar ne ba tare daya
dubeta ba,karon farko daya fara bata umarni irin haka tunda sukayi aure,saita miqe din tayi
yadda yace ta dawo ta zauna.

Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa saman table
din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci gaba da aikinsa,awa
biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya cikin nuna qosawa,ta sauke
numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje "Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa tayi ta
juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai

"Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a
zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido
"Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta sannan
ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna
"Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa ya daga
mata
"Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa aikin,wannan
aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa albashinma daya fi na kowanne
ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa tana kallonshi yana fidda qaramin
murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare
data tanka masa ba ta nufi qofar fita.

Gabanta yasha ya tsate hanya
"Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam"
"Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa shima,don
baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana ciki
"Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya juya zuwa
wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar yayi yana
dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon satin xuwa
yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan me kuma zata ce
masa ba,me yayi saura tsakaninsu?.

Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta kasa jurewa
da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani lokaci da ita miman ke
shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole tabi zabin ranta ta soma neman
khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta
gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa
kishi ya rufe mata ido haka ta tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi
ba?,bayan tasan cewa ka ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban
kuskuren data tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta
samu soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma ruwa,sai
taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi yaqi ta samawa
zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga baya su dora daga inda
suka tsaya.

Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta yafa
qaramin mayafi saman kanta ta fito.

Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana jiranta garta
kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta sani amma ta nuna
kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata shine dai dai
"Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace
"Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace

"Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don Allah
momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana miqewa
"Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice fa kuma
kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta bude qofar dakin
nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya,lallai
aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan iyayenta,wanda sune tsaninta na
nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam.

Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta shiga
bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah kan abun sallarsa
dake cikin office din.

Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude nashi ya
wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau halinshi nacin abinci
da hannu dai yana nan.

Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje daya,saidai sam taqi
zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi
kamfanin datayi yafi sau shurin masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta
gwammace tayita zaman gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi
daya kusa da juna sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da
har yau yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa
da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba.





Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan.

,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman bazai iya
hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina fes yake ba alamun
datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya,amma saika rantse ba
wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake fita kadan kadan,ya janye idanunshi
kenan yana shirin miqewa yaganta tana fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran
hannu,wadda tafitar da shape dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das
cikakku,zuwa mazaunanta da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake
daure waje daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da
alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma ta maze
taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace
"Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda kunnuwansa
dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da sha'awar ya takaleta,kwana
biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din ba,saboda haka ya hade rai qyam

sannan yace
"Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace a
qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya gefanshi,saiya daga
kai yana kallonta
"Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka saita
shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da qare mata
kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke janshi,idanu ta zaro data
fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen abinda ya fargar dashi cewa kallonshi
ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada rai
"Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa
gane me yake cewa?
"Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta
"Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata
"Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace
"tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya roqa" ta
gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace masa komai ba ta
wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da yaji wani abu yana ratsashi tun
daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah,baqon
feelings yakeji sosai wanda har yaso danne gajiyar da yakeji.

Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan
gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi controlling kansa
sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon tasoma takawa don barin
wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa "Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune
"Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da gardama data
soma masa ya zame mata jiki
"Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama ya
amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita
"Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa ciki
ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya bita yadda
mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya sauke bayan ta
bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata baya.n rayuwa_*Alqawarin
Allah*
41

_ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da sababbin
ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan da ixinin
ubangiji_

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU

Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana neman hanyar
wucewa
"Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa tayi
cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya
"Eh,gaskiya bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login